Showing 18001 words to 20649 words out of 20649 words
shigo dakin da murmushi a kan fiskarsa yace baba,,,, se kuma yayi shiru, da sauri ya qaraso
inda moddibo yake cike da damuwa yace baba badai har ka fara shiriba tin yau?
Murmushi moddibo yayi irin na dattijawan qwarai yace to yaro me kuma zan tsaya jira?
Tunda Allah ya amince mana min samu nasarar kawoka Gavan Iya yenka ai kuma nima sena
fara shirin komawa gida kodan sbda Rabe na!
Nasan yanzu tana nan cikin kewata , ban taba tafiya me Nisan haka na barta a gda ba, a Iya
zaman ta dani ban taba tafiyar da takaini ga kwana ba sbda tinanin halinda zata shiga idan
bana nan,
Dan haka Gobe da ikon Allah zan kama hanyar gda ,ya warashe maganar da murmushi a
fiskarsa
Shiru muzaffar yayi na dan lokaci tabbas yana mamakin shaquwa irinta moddibo da diyarsa,
yanzu idan tayi aure ya zeyi?
Kafadarsa moddibo ya dafa yace yaro naga daga jiya zuwa yau kanata farin ciki,
Murmushi muzaffar yayi sannan ya labirtawa moddibo komai, sosai moddibo yayi farin ciki
gamida yiwa muzaffar nasihu masu shiga jiki sosai,
Jikin muzaffar haka yayi sanyi sbda nasihun da moddibo yayi masa, a ransa seyaji dama
moddibo ya zauna tare dashi haka kawai dattijon ya gama shiga ransa,
Jiki ba qwari muzaffar ya miqe sbda jin kiran sallar ishsha'i, be cewa moddibo komaiba, ya nufi
hanyar fita
Murmushi moddibo ya kuma yi sbda ya fahimci muzaffar fishi yayi sbda yace ze tafi gobe
Miqewa yayi shima suka nufi masallaci, daidai lokacin da Mamie ta loqo ta window falon ta
bayan su ta hanga sannan ta koma taci gaba da jera abinci akan dining,
Koda aka idar muzaffar ya Dade yana addu'oinsa sannan suka shafa suka fito gaba daya,
Dai dai lokacin da Dady ma ya fito tare suka jera suna tafe suna hira anan muzaffar ke
shaidawa Dady tafiyar moddibo, sosai Dady ma yaji ba dadi sbda yanda ya saba dashi a
kwana daya kamar sun shekara da sanin juna, moddibo akwai sauri saboda mutane, gashi da
haquri da sanin ya kamata shiyasa yake da dadin mu'amala, Indai ya zauna dakai koda na wuni daya ne to Seka qaunace shi. Sbda dattijon a kwai shiga rai
Suna shiga Dady yacewa moddibo tunda gobe ze tafi don Allah yazo suje bangarensa suci
abinci tare amma fir moddibo yaqi amincewa , haka Dady ya haqura badan yaso ba yayiwa
moddibo seda safe sannan ya wuce bangaren Mamie,
Ban garen da aka sauki moddibo suka muzaffar yana biye dashi a baya har suka isa a falo
suka zauna, muzaffar ne ya fita dan dakko musu abinci a bangaren Mamiensa , be jima ba ya
dawo dauke da manyan food flasks guda biyu se zahra dake bayan sa hannunta dauke da flat
da spoons ajiyewa tayi sannan ta koma ta daukko wani flat dauke da kosilo Wanda yaji qwai da
bama ansa wata fara leda an rufe farantin da ita ta yanda kana Iya ganin abinda ke cikin flat din
da sallama ta shigo ta ajiye sannan ta gaida moddibo cike da girmamawa, da kulawa ya amsa
mata tareda sakin fuska, an an yake tambayar ta sunan ta murmushi tayi sannan tace zahra,
Murmushi moddibo yayi sannan yace Ashe mata nane da kanta, dukansu suka sa dariya
sannan ta miqe tayi musu saida safe ta wuce bangaren su
[8:55PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado頎巾笜_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 20*
Zaune suke kan dining suna cin abinci, Dady yake sanar da Mamie tafiyar moddibo da safe
idan Allah ya kaimu, gaban Mamie ne yay mugun faduwa sbda sunan da taji mijinta ya ambata
, take yanayinta ya sauya,
A hankali tace daga zuwansa har ze koma se kace ana korar sa?
