Showing 3001 words to 6000 words out of 17955 words
Chapter 2 - Azumin Ilu Book Compelet By Maryam Muhammad Hassan
ledar pure water hakora ko tunanin addua baiyi saita
abinda zaisa ma cikin shi .....basiru ne ya rike hannun ...mutumen a taimaka ayi addua tukun ...
An kwala kiran sallah ...da sauri ILU ya hau addua bai gama wata wata ke zuwa ....ya Riga
kowa FASA ruwa zuka biyu yayi ma ledar ya shanye... Ajiyar zuciya ya saki sannan ya dakko
wata ledar zai FASA... Basiru ya katse sa...
Kai ILU saika cika cikin da ruwa ka rasa inda zakasa abinci ...ina ba dai cikin ILU ba
..Ai nan da kake gani basiru komai da isashen wurinsa a cikin nan nawa ....
Basiru bai kara cemasa komai ba ya kyaleshi ya shanye ruwan kafin sannan ya tamne kosan
daya dakko guda goma Dan ball I ya na basiru ......
Ana kammala sallah ILU ne na farkon mikewa yana fadin... Nidai malam nayi gaba saika taho
kunsan Allah ma yace a gaggauta buda baki ....shiru malam yayi tunda aka dauki AZUMIN baiji
ILU yace Allah yace ba sai yanzu da yake maganar ci CE is... Girgiza kai kawai yayi yaci gaba
da adduar sa .... Mutane kam dariya suka hauyi kasa kasa cike da kaunar ILU....
Yana fita ya sheka da gudu yana fadin ....iya gani nan azubamin koko cikin kwanon shan ruwa
....iya gani nan ....
Asukwane ya isa gidan saura kadan yayi kwllo da bokitin kokon ....azabure iya ta dubeshi ..lfy
ILU waya biyoka ...
Yunwa ta biyo ni kinsan tun dazu take bina ....ya fada tare da nufar kayan da yaga an shirya
masa gefe... Dama jikin iya har rawa yakeyi ta sallameshi kafin ya iso....
Zaunawa yayi tare da bude kwanon kosai ganin shi yayi himili dariya yayi yasan cewa da kason
malam aka hada masa ...kai iya Allah ya biyaki da ana samun tsaffi irinki da bayin Allah irinmu
sun more ...,
Itadai iya batace komai ba tasan anjima kadan zaa amshe yabon.... Bibbiyu yake tura kosan
yana hadawa da koko ana haka malam ya shigo da kwano a hannu.,..
*muje zuwa*
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*
*AZUMIN ILU*
*peg 5*
*MAMAN MAMY CE*.....�
Nace Ku huta fansí ½í¸�
*wannan peg nakune masoyan ILU acici mai cikin Zane*í ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£
Hakuri ta hau bashi ....na tuba ILU bazan sake ba... Ganin yadda ta tsorata yasa ya wuce
abinsa yana masifa kamar shi kadai ke azumi kauyen ......
Misalin 6 na yamma ya fito sai dukewa kasa yake yana dafe cikin shi idanuwa sunyi jajir dasu
....malam ya hango ya Debi uban kosai aroba zai fita rabawa almajirai...
Da gudu ILU ya isa gaban shi ya riko robar kosan yana maida numfashi .....
Haba malam ya mu bamu koshi ba zaa kaiwa na waje kosan ya kalla ya kuma kalli sauran
Wanda iya ke toyawa ....koni kadai zan iya cinye wannan kosan ban koshi ba shine kuma sai
ahau rarraba dashi.....
Murmushi malam yayi ...haba ilun malam Wanda ka bada shine naka... Wanda kaci Masai
zaije.... Yanzu kai anaka haukan ko barinka mukayi da kosan nan duka zaka iya cinye shi?????
Wllh tsab zan cinye shi har in nemi kari ...kuma da kace Wanda naci Masai zaya Ai nan ma
wata sadakar nayi ma tsutsotsin dake cikin Masan tunda su zasu cinye kashin da nayi ...don
Allah malam kayi hakuri kabar mana kosan mu in zan bar kosai guda yayi kwantai Allah ya tsine
man ......
