Showing 1 words to 3000 words out of 17405 words
Chapter 1 - Auren Wata Bakwai Book Compelet By Aisha Muhd
[8/7, 9:47 AM] Xayyeesherthul-humaerathí ¾íµ€: *AUREN WATA BAKWAI*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
*© Xayyeesherthul-humaerath*
*Dedicated To NimcyLuv*
_*Auren Wata Bakwai!* daga jin sunan kun san cewa za ayi cakwakiya Iya cakwakiya,ba zan
dai baku satan amsa ba, kar ku bari a baku labari, wacce ta karanta ta huta.í ½í¸»_
Page-1&2
*MASARAUTAR BENONI*
Ihu take da magiya hannunta rike da get din shiga masarautar tana jijjigawa ,"Useni aççe am mi
nasta,Hokkam dama je Karshe useni,Don Allah ku barni in shiga Inga Yareema,ku bani dama ta
karshe,Miyida misandiri denyo 'am,Ballite yonki am, Baffana zai mutu, ku taimakawa rayuwata."
kuka take na fita a hayyaci.
Tana fada cikin muryar fulatanci wacce daga ji zaka Tabbatar da cewa hausar bata isheta ba.
Daya daga cikin dogaran ya ce, "Karya kike, Mayya anaci,turo ki akayi ki cutar mana da
yareema."
Yana fada suna janyeta daga jikin get din tana kara kankamewa.
Ta ce, "Aradun Allah,na Rantse ba abun da zan wa Yareema, taimakonsa nake nema, Don
Allah ku barni."
Bulala suka shauÉ—a mata wacce ta kara hargitsa mata tunaninta wani irin tsalle tayi ta dire da
gudu tana neman hanyar gudu.
Wata farar mota ce kirar MERCEDES-BENZ ML350 ta tawo a hankali.
Adnan dake gefen glass yana hangota cikin sauri ya ce wa Driver ya dakata.
Ya na tsayawa Adnan ya fita yana, "Kee! Kee."
Idonta a rufe ta daura hannu akai.
Jikinta na rawa.
Yarinyace da bata zarce shekara Goma sha hudu ba, sanye da kayan fulani, duk ya fita a
hayyacinsa kamar yadda ita ma ta fice a hayyacinta,kallo É—aya za ka yi mata ka tabbatar da
cewa tana cikin wani mawuyacin yanayi,ko dankwali babu akanta, gashi duk a cucure ga yawo
da santsi, Dogowa ce siririya mai dirin Fulani,ba a sata sahun farare can can ba kuma baza
asata sahun bakake ba,duk da yanayi na tashin hankalin da take ciki hakan bai hana bayyanar
da kyawunta ba.
Karasawa ya yi gabanta ganin kamar bata san yanayi ba ya cire hannunta da ta rufe fuska da
shi.
Cike da mamaki ya ce, "You ,?
Cikin isa da kasaita gami da Izza ta jinin sarautar da ke yawo ajinin jikinsa duk wata ilhama da
kamala ta bayyana a tare da shi, Prince Adeel Muhammad Rohaan ya fito a motar ya yin da aka
bude masa.
Cikin second guda ga gukkan kwayar Idon da ya kallesa zai fahimci tsantsar jinin sarauta ne
anan wanda Ubangiji ya tsara masa hallita mai cike da kwarjini da Izza, Fatar jikinsa bakine ba
irin sosai dinnan ba,baƙi mai kyau da sheƙi,ga idanunsa da suka kasance Sexy Eyes da ke
birkita yan mata, yana da fadin kirji da duk wani abu da 'Ya mace ke bukatar kasancewa ga
Namiji ko ince fiye da haka ma.
Kananun kayane a jikinsa kamar yadda ra'ayinsa da tsarinsa yake baya taba sa kayan sarauta
har sai in da wani dalili wanda ya zam dole.
Saukarsa kenan daga America wanda ba kowa ke sanin shigarsa da fitarsa ba domin tsaro.
Driver bai ajiyesa a ko ina ba sai daidai kofar part dinsa dake ta bayan masarautar kebantacce
wanda ba kowa yasan da nan din ba.
Yana Parking ya fito ya Bude masa kofa cikin hanzari.
