Showing 24001 words to 27000 words out of 27868 words

Chapter 9 - Abu Naka Book 2 Complete Hafsat C Sodangi


Mus’ab da Idris suna tasu hirar a nashi wurin.
“Kai angwaye suna qibar jin daxi kai kana zubewa?”
Mus’ab ya yi tsaki ya ce, “Wane angwanci nake yi ni da amarya ba ta magana dani, ba ta ma
yarda ta ci abinci sai in ta ga zan danneta in xura mata”.
Idris ya qyalqyale da dariya ya ce, “Borin nata har ya kai haka?”
Ya yi tsaki tare da sosa gefen fuskarshi da yatsanshi.
“To amma wannan borin ai ya yi yawa, in da nine kai sai in kawo qarshen abin gaba xaya, in
yaso in yi ta yin rarrashin mai dalili”.
Mus’ab ya yi shiru kamar bai gane abin da yake nufi ba, ya sako musu wani zancen, suna
hira Mus’ab yana kallon agogo, a zuciyarshi yana tunanin lokacin xora girki ya yi, sai dai ya ya
zai yi ya yiwa Idris wannan maganar. Tashi zai yi cikin hikima ko kuwa shiru kawai zai yi?
Saddiqa tana tare da Abida suna hira, ganewar da Abida ta yi maigidan ne mai girkin gidan
ya sata kallon Saddiqa ta ce mata, “To muje kicin mana muna hirarmu muna aikin abinci sai mu
yi mu gama kafin baban Umar ya ce mu tafi”. Ta ce mata, “To”.
Suna girkin suna zancensu, mafi yawancin maganar Abida ce take yi mata, nasiha ne kuma
kan ta daina fushin da take yi ta yarda ta zauna lafiya da mijinta.
Saddiqa ta ce, “Uhm!” A zuciyarta kuwa tunani take yi, wannan ba ta san halin Yaya Mus’ab
ba. Kalaman Gwaggonta suka sake zuwa mata.
“Zamanki da shi wahala ne saboda kishinki”. Ta xan rage fara’a kafin ta ce, “Gwaggo kullum
sai ki rinqa dangantani da kishi bayan na ji an ce bai da kyau”.
Gwaggo ta ce, “Eh, to ya dai wahalar da mace mai shi kam, musamman a ce ba ta yi dacen
mijin da zai tausaya mata ba, tausayinki ba zai sa wannan yaron ya haqura da son ranshi ya
barki ki mallake shi ke kaxai ba”. Ta girgiza kai don qara tabbatar mata da abin da ta gaya
matan. Abida ta katse tunanin nata ta hanyar tambayarta cewa, “Kin san daxin amarci kuwa?”
Ta xan yi murmushi kaxan da nufin zolayarta, ta ce, “Da kin san yanda abin yake da baki tsya
kina yi muku wannan takurar ba, kin qi ki kwantar da hankalinki balle ku ji daxin zaman naku,
kin tsangwameku gaba xaya kun zube kun rame, ban ga abin da kika rasa a wurin mijinki ba, a
shirye yake ya kyautata miki. Dubi yanda ya qara qayatar miki da wurinki a sati biyunki na
zaman wurin kawai, in kika saki jiki da shi kina zaton akwai wani abin da ba zai yi miki ba”.
Ga mamakinta sabodaa ta saba yin magana Saddiqan tana shiru, sai dai ta saurareta kawai
sai ta ji ta ce mata, “Ai ni ba abinshi nake so ba”.
Da sauri Abida ta kalleta cikin nutsuwa ta tambayeta, “Me kike so nashi?”
Ta yi shiru ta sunkuyar da kanta qasa nuna alamar jin nauyi.
“Ni yarki ce Aisha, in baki yi magana dani ba da wa za ki yi? Randa Abu za ta tafi da na zo
mata sallama kuka ta rinqa yi tana cewa, in riqe ki amana.
Jin hakan yasa ita ma Saddiqan ta soma yi mata kukan, ba ta hanata ba sai ta ci gaba da yi
mata magana.
“Ni dake dukkanmu jirgi xaya ne ya xauko mu, auren zumunci aka yi mana, yanda na san ba

