Showing 1 words to 3000 words out of 11539 words
Chapter 1 - Auren Dole Book Compelet Yar Mutan Dikkawa
[1/10, 11:05 AM] Nordin: *JIRWAYE....*
*DAGA ALK'ALIMIN NABEELA DIKKO*
*AUREN DOLE!*
_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM..._
*Shimfid'a:Da farko dai Aure shi ne Alak'ar zaman tare tsakanin namiji da mace,A bisa yardar
juna da Amincewar Dangi,Ta hanyar cika wasu ka'idoji,Na Al'ada da Addini.*
*Shi kuma Auren Dole:Shi ne tilasta yaro ko yarinya auren Wanda kowa acikinsu baya so,ko
kuma baya kauna mafi yawa iyaye da kakanni ne ke tilasta shi."*
*SHAFI NA D'AYA*
"Zaune take a gaban kakanta, mallam Buba mak'eri,Banda k'arajin kuka ba abinda
takeyi!"
"A fusace mallam Buba,Ya ce "Kinji dai na gaya maki...Wato ke gaki gagarau Ma'u!"Ni zan
gindiya sharad'i kice ki shure ki wuce!"Saboda kin raina ni,Ke da muguwar uwarki!"To daga
ubanki!Har uwar taki nafi karfinsu!"Aure ba fashi!Ko da ki amsa ki yarda kiyi Auren soyayya ko
kuma ki karbe shi a matsayin *AUREN DOLE*"
"Cike da firgici!Ta dago kanta!Tana kallon Baba mallam(Kakanta)Hawaye ke zuba a idonta
kamar an bud'a famfo!"
"Rik'e kafarsa tayi tace "Dan Allah kaka kayi min rai!Wallahi na tsani tsohon nan yafa tsofewa
Babana!"Ka taimake ni!Ka had'ani da wani Kaka....!"
"Marin da Kaka ya watsawa Ma'u ne ya katse maganarta..."Tasbahar da ke hannunsa ya dinga
zuba mata ta ko'ina!"Kururuwa!tah ta fito da ilahirin jama'ar gidan mai d'auke da
lungage..."Suna kallon Ma'u da ke kuka!Babu halin cetontah!"Saboda gudun b'acin ran Kaka."
"Ta da muryarsa yayi sosai!"Ya ce, Yoo....Duk gidan nan akwai mai yimin musu sai ke!Ma'u to
kinci gidanku kin qara tunzura ni nadawo da ranar aurenki kusa,idan yaso ki mutu agidan
Alh.Kalle nafi farin cikin hakan da in barki ki auri shashashan yaron nan da kike so Kamalu!"Me
yake da shi!me ya ajiye ke in kinsan asalin talaucin su baki kaunar ki aure shi!Saboda talauci n
su na gadi ne!A jinin su yake..!"
"Ma'u tashi tayi cikin kunar rai!Ta nufi sashen su jikin Innarta ta fad'a tana rusa kuka!"Kamar
ranta zai fitaa!"
"Kaka ahasale ya bar kofar dakinsa da ke gabas din gidan...butar da yasamu ajiye a hanyar fita
waje,yayi shuri da ita,yace munafukan banza!To ku koma tsayin me kukeyi anan!?"Yana hararar
sarakunan nasa da suka fito gulma.."Sum-sum kowacce ta fice sashenta domin sun San kaka
sarai da masifa!!!"
"Lami ta kalli 'yartah rai!Babu dad'i!"Ta ce Kiyi hak'uri Asma'u ki yarda da zab'in Baba mallam
shi ne mafita agare mu,kinsani sarai ni ko Babanki bamu isa muja da shi baah!"
"Duk gidan nan ba mai karya dokarsa!Kar ki bari zuciyarki ta rud'eki akan ki karyata,Ki barwa
Allah komai!Kin sani sarai, " *AUREN DOLE* A gidan nan Ba akanki aka fara ba!Bare ak'are
kanki!"
