Showing 9001 words to 12000 words out of 13755 words

Chapter 4 - Binta Yar Jagaliya Book Compelet

11 Aug 2026

305



hajiya turai tace


yusrah ki basu mukullan ɗakuna su zaɓa wannan barin ku gu ɗaya a kwai matsala

wani uban murmushi ta saki me cike da ma'anoni tace


"To hajiya ,

miƙewa tayi ta tashi domin wallahi ba zasu zauna a ɓamgaran nan ba in da ake kai baƙi zata kai
su ba har gori sukai mata ba

wannan kenan garin kura


fitowa tayi ta zabga wata uwar hamma ɗakin kahu labahani ta kalla tuni wata dariya ta kubɓuce
mata ta dinyi harda ruƙe ciki ganin saminu ya shigo yana waka tayi sauri ta haɗe ranta tace


"ke saminu zo ka siyomin indomi da ƙwai,


washe baki yayi domin yasan in ta aike shi tana yi mai hasafi abin hannunta be rufe mata ido ba
yace


"to anty binta gani ,


ɗaki ta shiga ta miƙo mai ATM card ɗinta tace


"kai ma ka siyi ta 500 sauran ka daɗe ,

anty binta bazan dade ba allah isa kar in sami lahi


Banza tayi mai ta sami gu ta xauna tana yar waka aguje kahu labahani ya fito riƙe da ciki da
alama bayi zaishi ga ɗaga murya tayi tace


"kahu lafiya kake tafiya a ɗur ƙushe?,


wani to tuƙuƙin bakin ciki ne ya zomai huya yace



"Binta ƙar de duk abin da akai ki ce baki jiba ?,


Zaro manyan idanuwanta tayi tace


Kahu ban sani ba me akai


banza yayi mata ya shiga ban ɗaki domin gaskiya fatalwar gimbiya su ta raina gashi ta hanashi
fita nema ta tsame yarta a ciki duk ta'asar da binta keyi


ringing ɗin wayarta taji da sauri ta shiga ɗaki ganin sunan alhaji ta saki murmushi domin har ta
ganota tana fantamawa da kuɗi hello alhaji


"my beb yau zai zo kura zan toro miki address ɗin sa kije mu gwada sa'ar mu kowa ya dubi
halittarki dole ya yaba ,


fari tayi da ƙƴawawan idanuwanta tace

"okay toromin amma da sharaɗi inga kuɗina ,


binta shegiyar kaya duk wata hanya da zaki cutu sai kin ƙauce mata

Alhaji kenan ina tare da ku ba dole in koyi fusaha ba ai sai abarni abaya


hakane my beb yaushe za muyi aurene


"hmmmm alhaji sai na gama cin duniyata da tsinke ,


ni kuma zan baki allurar kidinga tsiƙarar ta


dariya tasa sukai sallama


WANNAN KENAN




shugaban jam'iya yace


mu'azzam zaɓe na ƙaratowa amma banji maganar auran ka ba kasan a tsarin ƙasar nan ba a
bawa mara aure takara mu gashi mun tsayar da kai ƙar ka bamu kunya fa kowa ya zuba ido
yaga yarda zata kaya kuma kasan jam'iyar hamayyah ce ke mulki suna da damar kawar da
mu......


*BINTA YAR JAGALIYA*


By


Oum yasmee


Free page ya kusan karewa fa ku hanzarta mallakar naku

Shiru yayi nawasu sakanni yasan gaskiya suka faɗamai amma shi har yanzu be jin zai iya aure
domin bega wacce ta kwanta mai a rai ba yace


"Insha Allah zan kawo ƙarshan matsalalnan Allah ya dafa mana,


gabaki ɗayansu suka amsa da amin taro ya watsai fito wa yayi ya sami sam na jiransa ya shiga
mota yace me ya kaishi airport domin jirgin 10:45 zai hau gashi goma saura waya ya ɗauka ya
kira muzamfar bugu ɗaga ya ɗaga yace


Aslm muzamfar


daga can ɓangaran yace


"wslm gauro ya gari ,


tsadadɗan murmushi shin sa yayi yace


"tsoho ya sanran ka ?,


wallahi azzam shan tablet ne be ishe ka ba wata ran zai maka illa nasan ka sani sai ka ƙarar
mana da ƙwaiƙwayan mu ko


