Showing 15001 words to 18000 words out of 27868 words
Chapter 6 - Abu Naka Book 2 Complete Hafsat C Sodangi
Kyakkyawar yarinya mai
matsakaicin tsawo wankan tarwaxa, mai yalwataccen gashin kai. Sanye da kayan bacci tana
muttsuke ido tana fara’a saboda ganin baqi.
“Sannunku da zuwa”.
Ta faxi cikin murmushi.
“A’a, lallai amarya ce ta yi mana saukar dare cikin ruwa?”
Abu ta ce, “Cikin ruwa fa kam gamu nan jage-jage”.
Daga cikin xakin da ta fito yaro ya qwalla qara ta yi maza ta shiga ta xauko shi za ta baiwa
Idris shi, Abu tasa hannu ta karve shi tana cewa, “Dama da babban mutum ne a gidan?”
Mus’ab ya ce, “Eh, mai sunan liman ne Umar”.
Ta yamutsa fuska jin ya tsoma baki cikin maganarta.
Abida ta sake fitowa tana murmushi.
“To ga gajiya ga yunwa da wanne za a fara, wanka ko cin abinci?”
Abu ta ce, “Da wurin kwanciya kika bamu muka kwanta kawai”.
Ta yi murmushi ta ce, “Ai yanzu huxu da rabi ne na asuba, gara kawai ku yi haquri in mun yi
sallar asuba sai ku kwanta ku huta”.
“To bamu ruwan mu yi wanka don yarinyar nan ma ta xan ji daxin jikinta, ta wahala ta yi amai
yau har ta gaji, a jigace take, ga shi ko kaya ba ayi dabara an zo mata da shi ba, to ba a san
abin da za a zo a tarar ba kenan na vacin rai da tashin hankali, yanda mace ba ta yi sa’ar miji
ba ta gamu da matsala”. Abida ta bita da kallo ta ce, “Amma a haka Baba ai kin fita alamar jigatar”.
Mus’ab da ya san da shi Abu take yi ya cewa Idris, “Bari in shiga gida ina zuwa”. Ya ce mishi,
“To, a fito lafiya”. Da sauri ya fita
Kafin Saddiqa ta fito daga wanka har ya dawo, ya zo ya miqawa Idris leda mai xauke da
sabbin riguna guda biyu dogaye da aka yiwa xinki mai kyau a jikin asalin galila, ga ‘yan
kwalayensu da gyalensu, under wear da qananan ‘yan kunnaye.
Ya miqawa matarshi ita ma ta kai wa Saddiqa dake shafa, tasa hannu biyu ta karva ta saka
cikin murna da farin ciki, saboda ba ta san daga inda suke ba.
Ana idar da sallar asuba Abida ta kewaye su Abu da nau’’o’in abinci iri-iri na ci da na sha, ga
shi dama ta iya girki, ta tsara su ta tsara shi ta yanda ko baka jin yunwa sha’awa zai sa ka ci. To
balle su Abu da suka wahala wajen tafiya suka iso ba su ci komai ba, suka kuma kwana suna
kwara amai. Sai da suka ci suka qoshi har Abu tana cewa a kunna mata fanka sai ga Abida ta sake
shigowa da wani kwanon abincin za ta ajiye kusa da Abun, ta yi maza ta ce mata.
“Ke ‘yar nan in dai ba so kike mu ci sai mun kasa tashi ba gara ki barmu haka”.
Abida ta yi murmushi ta ce, “Ba za ku kasa tashi ba ai babu wani abu mai nauyi cikin abin da
kuka cin”.
Abu ta ce, “Ba zamu sake cin komai ba”.
An xan jima kaxan Abida ta ce, “To ai sai muje ku kwanta ku huta”.
Abu ta ce, “A’a, mu yanzu mota kawai za a kawo mana ta xebe mu ta mai damu inda muka
fito”.
Idris da tuni ya gane akwai matsala tsakaninsu da Mus’ab, ya ce mata, “To ku xan miqe mana
kafin in je in zo muku da motar”.
Ta ce mishi, “To”. Saboda mutuncinshi da na matarshi da ta gani.
Suna kwanciya kuwa bacci ya yi maza ya xauke su, basu sake sanin abin da ake yi ba.