"Asma'u ta tashi zaune,Ta kalli Inna tare da kama hannayenta,Ta ce"Yanzu Inna kuna kallo
Baba mallam zaiyi min *AUREN DOLE!?"* Saboda yana son cimma wata manufa tasa!"Tare da
kwad'ayin Abin Duniya!"
"Wallahi na tsani!Alh.kalle,Inna bana sonsa,ba zan iya rayuwa da shi ba!Yafa tsufa!Yaransa duk
sun girmeni!"Aure na zaiyi kawai, saboda budurwar zuciya!Da son zuciya!"Shi ne ya zubawa
kaka kud'i domin yabashi Ni,A dole!"Shin meye haka!Addini ko Al'ada!!?"Na rasa amfanin
wannan baqin aure da ake mana agidan nan......Wani Sabon kuka!Asma'u ta ke rerawa...."Inna
Lami ma hawayen tausayi 'Yarta ke zuba a kyakkyawar fuskarta,Tare da cigaba da rarrashin
Asma'u,da ido yayima luhu-luhu saboda kukaah!!!!"
[1/10, 11:05 AM] Nordin: *SHAFI NA BIYU*
*ALK'ALAMIN NABEELA DIKKO*
"A cikin jihar kebbi akwai wata qaramar hukumar mulki da a ke kira Argungu,"Babban gari
ne,Mai cike Al'umma,Ga su da manyan yan boko maza da mata,kuma ma'aikatan gwamnati ne
a kowanne fanni,Bugu da qari Albarkokin Allah sun yawaita A garin,Domin Allah ya albarkace
su da manyan rafi masu dauke da Kifaye naji, na gani na fad'a,kuma mafi yawa daga cikin su
asalin su D'aya ne akwai Kabawa,Lekayawa,Fulani,Zabarmawa da kuma gobirawa, noman
shinkafa,da kayan lambu ne,da na masarufi sune Ayyukan su,Mutane ne masu rik'e da Al'ada
ko kuma sana'ar gidan su ta gado!"Argungu gari ne na kabawan Asali wad'anda sukayi fice ciki
da wajen Nigeria."Akwai cigaba mai yawa da suka samu,sunyi suna dalilin bikin kafun
kifi(Fishing Festival) da akeyi aduk k'arshen shekara."Acikin wannan gari akwai wata unguwa da
ake kira Gobirawa,yawancin mazauna unguwar ada caan baya zabarmawa ne,Daga baya
hausawa suka yawaita acikinta."Gidan Mallam Aminu yana daga cikin unguwar layi na
uku,Gabas da masallaci Sheik Bashir."Da ke Unguwar."
"Mallam Aminu,mutumen kirki ne,Wankan tarwada mai tsayi da jiki,yana cikar zati da haiba
daka ganshi kaga irin malamman nan masu Da'awa,Sannan kuma ya fito daga gidan sarkin
mallaman garin,Duk gidan su malammai ne kuma shi ne magajin gidan, ya kasance babban
malamin da akeji da shi a jihar kebbi da kewayenta."Allah ya albarkace shi da samun ilimi mai
yawa,ya na ba mutane da yawa karatun addini."Yana da mata d'aya malama juwairiyya itama
tana da islamiyya ta kanta,mace ce mai kyau,ga kirki abin burgewa tana da ilimin addini,mutunci
da sanin girman Dan Adam,Sai yaran su akwai Muhammad Yaseer da yaseera sai qaramin
Abdul raheem."Yaran su sun taso acikin rayuwa mai kyau wato ilimin addini da na zamani."Tare
da tarbiyya."Muhammad Yaseer yana karatun aikin likita,A jami'ar Danfodio Sokoto."Sai
Yaseera da ta kammala karatun sakandaren mata a wannan shekarar,Abdul kuwa zai tafi aji
d'aya a sakandare."Dukkan yaran kan su a had'e yake suna da zurfin ilimi mai yawa,kowannen
su ya haddace Alqur'ani mai girma tare da wad'an su littafan sa ni,"Suna da kyau matuka,ga
biyayyah da kamun kai da nutsuwa."
