Showing 12001 words to 15000 words out of 17955 words
Chapter 5 - Azumin Ilu Book Compelet By Maryam Muhammad Hassan
ne sukaji yana babbaka dariya harda tafa hannuwa ...kallon shi sukai gaba daya lfy
malam??
Uhm lallai sannunku ...ai kun shiga tarkon ILU Ashe Ku har yanzu Baku gama sanin waye ILU
ba ...in banda abinku wake cin kudin ILU a kauyen nan bare har ya saya maku lemu mai sanyi
...
Shiru malam yayi saboda dariyar data kubce masa ...
Amma dai anyi jairin yaro wurin nan ..haba nidai nayi mamakin irin bacci n da nayi kuma na
Dade INA tunanin kyautar da ILU yayi man ban sake shiga mamaki ba said a naji maigari yace
shima ankai masa.. Oh! ILU ILU
Liman ya fada cike da takaicin abinda ILU yayi masa daga baya kuma sai dariya ta kubce masa
tunowa da yadda sukayi da ILU da irin ladabin da yayi masa Wanda baisanshi dashi ba ....
Shi kanshi maigari dariyar yayi ..kaga jairin yaro yasa gaba daya na fita hayyacina saboda
yunwa... Kila gara ni da liman .. Shifa liman takalman kafarsa daban daban ne saboda tsabar jin
AZUMIN ...
Tuni liman ya turbune fuska wane irin gara kai ...maigari tun daga gida fa ka taho da buta
ahannu da alama ba kasan ka taho da ita ba ....
Dariya malam yayi ...nidai yanzu don Allah kuyi hakuri ...ni kaina Dana haifi ILU bai ragamin ba
in shegantakarsa ta motsa baiji bai gani ....
Aa ba komai malam ...to amma me yasa yayi mana haka ne ...liman ya fada yana shafe zufar
dake keto masa ...
Uhm tun da kukayi masa dariyar dorere shine abin ya bashi haushi ni nasani yakace kuma sai
kunyi ...ai arayuwar ILU ba abinda ya tsana irin kaGanshi cikin wani hali kayi dariya saboda
haka saiku kiyaye....
Ikon Allah ...maigari ya fada.. Ba komai gobe ka turomin ilun da abokansa zan zartar masu da
hukunci saboda in baa hukuntashi abinda zai rikayi kauyennan ba karami bane ....
Da dai ka barshi kawai ...liman ya fada saboda shi ya tsorata da lamarin ILU ...
Shidai malam baice kar a hukunta ILU ba...saboda ana iya ganin don yana dansa...
Amma yasan bazasu iya yimasa komai ba ...saboda ILU ya ishi kowa Riga da wando...
Ahaka sukayi ban kwana kowa ya nufi gidan sa ...
Malam na zuwa gida ya hau yima iya bayan I tayi dariya sosai suna cikin hakane ILU ya shigo
yana fadin
WO! Ni ilu ilun malam wayace dani bani ba dara bataci gida ba .....
Malam ne ya dubeshi yana murmushi... To albishirinka jairin malam dara taci gidaje bama gida
ba...
*hhhhhhh Muje zuwa labarin ILU donjin hukunci da maigari zai yanke masa anya maigari bai
tabowa kansa ba*
*ni din daice maman mamy Nike cewa kunsha ruwa lfy*
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*
*AZUMIN ILU*
*peg 18*
*MAMAN MAMY*.....✍
*RAMADAN KAREEM*
*Allah ka yafemana albarkacin wannan wata mai albarka*
```barkanku da shan ruwa masoyan ILU ```
Cikeda mamaki ILU ya dubi malam ...bangane ba ya malam ILU ya fada yana gyara bajejiyar
rigar dake jikinshi ....
Eh ai bazaka gane ba... Yanzu kai ILU ka kyauta kenan kasa bay in Allah dorere ba gaira babu
dalili....wllh ILU kazo ka natsu kullum shekaru na gaba amma ba hankali ....