Tafiya yake tamkar ba zai taka kasa ba.
Shigewa Adeel ya yi kaitsaye ba tare da ko kalli inda Adnan yake ba,bare har ya yi tunanin yi
masa magana ko jiransa.
Adnan ya gyara tsayuwar sa ya na kare mata kallo ya ce, "What is your Name?"
Zaro masa manyan idanunta da taci kuka ta koshi ta yi.
Ya ce, "Oh Sorry Ya Sunan ki?"
Cikin Muryar fulancinta da gurbatacciyar hausarta ta ce, "Zainab a rugar Jauro ana she mun
Gaaji."
Adnan ya ce, "Alright biyo ni mu je." Ya karasa maganar yana mata nuni da hannu.
Bayansa ta bi tana kalle kalle har suka shiga cikin bangaren Adeel.
Kai tsaye bangaren Prince Adeel suka nufa cike da mamaki take kallon wajen tamkar wata
duniyar a zuciyarta take rayawa, "Oh ba don na san ban mutu ba nace nan shine Aljannata
yadda Baffa yake fadamun anya ma aljannar takai nan ko?"
ADEEL na zaune a parlour ya dan kishingida zama irin na sarauta.
ganin Adnan da Gaaji kawai sai ya tsaya yana kallon su ba tare da ya ce komai ba cike da
mamaki.
Adnan ya kalli Gaaji laɓe a bakin kofa duk alamar tsoro ya gama tattara game da ita.
Ya ce, "ke ya kika tsaya abakin kofa bakya tunanin za a dake ki ne?"
Fashewa ta yi da kuka.
Ta ce, "Don Allah ni taimaka mun Baffana zai mutu."
Adnan ya juyo yana kallon Prince Adeel ya ce, "Exactly da Mamaki,meyake faruwa ne? ni dai
san zuciyarka irin haka ba."
Prince ADEEL ya bi sa da ido kawai ba tare da ya ce komai aransa yana so ya yi
magana,amman saboda isa da Izza irin ta jinin sarautar da ke yawo a jinin jikinsa ya kasa furta
komai illa yanayinsa da ya canja na bayyanar da ɓacin rai.
Adnan kuwa sanin halin abokin nasa sarai yasa bai damu da shirun nasa ba ya ci gaba da
magana.
"Atlest koda zaka daina taimakon al'umma, wannan ya zama taimako na karshe da zaka yi, sai
ka ga Ubangiji ya kara buda maka hanyar samunka,idan ka taimaki wannan fulani girl din,ba ka
san wani hali take ciki ba,da condition din da mahaifin nata ya shiga ba,tunda ka ga har ta nace
zuwa wajen biyar, tana zuwa neman taimako baka saurarenta kana wulakanta ta,Don Allah ka
taimaka ba don halinta ba, kuma ba don ta isa ba,sai Don Allah,da kuma darajarata na
abokinka da nake rokonka."
A fusace Adeel ya juyo yana, "Kai Mahaukaci ne,ko mahaifiyata bata taba shigo mun parlour
ba,amman kai ka dauko wata kazamiyar fulanin yarinya ta shigo mun parlour."
Yana gama fadan hakan ya yi shiru.
Adnan ya ce, "Ai awajen Ubangiji da kai da ita duk dayane babu bambanci, kawai dai anan kai
mai kudi ita talaka,kai mai mulki ita baiwarka,so shine bambancin kuma ya zame maka dole ka
taimaketa."
Rai bace Adeel ya furta abun da bai taba furtawa ga duk wanda ya nemi taimako gunsa, "BA
ZAN TAIMAKA BA, may be ma uban nata mutuwa zaiyi,ka fitar mun da wannan kazamiyar
yarinyar daga part."
Nan Shi ma Adnan rai ya baci cikin fushi ya ce, "ba zan fitar da ita ba,in kanaso ka tashi ka fitar
da ita da kanka ta karfi in zaka iya ko kuma ni ka dakeni ka sa in fidda ta."
Girgiza kai Prince Adeel ya yi ya sunkuya yana wuce tare da kokarin danne fushinsa a zahiri.