Lumshe sexy eyes 👀 ɗinsa yayi sai kuma ya fasa ya buɗe yace

A gaskiya muzamfar baka da kunya ya kasuwancin komai na tafiya daidai


"Alhmdllh na rabawa kowa na turo maka da komai ta email sai ka duba ,

Masha allah ina daughter ta tana lafiya

tana lafiya qalau tace tana so taga ɗan daddy ɗinta



hhhhh ai wannan da ku take ba dani ba wallahi wayon yarinyar nan yana ban mamaki



wani zancan intayi wallahi cikin mu ƙullewa yake kai ma da tuni kana da yar ka ko ɗanka



"to to sai anjima ai ka haifamin shikkenan ,


be bari yayi magana ba ya kashe wayar ya lumshr idanuwansa ya shiga tunani wanne mataki
baffansa ya ɗauka zai kawo ƙarshan matsalalnan ne ko kuwa me son ɓata mai suna zai ci
gaba da ɓata mai suna har suka zo airport be sani ba sai da sam yayi mai magana ajiyar zuciya
yasake ya fito ba abin da ya dauko sai brief case ɗin sa kaya ma yana da su a nan ya shiga
reception sai nan nan ake dashi masauki ma me kyau a ka bashi kafin jirgin su ya tashi


wannan kenan


"ƙawas ƙwas kina ina ?,



jin muryar rufaida da sauri ta fito daga ɗaki tace


"RUFAIDA sannu da zowa shi go ,



kayan ta ta tattare domin a ƙwai ƙwata a gun tace


wallah ƙawas ni ba zuwa gidan ku ba sai mutum ya ɓaci

wani banzan kallo ta jefe ta da shi tuni ta haɗiye sauran zancan baƙinta

ta sani sarai duk amintar dake tsakanin ta da binta yanzu za aji kan su tace


"Allah ya baki haƙuri ƙawas ina su kahu naji gidan shiru ko anfita nemane,


kallon ƙofar ɗakin sa tayi tace


"tun safe suna ɗaki har iya me yashin madina ,


haɓa rufaida ta kama tace


"Topa lafiya?,


haɗa rai binta tayi tace


jeki ki tambaye su ta shige ɗakinta

bata da wata da bara ban da ita mata ta bita domin alƙawari ne ta ɗauƙar wa ƙanta sai ta raba
binta da kuɗin nan a komai ta fita ita ta jawota harƙar siyasa amma sun yada ita sun ɗauki binta
mutumin da take bala'in so suke ƙwallafa rai a kansa alhaji me tasa yana son binta da aure duk
da haryau binta bata san irin alaƙarsu ba shi da ita
shiga ɗanki tayi ta sami gefen katifar binta ta zauna mayafin da ta ruƙe shi a hannuta ta rataya a
huyan ta tace


"ƙawata ashe haka abin alkhairi ya faru ?,


kallon rashin fahimta binta take mata

dafata tayi tace


"zancan yiwa azzam ƙazafi nake nufi,

shiru binta tayi ta saki a jiyar zuciya tace

"rufaida na fasa shigowar ki nake jin wani wa'azi duk da banyi wani karatun addini me zurfi ba
nagane ba abu bane me kyau ina tsoran randa ubangiji zai tsayar dani da shi yayi mana hisabi
sharrin zina ba ƙaramin sharri bane abin duniya fararrene ƙararre bansan ko ina cikin yin masa
sharri in mutu ince da ubangiji me da wanne ido zan kalle shi kina ina shekaran jiya jami'an
tsaro har gidan nan suka zo suka tafi dani we yan unguwar nan sun kai musu ƙara zan ɓata
yaran su Rufaidah abubuwa summin yawa ga yawan mafarkai marasa daɗi danake,



wani kallo rufaida tayi mata na baki da hankali tace


"BINTU anya kuwa ba asami wani ko wata sun jefe ki ba domin wallahi wannan maganar da
kike kama tayi da wanda aka jefe iya sanina ba ƙƴashan ƙwaya anya kuwa lafiyar ki qalau
ƙawata kuɗi fa yanke taƙaicin duniya ,


dan murmushi tayi tace


"Sister wallahi lafiya ta ƙalau kawe yanzu bana son wannan aikin,


Dafa ƙafar ɗarta tayi tace


"Dan girman Allah bintu ki rufa mana asiri ki duba fa ki gani mu muke ci da kanmu sittira gashi
kina so ki nemo mahaifin ki in bata wannan hanyar ba ki faɗamin ta ina zamu samu kuɗi har
gwarani jikina shine jarina kefa kinƙi sakin jiki ki mori duniyar ki ,


shiru tayi tana auna zancan rufaida tambas ta wannan hanyar ne zata nemo mahaifin ta tunda
bata da wani kudi sai wanda yan siyasa in tayi musu posting su bata na kashewa