zan ce auren dole aka yi min ba, haka kema na san bana dolen bane. Don kun zo kun samu
abin da ya vata muku rai a cikin gidan nan bai zamo hujja a wurinki ba da za ki yi ta bijire mishi,
ba a kan idonki ya kawota ba, a yanzu in har kuka shirya ke da shi zai yi matuqar kiyaye abin da
bakya so, ba ma sai kin tsaya kina ce mishi ga abin da bakya son ba, ai shima ya xanxana
wahalar wannan dogon fushin da aka yi mishi”.
Har suka gama girkin nasu suna hirarsu, suka gama suka shirya komai tsaf. Abida ta kalli
Saddiqa ta ce mata, “To sai ki xauka ki kai musu”.
Ta ce, “A’a, ke daai ki kai tunda ni kam ai ban tava leqa wannan falon nashi ba”.
Abida ta ce, “A’a, ai yanzu suna tare da abokinshi don kin kai ba wani abu bane, sia ma ya ji
daxi ya kuma san kina shirye da a shirya”.
Ta yi maza ta ce, “Tafxijam! Wato ma nice mai neman shirin? Lallai ba za a shirya ba, ajiye
musu nan in ya zo wucewa ya gani zai xaukar musu”.
Abida ta qyalqyale da dariya ta ce, “Kin gani kuwa da yake na san daxin nawa auren bana
yarda maigida ya yi fushi dani, ina ganin alamar vacin rai a tare da shi nake yin maza in shawo
kan abina don bani da jarumtakar irin wannan zaman da shi”.
Hira sosai ta yi mata, sai wajen yamma suka tafi gida.
Washegari kuwa da yamma sai ga Abidan ta dawo tare da wata lafiyayyar yarinya budurwa,
ta shigo falon Saddiqa, Mus’ab yana ciki yana nazarin wata mujalla, ya yin da Saddiqan ke cikin
xakin a kwance. Sun gaisa ta soma yi mishi bayani.
Saddiqa ta fito tana mata sannu da zuwa, “Ku shigo”. Mus’ab ya bi bayan kyakkyawar
yarinyar da kallo, ya yi kamar ya tambayi sunanta sai kuma ya fasa saboda kar Saddiqa ta ji shi
yana maganar.
“Aisha ga qanwata na kawo miki Zainab, ‘yar Kawuna ce kwanan nan ta gama karatunta na
sakandire, baban Umar ne ya bani shawarar kawo miki ita ta xebe miki kewa kafin a samo miki
mai aikin”.
Wannan shine bayanin da Mus’ab ya jita tana yiwa Saddiqa.
Tun zuwan Zainab gidan al’amura suka soma daidaita, Mus’ab ya smau damar komawa kan
aikinshi, sai dai kullum in zai fita zai kukkule ko’ina na gidan, ta yanda wani ba zai shigo ba na
ciki kuma ba zai fita ba sai in ya dawo ne yake barin ko’ina a buxe.
Saddiqa kuwa tana tare da Zainab a gida ta mai da ita tamkar ‘yar’uwarta saboda yanda take
jin daxin zama da ita, zuwanta ya rage mata kewa da damuwa, ta fidda ita daga zaman shiru da
take ciki, matuqar suna tare zai jisu suna ta raha da dariyarsu.
Cikin qanqanin lokaci suka shaqu da juna, har girkin ma in za suyi tare suke shiga kiin xin
suna aikinsu suna hirarsu, tamkar sun daxe da sanin juna.
Shima Mus’ab ganin yanda ta saki jiki da Zainab xin yasa shi samun nutsuwa da kwanciyar
hankali, saboda ya lura Saddiqa ta samu sassaucin damuwa.
Ganin haka sai ya fara tunanin hanyoyin da zai bi wajen ganin al’amura sun daidaita
tsakaninshi da ita, ya shiga qoqarin keveta ita kaxai ya xan yi mata kalamai masu nutsar da
zuciya, duk da dai ba wani amsa mishi take yi ba.
Haka nan yana kiyaye lokacin dawowar shi gida, yana tasowa daga ofis bai yarda ya tsaya
ko’ina sai gida, ga kuma hidimomi iri-iri don dai ya faranta mata rai.

