Showing 12001 words to 15000 words out of 20649 words
motsa baki kala kala, kodaya Dady be taba ba
sabda shi yanzu ma ko wani irin abinci ya kalla Sam baya bashi shi'awar sa, dan haka kallo
daya yayiwa abincin ya dauke kansa,
A hankali sp majiya ya qaraso falon tare da sallamar sa, har ya qaraso falon Dady be San ya
shigo ba har seda ya tabashi sannan ya dawo daga duniyar tinanin kudan jininsa,
A dan daburce Dady yace barka da fitowa,
Sp yayi murmushi yace haba alhji abdul dubi fa yanda ka damu kanka da tunani wllh Harka
rame kayi baki kamar ba kaiba, kayi haquri ka yarda da qaddarar da Allah ya aiko maka kaifa
musulmi ne , insha Allah zamu samo inda muzaffar yake da izinin Allah, tunda sp ya fara
magana Dady ke kallon sa sannan yace naji abinda kace sp kuma na gamsu da bayanan ka
zanyi qoqarin cire ragewa kaina tinanin kamar yadda ka shawrce ni ngde Allah ya bar
zumunci,
Sp yayi murmushi yace ba komai, kada ka damu,
Kuma insha Allah zamu zage dantse wajan gano inda danmu yake da ikon Allah.
Sosai Dady yaji dadin maganganun majiya dan har ya samu nutsuwa a zuciyar sa kuma yadan
sake sunyi hira kadan,
Sannan sukayi sallama da juna cikin aminci har bakin mota sp majiya ya rako dady , ya shiga
mota suna masu dagawa junansu hannu,
Dady be koma gda ba se 6:00pm koda ya dawo be tsaya ko INA ba se dakinsa alwala yayi ya
sake fita be dawo ba se da yayi sallar magrib
RUGAR HARDO
tunda su muzaffar suka tafi kiwo bashi da aikin daya wuce kallon Rabe dik inda tabi idanunsa
na kanta,
A hankali ta bude baki tace yaya zafar meyasa kake yawan kallona?
Murmushi yayi sannan yace sabda zanyi missing naki!
Sosai take kallon sa sannan tace me Kalmar take nufi?
A taqaice yace zanyi kewarki to.
Dariya tayi sosai irin wadda bata tabayi ba a gabansa a Iya zaman da yayi dasu, daqar ta saita
kanta ta dena dariyar,
Tunda ta fara yake kallonta kamar wanda zeyi kuka yace, meyasa ki dariya haka?
Murmushi tayi tace abinda ka fada ne yasani dariya senaji Kalmar taban dariya,
Hade rai yayi yace to kada ki sake min irin wannan dariyar bana so, kinji yanda kika tsorata ni?
Sunkuyar dakai tayi sannan ta riqe kunnuwanta dika biyun kamar yanda yakeyi mata idan ya
bata mata rai, kamar zatayi kuka ta tsuguna qasa tace kayi haquri yaya zafar badan qara ba,
Dariya ta bashi sosai dan haka yay murmushi tare da Jan kumatunta yace shikenan na haqura
amma kadan.
Dariya sukayi dukansu, sannan suka kamo hanyar gida dabda magariba suka dawo,
Tunda suka dawo Rabe bata qara bari sun hadu da zafar ba, a cewarta wai bata so taga tafiyar
yayan nata !
Daki ta nifa tayi sallah tayi addu'ointa ta shafa, amma kuma bata tashi daga gurin ba,
Bangaren muzaffar kuwa tunda suka shigo yayi sallah amma bega shigo war Rabe ba se abin
ya fara damunsa, har akayi ishsha beganta ba se abin ya fara daga masa hankali,
Daqar ya Iya bude baki ya cewa moddibo dake ta faman dura madara ajarka yace, baba!
Ya a nitse moddibo ya dago yace yaro ya akayi ?
A daburce yace dama,,, dam,,,,, Rabe se kuma yayi shiru.
Murmushi moddibo yayi yace yaro INA zaton ko tayi bacci ne,
Kayi qoqari ka kwanta sbda gobe asibanci zamuyi ,
Bashi da yanda zeyi haka ya kwanta amma fir bacci ya gagari idanunsa ,
A hankali ya firta meke faruwa dani ne??
Bangaren Rabe kuwa baccinta take hankalin ta kwance babu abinda ya dameta ,
Qasar India
Mamie tana idar da sallar asuba bata tsaya ko INA ba se airports dan cika umarnin mijin nata
duka 5:30am suka daga zuwa Nigeria, tun da ta hau jirgi gabanta ke faduwa komeyasa????