Mus’ab yana tare da Idris yana ba shi labarin abin da ya faru, bai voye mishi komai ba. Idris
ya kalle shi cikin vacin rai da nadama ya ce, “Yanzu wannan abin da me ya yi kama? Ni dama
ina kallonka ne tare da mamakin wannan rayuwar da kake yi, saboda daga ganinka sai a gane
kai xin mutum ne mai asali da ya fito daga wuri na mutunci, amma ka zo ka biyewa wannan
sharholiya. Yanzu ina alherin wannan abin da ya faru? Me za ka cewa wannan yarinyar?”
Suka xan yi shiru. Jimawa kaxan ya yi tsaki ya ce, “Kai da aka yiwa gata da irin wannan
lafiyayyar yarinyar me za ka yi da waxannan da kake kwasa masu gashin doki a ka?”
Mus’ab ya ce, “Uhm! Don ma baka san artabun da aka yi da mahaifiyata ba kafin aka bani
ita”.
Idris ya sake wnai tsakin ya kawar da maganar ta hanyar qwalawa matarshi kira.
Ta amsa da “Na’am, gani nan zuwa, minti biyu.
Ta iso kafin cikar minti biyun da ta ambata cikin kwalliya da qamsohi, tana goye da xansu
dake ta miqe-miqe nuna alamar bai son goyon. Hannunta kuma xauke da tiren abincin da ta
shiryo musu ta ajiye a gabanshi.
“In zanin ya kwance ya faxi fa Abida?”
Ta ce, “Sai ya ji da shi”. Ta faxa daidai ta kwanto shi za ta ajiye mishi shi, ganin irin kallon da
ya yi mata yasa ta yin murmushi tare da faxin “To ka yi haquri”. Ta samu wuri ta xan zauna tare
da sauraron abin da yake gaya mata.
“Babu zuwa cikin gari yau”.
Ta yi murmushi ta ce, “Na sani ai tunda muna da baqi”.
Ya sake cewa, “To muna da ‘yar matsala tare da baqin namu”.
Ta sake cewa “Na gane, don na ji Abu tana cewa Aisha gaskiyar uwarta ne da ta cewa fitina
kawai aka xauko mata, don haka ba za ta barta cikin fitinar ba za ta tasa ta a gaba ta mayarwa
uwarta da ita”.
Gaban Mus’ab ya sake faxuwa. Idris ya cewa matarshi “To a irin hikimarku ta mata ki san
yanda za ki yi ki rarrasar mana su mana, musamman Abu ta yi haquri”.
Ya miqa hannu ya jawo musu tiren abinci ita kuma ta miqe ta shiga ciki.
Wajen sha biyu da rabi na ranar ne Abu ta farka cikin salati da miqa, tana buxe ido ta xaxawa
Saddiqa duka.
“Ke tashi sakarya mara zuciya, kin kwanta kin saki jiki kin hangame baki kina ta yin bacci sai
ka ce ba da vacin rai kika kwanta ba”.
Saddiqa ta ce, “Kai Avbu kenan, sai ka ce ba tare muka yi baccin ba”.
“Tashi ni mu shirya mu tafi”.
Saddiqa ta yi maza ta miqe.
“Fita ki tambayi matar gidan ko an kawo mana motar?”
Ta fita tana magana da Abida, ita kuwa sai kallon Saddiqa take yi cikin sha’awa.
Gasu nan dai a falo yanzu suka dawo bari in tambayesu.
Ta ce, “To”.
Ta koma xaki tana yiwa Abu bayani, ita kuma Abida ta nufi falon mijinta ta gaya musu
tambayar da Abu ke yi.
A hankali Mus’ab ya buxaa baki ya ce, “Xan kira mana ita Abun”.
Ta ce, “To”. Ta tafi.
Idris da Sani suka gaisheta ta amsa, ta qi amsa ta Mus’ab.
“Haba Abu, ai tamu dake ba ta vaci, muna ‘yar haka dake ne? Ai Aisha ce ya kamata ta yi
fushi dani, ke kuma sai ki haxamu ki yi mana faxa ki sasantamu ki ce mu zauna lafiya, tunda na
saba jinki kina cewa shi aure sasanta shi ake yi ba lalatawa ba”.
Da sauri ta ce, “Ba irin naka auren ba, ai kaimaa baka nufin yinshi, mai nufin yin aure ba zai
yi wannan abin da kake yi ba, tunda dai duniya ka tasa a gaba ai sai ka je ka yi ta yi, amma
Saddiqa kam zan mayarwa uwarta da ita, don suna kuka aka raba su ta kuma roqeni in har na
ga ba daidai ba kar in bar Saddiqa don ba za ta iya da kai ba”. Sani ya yi murmushi ya ce, “Haba Abu…..”