Murmushi Dady yayi sannan yace wllh nima haka nace dashi amma fir yaqi yarda ya qara
kwana ki,
Dik wannan hiran da suke itada Dady qarfin hali kawai take tinda taji sunan moddibo, sunan da
bazata taba mantawa dashi ba a rayuwata
Dady ne ya katseta ta hanyar sanar da ita yayi kewarta,
Murmushi Mamie tayi sannan tace abban muzaffar kenan sekace wasu yara?
Dariya yayi sannan yace mata au yara ne kawai suke soyayyah?
Bata CE masa komaiba dan ta fahimci Neman magana kawai yakeyi,
A hankali ta ajiye cokalin dake hannunta ta miqe a taqaice tace seda safe,
Sam beyi qoqarin hanata tafiya ba sbda ya fahimci yana yinta ya canza tunda ya ambaci sunan
moddibo.
Abinda ya qara daure masa kai shine meyasa bata son taji wani me suna irin hka?
A hankali ya rintse idanunsa, sbda baya son abinda ze batawa matar tasa rai, a daddafe ya
kammala cin abinci, ya miqe ya nufi bedroom din shima, a zaune ya sameta da alama daga
toilet ta fito, kana kallon ta zakasan tayi kuka, bece mata komai ba ya shiga toilet yayi brush
sannan yayi wanka yafito, beyi mamakin ganin ta ajiye masa jallabiya ba sbda hakan al'adarta
ce, murmushi yayi sannan ya sanya a jikin sa, yana gama sawa haye gado abinsa bece mata
komaiba ya ka bargons da nufin ya kwanta,
Da kanta ta fahimci yayiwa megidan nata laifi dan hka ta bude baki tace don Allah kayi haquri
bani da yanda zanyi ne dolece tasa,
Sanin kanka ne kasan bazan taba mantawa da me wannan sunan ba seta fashe da kuka,
Sosai me Gidan nata ya tausaya mata, dafata yayi sannan yay mata nasiha sosai tareda sake
nuna mata mahimmancin yarda da qaddara,
Jikinta ne yayi sanyi sosai a hankali taba bargo ta kwanta, a nan ne Dady yake tambayar ta
me take ganin zeyiwa moddibo idan ze tafi sbda nuna jin dadin abinda yayiwa dansa Wanda
yasan ko duniyar nan yabashi be biyasa ba ,
Murmushi Mamie tayi me sauti sannan tace ka bari tukunna seda safen mayi maganar,
Bata qara cewa komaiba tayi addu'ointa ta tofa, ba jimawa bacci ya dauketa ,
Ban garen su muzaffar kuwa hira suke sosai da moddibo sekace ba dare ba, sun jima suna
hiran sannan moddibo ya tashi ya wuce daki sbda bacci daya ke ji, kuma gashi fitar wuri yake
so yayi,
Murmushi muzaffar yayi tareda dadin seda safe
A hankali ya tashi ya kashe TV sannan ya rage ywan Ac dake falon sannan ya rage wutar
falon ya mike ya nufi bangaren sa, bisa ga mamakin sa seyaga an qara gyara masa dakin, ko
ba'a fada ba yasan zahra CE da wannan aikin
Murmushi yayi sanan yace Allah sarki my Darling,
Wanka yayi sannan ya fito daga toilet din sanye da wata farar jallabiya, dik da cewa shirin bacci
yayi amma rigar ba qara min kyau tayi masa ba, a hankali ya qraso bakin makeken gadon sa
qirar Italian ya zauna yayi shiru, kallo daya zaka yimasa ka fahimci damuwa a fiskarsa,
Wani abin hannun roba dake hannunsa ya taba se kuma ya saki wani tattausan murmushi, a
hankali ya firta I miss you Rabi'atu, I miss everything about you, murmushi ya sake yi a karo na
biyu sannan ya hau gadonsa yaja bargo ya kwanta, ya jima yana nazarinta tareda Tina wasu
abubuwa na quruciyarta gami da yawan murmushin ta, Yajima yana aikin tinani sannan bacci yay a won gaba dashi,
Kiran sallar farko moddibo ya mike ya shiga toilet yayi Wanka yayi alwala ya kimtsa.