Yar dariya ILU yayi ..kayi hakuri ya malam ..ILU zaiyi hankali nan bada dadewa ba ...kuma
daman ai hakane ya kamata da mai dariyar mugun ta bakaga da liman namin dariya jiya ba har
wani dukewa yake ...
Kai ar jairi... Malam ya katse masa tunani ..towai ma me kasa masu a lemun ...
Dan kwanbare kafada ILU yayi ba wani Abu bane ya malam Dan maganin bacci ne irin mai
nauyin nan ...sai kuma ya dubi iya ...wllh iya yau liman yana jin jiki Ashe haka limamai ke
rudewa sukaji yunwa ...sai kuma ya babbake da dariya ...
Takalmin dake kafar malam ya cire ya jefe shi dashi ya kauce yana fadin tuba Nike ya malam..
Ajiyar zuciya malam ya saki ..ai gashi nan kajama kanka da abokanka gobe maigari na Neman
ku ya zartar maku da hukunci dai dai da laifinku kuma wllh ban bashi hakuri ba kuma kasan
halin maigari Allah dai ya kyauta ...daga haka maigari bai kara cewa komai ba ya mike ya shige
dakinshi yana murmushi yasan ILU da tsoro ....
Ragwaf ILU ya zauna yana yake mai kama da dariya dariya ...uhm wllh iya maigari ya kuskura
ya sani kiwon awaki cikin AZUMIN nan zaisha mamaki nasan karshen hukuncinsa kenan ...
Dariya iya tayi ..a to ai in mutum baaiji bari ba yaji hoho duk kuma Wanda baiyi sharar masallaci
ba yayi ta kasuwa ...ai gara ya turaka kiwon dani nace kajemin kiwon bazaka jeba ....
Mikewa ILU yayi yana jujjuya wa dubi nifa iya babban yaro dani duk kauyen nan ba mai
kyawuna ..sai ace in rika yin kiwo ...ai iya dani mai kudi ne wllh zaaga takama da iko ...
Hararsa iya tayi da wannan bajejiyar rigar taka zakayi iko da takamar ji cikin ka wane mai kudi
zai zauna yayi katon ciki irin naka ....um ni kaga bari in tashi inyi sabgar gabana da wannan
sokanar taka ..wai kudi ko yaushe zai yi kudin ..
Yar dariya...ILU yayi ya dubi iya data tashi ta nufi kicin tana dariya... Uhm insha Allah sai nayi
kudi iya nasa an gyara maki kafafuwan nan naki da kike dungurawa ya kara babbakewa da
dariya ....
ILU fa lamarin yayi masa kyau mussaman suke labe bayan gidan liman suna kwasar dariya
saboda kofar gida ya baje yana dafe ciki kamar ba namiji ba ...
Daga karshe liman bai kara komawa massalaci ba sai gaf da zaa kira sallar magariba ya fita
yayi zaune bakin massalaci yana Jan cazbaha gsanin ban tausayi .....
Bayan an sha ruwa ne liman ya tsare ILU sai nasiha yake masa kamar zaiyi kuka... ILU kam sai
to yake
cewa in ta shiga tanan ta fita tanan ba alamun nasihar na shiga kunnuwansa baima gama
nasihar ba ILU ya mike yana fadin ...ngd sosai ya liman Allah ya biya ..bai jira amsar dazai
bashi ba ya kara gaba yana baje rigarsa..
Girgiza kai kawai liman yayi tare da fadin Allah ya shirya mana ILU ...
*nima dai nace ameeen*
Washegari ILU ankusa ma kara ...saiga iya da asabe da ILU na cin abinci kwano guda saboda
basu ma tsaya wani kasa wa ba saboda karancin lokaci ...
Washegari da wuri maigari ya aiko kiran ILU da abokansa ....
Fito wa ILU yayi yana dariya to iya mu zamu fita Allah dai ya fidda ai ga rogo..