Kan ya yi maganar da zai yi ta yi maza ta kwave shi, ta ce, “Kul! Kar ka ce za ka ce min
komai, ina ce ku dukanku iya shegen kuka tasa a gaba, ai ina ganin lokacin da ka dawo. To ko
varawo ne ya dawo gidanshi a wannan lokacin ai yaa isa lalaataccen varawo”.
Idris ya ce, “Gaskiyaa ne Abu, ita wannan rayuwar ai ba rayuwa ba ce, yaushe za a haxa
matan bariki da matan da kuka bamu?”
Abu ta ji daxin zancen shi, ta saki jiki suka yi ta hira. Ta kwashe bayani duk ta yi mishi, tun
daga ranar da Mus’ab ya zo gidanta da zancen neman auren Saddiqa, har kawo barowarsu
gida jiya da abin da ta zo ta tarar a nashi gidan, wanda idonsu ya ganar musu ba ta rage komai
ba sai da ta gaya mishi. Cikin nutsuwaa ya ce mata, “Ya gayaa min Abu, saboda shima ya san bai kyauta a. to amma
kuma abin da ya yin bai kai na ki tafi mishi da maatarshi ba, ki yi haquri”.
Ta yi maza ta ce, “A’a, abin da ya kamaceni kenan in yi adalci a tsakaninsu, ba za ta iya da
shi ba ya fi qarfinta, baqin ciki kawai zai yi ta qunsa mata, yarinya ce ‘yar qarama”.
Idris ya ce, “Na ganta ai”.
Ta yi maza ta ce, “Yauwa, to wannan randa ya ce zai yi mata irin dukan da na ga ya yiwa
wata jiya ai falle-falle za a xauke ta. Amma da yake ita wancan xin mai qoqari ce sai na ga ta
fito da qafarta tinqis-tinqis har tana iya magana”.
“To amma Abu”…….
Abun ta yi maza ta kalli Mus’ab ta ce, “Kai kar fa ka ce za ka rinqa tsoma min baki”.
Ya yi maza ya yi shiru. Idris ya ce, “To ki yi min wata alfarmaa mana”.
Abu ta ce, “Ta mene ne in ji in zan iya”.
A hankali ya ce, “Za ki iya, so nake ki bar maganar tafiya a yau ki haqura har zuwa jibi, ke da
kanki kin ce yarinyar nan a jigace take, ke kanki ba ta fiki jigata ba. To ku xan hutaa mana kafin
ku tafi”.
Ta ce, “To sai dai gobe, amma jibi kam ya yi yawa”.
Ya ce, “To na gode, Ubangiji ya saka da alheri”.
Ta ce, “Amin”.
Da yamma Abida tana aikin abincin dare, ta bari ta leqa xakin da su Abu suke ta kira
Saddiqa.
“Aisha ko za ki fito ki xan taimaka min ne?”
Cikin sauri ta tashi ta fito suka shiga kicin xin tare suna aikin tare da hirar da Abida ce mai
kawo zancen, ita amsa ne kawai nata shima a taqaice.
Zirga-zirgar Umar ta dame su, Saddiqa tasa hannu ta xauke shi ta goya shi suka ci gaba da
aikinsu.
Idris ya shigo kicin xin riqe da ledar yankakkun kaji, Abida ta karva tana yi mishi sannu. Ya yi
murmushi ya ce, “Amaryar kike sawa aiki? To bari in kira angonta ya ganta”.
Saddiqa tana jin haka ta yi maza ta bar kicin xin ta xauka da gaske kiran nashi zai yi.
Abida ta ce, “To ai sai ka shigo ka tayani tunda ka korar min ita”.
“Haba Abida, ai sai Abu ta ce yanda kika ga damaa kike juyani”.
Abu dake kusa bai sani ba ta yi maza ta ce, “Ai gara maka haka, a juya kan da wannan
tanbaxa da su Mus’ab suke yi”.
Da daddare bayan cin abinci Mus’ab da Idris suna tare da Abu, saqarta take yi tare da
sauraron bayanin nasu.
“Haba Abu, ki taimaakeni mana irin taimakon da na saba ganin kina yi min, kar ki tafi min da
Aisha ki yi haquri ki samu kwanaki biyar zuwa bakwai don ki rarrasar min ita. Shi Kawuna da ya
ce zai kawo min ita ai bai ce miki in kinga ba daidai baa ki mai da ita, ke kin san ba zan cuceta
ba, don kin fi kowa sanin ina sonta, don haka ki taimakeni ki rufa min asiri”. Ta harare shi ta ce, “In yi qarya kenan?”