Sai da suka haura sama sosai, ita kuwa Gaaji mamaki take tana kallonsa cikin ranta take
sakawa daman akwai mutumin da zai iya yiwa dan uwansa mutum fatan mutuwa? Kenan zuwa
zaiyi har rugar su ya kashesa? Ban da haka don kawai baffanta na kwance bai da lafiya sai
yana yi masa fatan mutuwa? Wani abu take ji na yawo a cikin ranta na rashin son ganin Prince
Adeel bata san miye tsana ba Amman ji take ta washe sa kamar yadda ta washi mutuwarta.
Shiru suka yi dukan su na yan mintuna
Sai da ya ja numfashi kafin ya ce zan iya taimakonta in ta yarda Amman da sharadi zan.....
Ya yi shiru nan zufa ta fara keto masa tamkar mai nakuda.
Ya yi shiru.
Adnan ya ce, "Kai muke sauraro fa kuma yi shiru."
Goge zufar da ke kokarin jika masa jiki ya yi ya ce, "Zan... Zan....zan Aureta na tsawon Wata
Bakwai kawai in ta yarda, Ana daura auren zan biya ko million nawa ne a fidda mahaifinta waje
a masa magani,sannan duk inda wata bakwai ya yi zanyi signing a takadda in saketa."
Cike da mamaki Adnan ya ce, "Aure? Kuma wannan? Prince,Why?"
Da hannu ya masa alamar dakatarwa kawai ba tare da ya ce komai ba.
Gaaji ta kallesa ta yi tsalle ta diri tana, "ni? Aure ka? Inma kai mai yankan kai ne ki yanka ni?
Cab Allah Saa'anam mi yiÉ—a ma. Allah ma ya sutura ni bana shonka."
Murmushi Adeel ya yi yana mamaki wai wannan yarinyar ce ke cewa bata sonsa, shi da yan
mata ke bi amman wannan kwailar kazamiyar ce ke cewa bata sonsa.
Tashi ya yi ya shige ciki yana, "In ta yi tunani to,in kuma so take Mahaifin nata ya mutu fine
wannan ba damuwata ce ba,ban da hadi da shi."
Adnan zai mata magana kenan ko tsayawa batai ba ta fice a zuciyarta tana sakawa,me ma zata
yi da wannan wanda yake yiwa Baffanta fatan mutuwa.
da take ji hanjin cikinta ban da kadawa ba abun da suke.
Waige-waige take ko zata samu abun taɓawa ban da ruwan wani kogi ba abun da ta samu.
Haka ta tsaya bakin kogin tasa hannunta ta dibo ta sha sannan ta ci gaba da tafiya.
Tsakanin Rugar Jauro da cikin gari sai anyi tafiya ta kusan minti arba'in ko fi ma wani zubin
akanyi awa guda indai tafiyar kafa ne,domin mota bata shiga Rugar har sai ranar kasuwa kadai
sau daya a sati.
Tun tana tafiya da kwarinta har sai da ta koma jan kafa a haka ta isa rugarsu.
Shigewa bukkar su tayi jiki a mace.
Numfashin da taji na tashi sauri sauri a cikin bukkar yasata saurin karasawa ciki.
Aiko baffanta ne ranga-ranga jiki ya kara tsanani tuni ta birkice ta ma rasa abun yi tamkar za a
zare ransa.
Ta kasa yi masa komai ban hawaye da ke ambaliya daga idanunta.
Ficewa tayi da wani mugun gudu.
Tuni har ta manta gajiyar da ta kwaso a hanya.
Gudu take ba kakkautawa ta fadi ta kurje ,ta kara tashi bata fasa ba,har saida ta isa cikin gari
tsabar sauri a minti talatin ta isa.
tana zuwa kuwa
Bangaren Prince Adeel ta nufa kai tsaye da mugun gudu kasancewar babu kowa agun.
Tana shiga ta na numfarfashi daga kan da zata yi ta ga abun da kara firgitata tuni jikinta ya dau
kyarma.
Price Adeel ne kwance da wata matashiyar budurwa suna Wasanni, babu komai jikin budurwar
shi kuwa daga shi sai gajeran wando.
Jikinta ne ya fara karkarwa ta kasa motsawa tsabar tsorata bata san lokacin da ta sake fitsari
ba.
Sautin Numfashinta na kara fita da sauri-sauri
Dogowan da zaiyi suka hada ido da ita nan fa ta kara firgita ta ja kafa zata gudu.
