Showing 15001 words to 18000 words out of 20649 words
Ta qarasa maganar tareda nuna Mamie da hannunta, baki ameerah ta
murgudawa zahra sannan tace an fada din ta qarasa maganar cike da tashin kunya,
Tunda ameerah ta fara zuba rashin kunyarta Mamie ke kallon ta, bata CE komaiba sema ja
baya datayi daga kusa da ita ta koma kan daya daga cikin kujerun falon, sun jima a dan
zaune sannan Mamie ta koma daki dan ta dakko wayarta a hanya suka hadu da Dady yana
shirin fitowa falon shima, murmushi yayiwa Mamie sannan ya wuce ta gefanta ya nufi falon, yna
shiga ya zauna a kan kujerar dake daukar mutum biyu, yana zama zahra ta sauka qasa tare
da yiwa mahaifin nata barka da fitowa,
Sosai Dady yaji dadin abinda zahra ta yi shiyasa yake sonta sbda baba daya yaransa idan ka
cire muzaffar a kyawawan halaye to se zahra ameerah kuwa yana zaune da alama ma bata da
niyar sauka daga kan kujerar.
Tsawa Dady ya dakawa ameerah da sauri ameerah ta sauka qasa sannan ta fashe da kuka
sbda tsoratar da tayi,
Ummah CE ta fara shigowa sannan Momy ta biyo bayanta se kuma fadilah dake bayan Momy
n, Ummah CE tayi qarfin halin yin sallama,
Kallo daya Dady Yayi musu sannan ya dauke kai, a daqile ya amsa sallamar, sosai suke kallon
falon sbda yanda ya hadu, koda wasa basu taba shigowa falon ba se yau, cike da masifa Momy
ta fara magana tacewa Ummah kin gani ko? Ai dama na fadamiki gashi nan ai kin gani wllh
dama na san tsugune bata qare ba, mun gudu ne bamu tsira ba da sauri Ummah ta dannewa
Momy baki, tace haba zuwaira me kikeyi haka sekace wata qaramar yarinya?
[8:54PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado頎巾笜_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 17*
Gaskia zuwaira baki kyauta ba, kuma gaskia ya kamata ki bawa alhaji haquri yanzunnan, ta
qarashe maganar tare da kanne mata ido daya.
Nan da nan Momy ta fahimci manufarta dan haka ta sunkuya ta bawa Dady haquri,
Be ko kalleta ba ya juyar da kansa yace mata ya wuce,
Guri suka samu suka zauna, sun dan jima a zaune sannan umma tace alhaji ka kira mu amma
har yanzu baka CE komai ba,
Shigowar Mamie ce ta sa umma hadiye maganar ta, da sallama Mamie ta qaraso falon kusa
da zahra ta zauna , da murmushi a fuskarta tace sannan ku ya gda ?
Ummace tayi carab tace lfy qalau ya hanya? Ta qarasa maganar tana hararar Mamie,
Da kulawa Mamie ta amsa mata tare da jefa mata tambayar ta same su lfy.
A taqaice suka bata amsar lfy,
Dady yana zaune a inda yke wayarsa ya dauka a gefen kujerar daya ke zaune , ya kira wayar
telho din dake dakin saukar baqinsa bugu daya muzaffar ya amsa, a taqaice Dady yace kazo
falon Mamien ka Ina son Zama daku gaba daya,
Be ce komaiba ya ajiye wayar
Moddibo dake zaune kan sallayar da suka idar da sallah, bece masa komai ba se kallon sa
kawai daya ke yi, jiki ba qwari muzaffar ya qaraso kusa da moddibo yace , baba wllh har ga
Allah ina jin tsoron muta nan nan!
Cike da rashin fahimta moddibo yace yaro ban fahimci maganar ka ba, tsoron me kake ji?
Muzaffar yace baba INA magana ne a kan mutanen Gidan nan, ina jin tsoron kada su sake
shirya min wani mugun abin!
Murmushi moddibo Yayi sannan yace yaro kaifa namiji ne dan haka ka daure ka zama jarumi,
kuma ka dage da addu'a haqiqa babu abinda yafi qarfin Allah dan haka kada ka bari tsoronsu
ya samu gurbi a cikin zuciyar ka, kaji yaro? Maza kaje kiran mahaifinka, Sam kada ka nuna
rauninka a gaban maqiyanka, Muzaffar yayi sannan Ya nufi qofar fita daga Falon,
Site din Mamie ya nufa , da sallama ya shiga Fallon da uban rawani kamar wani ba Sarake,
tunda ya shiga falon muta nan dakin suke kallon sa dik da cewa basu gane shi ba , ciki kuwa
harda Mamie, murmushi Dady Yayi sannan ya miqa hannayensa alamar yazo gare shi , da
sauri muzaffar ya nufi mahaifin nasa ya suka sake rungumar juna , umma CE tayi qarfin halin
cewa wai alhaji waye wannan din da kashigo dashi cikin gida har falo?