Dariya asabe tasa ...Allah yasa kar ta fita ai n ..
Dariya iya tasan ya harda dukewa.. Harara ILU ya zabgawa asabe ..ai asabe tuni na gano baki
kaunata ...yayi waje yana fadin Muje ai maigarin ba Allah bane ...
Har ya kusa fita ya dawo ya dauki ashana ...ya dubi iya ki dakamana tasshi mai dadi ...
Cikeda mamaki iya ta dubeshi me zakayi da ashana da tasshi ...
Kila maigari zai soye ko ..asabe ta fada tana dariya... Binta yayi aguje ta shige daki tare da
banko kofar...
Fita yayi yana haki... Zaki sani innadawo iya na tafi ...
To ILU Allah ya tsare ....
Said a ya biya ma basiru da mudi sannan suka dau hanyar gidan maigari ..basiru na fadin
alkuran ba ruwana...
*Muje dai zuwa labarin ILU*
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*
*AZUMIN ILU*
*peg 20*
*MAMAN MAMY*......✍
*ba dai zan gajiya ba da godewa masoya ako INA ma suke tabbas ILU ya Tara masoya to Allah
yayima masoyan sa albarka ameeen*
Wata uwar harara ILU ya rafkawa basiru ....dad in a dakai gajen hakuri Allah dai ya kaimu
goben ka ba idanuwan ka abinci ...ILU ya fada yana yana kara daga wata katuwar kaza mai
manyan cinyoyi ....kai Allah yayi halitta wurin nan jar uba mudi kaga kaza kamar wani Dan
akuya .......
Dariya mudi yasa hadda buga kafa ...kai wllh naji dadin kiwon nan amma ILU gobe ma zamuci
ko???yar dariya ILU yayi ah sosai mana mudi ai naga maka gobe akuya zamuci mu ....ai mun
dosa cin dadi har nan da sati biyu duk wani gefe na cikina daya lomake saiya taso .....
Hhhhhhh basiru yayi dariya to taya zamu yi sati muna cin kaji bayan maigari kwana ukku
yabamu hukuncin sa ......ILU ne ya dubeshi I do cikin I do ai a bsyaninsa yace duk Wanda bai
zo ba zai kara masa kwana ukku to jibi mu dukanmu bazamu zobs kunga kenan zai kara mana
kwana kan cin kaji ....kai dai wllh kanka baija basiru ....
Eh din naji baija amma ni tsoro na daya muci naman maigari cikin azumi ai haram mukaci
.....injiwa ai zamu rokeshi gafara bakiji me nace dazu ba ..kai basiru cin kajin nan fa ba dole don
ni nan da kake ganina sai incinyesu duka banji komai ba bare dama anrabi da haduwa yaushe
rabon da inci kaji mudi ya dubi mudi cdake gashin nama yana share zufa...
Kai rabu dashi ILU nidai wllh ci zanyi yana gani mai gari ko zakkar kajin nan bai bayar wa
..kuma basiru dake fadin haka baifi kowa hadamar nama ba ko ka mance lokacin da muna yara
basiru fa don tsananin kwadayi mai tsiren bakin Santa yake ma wanke wanke in yayi ya
yanmasa tsoka guda ....
Dariya suka sa gaba daya hadda basirun yana fadin to naji aiba filin tone tone bane ......
Ahaka suka gashe kaji Tass! Suka sakasu cikin Leda mai nata diga sai kuwa kamshi suke duk
da bawani magi akasa ba sai kamshin suyar .....
Basu dawo gida ba sai gab da azhar anma fara kiraye kirayen sallah ...mudi aka ba rikon kaji su
kuma suka tsaya hado kawunan awakai kaf ...