Dariya malam yayi ka fahimceni ILU ita sadaka ba lallai sai ka wadatu ba zaka bayar ....a
musulunce anfi so ka bayar da abinda kafiso to Allah zai Baka lada sosai ....ka bada kadan
Allah ya baka Wanda ya fishi ..sadaka maganin talauci duk mai sadaka Allah bazai taba barin
shi cikin talauci ba zakaga da ya bayar Allah zai mayar masa da Wanda ya fishi sannan ga
lada.. Bare cikin wannan watan mai RAHAMA .....ILU ka bari abada sadakar nan ni zan hada
maka da nawa kason saika cinye ni nasha koko...
Sakin robar ILU yayi yana turo baki.... Abasu amma Allah da kasonka zan hada inaji ina gani
bazaa kware niba .....murmushi malam yayi ya Ciro nera hamsin aljihunsa karbi wannan maza
tashar alu ga kankara can ankawo ka siyo mana mu jika musha....
A wahalce ILU ya karbi kudin ya fita yana rangaji ..malam yabi bayansa da robar kosan da zai
rabama yara ....saida ya tsaya ya gama Harar almajiran sannan ya wuce tare da fadin
munafukan banza ......
Tun daga nesa ya hango Layin da ke akwai can ya hango basiru da mudi abokan sa nata bin
layi ...dariyar mugunta yayi duk da uwar yunwar dake kwalkwalarsa .....
Can ya zagaya bayan mai sayar da kankara ya fara rada masa ....sannu da aiki bawan Allah
dama maigarine ya aiko ni abashi kankara ....dubanshi mai saida kankara yayi ....yaga ILU yaci
magani kamar bashi ba ....ba musu ya karbi kudin ya bashi kankara ukku harda kyautar daya
gudu kenan....
ILU na dariya ya daga ma su basiru hannu yayi tafiyar shi .....
Lokacin daya isah har sun gama komai suna zaune sunata laximi ...mika masu yayi yai kwance
kasa yana fadin... Astagafirrillah da karfin gaske.. Malam ne ya dubeshi ILU kayi cikin zuciya
mana...
Aa malam bari inyi afili kunfi sanin halin da Nike ciki na yunwa....
í ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*
*AZUMIN ILU*
*peg 7*
*MAMAN MAMY CE*.....�
Nace Ku huta í ½í¸†
Saida malam ya gara zama ...sannan Iya tayi mashi barka da shan ruwa asabe ma tayi mashi
banda ILU ko kala baice ma malam ba sai zubawa uwar hanji yakeyi ......
ILU barka da shan ruwa ...malam ya fada cike da zolaya dai dai lokacin daya kai kofin koko
bakin shi .....a haba malam duka yaushe nasha ruwan bare afarayiman barka tukunna dai...ILU
ya fada yana kara dagwalo yaji ga kosai.....
Wasa wasa ILU ya kasa cinye Rabin kosan nan... Duk hadamarshi saiga ila na zare idanu gashi
daya motsa sai cikin ya bada kululu alamar ruwa ya cika cikin...bare kunsan azumi Nada haka
sai kaga kamar zaka Iya cinye Abu amma sai ka kasa
Malam yana kallon shi yanaso yayi dariya amma yaki yarda ta fito ....
Wai Iya kodai AZUMIN nan da nayi an rage min fadin cikina ne ...duka dubi Dan kosan da naci
da koko n da nasha amma naji cikina ba sauran wuri gashi banci abinci ba ......
Dariya Iya tayi ...wa zai rage maka fadin ciki ILU... Kawai daga yin azumi sai ciki ya ragu ...uhm
dama haka azumi yake sai kaita hadama amma abinda zakaci ba wani bane .....
Ikon Allah ILU ya fada yana satar kallon malam dake tamnar naman kaji Ashe sune a kwano ....