Masallaci ya nifa, yana shiga masallaci ya gabatar da raka'atanul fijir bayan ya idar ya dan jima
a zaune yana addu'ah sannan aka gabatar da sallar asuba,
Bayan ya fito masallaci suka hadu da muzaffar suka wuce gda suna hirarrakin su,
Ban garan moddibo suka nufa ya tayashi ya hada kayan sa ya daure seda gari yayi haske
sannan Dady ya shigo bangaren dan su gaisa da moddibo, bayan sun gaisa ne Dady yace
masa yazo su gaisa da mahaifiyar muzaffar sannan yayi breakfast, se su wuce, murmushi
moddibo yayi sannan ya CE to babu damuwa idan ka shiga seka sanar da iyalin baka shigo war
tawa,
Murmushi Dady yayi sannan ya kalli muzaffar yace ka shigo dashi falon Mamie n ka idan ya
kammala murmushi shima yayi ya amsa da to Dady,
Dady na shiga ya sanar da Mamie cewar moddibo ze shigo yayi mata sallama, murmushi tayi
sannan tace gaskia be kamata ya tafi yanzu ba dama ya qara mana kwana 2 murmushi Dady
yayi suna ta hira abinsu,
Mamie tace ina zuwa naji kamar abinda na Dora yana kamawa , kichin ta nifa dan ta sauke
abinda ta Dora,
Tana fita su moddibo da muzaffar suka shigo falon, guri muzaffar ya nuwa moddibo sannan ya
zauna shima hira suke dan yi da Dady jefi jefi, a haka Mamie ta fito ta samesu , ko kadan
moddibo be kalli fiskarta ba itama haka ta qaraso falon fiskarta dauke da murmushi a nitse ta
zauna a gefan Dady sannan ta fara gaida moddibo a nitse ya fara amsawa cike da kulawa, Cike da tashin hankali Mamie ta dago sbda jin muryar da ko a INA take tasan mamallakinta,
Kallon moddibo take haka shima kallon Nata yake cike da tashin hankali yake nuna ta da
yatsa,
Kasa cewa komai yayi dan haka kawai ya miqe da nufin yabar falon gaba daya,
Da sauri Mamie ta riqe qafafuwansa tana kuka me tsima zuciya, cikin kukan take fadin dan
Allah Iya kayi haquri ka yafe min nasan nayi kuskure a rayuwa ta yanda bazan Iya gyara laifi
naba! Ta qarasa maganar tana kuka sosai
Cike da rashin fahimta Dady yake kallon su haka ma muzaffar da kansa ya gama daurewa,
Cike da damuwa Dady yake tambayar Mamie shin tasan moddibo ne? Kuma meye hadinta
dashi da har take fadin ya yafe mata?
Da qar ta Iya bude baki tace dan uwa nane shine yayana moddibo da mukaje nema shekaru a
shirin da biyar da suka wuce, to shine wannan ta qara fashewa da kuka,
Qarfin hali moddibo yayi ya fisge qafarsa daga hannunta ya fice daga falon da sauri yana zubar
da hawaye,
Ko kayan sa be dauka ba ya fice daga Gidan gaba daya,
Yana fita ya samu keke na pep ya shiga batare da ya gaya masa inda ze kaishiba !!
Seda suka fara tafiya me napep din yace mlm INA zan kaika?
A taqaice yace masa tashar mota zaka kaini, don Allah idan kasan inda ake lodin abuja ka kaini
gurin sabda sauri nakeyi,
A kan titin Zaria road ya sauke moddibo sannan yasa shi a motar abuja,
yakoyi sa'a ciko ake Neman , kudinsa ya bashi sannan yayi masa godiya suka kama hanyar
abuja,
[8:56PM, 2/6/2018] +234 813 272 6929: 頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己頎柬己
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado頎巾笜_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 21*
Tun bayan tafiyar moddibo Mamie take kuka, gaba daya hankalin Dady ya gama tashi yama
rasa me zeyi guri ya samu ya zauna tare da dafe kansa daya ke masa wani irin nauyi,, falon ne
yayi shiru ba'a jin komai se sautin kuka Mamie, muzaffar ne yayi qarfin halin cewa Dady
wannan zaman fa ba shine mafita ba fa, Kawai tashi zamuyi mubi bayan sa, nasan ze sauraremu inayaso se'a gyara matsalar senake
ganin hakan zefi da wannan zaman da muke,, cikin kuka Mamie tace nasan halin sa muzaffar
yana da matiqar haquri amma idan yayi fishi yana da wuyar sha'ani!