Said a suka sakasu gidan su sannan suka nufi hanyar fita ILU ne ya dubi bangaren kaji
....sannunku namomi sai goben kuma soyayya kuda ILU har nan da sati ...ILU ya fada yana
gyara katuwar rigarsa ta gado saboda yawan sata da ILU keyi har ansanshi da ita da
anhangoshi zaace ga ilun malam can kosu basiru wani lokacin da sunganshi da ita zasu fara
fadin yar gado ta ILU Riga daya tamkar da dubu .....
Suna fito wa aka tsaya shawarar yadda zaakaiwa maigari makulli saboda kajin dake hannun su
.....ILU ne ya karbi makullan kujirani bari inkai masa ....
Zaune ya iske maigari yana alwalla azahar yana ganin ILU ya hau was he baki .....sannu ya
maigari inji ILU makullin ya mika masa gashi mun dawo ....
Karba yayi yawwah ILU sannunku kunsha kiwo Allah dai ya bada lada ...awakan sun dai koshi
ko?? Yar hararssa ILU yayi a fake eh kwarai kau sun koshi sosai saika gansu ...
To shi kenan jeka sai kuma goben Ku dawo ina sauran ne... Tafiya ILU yayi tare da fadin suna
waje ..kafin mai gari ya kara wata magana yayi waje yana gyara tashi da kwakwar dake kanshi
...
Dai daya suka raba kajin maana kowa ya tashi da dakwale guda guda ...mudi sai was he baki
ake shi kanshi basirun murmyshin farin ciki kawai yake to bare uban gayya ai kunsan basai
nace komai ba ...
Tun daga nesa su iya suka fara jin kirarin da ILU keyi ...ilun malam wane mutum bare buzunsa
munga jiya munga yau gobe ma in Allah yayi gani zamuyi .....iya CE ta dubi asabe anya ILU na
azumi ji fa yadda yake daga murya ..
Dariya asabe tayi uhum tasamu kenan duk in kikaji wannan kirarin
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *BRRLIANT WRITER'S ASSOCIATION*⚜
*AZUMIN ILU*
*peg 21*
*MAMAN MAMY*.....✍
```allah yasa mudace duniya da lahira Allah kasa muna cikin intattun bayi```
*barkanku da shan ruwa masoyan ILU
Nasan dai da yawa sun hadewa kajin maigari miyau duk da dai kunsan ILU da
Rowa
Gaskiya na yarda asabe ta samun iya ta fada tana kara kallon kofa... Har asabe zatayi magana
ILU ya shigo buguzun buguzun tsayawa yayi yana masu murmyshin nan nasa..... Sai kuma yayi
wucewarsa yana fadin duk Wanda ya zauna ai yaga zama ....
Iya CE ta dubi ledar dake hannun ILU sai mai ke diga.... Aa ILU andawo kiwon toya gajiya
nasan dai baa rasa gajiya ba......
Dawowa yayi ya zauna bisa kujera yar zukunne ...bari kadai iya ai dawa tayi nama kiwo
alhamdulilah hukuncin nan yayi min dadi saboda in zaayi wata ina zuwa kiwon nan banjin komai
ya fada yana kara daga ledar dake hannun shi .....
Asabe ce ta dubeshi sosai ...uhm ILU kenan ai nasan ruwa baya tsami banza to meye kasamo
acikin ledar nan ....
Yawwah tayani gani asabe nima abinda nikeson tambaya kenan kika rigani iya ta fada tana kara
leka ledar ....
Mikewa tsaye ILU yayi yana fadin shi kenan iya asabe ta koyamaki ganin kwaf yanzu daga
kuganni da Leda sai akama a like sai ansan ko meye ciki eh amma da ya malam ne ya shigo da
Leda ko kwano bamai cewa meye ciki saini da aka raina ...
Dariya iya tasa oh! Ni salame na godewa Allah to ILU kaida malam daya ne .....hhhhhhh haka
yake gani tunda ya girma asabe ta fada tana to she baki ....
Harara ya galla mata oho kodai me zakice sai dai kice wannan da kike gani ya daga ledar
naman... Kazar daji CE gasassa kuma kwalelenku karma kusa rai kunji na fada maku .....