Tuni miyan ILU ya tsinke ..dubarace ta fado masa da sauri ya dauki kwanon kosan ya isa gaban
malam ya dukar da kai kasa ...
Barka da xshan ruwa Babana.... Kasan soyayya ta da da uba bazan Iya cinye kosan nan da
kason ka ba dama wasa Nike ma Iya ...Itakuma ta hada min da naka ..INA wane ni ...tuba Nike
dattijo mai ran karfe .....
Wllh malam karka kulashi ..wayo ne dashi karya yake.. Ka tsare shi ya cinye shi tunda shi yace
yaji ya gani ....asabe ta fada tana ma ILU dariya kasa kasa....
Kai kai wai asabe meyasa ke Yar bakin cikina CE duk gidannan kin tsani kiga INA warwasawa
...yinin yau INA lura dake kina min dariya to wllh ki shiga hankalinki dani .......
Ya isa haka malam ya dakatar dashi... Naji ni yanzu na koshi da kosai kaje ka ajiye anjima kaci
naci guda biyu wurin salame ya isheni... Amma daka hana abada sadaqa da duk ina zaka kaishi
...malam ya fada tare da yagar naman kaza....
Kuttt! ILU ya hade miyau ...kai dai bari malam Ai gobe in zaka bada sadakar aba harda kaji
..ILU ya fada yana kallon naman kaza yana murmushin dole ....
Malam baisan sadda dariya ta kubuce masa ba... Duk yagama dago ILU... Kara cirar naman
yayi ya mika masa kwanon ...ungo anshi ka diba ka basu sauran.....
Jiki na rawa ILU ya karba ya mike tsaye tare da fadin godiya muke ya malam... Saida ya yagi
kafcececiyar tsoka sannan ya dubi asabe.....
Wllh asabe yau sai da naga kana nan malaikun mutuwa da manyan nagani da tuni na mutu....
Uhm ni ina ruwana koma waka gani ...nidai ka bamu kason mu sai kaci gaba da bamu labarin
......
Kash! Asabe kin cika kwadayi ki rage wllh ....wata tsokar ya kara yagowa ...asabe! Ya fada da
karfi . .yau anyi rana yau naji ki shirya kamar ma banda makogwaro naji.... Oh! Ni salame.. Iya
ta fada tana kallon ILU ...
Ai yi hakuri Iya karbi kason ki.. Kafafuwa ya miko mata ...taki karba tacigaba da hara rarsa
..ungo mana Iya abinda yasa na baki saboda na taba mafarki ...ance in tsaffi mata nacin kafar
kaza to kafafuwansu za suyi kwari sosai ...kinsan ita kaza akwai kwarin kafa ...bare ke dazu da
kina aiki kina dingisa su ji nayi kamar insa hama in bigesu kowa ya huta.....
Ai da kasa hammar ka dai daita minsu Iya ta fada tana dariya tare da amsar kafafun tasan
karamin aikinsa ne ya hanasu duka.....
Ke kuma asabe ungo kai.. Ya mika mata kan kazar ...saboda na lura irin kanku daya da kaza
...kinga kin kara hankali ma ...wani dogon tsaki asabe taja wllh banci ...
Alhamdulillah ....shiyasa kike birgeni asabe biya ...komawa yayi zauna yaci gaba daci...
Asukwane asabe ta warci irin bayan nan ta ruga daki ta turo kofa ....
Dariya ILU yayi haba yarinya bashi kikaci ...Iya kau da malam sai dariya suke tsokar dake
hannun malam yaba Iya ta kara...
Kiran sallar ishai aka hau kira... Malam ne ya dubi ILU tashi kayi alwalla mu tafi masallaci.....
*Maman MAMY CE*
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*
*AZUMIN ILU*
*peg 8*
*MAMAN MAMY*.....�
To malam ILU ya fada tare da yin wata mika ta mussamman... Iya ga kosai na nan a ajemin
saura ki badashi sadaqa nasanki da tausayin Dan almajiri ....wa ni na isa in taba abinci ILU
...iya ta fada tana murmushi ....