Wata irin tsawa ya mata yana janyota, "Mene ne ke kuma?" Ita ma budurwar sai a lokacin ta
juyo tana kallonta."
Cikin yanayin firgici ta ce, "Naaa,naaa,naaa ga fada kuna yi ne na zo na fada ma na amince
ne,na yarda."
Like, Comments And Share Pleaseí ½í¸»í ½í¹�
08103080717
Xayyeesherthul-humaerath
[8/7, 9:47 AM] Xayyeesherthul-humaerathí ¾íµ€: *AUREN WATA BAKWAI*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
*© Xayyeesherthul-humaerath*
Page-3&4
Tashi ya yi daga Kan Safina Yana kokarin janyo rigarsa ya sa.
Ita kuwa wani irin takaicine ya turniketa da jin tsana cike da haushin wannan gazamiyar yarinyar
da ta katse mata jin dadi, domin har cikin ranta ta gama kudurta cewa lallai yau sai tayi nasarar
kasancewa da Prince Adeel amman sai dai kash wannan yarinyar ta hana hakarta kaiwa ga
ruwa. Cikin kasalalliyae muryarta ta ce, "Prince ina zaka kuma? Me wannan yarinyar take anan kasan
fa bamu gama ba kuma?"
Ko kallon inda take baiyi ba take ya shige toilet, ganin hakan tasan sarai ba zata taba samun
kansa ba yasa ta tashi ta maida kayanta jikinta tana bin Gaaji da wani irin mummunan kallo.
Ita kuwa kanta a kasa bata ma san tanayi ba domin har yanzu jikinta rawa yake,karo na farko
da ta fara ganin mace da namiji cikin yanayi irin haka.
Yana fitowa ya sanya riga sannan ya dauki Wayarsa ya kira Shamaki ya sanar da shi ya je
bangaren Uwar Soro.
Sanan ya kira Adnan ma a waya ya fada masa.
Tashi ya yi sai da yaje har kofa zai fita kafin ya juyo ya ga tana tsaye ya mata alama da hannu
kan ta biyosa, sannan ta bi bayansa.
�angaren Uwar Soro dake daf da bangarensa suka nufa wanda yake shima keɓantacce ne ban
da Yarima ba mai zuwa in ba da wani babban dalili ba, kasancewarta wacce ta raine shi tun
yana karami har kuma ya girma a yanzu babu mai sanin sirrinsa fiye da ita.
Yana shiga ciki Gaaji ta bi bayansa da mamaki Uwar Soro take binsu da kallo daga shi har gajin
cikin sauri ta gyara zama tare da amsa masa sallamar da ya yi.
Yana zama sai ga Shamaki da Adnan sun shigo.
Bayan sun zo duka ban da kallonsu babu abun da Prince Adeel Ke yi.
Har cikin ransa yana jin nauyin furta masu abun da ke zuciyarsa ta wani fannin yana jin cewa
hakan ba karamin kaskanci bane garesa,amman ya zaiyi? A tunanin sa hakan dai shine kawai
mafitar da zai dakile duk wata kofa da ke kokarin bude masa.
Zufa ce ta ci gaba da keto masa tamkar ba yanzu ya fito daga wanka ba.
Adnan ya ce, "Prince, ka kiramu kuma ka yi shiru Go On Please."
A gajarce ya ce, "Daura mun Aure da wannan Yarinyar za ayi."
Cikin yanayi na Mamaki Uwar Soro ta ce, "Ran Yareema ya dade, Aure kuma wannan? Ina
tunanin in ma itan kake so akwai bukatar a gyarata kuma a Yantata daga baiwa tukunna kafin a
gabatar da ita ga MAI MARTABA da FULANI."
Dakin ya dauki shiru na kusan Second Arba'in kafin Prince Adeel ya kara da, "A haka za ayi, ba
tare da sanin kowa cikinsu ba, kuma a yanzu nake so a gabatar da komai."
Dukkannin su suka koma kallon kallo.
A ƙarshe Adnan ne ya katse shirun da fadin, "Shikenan Shamaki ki kira liman yazo."
"An gama ranka ya dade."