Ga kuma uban rawani kamar wani bafade!
Momyce ta qara da cewa inda duniyar nan ba gaskia ka jajibo mana shi baka tsoron yazo ya
cutar damu a gaba?
Itadai Mamie bata CE komaiba sema kallon su da take, ta Kali wannan ta kalli wannan,
Murmushi Dady Yayi sannan ya kalli Momy yace kin taba ganin inda da ya cutar da ubansa?
A taqaice tace yo alhaji nawa akayi?
A hasale yace idan kuwa kika ga da ya cutar da ubansa to wllh wannan dan ba dan halak
bane,
Ynan gama bata amsa yace zoka zauna Dana ,
Umma CE tace danka kuma alhaji ?
Kodai batan muzaffar yasa kanka ya fara kwancewa ne?
Ya zaka samo wani bafulatanin daji da uban rawani kace danka ne shi?
Da sauri Momy tace yauwa gaya masa dai maman zahra,
Murmushi Dady Yayi Wanda yake dauke da manufofi masu yawa, sannan yace, babu tabin
hankali balle a samu matsalar qwaqwalwa!
A yau da yamma cin nan lbri mafi dadi a duniya ya sameni,
Ba wani lbri bane illa labrin baiyanar gudan jini na wato Dana namiji tilo wato muzaffar!
Gaban Ummah da Momy ne Yayi mummunan faduwa, nan da nan gumi ya fara karyo musu dik
da sanyin Ac dake dakin hakan be hanasu fitar da zufa ba,
Kallo daya zaka yi musu ka fahimci suna cikin wani yanayi!
Momy CE tayi qarfin halin cewa to alhaji INA muzaffar din yake yanzu?
Bece mata komaiba se nuna mata shi da Yayi da yatsansa,
Cike da rashin fahimta Mamie tace abban muzaffar nifa ban fahimce Ku ba wai don Allah
meyake faruwa ne??
Sam Dady be boyewa Mamie komaiba tun dga batan shi muzaffar din har zuwa yanzu da Allah
ya baiyana shi, da sauri Mamie miqe daga inda take ta saukko qasa Inda muzaffar ke zaune,
ta Dora tafikan hannayenta a kan fiskarsa tana me zubar da hawaye tana kallonsa cike da
tsantsar so da qauna tace, haqiqa INA matiqar qaunarka Dana kuma dik duniyar nan dik
Wanda ze soka wllh a bayana yake muzaffar!
Dama abinda ya faru dakai kenan yasa kwana kin baya nake ji a jikina wani Abu ya faru da
gudan jini na?
Ashe shiyasa na rasa kwanciyar hankali? Ta qarasa maganar cikin kika me matiqar ban
tausayi!
Daqar ta tsagaita kukanta sannan tace INA matiqar sonka dana, idan wani abin ya sameka wllh
har abada zanyi Dana sani!
Cike da makirci umma tace ke kinga fa bawaifa fin mu sonsa kikayi ba! Kin wani sashi a gaba
se kuka kikewa muta ne, kafin kisanshi fa mumuka sanshi, tunda mu muka fara auren ubansa
kafin ke,
Da sauri Momy tace gaya mata dai zata yiwa mutane kini bibi wai ita matar uba,
Mamie batace komaiba se kika da take, muzaffar ma kukan yake yana me mamakin irin
qaunar da Mamie take masa !
Tabbas koda mahaifiyarsa CE irin son da zatai masa kenan,
Hawayen fiskarta ya fara goge mata da hannayensa,
Dik wannan abin Dady yana kallon su sannan yace dikkan Ku Ku dakata sbda wannan abin ba
shine mafita ba, yau kowa zeji abinda na Dade ina boyewa a gare Ku
Wata qila ya bku mamaki amma kuma Sam ba abin mamki bane
A cikin masu mama kin nasan harda kai muzaffar!
