Showing 27001 words to 27868 words out of 27868 words

Chapter 10 - Abu Naka Book 2 Complete Hafsat C Sodangi

ta yi ba, ya
kamata ne mu yiwa juna adalci ni in rage wasu abubuwan ke kuma ki yi haquri da wasu, sai mu
haxu a wata matsaya da zamu ragewa kanmu damuwowin da muke ciki ko kuwa?” Kan ta yi magana sai ga Zainab ta shigo cikin falon xauke da tiren abincinsu.
“Yaya za a kawo maka naka nan ne ko falonka za a kai?”
Ya ce, “A’a, bar shi a kicin xin in ina buqata zan xauka”.
Ta ce, “To”. Ta juya ta fita.
“Aisha!”
Yana nufin ci gaba da maganar ta hanyar ba ta umarni ta kai mishi nashi abincin wurinshi, sai
qarar wayar landline ta katse shi. Ya yi maza ya miqe ya nufi falonshi don amsa wayar a can,
zuciyarshi cike da farin cikin damar da ya samu tare da Saddiqa.
“Kwanan nan zan shawo kanta ta yanda al’amura za su daidaita a tsakaninmu”.
Kalaman zuciyarshi kenan.
Ita ma Saddiqa ta miqa hannu cikin dabara ta xauki kan wayar dake ajiye kusa da ita a tata
zuciyar tana tunanin, “Ai ko za ta saki jiki da shi kyakkyawar mu’amala ta shiga tsakaninsu to sai
ta tabbatar ya rabu da ‘yan iskan ‘yammatanshi tukunna”.
Tana jona wayar da jikin kunnenta sai ta jishi yana cewa, “Zan amsa gaisuwar nan kuwa
Sarah? Aui na yi zaton kin riga kin share sunana a dairy xinki”.
Ta yi ‘yar dariya ta ce, “A’a, sai dai in kai ne ka yi hakan, tunda baka tava nemana ba gara ni
ai na je ofis xinka aka ce min kana gida kana hutun angwanci, shine na ce to ango kuwa ai bai
da lokacin sauraron abin da ke waje, musamman ma a ce bai danganci amarya ba. Shi yasa na
ce bari in saurara sai ka fito tukunna, yanzu ma dai na bugo ne in ce maka congratulation, ina
tayaka murna”.
Ya yi dariyar jin daxi ya ce, “To na gode Sarah, sai dai ko ina angwanci ai bai kamata in rasa
lokacinki ba, kina gida ne?”
Ya ce, “Eh, to yanzu dai bana gida amma zuwa awa xaya xan isa gidan”.
Ya ce, “To sai na zo”.
Ya ajiye wayar, ita ma Saddiqa ta mai da tata ta ajiye.
“Aunty kin gama wayar ne?”
Saddiqa ta xago ido ta kalle ta jikinta sai rawa yake yi, zuciyarta tana raya mata zai fita ya
barni ya tafi wurin ‘yammatanshi na banza saboda na tsare mishi inda zai kawo su. Gara in ba

shi wuri, bari kawai in tafi in bar mishi gidanshi ya sake ya yi abin da ya so, dama abin da ya
saba yi kenan.
“Mu ci abinci mana”.
Zainab ce take yi mata magana saboda ganin halin da ta shiga shirunta ya yi yawa.
“Ci ki bar min Zainab, kinga ai xazun nan na karya”.
Ta miqe ta shiga xakinta ta shafa jikinta ta ji lalitar kuxinta da Gwaggonta ta ba ta, ta duba
kuxin suna nan a ciki. Ta yi saxaf-saxaf cikin sanxa ta wuce Zainab a kicin tana gyare-gyare
tana tsaftace wuri ta fita harabar gidan dake buxe, cikin sa’a babu kowa balle ya ganta. Tana
baro gidajen nasu da kaxan ta yi sa’a ta samu mashin ta xane zuwa tashar motar garin dake
kusa.
Shigarsu tashar ta ji ana Kano ciko mutum xaya a tasi. Tana jin haka ta faxa ciki a zuciyarta
tana tunanin daga can sai ta shiga mai zuwa Misau ya fi mata ta zauna jiran ta Bauchi ta cika
don kar ya gane ta fita ya biyo bayanta ya sameta.
Nan da nan aka gama haxa kuxin fasinja aka sallami direba yaja mota suka soma tafiya.
Saddiqa tana zaune cikin mota sai faman sharara gudu take yi, zuciyarta cike da farin ciki
yau kam za ta koma Misau gaban Gwaggonta. Ta tuna Gwaggon nata da irin kalamanta da ta
sha gaya mata a kan Mus’ab.
“Halin wannan yaron sai shi babu mai iya mishi sai mace ‘yar bariki irinshi, amma bake ba
Saddiqa”.
Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Ubangiji ka sakawa Gwaggona bisa gaskiyarta da riqon zumuncinta,
babu wani abin da ta gaya mata a kan xan nata face sai da ta ganshi a zahiri”.
Za ta koma gaban Gwaggonta, za ta je can ta same ta suyi zamansu ta qara sonta a kan son
da dama can take mata, don ta qara gane ba ta da masoyi a duniya wanda ya wuce ta.
Mu sadu a littafi na uku don jin yanda za a kwashe.
Taku.
Hajiya Hafsat Sodangi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0