Ban garan su muzaffar kuwa tunda gari ya waye suka gabatar da sallar asuba suka fara shiri
ba yanda beyiba dan su hadu da rabe
Amma fir taqi da abin ya isheta ma seta bar Gidan tayi tafiyarta gidansu danejo qawarta,
Ba yadda ya Iya haka suka tafi ya naji yana gani suka shiga wata a mortar shanu suka kama
hanyar garin kano garin alfarma!
Dik wannan uban sammakon da sukayi basu suka isa kano ba se qarfe 4:00pm
Wanda yayi dai dai da saukar mamie a qasarta ta haihuwa!
Cike da kulawa moddibo ya kalli muzaffar yace yaro zaka gane gida ko?
Muzaffar yayi murmushi yace zan gane,
Adaidaita sahu suka tare sannan muzaffar yace malam nasarawa g.r.a zaka kaimu ,
A take me napep yace musu dubu daya !
Bece komaiba suka shiga suka tasarwa nasarawa g.r.a
Mamie na sauka daga jirgi bata wani jima ba driver yazo ya dauke ta tana cikin motar gabanta
yay mummunar faduwa!
Da sauri ta firta innanillahi wa'inna ilai hirraji'un.
Qofar wani gida na alfarma muzaffar ya nunawa me napep din tare da bashi izinin shiga horn
me napep din yayi amma shiru ba'a bude gate din ba ,
Muzaffar ne ya zuro qafarsa da nufin ya suka , amma se moddibo yayi carap ya riqeshi yace
yaro Sam be kamata ka shiga kanka tsaye ba, dolene ka badda kamannin ka,
Cike da rashin fahimta yace ban gane ba!
Murmushi moddibo yayi ya fito da wani rawani ya CE bani kanka, ba musu ya miko masa kan
NASA ya shiga Nada masa,
Watabara'kallahu'ahsanulkhaliqin,
Abinda moddibo ya Iya fada kenan sbda wani azababben kyau da rawanin yayi wa muzaffar
Gashi sanye da kayan Fulani seya koma kamar wani balarabe!
Horn suka sake yi a karo na uku sannan me gadin ya bude yana ganin baquwar fuska ai seya
dakatar dasu yace daga malamai daga INA?
Moddibo ne ya bashi amsa yace daqa rugar hardo!
Ba musu me gadi ya bude musu qofar suka shige sbda kwarjinin da moddibo yayi masa
Sauka sukayi shi kuma me napep suka bashi hagginsa Harda qari, mebawa fulawa ruwa suka
samu su kace dan Allah ya sanarwa da alhaji abdul yana da baqi daga rugar hardo, cike da
girmamawa ya amsa tare da kaisu falon saukar baqi
Se ince fatan alkhairi mlm moddibo頎巾睆
[8:53PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado頎巾笜_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 15*
Sun jima suna zaune, sannan aka kawo musu abin motsa baki.
Lokacin da aka sanar da Dady zuwansu moddibo yayi mamaki sosai sbda shi bema taba jin
sunan garin ba, amma dayake mutum ne shi me jama'a da kuma son mutane shiyasa be wani
yi mamakin zuwan su ba, tashi yayi ya nufi falon sa na da yake saukar baqin sa,
Da sallama ya shiga falon, ya nemi guri ya zauna sannan suka gaisa da moddibo.
Kwata kwata be lura da wanda ke zaune a qasa ba,
Sosai Dady ya sakarwa moddibo fuska, a nitse moddibo ya fara magana tare da yiwa Allah
godia yace da fari alhaji ka godewa Allah bisa ni'imar da Allah yayi maka a wannan rana!
Cike da rashin fahimta Dady yace ban fahimceka ba dan uwa?
Murmushi moddibo yayi sannan yayi masa nuni da muzaffar dake zaune da uban rawani a
kansa gaba daya ya badda kama
Sosai Dady yake kallon dan nasa cike da so da qauna, da sauri ya nufi inda muzaffar yake da
nufin ya rungume shi, haka shima muzaffar din beyi qasa a gwiwaba ya nufi mahaifin nasa
suka rungume juna suna masu zubar da hawaye頎巾腑
Sosai suka bawa moddibo tausayi, sun jima suna rungume da juna sannan Dady ya cire
jikinsa daga na muzaffar ya zubawa fukar dan nasa ido sosai rama ta baiyana a jikinsa sedai
kuma beyi duhu ba haskensa yana nan yanda yake!
Se kuma alamar ciwon dake gefan kansa na dama Wanda be gama bacewa gaba daya ba.
Cike da damuwa Dady yake tambayar dan nasa meya faru dashi? Kuma ina ya shiga har
tsawon wannan lokacin?
Muzaffar yayi shiru kamar bazece komai ba, seda ya dan nisa sannan ya gayawa Dady komai
sedai be gaya masa da sa hannun su Ummah da Momy ba akan abinda ya faru dashi ba!