Ahayye sama duniya tayi dadi!!! Haba ina amfanin yunwa da zan ganta ido da ido ...saina kashe
ta ..koni ko ita wllh iya....
Har malam zaiyi magana sukaji ankwada sallama kofar gida... ILU fito mu tafi massalaci
..muryar basiru yaji daga kofar gida...
To basirun inna mai yan kunnuwa gani nan.... Lol! Wai ILU yaushe zaka daina radawa mutane
suna ne ...iya ta fada..
Uhm kyaleshi yayi Ai ansha ruwa da dazu ne ko bakin shi bakiji sai idanu.... Aa malam wllh bani
kadai nasha wahalar azumi ba ..tsaya kaji..sai kuma ya fara dariya ..ina ganin maigari dazu zai
shiga gida saura kadan ya bige kai da alama bai ganin kofar gidan saboda yunwa í ½í¸†í ½í¸†
Dif wutarsu ta dauke mussaman malam da dariya ke cinsa ..ILU ba karamin sha kiyi bane...
Saida ya gama kwasar dariyar sa sannan yace ....shi kuma liman dazu ana sallar azahar sau
biyu karanta bisimilla ...nan ma wata dariya r ya saki .....
Ita kuma iya ...wani Dan karamin icce malam ya fizgo ya kaimashi bugu ya kauce ..yayi waje
yana fadin muje basiru tun kafin tsohon nan ya kaini kasa....
Aida ka tsaya Dana koya maka hankali ...Ai dama nasan da yagama shsrrance yan waje zai
dawo kanmu ...yana gamawa dake zai dawo kaina tunda shi jairine ....Ai ni garama ayita
AZUMIN mun samu saukin ka ....
Yar dariya iya tayi ..uhm Allah dai ya kimtsa ILU v..kullum shirmensa gaba yake yi ....
Alwalla malam yayi yabi bayansu zuwa masallaci. .....
ILU fa ya mike duk ya ishi mutanan kauyen da tsokana ba Wanda yake ragamawa ba
babba...koda aka gama sallah lulawa sukayi cikin kauyen daukar magana shida abokan sa ..bai
dawo gidan ba sai wurin goma na dare ...
Sanda ta hauyi yadda kar malam yaji sadda ya dawo ....iya CE ta fito fi tsari saboda har sunyi
bacci ..inwa tagani tsaye cikin razsna tasaki butar tare da fadin auzubillahi waye nan....
Da sauri ILU ya fito karta tona masa asiri ..nine iya ..kai kudai mata Allah yayi maku tsoro wllh
kin kuma san ko barawo ne ko kallon arzuki baki Ashe shi ba....
Haka ya ratsata ya wuce yana mita saura inji zancen wurin malam wllh saina ballswa tunkiyarki
kafa... Aa bazai ji ba ni na isa iya ta fada da karfi... Saboda tasan in ILU yace zaiyi Abu to sai ya
aikata shi ....
Saida ya cinye sauran kosan da tuwo mai yawan gaske sannan ya kors da koko ya kwanta ....
Tun da suka tashi sahur asabe ke faman tada ILU amma yaki tashi saima gyara kwanciya yake
....
Malam ne yace ..kyaleshi asabe jekiyi sahur dinki.. Ai gobe ya sani yayi csahur din ma ya aka
kare bare baiyi ba ...
Asabe kam komawa tayi taci gaba da sahur dinta ...iyace ta mike Umm bari inkara tada shi ni
kadai nasan balain da zai mana gobe ....
Ki kyaleshi ya Dade baiyi ba laifin wa ..malam ya dakatar da ita.. Mikewa tayi aa malam nasan
fitinar ILU kamar yunwar cikina bari dai in gwada .....
Iya ta tada ILU ta tadashi amma ILU yayi kunnen uwar shegu da iya haka ta hakura ta dawo taci
gaba dacin abincin ta kafin lokaci ya kure .....
Haka dai suka gama suka kwanta ba tare da ILU ya tashi sahur ba..