"Kamar kullum matukar mai gidan yana gari ko baya nan hakan ke faruwa agidan,wato karatu
tun kafin sallah Asuba har zuwa wayewar gari, Mallam ne acikin iyalansa,Suna ta karatu ya
fadiwa matarsa da yayansa,daga bisani Addu'a sukayi kowa ya shafa,Daga nan suka cigaba da
fira kowa na fadin ra'ayinsa ko buqatun su da abinda suke so."Kasancewar Yaseera da Abdul
ne kawai agida domin yaseer yana makaranta."
"Mallam ya tambaya Abdul na tambayeka ba ka bani amsa ba!?"
"Abdul ya ce"Abbu daman ni inason idan nagama karatuna na sakandare ka kaini jami'ar nan ta
madina ina so nayi karatun likitan musulunci."
"Dariya mallam yayi tare da miqawa Abdul hannu sukayi musabaha yace masha Allah,
"Allah ya cika maka burin ka Abdul raheem,Amma kasan tufin Asirin Allah ne,muke da shi idan
Allah ya kaddari hakan zanji dadi Allah yaqara tufa mana Asiri."
"Ameen ya rabbi,Umma ta itada Yaseeara suna dariyar Abdul."
"Naga bakin ki na motsi ke kuwa me kike buqata?.Umma ta tambayi yaseera tana murmushi."
"Abbu ni yaushe zan tafi makanta!?"Yaseera ta tambaya."
"Amsa ya bata na gaya maki makaranta ba yanzu ba!Ki k'ara hakuri akwai tunanin da nikeyi
akai!"Inji Abbu.
"Yanayin yaseera ya sauya!Domin tana son cigaba da karatun ta wataqila Abby bazai barta
ba!Tace acikin zuciyarta!"A cewa fili cewa tayi to Abbu,Nagode." tashi tayi ta nufi madafar
Abinci domin hada abin Karin safe."
"Abdul ma yasan aikin falon Abbu yaje ya share tare da harabar gidan,sannan ya fara wanke
motar Abbu da yake yau Assabar ba makaranta sai goma suje islamiyya su dawo sha biyu,su
koma karfe biyu,su komo shidda na yamma."
"Abbu ya kalli Umma yace"Juwairiyya ina ganin kamar lokaci yayi da zan fadawa yaseera mijin
da na zaba mata,saboda naga tana son karatu ni kuma sai anyi auren su nikeson ta tafi
makaranta tana gidan mijinta,ba wai saboda na raina kamun kanta ba!"Wannan shi ne ra'ayi na
amma me kike ganin ya race!?"
"Umma Ta numfasa tace Mallam nima,In bayanka gwara kawai tayi karatunta bayan auren,sai
dai wani hanzari ba gudu ba!"Ya kamata tasan da maganar Aurenta da Najibullah shi yafi
cancanta."
"Hakane In sha Allah an juma da dare zan sanarda ita!"Inji Abbu."
"To Allah ya yarda yasa mudace saboda kowacce uwa tana alfahari da samun suruki kamar n
Najibullah...Umma tace tana kokarin tashi,Bari naje na duba me ake hada mana na kari,Abbu
yace to kuyi himma Ku gama Ina son nafita yanzun nan."
"In sha Allah,mallam yanzu za'a gama.."Umma tace ta nufi hanyar madafa."
*GIDAN MAK'ERA*
"Babban gida ne,Mai dauke da lungage da dama,Mallam Abubakar wanda akafi sani da (Malam
Buba)shi ne shugaba agidan,Yana da mata biyu Inna Karime wato uwar gidansa wacce ta rasu
shekarun baya!tanada 'ya'ya tara maza biyar,Umar,Nasiru,Aliyu,Badaru da sani sai
mata,lubabatu,sahura,sai Mariya da sakina dukkan sunyi aure har da yaran su wasu kuma
sunada jikoki,Sai matarsa ta biyu Amina wacce suke kira da (Anna)Da dadewa suka rabu da ita
akan masifar sa,yanzu hakan shi kadai yake rayuwa sai halinsa,Anna tana da 'ya'ya
shidda,Tare da Malam Buba,Mata biyar,Zainab,Ruqayya,Hassana da usaina,Aysha,sai namiji
d'aya kuma shine babba acikin su wato Yusuf Mahaifin Asma'u."Tunda Anna tabar gidan
malam tayi aure a kauyen felande yanzu hakan scan take rayuwa da yaranta biyu maza da ta
samu Idirisu da mustafa."