[8:55PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado頎巾笜_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 18*
Cike da rashin fahimta muzaffar ke kallon mahaifin nasa sedai bece komaiba,
Dady Yayi ajiyar zuciya sannan ya ci gaba da magana kamar haka
Haqiqa na boye muku wani al'amari a Iya zama na daku, ya nuna umma da Momy
Sannan ya cigaba da magana,
Na gwada Ku a baya ta hanyar kawo muku Dana muzaffar tin yana shekara daya a duniya na
raboshi da mahaifiyar sa na kawo muku shi,
Sbda na gwada tsoron Allah n Ku da kuma tausayin Ku,
Amma se kuka kasa riqeshi da gaskia, kuka dnga cutar da shi, abinda Baku sani ba shine
mahaifiyar muzaffar tananan a Raye bata mutu ba,
Cike da tashin hankali gami da fir gita muzaffar yake kallon mahaifin nasa yace, Dady kana
nufin kace min mahaifiyata tana nan da rai bata mutu ba?
Amma Dady meyasa ka rabani da mahaifiyata?
Meyasa ka zabi na rayu da wasu sabanin mahaifiyata?
Meyasa kace min mahaifiyata ta rasu? Pls Dady ka cireni a cikin rudanin Dana ke ciki don
Allah
Da rarrafe ya matsa gurin Mamie ya riqe hannayenta yace Mamiena don Allah ki cewa Dady
ya kaini gurin mahaifiyata na ganta koda so daya ne don Allah Mamie!
Ya qarasa maganar yana kuka sosai kamar wani qaramin yaro,
Da qyar Mamie ta saita kanta sannan tace ka kwantar da hankalin ka yarona baka da wata
Uwar da ta wuce ni kaji ? Nice mahaifiyarka ba wata ba,
Momy CE tace haba malama kinga ki dakata ki barmu da almarar data muke ciki, ya za'ai kizo
kisamu a gaba kina yimana kukan kirsa da makirci,
Ki rufe mana baki muji qarshen zance,
Ummah tace muma fa muna son yaron nan kawai dai tsautsayine da kishi yasa muka kasa
riqeshi tun farko, shiyasa ma ya kawo miki shi amma bawai finmu sonsa kikayi ba
Kuka sosai muzaffar yake yi, dadyne ya katse su ta hanyar ce gaya musu cewar Mamie itace
mahaifiyar muzaffar, kuma itace matar daya fara aure a rayuwar sa, dan haka itace Uwar
gidansa kuma mahaifiya ga muzaffar!
Dikkansu seda suka girgiza musamman ma momy, sbda tashin hankalin da momy ta shiga
numfashinta har sama ya fara yi,
Umma ce tayi qarfin halin zaunar da momy,
Sun jima suna alhini
Mamie qara rungume dannata tayi cike da soda qauna,
Seda suka dauki lokaci me tsayi babu Wanda yace komai ,
Fadilah CE tace momy tashi mu tafi sbda ki samu nutsuwa,
Ba musu momy ta tashi dan dama hanya take nema
Suna shirin fita umma ma ta bisu,
Suna fita ameerah tace zahra zo mutafi muma, harara zahra ta zab gawa ameerah tace ba
inda zani kawai kiyi tafiyarki,
Tashi ameerah tayi tabar falon kamar zata tashi sama,
A hankali zahra ta sakko qasa daidai inda qafafun Dady suke tace Dady don Allah kayi haquri
da halayen da iyayen mu suke Nuna maka nasani dole wata rana zasuyi nadama,
Tana gama magana da Dady ta juya ga muzaffar tace yaya, haqiqa ina me jajanta ma abinda ya
faru dakai ina me yi maka addu'ar alkhairi a koda yaushe sbda kai dan uwa na ne kuma guda
daya tilo, nasani wata rana dole Kaine zaka zama uba a garemu gaba daya,
Nasani bamuyi sa'ar iyaye ba, amma don Allah INA me roqa masu afuwa akan abinda suka
aikata maka kana yaro don Allah yaya muzaffar kayi musu afuwa, tana maganar ne tana
hawaye,
A hankali ta daga jajayen idanunta ta kalli Mamie tace , haqiqa ke uwa CE wadda ta cancanta a
yaba mata tunda har kika Iya sadaukar da danki guda daya tilo dan farin cikin mijinki, wllh dik
inda uwa ta gari Takai kinkai Mamie, dama kece kika haife ni wllh danayi alfahari dake,
Tana kaiwa nan ta miqe ta fice daga fallon tana me zubar da hawaye
A wannan rana muzaffar kwanan farin ciki Yayi, hakama Mamie da Dady
Su umma da momy kuwa kamar su mutu din bakin ciki
RUGAR HARDO
Tunda muzaffar ya tafi komai ya dena yiwa rabe dadi
Gashi yau kwanan sa daya da tafiya amma har ta rame sbda kuka , bugu da qari ga kuma
azabar da Laure take gana mata, abin gwanin ban tausayi,
Tashi tayi daga dakin ta fita chan gurin garken shanunsu Inda suke zama ita da muzaffar,
dutsen daya ke zama a kai ta Dora hannunta akai seta sake fashewa da matsanancin kuka me
cin rai
Cikin kuka take fadin ya Allah Kaine ka bani farin ciki a lokacin da bani tsammani ba!