GARIN MISAU

Abu tana kwance a xakinta cikin dare iska sai faman kaxawa take yi, kasancewar lokacin
kaka ne. Abu ta miqe zaune a tsakiyar gado ta yi tagumi zugum, tunanin yanda ta baro Saddiqa
take yi a gidan Mus’ab. Mafarkinta na daren jiya ne ya fi tsaya mata a rai, ta tuna yanda ta ga
Saddiqa a mafarkin, bayanin dukan da Mus’ab ya yi mata take yi, tana nuna mata raunukan da
ya yi mata.
Ta yi shiru cikin tunani mai zurfi tare da tuna irin dukan da ya yiwa Jennifer a kan idonta,
jikinta ya xauki rawa saboda tabbatarwar da ta yi in har ya ce zai yiwa Saddiqa irin wannan
dukan to ba za a haifi xa mai ido ba.
Dare ya yi nisa Abu tana zaune a bakin gadonta taqi yarda ta kwanta balle ta samu ta yi
barci, saboda babu halin ta rufe ido ko gyangyaxi ya xan xauke ta sai ta ga Saddiqa tana tsaye
gabanta tana kuka tana faxin “Ke kika ja min wannan musibar Abu da kika qi yarda ki tahowa
Gwaggona dani kika barni wurin Yaya Mus’ab, saboda kin fifita sonshi a kaina, bayan kuma
Gwaggona ta roqeki ki tausayawa maraicina in kinga ba daidai ba ki dawo mata dani gabanta”.
Abu ta rasa inda za ta tsoma ranta ta ji daxi, ita da kanta ta zargi kanta da rashin iya tsai da
adalci a tsakanin Mus’ab da sauran jikokinta a ko’ina, ba ta iya voye shi daban ne, ba ta iya
voye sonshi a zuciyarta, ba ta barwa kanta wannan sirrin.
To wai ma mene ne dalilin da yasa ta fi sauraranshi a kan sauran? Ta fi tattalin farin cikinshi a
kan kowa? Ta fi son ganin ya samu abin da yake so a kan kowa? Me yasa take yi mishi irin
wannan son?
Mus’ab ne ya fi kowa biyayya a cikin jikokinta ko kuwa ba haka bane, shine ya fi kowa jawo
musu magana, shi ya fi kowa taqadaranci, ya fi kowa rashin tsoro, ya fi kowa yin yanda ya so.
Amma ta je ta kasa hana shi Saddiqa saboda ta gane babu abin da yake so irin a bar mishi ita.
Nan take ta soma kuka tana faxin bai cancanci abin da take yi mishi ba, ba ta yiwa kanta
adalci ba da ta bari sonshi ya rinjayeta. Ta miqe ta yi alwala ta dawo ta soma gabatar da
addu’o’i na Ubangiji ya kare Saddiqa daga dukkan sharri.
Nan take ta qudurawa ranta gari na wayewa za ta je gidan Malam Abdullahi ta gayawa Inna
Habiba halin da ta baro mata ‘yarta na gaskiya, don ta san abin da za ta yi ta taimaketa ta san
matakin da za ta xauka.
Saddiqa tana kwance kan doguwar kujera tana nazari da tunanin al’amuranta da Mus’ab kan
irin kai kawon da yake yi da yanda yake nuna qauna da kulawa a gareta, yanda yake qoqari da
tattalin ganin sun shirya shi da ita. Duk da har yanzu ba wani amsa maganarshi take yi ba, ba
ya fushi ko nuna vacin rai game da abubuwan da take yi. Kalaman Abida kashedin da ta rinqa yi mata kan haqqin aure suka dawo mata.
“Ki fa yi hankali Aisha kar ki yarda ki shiga haqqin mijinki. Wannan bijirewar taki tana nema ta
wuce gona da iri, don kun same shi da wata a gida bai zama miki dalili ba fa, don kuwa samun
ta kika yi ba ita ta zo ta same ki ba”.
Ta yi ajiyar zuciya daidai lokacin da Mus’ab ya shigo falon.
“Ajiyar zuciyar me kike yi? Ko kina jin yunwa ne?”
Ta xaga ido ta kalle shi, kwalliyarshi ta qananan kaya ta burgeta, ga qamshinshi mai daxi, in a
Misau da Bauchi kaxai ka san shi ba za ka tava sanin yana amfani da qananan kaya ba.
Zuciyarta ce ta raya mata hakan.
“Bari in shiryo miki abincinki”.
Ya juya zai shiga kicin. Da sauri ta ce mishi, “Ni babu halin in yi wani motsi sai a ce yunwa