"Dukkan gidan kowa na tsoron Baba mallam,Saboda mutum ne,mai akida da dokoki,Shi ke
hada aure shi ke saki harkar gargajia ta yalwatu arayuwarsa Duk yaransa maza agidan suke
zaune da iyalan su kowa da nashi lungu."
"Gidan mallam Buba,Babban gida ne,Wanda 'ya'yansa da jikoki har tantab'a kunne ke rayuwa
acikin gidan,Sana'ar gidan tun kaka da kakanni ita ce Kira, kamar
irinsu(Wuk'a,Adda,b'ota,gatari,da kwasa,tsinke da sauran su,)Shiyasa akafi sanin gidan da
gidan mak'era."Suna bayarda taimakon wuta hakan da sauransu."
"Duk 'yammatan gidan da sun tasa mallam Buba ke zab'a masu miji,suyi aure,tun kan diyansa
mata da maza har izuwa kan jikoki,"Gulma da hassada ta yawaita acikin gidan saboda kowa
naji da kansa."Ba komai bane yakawo haka saboda bawani ilimi ne da su ba bare matansu da
Baba mallam ke nemo musu."
"Lungun yusuf,shi ne daban agidan saboda yasa mu mata mai kirki,Wato sadiya (Lami)yar
gidan limin,Haka yaranta uku Asma'u,Sauda,da Baraka,sunada tarbiya sosai."
"Duk gidan suna jin haushin lami wacce suke kira da uwar mata!Wai batada d'a namiji!Sun
tsaneta bata jin sanyi kowa agidan sai Baba mallam domin shi ba ruwan shi da bambanci,Duk
Wanda ya taka dokarsa takashi yake! ,Kaf mazan gidan,kyashi da shin yusuf Saboda shi kadai
ne namiji dakin su,sai qannansa mata da yake taimakawa kuma suna masa biyayya, Akai kai
suna zuwa garin da Anna ke aure su dubata tare da mata sha tara na arziki,Su Asma'u suna
son kannen babansu domin sune masu kaunar maman su,komaina yusuf shi kadai yake yinsa
sai qannan sa mata,shiyasa aka fitarda shi daban agidan haka matarsa lami batada shaqat
acikin matan saurinta(facaloli)shiyasa suke hade mata kai,Kullum cikin tuggu gulma da shirya
mata munafunci sukeyi agidan,Mijinta Yusuf ko duk acikin yayan malam babu yafisu tufin
asiri,Shiyasa yake sakewa Baba mallam kudi,shi kuma yana sonsa da diyansa sosai."Kuma
wataran yana auda kai!A al'amuran su saboda akwai kwadayi da son abin duniya,Abu daya ya
hadasu nacewar Yusuf yayi akan sai yaransa sunyi karatun boko,Wanda al'adar gidan Arabic
kawai ake,Asma'u kawai ce tauraruwar da tayi nasarar gama sakandare,daga kanta mallam
yayi rantsuwa ba Wanda zaiyi boko sai bayan ransa! shiyasa mallam ya tilasta mata aure
yanzu,domin ya zaba mata miji mai arziki."Duk gidan sunji bakin cikin auren da Ma'u
zatayi."Amma agefenta ita da Iyayenta baso sukeyi ba!Hakuri kawai zasuyi saboda gudun
zuciya da masifar Baba mallam,A ganin Yusuf ya karya dokar Mahaifinsa Asma'u tayi karatun
boko,yanzu kuma taya zai karya auren hadin da za'ayi mata,Saboda koshi din dan yayi dace da
tagari ne,Amma yana bakin cikin Asma'un sa yarinya mai ladabi da biyayya mai kyau da ilimi ta
auri jahili kamar Alh.kalle,Wanda aqallah zai girme masa,Gashi da mata har uku da yaran da shi
kanshi bazai san adadin su."