A hankali Dady ya sauke ajiyar zuciya sannan yace abinda muzaffar ya fada shine daidai ki
tashi kije ki wanke fuskarki ki shiya mubi bayansa , hakan shine mafita, haka kuwa akayi, a
gurguje Mamie ta gama kimtsawa ta fito, koda ta fito bata samu muzaffar da dady a falon ba ,
dan haka bata tsaya jiran komaiba ta nufi waje tana fita ta hangi muzaffar a parking space yana
tsaye a jikin wata ibgegiyar mota qirar ford,da alama fitowarsu yake jira, sanye yake cikin wata
dakakkiyar shadda milk colour ammata dinkin tazarce, aikin dake jikin shaddar maroon color ne
dan haka ya sanya hula maroon da ratsin milk a jiki ta kalmin qafarsa me danyasa ne shima
maroon, se agogon dake hannunsa qirar Gucci, sosai yayi kyau kayan sunyi matiqar amsar jikin
sa, a hankali Mamie ta qarasa inda yake kallo daya zakai mata kasan tana cikin damuwa mara
musaltuwa, amma dik da haka damuwar bata hana futowar kyawun da Mamie n keda Shiva, da
sauri dan nata ya matso kusa da ita ya rungumeta yace don Allah Mamie ki ya rage damuwa
indai baba ne wllh ze fahimce ki, nasan shi yana da sauqin hali a Iya zaman danayi dashi , pls
Mamie ki cire damuwa haka don Allah!
Batace komaiba se cire jikinta zatayi daga nasa , sannan tayi wani marayen murmushi me
baiyana karayar zuciya da qarfin gwiwa tace hka dai kace yaro amma ni nasan da wuya
moddibo ya yayfemin abinda nayi masa ,
Be sake cewa komaiba sbda fitowar Dady dasu umma daya gani, a nitse suka qaraso gurin
murmushi Mamie tayi musu tareda CE musu muntashi lfy ?
Umma CE ta amsa mata da fara'arta , Momy kuwa ko kallon ta batayi ba, da sauri zahra ta
matsa kusa da Mamie tace Mamie INA kwana ? Da kulawa Mamie ta amsa, muzaffar bece
musu komai ba sbda shi gaba dayansu ma haushi suke bashi , daya ga abin nasu bana qare
bane, se yace pls Dady Ku shiga muje sbda mu isa da wuri, daga haka ya bude driver seat ya
zauna, yana qoqarin rufewa zahra ta riqe hannunsa da sauri tace pls yaya nima zan biku tunda
ba school don Allah!
Ta qarasa maganar tare da langabar da kanta kamar wata yarinya,
Dariya ma ta bashi dan haka yace ta shiga suje da gudu ta bude qofar gaba ta shige tana yiwa
ameerah qwalo,
Mamie CE ta fara shiga sannan Dady da sauri ameerah ta matso ta cewa muzaffar yaya nima,
ai be jira cewarta ya daka mata tsawa yace bacemin da gani ba inda zamu dake Mara kunya
kawai!
Da gudu ta bar wajen tana kuka, cike da masifa Momy tace to seme in baka je da ita ba?
Ta juya itama ta bar gurin,
Be jira cewarta ba ya tashi motar suka bar harabar gidan , suka nufi hanyar RUGAR HARDO!
Se wajen qarfe uku sannan moddibo ya isa yana hanyar sa ta shiga gida ya hangi Rabe a
zaune cikin garken shanu ta rafka uban tagumi, inta take ya nifa ya kamo hannunta yana
kallon fiskarta sosai yaga rama a tare da ita, ga kuma duhu da ta danyi ba komai a fiskarta se
daradaran idanunta da suka sake fitowa se dogon hancinta shima daya baiyyana alamar
rama, be jira cewarta ba ya ka hannunta sukayi gida, mamaki ne kwance a fiskar Laure
Dan haka tace mlm har ka dawo?
Sbda takaici ko kallonta beyi ba ya jata sukayi daki