nake ji?”
Ya yi maza yaja ya tsaya nan take, ya juyo ya fuskanceta can cikin zuciyarshi daxi ne ya
kama shi, bai tava jin ta yi mishi wata magana da jimlarta ta yi tsawo kamar wannan ba.
“Za ta fara magana dani kwanan nan”.
Tunanin da ya zo mishi a ranshi kenan.
“To in ba yunwa ba ce mene ne Aisha?’
Ya yi tambayar daidai isowarshi kan kujerar da take zaune. Maimakon ta zabura ta miqe
kamar yanda ta saba yi mishi sai ya kamota, sai ya ga ba ta motsa ba.
“Zan iya zama kenan?”
Zuciyarshi ta sake raya mishi, don haka ya smau wuri a gefenta ya zauna, ita ma ta miqe
daga kwance ta zauna cikin nutsuwa kanta a sunkuye.
“Kina son wani abu ne ko kina da wata damuwa ne?”
Ta girgiza kai tare da faxin “A’a”.
“To in baki da ita ni ina da ita Aisha, ko baki da damuwa da abin da ya dame ni?”
Ba ta tanka mishi ba, sai dai ganin ba ta yi yunqurin tafiya ta bar mishi wurin ba yasa shi jin
daxi, nan take kuma ya yi nufin amfani da damar da ya samu wajen yi mata magana.
“Ban tava tunanin don an gaya miki mugun halina ko kin kama ni da wani laifi za ki nuna min
qiyayya da tsana irin wacce kike yi min ba, saboda ni na san waxannan abubuwan guda biyu ba
sune matakan da ake xauka wajen gyara mutumin da ake ganin yana buqatar gyara ba. Sanda
Abu ta kaiwa Kawu Gixe ni shi kuma ya damqa al’amurana a hannun Mama, ko in ce Innata, ni
da kaina qyamar kaina nake ji, zuciyata ta yarda da cewar ni xin ba komai bane face wata
jarrabawa da aka jarrabi iyayena da ita, saboda kullum abin da ake gaya min kenan.
Don haka sai na zama a takure bana ko iya sakewa in shiga mutane balle in yi mu’amala
dasu, saboda ko da na kasa barin abin da ake so in barin to kuma bana jin daxin vata musu ran
da nake yi, da yanda nake ja musu magana. Tunda a gabana an yiwa babana gori a kaina, ba
sau xaya ba, ba sau biyu ba. Don haka ko da aka kawowa Kawu Gixe ni na bi umarnin Abu ne kawai na biyota, amma
cikin zuciyata na yi niyyar fakon idonsu in yi tafiyata don kar suma in ja musu irin abin da na
jawa iyayena a Misau.
Sai dai ban iya tafiya na barsun ba Aisha, saboda cikin xan qanqanin lokaci ne na fahimci su
basu xaukeni abin kunya ba balle su kalleni a matsayin jarrabawar rayuwarsu, ban tava sani ko
tunanin ina da wani alheri a tare dani ba sai da na ji Mama tana rama gorin da aka yi mata a
kaina da wasu kalamai da ba zan furta miki su ba. Amma bayan lokacin ne ni da kaina na gane ashe duk abin da na yi a rayuwata ban tava
xaukan abin wani ba, haka nan na kan faxi laifina ni da kaina, ko kuma in faxi gaskiya kan abin
da aka tambaye ni. Sai da na ji wannan shaidar a bakin Mama kafin ni kaina na san eh, ashe
haka xin nake. Da na zauna da ita sai da ta yi min wani irin riqo, ta yi mu’amala dani wata irin mu’amala da
ta tilastani jin kunyarta, na zama mai gudun vacin ranta, na zama ban da abin da nake so irin na
burgeta, in sata ta ji daxi, in jita dai tana sanya min albarka tana roqon Ubangiji ya shiryar mata
dani. Ba duka ta rinqa yi min ba, ba zagi ba, kalamai ne kawai masu sauqi da suka fi kama da
nasiha. Yanzu mene ne amfanin yaro kamarka a same shi yana irin waxannan abubuwan da

kake yi? Yanzu ko don in ji daxin zuciyata ba za ka daina ba? Ba za ka bar abin da nake cewa
ka bari ba? Don Inna ta ji daxi, don in sata ta yi farin ciki. Sai na wayi gari na daina abubuwan
da take faxin in daina, duk da wuyar barinsu”.
Ya xan yi shiru kaxan kafin ya buxe baki cikin nutsuwa ya ce mata, “Na xauka tunda ita ta
haifeki halayenki za su zamo masu sauqi irin nata”.
Duk da kalaman da ya yi mata sun ba ta tausayi, sun kuma kashe mata jiki hakan bai hanata
xagowa ta kalle shi ba, kan ta gama tunanin dake zuciyarta sai ta ji ya ce.
“Ko da yake dama an ce wai a kan haifi xa ne ba a haihuwar halinshi”.
Ta yi maza ta gyaxa kai. Ya yi murmushi ya ce, “Nima da halin Inna ne dani ai da bamu samu
matsala dake ba ko?”
Ta sake sunkuyar da kanta qasa.
“To amma ko baki yi min yanda Inna ta yi min ba tunda Kawuna ya riga ya bani ke duk da ya
fi kowa sanin yanda nake xin, ai ina ganin ba irin wannan zaman ya kamata mu yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0