*muje zuwa dai fans.. Kunsan akwai bidiri ILU zai tashi da dorere*í ½í¸†
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*
*AZUMIN ILU*
*peg 9*
*MAMAN MAMY*..�
Nace Ku hutaí ½í±�í ¼í¿»
*wannan peg nakine zuzun Alkhairi ...Allah ya raya mana hafeez da hanan*í ¼í¼¹í ¼í¼¹
A firgice ILU ya tashi ji yayi kamar ana kiran sallah.... Da gudu ya nufi dakin Iya yana kwalamata
kira... Iya Ku tashi wllh lokaci ya kusayi Ku tashi muyi sahur.. Gani yayi zuwama dakin Iya bata
lokacine sai kawai ya wuce kicin da makekiyar rigarsa yana fadin....
Nidai duk Wanda bai tashi ba Matsalar shi CE ..nidai innayi sahur kowa ma ya gane sai ayita
tadaku kunaji kuyi banza da mutane ...
Yana fitowa da kwanon abinci malam na fitowa dama sallah yake yanajin duk abinda ILU ke
fadi.... Kardai ka kuskura ka ci abincin nan saboda lokaci yayi ...
Sakin kwanon ILU yayi woyyo Allah na shiga ukku ni ILU yanzu shine zaaki tadani wayyo
Allah... Saiga ILU na ruwan hawaye ....
Iya CE ta fito da hijab jikinta ...haba ILU sai kace ba namiji ba don bakayi sahur ba sai ka
ishemu da ihu sai kace Wanda ya rasa iyayensa ...
Kyaleshi yayi salame wane irin tadine ba a yi masa ba yaki tashi ...kuma dorere ba fashi akan
shi tunda ba kanshi farau ba....
Aa malam ba kowane tadi aka yimin ba naki tashi.. Tsakani da Allah an watsa min ruwa anga
ban tashi ba ko anturamin lomar abinci anga ban tashi ba... ILU ya fada cikin muryar kuka ...ni
banma ga alamun anwani tadani naki tashi ba... Kawai dai kunaso yunwa ta kashe nine shiyasa
...
Eh yunwar ta kashe ka .....Ai wurin
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*
*AZUMIN ILU*
*peg 10*
*MAMAN MAMY*..�
*fans Ku yafeni ganin peg 9 kadan wllh bisa kuskure ya tsaya haka plsss ayi hakuri*
Ai wurin ibada ka mutu... Kaga maza kaje kayi alwalla mu tafi massalaci kar mu rasa sallah
...wucewa ILU yayi yana fadin shikenan dai an cuceni wllh ancuce ni sai Allah ya sakamin ...
Salame dake gefe ..dariya tahauyi kasa kasa .....ahaka yayi alwallar suka tafi massalaci sai
gunguni yake shidai malam bai kara CE mashi kanzil ba dama yasan zaa Rina ansaci zanen
mahaukaciya ....
Bayan an fito salla h ne aka tsaya ana gaggaisawa liman ne ya lura da yanayin ILU ....aa
mutumen lafiya na ganka haka... Daure fuska ILU yayi tare da dauke kai can sama baida
alamar ba liman amsa... Malam ne yayi murmushi ..Ai liman yau mutumen ka baiyi sahur ba
shine yake wannan tubukurin .. Saiga liman da maigari na dariya harda dukewa jin cewa yau
ILU baiyi sahur ba sunsan cewa akwai bidiri kenan ...
ILU kau kara daure fuska yayi basu San cewa dariyar nan ta bata masa rai ba....liman ne ya
dafashi haba namijin duniya ka nuna mana kai jarumi ne ba raggo ba ...duk da dai gaskiya
bantaba yin dorere ba kusan shekara biyu kenan rabon da inyi dorere bansan wahalar shi ba
amma nasan namijin kwarai lfy Lau zaiyi shi ba irinka ba ILU ..yana magana suna dariya da
maigari malam ma murmushi kawai yakeyi ...