Idris ya karve da cewa, “Ba qarya bane Abu gyara ne, ai kinga ni bana goyon bayan abin da
yake yi, zan sa miki ido a kan zaman ina ganin ba daidai ba ko somi-somin wulaqanci zan sata
a mota in kawo miki ita har gida Misau, don ba ta cancanci ganin irin wannan baqin cikin ba”.
Abu ta yi shiru cikin nazari, zuwa can ta ce mishi, “Kai a’a, ba zan iya barinta ba, na kuma
roqeka kaima kamar yanda ka ce min in yi maka alfarma in qara kwana, to nima ka yi min
alfarma ka kawo min motar da za ta mai damu gida gobe”.
Da sauri ya ce mata, “Cikin yardar Ubangiji zan kawo muku”.
Ta ce, “To, na gode”.
Ta miqe ta shiga ciki ta barsu a nan. Ya kalli Mus’ab cikin nutsuwa ya ce mishi, “In har baka
samu wata hanya ta hanasu tafiya ba zan ba da motar da za ta mai dasu, saboda ba zan yarda
in vata mata ba, saboda tsohuwa ce mai mutunci da addini”.
Mus’ab ya yi shiru sai dai hakan bai hanasu ci gaba da tattaunawa ba.
Washe gari da asuba daga fitowarsu daga masallaci ya bar unguwar a cikin motarshi, daga
Idris har matarshi dama Abun sunyi zaton bai son ganin tafiyarsu ne yasa ya yi hakan.
Suna ciki suna shirye-shiryensu na lodin tsarabar da Idris ya yi musu, ga kuma Abida da take
ta yi musu girke-girken da wai za su riqe su ci a hanya.
Qarfe bakwai da rabi daidai motar da za ta xauke su ta iso aka shiga fitar musu da kaya
saboda ba qaramar tsaraba Idris ya yi musu ba.
Suna cikin haka sai ga Mus’ab ya iso gidan xauke da limamin babban masallacin garin cikin
motarshi, wanda kuma shine kakan Idris. Dattijo mai kimanin shekaru tamanin a duniya, yana
riqe da sanda a hannunshi saboda matsalar qafa da yake da ita.
Gaba xaya su Idris suka iso wurinshi suna yi mishi sannu da zuwa.
“Har baqin namu sunyi harama ne?”
Idris ya amsa “Eh, malam ai har sun kammala shiri”.
Ya ce, “To ai sai mu xan shiga daga ciki don mu gaisa”.
Ya ce, “To”.
Ya gayawa Abu ta amince da hakan cikin yanayi na girmamawa.
Liman ne kaxai zaune a kan kujera, sauran duka a qasa suke har da Abu suna sauraron shi
bayan an gama gaisawar.
“Ki yi haquri, ki yi haquri da duk abin da ya yi, mu yi ta addu’a muna roqon Ubangiji ya shirya
mana su. Ai abin da ya saura tsakaninmu dasu kenan a yanzu, don haka kar ki tafi mishi da
matarshi na roqi wannan alfarmar ina fata za ki yi min ita”.
Abu ta gyaxa kai nuna alamar za ta yi tare da faxin “To Allah gafarta malam Ubangiji ya yiwa
zuriyarta albarka, ya kuma sa ta gama da duniya lafiya”.
Aka ce “Amin”. Sai ya yi tambayar cewa, “Ina yarinyar take?” Abida ta yi maza ta miqe ta
shiga ciki ta fito tare da Saddiqa, ta zo ta durqusa ta gaishe shi ya amsa tare da sa mata
albarka.
Da aka sake nutsuwa sai ya kalli Abu cikin fara’a ya ce, “Kin kawo mishi alheri irin wannan
kuma ki ce za ki tafi da shi? Bar mishi ita ai tashi ce, Ubangiji zai daidaita tsakaninsu, mu dai mu
yi ta addu’a. in kinga ka dage a kan roqon abu, to kuwa Ubangiji ya yi nufin biya maka
buqatarka ne, in ba haka ba, ba ma zai baka ikon ka roqa ba”. Ta sake cewa, “Haka ne”. “Mu yi sallati ga manzon rahama”
Liman ya ba da umarni. Nan da nan aka shiga yi, liman ya yi addu’o’i ga ma’auratan dama
sauran