Kazar daji ...iya ta maimaita nidai tunda Nike ban taba ganin ko jin wani yace kazar daji ba sai
yau ...ILU nuna min ita in gani....
Barta basai kin gani ba tunda baki Santa ba shi kenan Ku dama tsaffi haka kuke koni watarana
cewa zakiyi baki sanni ba ....ya nufi dakinsa yana fadin saura kuce Baku dakamin yajin da nace
ba wllh yau inhana ayi koko da kosai gidannan ya shige tare da banko kofa yadda zaaji dadin
boye kaza ....
Asabe CE ta dubi iya a firgice ...Allah dai yasa kin daka masa yajin kinsan halin ILU abinda ya
fada zai iya aikata shi ...wah! Ai tuni na daka shi ai ni nasan halin ILU kamar yunwar cikina ...
Dariya suka sa gaba daya asabe na fadin ILU balai ne amma ni ban yarda da ledar can ba
dagani akwai wani ciki.... Yi shirunki iya ta katse ta intayi wari munji sanya masa I do kawai...
Shiru sukayi ganin ya fito yanata kakaniyar rufe kofa ...
Saida ya rufe yabi da tsumma ya kulle sannan ya dawo ya dubi asabe ....saura ki bude min daki
wllh na lahira sai yafi ki jin dadi bare na lura kwannan haye min kike ke kin girma ko??
Ya fada yana girgiza kafa ..
Kaga ILU banson Neman fitina yama zaayi ina gani ta bude maka daki ...da wannan babatun
Naka ga ruwa can bayi nakai maka ka watsa kaji sanyi tun dazu nakai maka su ,...
Wuce wa yayi bay in yana fadin ato nidai na fadi duk Wanda ya bude dakin can yau ya budowa
kansa kema iya kijama bunsurunki kunne naga alamar yana yawan shigar min daki banna
rannan sauran tuwona ya cinye to yau ya bude min daki Allah saina targada shi tunda ni ba
abokin wasansa bane yawwah ....ya ida shigewa bayi wanka...
Asabe CE ta dubi iya yaufa ya karo wulakanci ji yadda yake wani cika yana batsewa sai kace
wani yace zai bude dakin in wani yaji saiya dauka buhun kudi ne ya aje ....
Kedai ba ruwanki ....dole yayi wannan fitinar ga azumi ga kiwo aini nayi tunanin abinda zaiyi ma
sai yafi haka iya ta fada tana kokarin tashi ...
Tunda ni fito wankan yake takalar fada ba Wanda ya biye masa dama yafi Jan asabe itakam
kwanciyarta tayi kamar mai bacci tana jinsa hadda fadin asabe in tana bacci wai minshari take
kamar bijimin sa ita kuma iya intana tafiya kamar ana koyawa yaro tata ....da daidai yaga ba
Wanda ya kula shi saiya yayi awallahr laasar ya fita yana fadin tumakan gidannan duk asabe ta
koya maku kilbibi ...
Yana fita suka hau dariya tare da fadin morewa ILU kenan in yana fitinarsa ai banza a kyaleshi
....
*bayan sallar magriba*
Can nesa dasu iya ILU yayi shimfida don karma wani yaga abinda ke cikin ledar a hankali yake
yagar abinsa yanaci ga tashhinsa gefe yana dangwalawa ....
Malam ne ya dubeshi aa wai yau ILU me aka samu ne ??
Bakomai ya malam kazar daji CEdazu. Da mukaje kiwo muka kama shine muka gasa ko
zakaci???
Aa ILU aci lfy kasan bandamu da irin wadanan abubuwan ba ...
Shi kenan ya kara afki ILU ya fada yana tura tsokar nama baki...
Aiba ya kara affki ba bazaka yanma su asabe ba ko kamanta I do guba inji malam...
Hmmmmm yanzu ina iya basu suci suce maka kamar kazar gida kasan su da. Santi shiyasa