Har abinda ado yayi masa be gayawa Dady ba, kawai CE masa yayi 'yan fashi ne suka farauci
rayuwarsu kuma sukayi yunqurin kashe shi, badan wannan bawan Allahn ba da tini na rasa
rayuwata, ya qarasa maganar tare da zubda hawaye!
Da sauri Dady ya qaraso kusa da qafafuwan moddibo ya rige yana fadin ngde, Allah ya saka
maka da alkhairi, haqiqa banida abinda zan biyaka dashi a wannan duniyar sedai kawai ince
Allah ya biyaka da Gidan aljannah頎巾睆
Ya qarasa maganar tareda hawaye!
Murmushin qarfin hali moddibo yayi sannan yace haba alhaji dan Allah ka dena godemin sbda
ni nayiwa yaro taimako ne don Allah ba dan kayi min godiya ba, dan haka ka bari godiyar ta
isa haka, sedai kawai abinda zancema shine kayi a hankali sbda maqiyanka Dana danka suna
tare dakai kuma sune sukafi kowa kusanci dakai! Cike da rashin fahimta Dady yake kallon moddibo, kai moddibo ya daga masa alamar ae,
Kiran sallar da aka fara kira ne ya katse Dady daga tambayar da yaso yayiwa moddibo,
Tashi sukayi suka nufi masallaci dan su gabatar da sallar magrib,
Bayan sun idar ne suka nufi qofar da zata sadasu da Fallon,
Horn akayi daga bakin gate hakan ne yaja hankalin Dady da muzaffar, shiko moddibo
shigewarsa yayi ya samu guri ya zauna, sannan ya fara nazari akan maganar da muzaffar ya
gayawa mahaifin sa, to meyasa be gayawa mahaifin sa gaskia ba??
Lallai muzaffar yaro ne me sanin ya kamata kuma me gudin masifa.
Sbda gudin ta da fitina yayiwa mahaifin sa qarya dan ya fanshi kishiyoyin mahifiyarsa!
Gaskia samun irin sa se'an tona a irin wannan zamanin, haka kawai seyaji yaron ya qara shiga
ransa.
Wata baqar Toyota benza ce ta sako kai cikin Gidan ko ba'a fada ba Dady yasan Mamie ce
parking space suka nufa sukayi parking tana fitowa daga motar Dady ya yiwa muzaffar nuni
daya shiga falon tun kafin ta ganshi,, haka kuwa akayi
Da sauri Dady ya nufi inda Mamie ke tsaye da murmushi a kwance a fiskarsa yace sannu da
zuwa Uwar gida ran gida,
Murmushi Mamie tayi ba tace komaiba ta nufi bangaranta visa ga mamkinta ba ta ga qura ko
daya ba harta isa falon ta ko INA tas tas ba datti daret bedroom dinta tanufa, tana shiga toilets
ta shiga bisa ga mamakinta dik abinda take Amfani dasu tin daga sabulun Wanka har zuwa
MacLean komai a kawai a ciki kuma dika sababbi, haka ma su towels, Murmushi tayi sannan tace abou muzaffar kenan har yanzu kana nan yanda kake baka canza
ba!
Dady ne yasa masu aiki suka shigarwa da Momy kayanta bangaren ta sannan ya nufi falon da
moddibo ke zaune shida muzaffar,
Dady ne ya yiwa muzaffar izinin yakai moddibo bangaren saukar baqi dan yaje yayi Wanka ya
huta
Haka kuwa akayi suna fita Dady ya nufi bangaren sa dan ya samu yayi Wanka zuciyar sa cike
da farin ciki Mara musaltuwa,
Suna isa ban garen baki ya nunawa moddibo ko INA sannan suka zauna , a nan ne moddibo
yake tambayar muzaffar meyasa baze tafi bangaren sa ba?
A taqaice yace Dady ne yace na zauna a nan har seya nemeni!
Lallai akwai magana a qasa se ince Allah ya huta gajia Mamie頎巾睆
[8:54PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado頎巾笜_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 16*
Seda ta yi Wanka sannan ta gabatar da sallar dake kanta, ta jima tana adduo'inta sannan ta
shafa,
Bangaren Dady kuwa yana shiga cikin gda dakinsa ya wuce seda Yayi Wanka ya kimtsa,
sannan ya gabatar da sallar ishsha'insa, sannan ya nufi falon su momy,
Yana shiga falon ya same su dukansu akan dining sunacin abinci suda yaransu, kallo daya
zakayiwa Dady ka fahimci yana cikin farin ciki, dan haka umma cike da gulma tace alhji da
dikkan alamu kana cikin farin ciki, kodai an sake samun riba a company n ka na takalma ne?