"Cikin sati d'aya Asma'u duk ta rame!tayi baqi damuwa ce,A zuciyarta abubuwa da dama take
ayyanawa aranta!Ko ta gudu tabar gidan...kuma tana tausayin rayuwarta da ta iyayenta!"Domin
kuwa barin gida babbar illa ce ga rayuwar 'ya macce."
"Ta rasa ya zatayi an rabata da Wanda takeso matashi dai-dai aurenta!"Za'a yi mata *AUREN
DOLE* da sa'an mahaifinta!"Kuma babu Wanda taga alamar zai takawa Baba mallam burki!"
"Duk mutunci da tarbiyar Asma'u ta dauki aniyar ajiye su gefe domin idan Alh.kalle yazo
gidan tatas take masa,Amma dariya yake mata ko tausayinta bayaji aganin kurciya ce,ke
damun ma'u."
"Ana hakan har akasa ma'u ruwa saura sati d'aya ayi aurenta Alh.kalle an kawo kayan lefe
akwati biyu,Wanda shi aganin sa ya nuna bajinta...haka agidan sai nuna baqin ciki sukeyi tare
da kyamar su Asma'u."
"Gidan Gwaggo Hassana kanwar Yusuf,Asma'u ta tafi abinta,Rarrashinta gwaggo,keyi...Domin
ta hakura da zabin mahaifinsu,Suma haka akayi musu auren gashi har yanzu sun zauna lafiya
harda yara."
"Shirye shiryen aure akeyi ta kowanne fanni Alh.Kalle ya gyare gida an fente ko ina,Matansa sai
dariyarsa sukeyi suna kiransa da mijin yarinya."
[1/10, 11:05 AM] Nordin: *SHAFI NA UKU*
*ALK'ALAMIN NABEELA DIKKO*
*BABI NA BIYU*
*GIDAN MALLAM AMINU*
"Bayan sallar isha,Mallam ne zaune acikin qayataccen falon sa mai kyau da tsari,da yake yana
da tufin asiri,yana da shaguna magungunan musulunci,ga makarantu sannan yana aikin
gwamna gidan marayu."Shiyasa yake da tufin asiri dai-dai gwargwadou."Fira yakeyi shi da
matarsa,Suna kallon wa'azin sheik Daurawa,A sunnah t.v, daga bisani umurni ya bata da takira
masa yaseera."
"A dakinta ta sameta tana karatun Alqur'ani mai girma."
"Bayan ta kai aya,juyowa tayi ta kalli ummanta tare da gaita."
"Umma ta ansa sannan tace"Idan kin gama Abbunku yana kiranki."
"Yaseera tace"yawwa Umma daman nagama kuma yunwa nikeji abinci zanci muje!"
"Tare suka jira ita da ummata sai da suka kai kofar falon yaseera ta dawo baya Umma ta fara
Shiga sannan yaseera ta biyo bayanta,aqasan lallausan kafet din,ta zauna dai dai kafafuwan
Abbu tare da gaida shi."
"Umma ko agefensa tayi mazauni saman kujerar nan ta zaman mutim uku,"
"Amsa gaisuwar yayi,fuskarsa asake."
"Sai dai yaseera jikinta yayi sanyi!"Duk gabban jikinta rawa ya ke saboda wata fargaba da taji ta
ziyarci gangar jikinta."
"Gyaran muryar Abbu,ya dawo da ita hankalinta.."
"Ya ce, ''Yaseera dazu naji kinyi magana akan kina son ki koma makaranta ko?"
"Eh,Abbu tace da sauri!tare da ajiyar zuciya."