ganin tayi shiru rufaida tace

"ƙawata tashi muje gidan gwamnati kinsan fa yau muna da taro ko ankusan primary Election ko
?,


ajiyar zuciya ta saki tace


"Eh gobe ne ,


yauwa yar gari tashi yanzu lokacin samun mune yau ba zamu dawo ba sai dare


tashi tayi tace


Bara in shirya gashi wannan yaron be kawo min abin kari ba wallahi tsiyar aiƙen saminu kenan
zani ta dauka ta cire kayan ta


duban ta rufaida tace


"Wallahi bintu da zaki fara harƙar nan zaki sami kuɗi komai naki me kyau ne ,


Wani banzan kallo Binta ta jefe ta dashi tace


"Wallahi wallahi rufaida kika ƙara yimin maganar nan sai nayi maganin ki wato ke kin sulhuntar
da naki so kike nima in bayar dashi ba lada sai huya da zunubi ko ,


kwanciya tayi kanta na kallon rufin ƙwano tace


'Allah ya baki haƙuri na dena,


ƙwafa tayi ta fita


Wannan kenan

MU'AZZAM ita siyasa kasuwar buƙata ce wasu mutanan kana zamane da su bawe dan suna
sonka ba a'a sai dan akwai abin da suke nema a gunka lokacin da ya ƙare to zasu gudune su
Barka ka kula sosai da kowa in Allah ya baka kujerar nan



sai a lokacin ya iya duban kakan nasa yace


"BAFFA ina tunanin ajiye takarar nan baffa abin har ya kai da yi min ƙazafi lamarin ƙasar nan
bashi da lokacin gyaruwa komai an lalata ,


kaf cikin jikoƙina kai na dauko saboda nasan zaka iya zuciyar ka irin tawa ce ko mai nawa naka
ne ƙar ka zamo me sarewa kai al'umma ke jira in ka fasa gwiwowin su zasu sare bame iya kula
da ƙasar su in sukai rashin adalin shugaba wa zai maye gurbin ka sau da yawa muna kuskure
amma in muka dawo muna iya gyarawa ina gab da gama binkice akan yarinyar nan


Duban sa yake da manyan idanuwansa yace


"BAFFA wacce yarinya,


Binta yar jagaliya nasa a dinga bibiyar ta ko inta kanta bata sani ba saboda tana da
mahimmanci a tafiyar su me tasa dole ta dawo ƙarƙashin iƙon ka bayan mun gama sai mu jefar
da ita saboda amfaninta ya ƙare zata iya sawa kujerarka ta waɗi amma in muka ɗauke ta komai
yazo ƙarshe bazan yafewa kaina ba inhar ka waɗi saide ban cika me faɗa aji a ƙasar nan ba
suwane dadtawan in bamuba su me tasa yarana ne butulcemin sukai


baffa banga amfanin sako mace a cikin siyasar mu ba


tashi yayi ya ɗo gara sandar sa ya fara tafiya yace


zaka iya tafiya ni kaifi ɗaya ne na gama magana duk abin da na ce maka dole kabi bazan taɓa

cutar da kai ba maganar aure kan tana hannu na insha Allah baza kai dana sani da ni ba

yana fadar haka ya shige ciki yabar shi da kallon hanya gun hajiya babba ya shiga domin su
gaiyasa sosai tayi murna da ganin jikannata tace


Mijina yau kaine a gari


Zama yayi yace

Hajiyan kura ina huni


"Lafiya qalau ya Maman taka ?"


Tana lafiya tsohuwa


Akwai tsohonwan tuzuru irinka shekaru na ja ba aure anya ba zan zaɓo yarinya in aura maka
ba wacce zaka iya haifarta kaga girma ya wadi ko


tanƙwashe kafafunsa yayi yace


"Uhmm kina auramin a ranar zata zama karamar bazzawara ya kikaji wannan zancan,

Muzuba mu gani (next book ɗina )

ba yarda zakai dani wallahi dole ka zauna da ita


Hajiya ina da taro na tafi ki gaida su hajiyan taura


pillow case ta jefu mai tace


Ja'iri anya ba aljana ce ta aure ka ba ana maganar aure sai guduwa

Au tsohuwa baki sani ba ai sunan ta yar mero yafita yana ɗan murmushin


Ya mu'azzam sannu da zuwa


Yauwa jiddah ya Maman taki


Tana lafiya shiga gun hajiya tayi shi kuma ya fita kullum addu'ar ta Allah ya mallaka mata azzam
amma ko kallon ta baya yi ......✍🏻

*BINTA YAR JAGALIYA*


By


Oum yasmeen


Ƙarshan free page


Ku hanzarta mallakar ci-gaba.