Ya Allah ina ina roqonka da sunayenka kyawawa, ya Allah ka cika rayuwata da farin ciki me
dorewa, ya Allah ka bani ikon jure ko wacce irin jarrabawa!
Tanayi tana kuka sosai abin qwanin ban tausayi,,,,,,
[8:55PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado頎巾笜_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 19*
Hka tayita rusar kukanta babu me rarrashinta, sda rana ta bude sosai sannan ta Tisa dabbobin
suka tafi kiwo, haka ta dinga tafiya jiki ba qwari, inda suke zama da muzaffar idan sun gaji ko
kuma zasuyi sallah, a nan ta zauna ta sake yin shiru, nan da nan ta tafi duniyar tinanin yayan
nata! A ranar dai haka ta wuni sukuku da ita
Momy ce tsaye a cikin dakinta tana ta safa da marwa da Waya a hannunta, falo naga ta nufa
fiskarta a daure fadilah ta samu a zaune bata ko kalleta ba tace tashi kije ki kiramin Umman
zahra, bata jira cewarta ba ta koma dakin ta
Ba'a dau lokaci me tsayi ba sega umma ta shigo dakin , Sosai take kallon Momy sannan tace
nariga na fahimci me kike son gaya min tin daga qwayar idanun ki, yanzu meye mafita ?
Tambayar da Momy ta jefawa umma kenan,
Bata CE mata komai ba ila daga wayar hannunta da tayi da alama wani take son kira,
Ba'a dau lokaci ba ta fara magana cikin isa da nuna gadara tace ado haka mukayi dakai?
Nawa muka baka a kan ka kashe mana wannan dan iskan?
Da kasan ba zaka iyaba kuka karbar mana kudi?
Cike da mamaki ado yace haba hajjaju, ai tin tini aka gama wannan aikin dan sda na tabbatar
baya numfashi sannan na qyaleshi!
Kema kinsan Baku taba bani aiki na kuskureba,
Momy CE ta fisge wayar daga hannun umma ta kara a kunnenta cike da masifa tace har kana
da bakin da zakace baka kuskure a aikin ka?
Kai daqiqin inane da zaka yarda shi a Inda mutane suke shige da fice?
To gashi yanzu ka jiqa mana aiki yaron ya dawo gida da ransa da kuma lafyar sa, kuma kasan
dole 'yansanda zasu karbi bayanai daga bakinsa , dan hka seka zauna cikin shiri, at any time
zasu Iya zuwa kamaka!
Ta qarasa maganar cike da masifa gamida tarin bacin rai
Umma CE tayi saurin karbar wayar tace ado kana jina?
Cike da tsoro yace ae Hajia inajinki
Maza- maza ka shirya kabar garinnan kayi nesa da kano Sam karka dawo semun nemeka, da
sauri yace to Hajia, sda ta dan nisa tace masa amma dai a kwai kudi a hannunka ko?
A'a yace mata nan da nan tace yaushe na saka maka million daya a account dinka da zaka
cemin ba kudi?
A daqile yace sorry Hajia na shiga rudani ne, bata sake cewa komaiba ta katse wayar sannan ta
bude wayar ta cire sim din ta karya sbda gudun seta kwana!
A hankali umma ta dafa kafadar Momy tace haba zuwaira kada ki bada mata mana, ai yanzu
damace tazo mana,
Cike da rashin fahimta Momy tace kamar ya ?
Murmushi tayi irin nasu na 'yan duniya sannan tace shishigewa waccan matsiyaciyar zamuyi,
idan ta saki jiki damu se mu aika shegiya garin da ba'a dawowa! Koya kika CE?
Dariyar jin dadi Momy tayi sannan tace wllh kamar kinsan abinda ke raina,, suka sake
kwashewa da dariya suka tafa(haqiqa kishi da rashin tsoron Allah yana kai mata dayawa ga
halaka, mugun nufi bashida wata fa'ida illa yakai mutum ga na dama! Dan Allah mata mu gyara
zukatan mu, kishi halitta ne kuma kowace mace tana dashi a tare da ita muddin tana da lfy,
amma idan kika bishi ta hanyar daya dace wllh zaki zauna da kowa lfy, wannan abin nasu
Momy Harda son zuciya gamida tarin rashin tsoron Allah, ya ubangiji Allah kasa mufi qarfin
zukatan mu)
Moddibo ne zaune qasan kafet yana daure boronsa da alama shirin tafiya gda yake muzaffar ne
ya