Shamaki ya amsa da haka ya fita domin kiran liman kamar yadda aka umarta.
Ba jimawa sai gashi da liman, Adnan ne da kansa ya sanarwa da Liman dalilin kiransa domin ya
san in Prince ne zai kara magana sa gaji da zaman jira.
Ba tare da bata lokaci ba Liman ya aiwatar da abun da aka umarce shi da yi, Adnan ya zam
Waliyin Amarya, Shamaki ya zama Waliyin Ango Bisa sadaki Million Uku wanda Adnan ke
hasashen ya wadatar a fidda mahaifin Gaaji kasar waje har a kammala masa komai na bukata.
An daura auren amman har yanzu mamaki ya gagara barin zuciyar Adnan domin ya gagara
sanin dalilin da zai sa Prince ya ce zai auri yarinyar nan wanda ya tabbatar da cewa koda
kyauta aka basa bazai taɓa karɓa ba, mutum da a kullum ma bijirewa batun aure yake,tare da
nuna cewa bai da lokacin tsayawa kula wata mata da niyar aure,dole akwai Dalili,to Amman
miye dalilin?.
Ana kammala daurin Adnan ya ce da Uwar soro , "Baba zamu tafi yanzu, ki ajiyeta agunki ana
yi mata dukkanin abun da ya dace kawai."
Sun tashi zasu fita itama ta tashi tana kokarin binsu.
Rike mata hannu Uwar Soro ta yi da alamar su tafi Gaaji ta ce, "Aa Baffa, Baffana Yana shen."
Adnan ya juyo yana, "ki zauna anan kinji zamu je akai Baffanki gun mai magani ne yanzu In
Sha Allah."
Haka ta bita ba don ta so ba zuciyarta fal tsoro kar suje su kashe mata baffa tunda daman
Yareema ya fara yi masa fatan mutuwa, ita kuma su cinyeta.
A cikin Part din ta shigar da ita wani dake, dake babban wajene tamkar gida guda wanda ciki da
wajensa ya tsaru cikin ƙawa tamkar wata duniya ta daban.
Ko da suka shiga dakin kara binsa da kallo kawai Gaaji keyi tana mamakin kasancewarta a gun
shin da gaske nan kuwa duniya ? Cai wannan duniyar inaga dai wacce ake zuwa lokacin da
mutum zai bar duniya ne.
Abun da take ta radawa aranta kenan.
Uwar Soro ce ta katse mata tunani tare da fadin, "Ranki ya dade mu shiga banÉ—aki na haÉ—a miki
ruwa zan miki wanka."
Binta da wani mugun kallo tayi tana zare ido, wanka kuma? Ita ai ta jima da manta cewa ana
wani abu wai shi wanka,ko da baffanta ke lafiya ma ita sai ranar sallah kadai suke wanka a rafi
da sauran matan karkararsu, wannan shekarar kuwa da yazo bai da lafiya ko yi bata yi ba,bare
kuma yanzu da ba sallah ba mai zai kaita yin wanka? Katse tunanin tayi da furtawa a zahiri,
"Cab Wanka? Aradun Allah banyi haka kawai ba sallah she tazo ba zaki ce nai wanka? She
kace fara?"
Uwar Soro ta ce "Ranki Ya Dade ai ba sai agwagi ne masu wanka ba, hakan tsaftane da
tsaftace jiki,kuma kin ga Yareema Baya son kazanta ba za kuna shiri ba in bakya wanka zai ce
ma baya sonki."
Gaaji ta cuno baki ta ce, "Ni bana shon shi daman ai tunda yake yiwa Baffana fatan mutuwa
kuma sai dai shi ya mutu ya bar mun baffana raye."
Dakyar ta samu ta shawo kanta tare da Tabbatar mata cewa in bata yarda an mata wanka ba
Yareema ba zai kai Baffanta a masa magani ba.
Suna shiga Toilet din ta fara ihu tana, " nan ai ba gun wanka ne ba ni ki barni kawai ai DauÉ—a
karin karfine karki ragemun karfina a dakeni in kasa ramawa."
Uwar Soro ta ce, "nan ne ban dakin wanka anan duk haka suke,kuma in kika yi wankan ma
kara karfi zakiyi saboda muna da sabulu mai kyau."