*BINTA YAR JAGALIYA*



Me suna


*JIFAN GAFIYAR ƁEDU*

(Ba tsuntsu ba farko)

Ku biyoni domin jin harda zata kaya domin kowa yasan


*Ramin kura da wuyar shiga a gayawa kare ya yi hankali*

Ya wasan zai kaya tsakanin mu'azzam da binta yar jagaliya




shirya wa tayi cikin wani lace onion colour an mai ado da flower blue ba wani me tsada bane
amma saboda kwalliya ta zauna mata sai ka rantsai me tsada ne anmai dinkin have bubu da
strength skirt me tsaka ɗaurinnan tayi ture kaga tsiya ta yafa mayafi a kafada tasa have shoe ta
feshe jikinta da turarurruka agogo tasa da sarka tace

"Rufaida taso ba muga ta zama ba ,


tashi tayi ta ɗauki jaƙar ta da wayar ta suka fice tsayawa tayi dai dai ƙofar su iya domin ita
wallahi tayi dana sanin abin da tayi musu ta buɗe labule tace


"Uwani kahu saminu zai kawo muku indomie sai kuci yau bani da wani kudi sai wanda zan hau
napep ,


idon su a rufe uwani tace


"mun gode binta ,

Kahu kuwa da ƙarfi ya ƙare mai yana jin zancan ci ya taso yace


"Bara in kar ɓo,

karab iya tace


Wallahi labahani kar ka sake ka fita ba fatalwa ta hanaka fita ba kuma in kafi ta balalle mu sami
abincin ci ba saboda nasan halinka cinyewa zakai danni yau zan tafi gida


Iya we wacce fatalwa kuke zance

Uhmm yar nan ba za'aji mutuwar sarki a bakina ba


Uwani ce tayi ƙarfin halin kwashe komai ta faɗa mata


Wallahi ku saki idanku ba wata fatalwa


Banza sukai mata dan ba ita za'a yi sama da itaba


Sister kawe ki ƙwace abincin ki tunda sunki yar da kowa yayi harkar gabansa


Kahu labahani yace


"to manna illir khairi irin ku ubangiji ke faɗa shegiya me yawo da fuska yawa ta hoda bahur duk
kin kwaye fata jijjiɓar kawe matsamin daga gani ba shakka tauraruwa me wutsiya ganinki ba
alkhairi ba hammata duk wari a daure a dinga aski ni wallahi ina tausaya wa masu neman ki yo
ubangiji ya kamaki duk warin zina kike,

fuuuuu ta fice yawa kubu buwa dan yasin ta gaji da cin mutuncin da kahun binta yake mata
wataran sai ta rama dan tana tsoran binta


Kahu kahu kahu wallahi kaji sau uku nakira Sunan ka kadena ciwa ƙawata munci in kaƙi ba
zaka ƙi ganiba su cleaner zan ɗauko maka ku kuma tun kafin in saƙar muku muciji kubuɗe
indon ku


ae suna jin haka suka buɗe idon su saidai basu saki jikin suba dan gani suke za ayi sama da su
tafiya tayi ganin sun dan warware ta saki ajiyar zuciya ae hakkin sai yayi mata yawa masu
majalisar gidan su suna zaune ana zaman banza juyowa tayi zata yiwa rufaida magana taga
anliƙa mata poster din azzam cikin bala'i tace

"Wanne dan bura ubanne ya manna min hotan ko dadɗan mutumin nan wallahi yau alo tsiya alo
danja ,

ganin ta fara bala'i wani ya taso yace


"Ki haƙuri bara in ɗaye wanine ya manna yau su namatasa zai fito zagaye ,


banza tayi mai ta kama hannun rufaida suka tafi ko da suka je gidan gwamnati a waje suka
tsaya suda yan da ba Alhaji ne ya fito yana gyara babbar rigar sa yace


"Yauwa binta ke zaki ja wannan runduna ku watsa taron wannan shegen ƙwaron kai laboss,


Tashi yayi yana lanƙwashe ƙafafuwa yana cije baki yace


"Yess oga gani ,


da ga yau binta ce shugabar ko wanne shege a gidan nan sannan duk wanda a Ka kama karya
sake ya ambaci sunana ni zan san yarda na fito da mutum duk da mun hada maki da yan sanda


Angama oga amma zuciyarsa cike take da haushin binta ko wanne matsayi ta ƙwace musu


Binta ungu ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0