Cike da masifa Momy ta fara magana tace riba? Ba wata riba da aka samu, wannan farin cikin
da yake ba komai bane dalili ila zuwan matar sa, kuma wllh ka sani tunda ka jajibota cikin mu
to wllh kayi bankwana da kwanciyar hankali, tana gama magana ta mike da nufin ta wuce
dakinta, Tsawa Dady ya daka mata wadda seda hanjin cikin ta ya kada yace ke kishiga hankalinki niba
sa'anki bane da zaki sani a gaba kina yimin ihu, ko ba komai ni mijin ki ne kuma uban 'ya'yanki
ko banci darajar kowa ba naci darajar 'ya'yana yana gamawa ya juya da nufin yabar falon, se
kuma ya dawo yace idan sun gama suzo falon sa yana son magana dasu a bangaren da aka
fat din Mamie kuma su zo da yaransu gaba daya sbda a kwai Abu me mahimmanci,
Yana kaiwa nan Yayi waje abinsa ban garen Mamie ya nufa da sallamar sa ba kowa a falon se
qamshi dake tashi a falon sosai yake kallon falon Yayi matiqar kyau kamar yanda yake buqata,
hanyar da zata sa dashi da dakin Mamie ya nufa tin kafin yakai ga dakin qamshin turarenta ya
baqunci hancin dady, murmushi Yayi a zuciyarsa yace salma kenan kedai Allah Yayi miki son
qamshi
Yana shi shiga ya sameta tana daura dan kwali a kanta sallamar ta amsa sannan tayi
murmushi tace sannu abban muzaffar na sameku lfya ?
Dariya Yayi sannan yace Uwar gida ran gida lfy. Qalau mun godewa Allah ya gajiyar hanya?
Murmushi tayi sannan tace gajiya kam akwai ta Baban muzaffar.
Shiru suka dan yi na wani dan lokaci sannan Dady yace idan kinci kin gama shiryawa akwai
maganar da zamu dan tattauna daku, gabanta ne ya fadi! da sauri ta furta
innanillahi'wa'innah ilaihirraji'un, da Sauri Dady ya matsa kusa da ita ya dafata yana tambayarta
meya faru? Kuka ta saki sekace wata qaramar yarinya, beyi yunqurin hanata ba, seda tayi me isarta
sannan tayi shiru,
A hankali ta fara magana ban San meyake damuna ba Sam! Koda yaushe a ' se in dinga jin
gabana yana yawan faduwa, musamman ma yau ,
Lamarin nifa ya fara bani tsoro wllh, kodai wani abin ne ze faru dani? Ta qarashe maganar
tana zubar da hawaye,
A nitse Dady ya fara magana yace haba salmah, har zuwa wani lokaci zaki kai kina wannan
kukan?
Yakamata kisani cewa ko wani mutum da zanan qaddarar sa, kuma ko wani mutum da irin
tasa qaddarar, don Allah kiyi haquri ki dena zubar da hawaye haka, insha Allah zamu samu
cikar burinki da izinin Allah wata rana zamu hadu da su!
Cikin kuka Mamie ta fara magana tabbas nayi kuskure a rayuwata Abdul, gashi hakan yajamin
rashin kwanciyar hankali da nutsuwa,
Kuka sosai takeyi, har ga Allah ya tausaya mata dan haka yayta rarrashinta har ya samu tayi
shiru,
Kicin ta nufa ta sa ruwan zafi ta hada tie sannan ta fito ta zauna a kan dining ta fara sha, tana
cikin sha ameerah da zahra suka shigo falon da sallamar su cike da kulawa Mamie ta amsa
sallamar tare da sakin fuska sosai baki ameerah ta saki tana kallon Mamie, zahra kuwa
hankalinta yana kan Falon musamman yanda taga komai sabo ne bugu da qari ma gurin Yayi
matiqar haduwa, a hankali ta furta waw gaskia falon nan ya hadu,
Ta juya da nufin ta tabo ameerah ai se sukai ido biyu da Mamie, air se itama ta tsaya tana
kallon Mamie n, murmushi Mamie tayi sannan tace Ku shigo Ku zauna mana sekace baqi?
Maza Ku shigo mana
Jiki a sanyaye suka shigo falon suka zauna ameerah CE ta fara gaida Mamie sannan zahra ma
ta gaisheta, sosai Mamie ta sakar masu fuska suka dinga hira, a nan ne ameerah tacewa
Mamie aunty gaskia ke kaykkyawa ce, daria Mamie tayi sosai dan har ga Allah ameerah ta bata
daria, A hankali Mamie ta sunkuyo taja hancin ameerah tace kema ai kyakkyawa ce,
Darirya ameerah tayi sannan tace aunty ni suna na ameerah wannan kuma zahra,
Murmushi Mamie tayi sannan tace ba suna na aunty ba Mamie zakice kinji?
Dariya zahra tayi sannan tace ke in banda baki da hankali Waya fada miki ana cewa babba
kamar wannan aunty ?