"Ya ce,Masha Allah."Zaki tafi makaranta amma da sharad'i d'aya...sai nayi miki aure,Idan mijinki
ya amince sai kitafi kina a matsayin kamilar macce,Hankali yafi kwanciya kina gidanki kina
karatu saboda ina tsoron wannan zamani mai cike da abubuwan tashin hankali da al ajabi."Na
sanki da hankali da nutsuwa kuma ina da kamun kai,Amma ita rayuwar nan da kike gani komai
yana iya canjawa ko dole,ko ta wuya ko kuma ta dadi!"
"Dan haka nayi tunanin zab'a maki miji nagari!Wanda zai iya riqeki da gaskiya da Amana wato
Najibullah Dan gidan Alaramma Usman..."
"Tunda Abbu ya ambaci kalmar aure yaseera ta sadda kanta aqasa zuciyarta nayi mata
tafarfasa!Domin sam batasa aure agabanta yanzu ba!Karatu takeso shiyasa ba ta kula duk
wanda zaice yana sonta,kwallah!ke kokarin gangaro akan lafiyayyar fuskarta mai kyau
kallo,kokarin hadiye kukan take!"Sai taji Abbu na cewa..."
"Nasan zakiji maganar kamar a mafarki!To gaske ne,Tun kina makaranta mukayi zancen
auranku da najibullah,ni da mahaifinsa,kin sani sarai mu abokan juna ne duk wa'Azi tare muke
zuwa,Alfarma ya nema gareni ni kuma na amince saboda nasan irin tarbiyar da na baki
Yaseera."
"Sannan Najib yaro ne mai zirfin ilimin addini da na zamani,shi kan shi Alaramma ne,yana da
hakuri,ga shi ya san girman manya,yana da mutunci,Hakika na tabbata rayuwarki zata inganta
agidansa,yana da abinda zai ciyarda ke yayi miki sutura sannan ya kula da lafiyarki dan kuwa
yana aikinsa da 'yan Sana'oi,sannan zai cigaba da baki ilimi har karsheb rayuwarki."
"Yanzu hakan ya tafi madina yayi wani kwas,na wata shidda,tun kina makaranta,in sha Allah
munasan ran zai dawowarsa akarshen watan nan na muharram sai kuka juna sannan ayi
buki,bayan nan idan yabarki kiyi karatun idan kuwa bai barki ba sai ki hakura!"
"A karshe ina rokon ki alfarma yaseera idan har zabin da nayi maki baki gamsu da shi ba!Kina
da damar zabin wnda kike so kike ra'ayi domin *AUREN DOLE* ba aure bane matukar matsaloli
zasu dinga kunno kai!"Ni dai amatsayina na mshaifinki kinga ya dace in san waye zanba
aurenki,"Kuma hakkina ne nazaba maki miji nagari mai nagarta,Wanda Addini sa da dukkan
halayensa sunyi dai-dai da fadar Allah (SWT) da manzon rahma Annabi (SAW)"
"Amma kuma Allah yace"Muji tsoronsa muyi muku adalci shiyasa nace idan baki ra ayinsa ba
komai nasan yadda zanyi na sanarda su!Farin cikinki shi namu."
"Ya kalli umma ya ce,"juwairiyya ko ba haka ba!"
"Umma ta ce"Hakane Abbu,Hakika yadda kayi shi yafi cancanta ga kowane uba nagari yasan
wa yarsa zata aura meye addininsa,muhallinsa da kuma aikin yinsa,yadda yarinya bazata shiga
acikin wani hali ba!"Yaseera nasanki da nutsuwa to ki nutsu kiyi tunani mai kyau akan ra'ayin
Mahaifinki ba wai ya tilasta ki bane ko zai maki *AUREN DOLE* A'ah idan baki sonsa ki fada
mana!Mu hakki da Allah ya daura mana akanki mukeson saukewa saboda Yadda muke da
hakki!Akanki hakan kema kinada hakki akanmu yaseera!"
"Saboda haka wajibi ne,agaremu sauke Hakkin ki da ya rataya awuyan mu,saboda Annabi
(SAW) ya ce,Hakkin D'a akan iyayensa,sune :"Na farko,Ya sanarda shi karatu,da rubutu."