Showing 6001 words to 9000 words out of 13755 words

Chapter 3 - Binta Yar Jagaliya Book Compelet

11 Aug 2026

306

ba zai bacci ba jajar uban can lalle ,

Iya da take sharar bacci bata san wacce wainar Binta ke toyawa ba

A fusace ta fito ta fara dukan ƙofar ɗakin kahu labahani

Cikin magagin bacci yace

Wane mara neman albarka ne yake tashi na tun asuba da na fita nema ban dawo ba sai hudu

Wata da bara ce ta haɗo mata ta maƙe murya tace

"Fatalwa ce ,

Cikin ɗaki kuwa tuni wani irin tashin hankali ya ruske shi Oni labahani a haka mutuwa ta zo ban
cika burina ko ɗaya ba a duniya ashe a fili yake


Gyara tsayuwa tayi tace


"Ai kuwa yau zaka baƙunci lahira domin mun gani ana ta'asa a gidan ,


Dan girman Allah fatalwa kiyi min rai Wallahi ban sani ba cikin yar da bara ya sa ƙafa ya doka a
wa uwani domin Wallahi ba zai fuskanci tashin hankalil nan shi ka ɗe ba yace

"Uwani tashi daman ance in da rai zaka sha kallo yau ga fatalwar gimbiya nan ta dawo kan mu,

Aikuwa cikin masifa ta ɗauko tasar da taci abinci ɗazu ta buga mai tace


"Zan fasa maka kai kafin ni ka fasamin fatsarmama in ban da ka mai dani mara hankali fatalwar
gimbiya ce za tazo gidan nan?"


*Ya ku yan adam har kuna da lokacin yin faɗa alhalin yau zaku mutu*


Innalilahi dan girman Allah ai bansan gaskiya yake faɗa ba kaimin rai Wallahi bacci nake ya ta
sheni

Ai kuwa yau zaku yi kwanan barzahu

Tuni uwani ta saki gudawa a zaune yayin da numfashin labahani da ƙƴar yake fita saboda ta
shin hankalin da yake ciki ko mutsi ba yaso yayi ƙoƙari yake ya tuno addu'a amma ina ya kasa

sai mun jaye nu'ara kulya li'ilafi yake mai mai tawa tun yanayi ahankali har ya dawo da
ƙarfi.........…..✍🏼


*BINTA YAR JA GALIYA*




free page



Dariya ce ta kusan kuɓucce mata ta danne tace

"zan baku zaɓi ku zaɓa in kuna so in barku da ranku sai kun hana saurayin meragaje zuwa
gidan nan in da gaske yake ya fito ya aure ta

ko in hana ku ba haya na tsawan shekara ɗari ko in saƙar maka gudawa ta tsawan shekara
tamanin ,



zaro ido yayi tuni wata gudawa ta kuɓucce mai ji kake tsuuuuuu yawa an saki fanfo taɓa ƙasan
shi yayi ga wani irin wari da ya game ɗakin a zuciyar shi yace


"anxu gun har an fara saƙar min tawa yasan wataran ba gudawa zaiyi ba sai de ya kashayar da
ƴa'yan hanjin sa ,



duban uwani yake amma a baɗini wasu taurari yake gani sun za gaye shi yau yasan ƙar shan
sa ya zo shekara ɗari ba kashi ko ƙwana ɗaya mutum beba yake ji balle mutum yayi shekara
ɗari

futsari ne ya biyo baya jin har da gudawa yo rana daya mutum yayi gudawa yake fita hayyacin
sa balle shekara tamanin ai kawe mutuwar tsaye zaiyi da kƴar ya iya buɗe baki yace



Innalillahi fatalwar gimbiya ku yimin min rai dan allah wallahi ba laifina bane laifin uwani ne na
matsani yaron nan ita ta dage sai ya zo gun mairo

Zuface ta ƙaryowa uwani tace

Wallahi sharri yake mun kullum sai ya bashi kuɗi ko mero


MERO da ta fita hayyacin ta tayi dana sanin shigowar ta ɗakin nan tace

"Eyyy eh wayyo allah,

banzan kallo labahani yayi mata yace

"tsakani na da gimbiya a ƙwai ƙauna ta gaskiya da amana kowa na garin nan ya sheda,

FATALWAR GIMBIYA ni na zaɓi na farko zan hana shi zuwa

a'a ke naki da banne waccan tsohowar da ta kwanta a ɗakin binta zaki taso ta sannan ƙarta
ƙara ƙwana in ba haka ba mu shanye muku ƙafafuwa ke da ita

"To, zan taso ta insha allah haka baxata faruba ,

Duk da halin da yake ciki be hanashi zabgawa uwani wata uwar harara yace

"hmmmm ai duk ke kika jamini saboda san ƙuɗin ki shegiya me subfar ƙaguwa ,

"kun ceci kan ku ni zan tafi chaina ,

Ɗif suka ji da sauri uwani ta tashi ta fito domin tada iya mahaifiyar ta da tazo daga ƙauye


da gudu binta ta waɗa ban ɗaki cikin ta har murɗewa yake saboda dariyar da ke cin ta in
bahaka tayi ba iya ba zata fitar mata daga daki ba in tujara dake ji da ita to iya tafita

Jin alamar gudu yasa uwani ta dafe kanta domin a tunaninta fatalwar gimbiya ce ta tashi sama
domin ƙarta warce mata kanta yasa ta dafe shi


"IYA IYA IYA ,

sosai tsohowar ke sharar munshari har da yahun bacci

Hannu uwani tasa ta buga matashin iya a fusace iya ta sa hannu ta buge hannun uwani tace

Dan allah ku barin na huta tun ɗazu kuke ta shina yawa wanda na ciwa wani bashi


"hmmmm iya yau fatalwar gimbiya ta zo gidan nan ɗazu ta tafi wallahi tace ƙar ki ƙara ƙwanciya
a ɗaƙin ƴar ta in ba haka ba sai ta shanye mana kafafu,

cikin sauri IYA ta tashi ta zabgawa yar tata harara tace

Owani lami me yashin madina ƴar da na haifa da cikina ita ke sharara min ƙarya uwani
bura'uban ki uwani na yi miki kama da wacce fatalwa zata ambaci sunan ta to yasin har in bar
gidan nan a ɗakin nan zan ƙwana


Wasu hawayene masu yaji suka zubu a idon uwani tace dan girman allah iya ki zo mu tafi ƙar
suji ja'in jar da muke da ke

zani ta gyara ta fyace majina ta sai ta matashin ta ƙwanta tace

Alƙur'an uwani ki fita adona in rufe wallahi uwani ina raga miki da iliyane da tuni na zubar mai
da haƙura ai ɗazu itama shegiyar ina jinta nayi mata shiru domin ban zo gidan nan in ƙwanta a
tabarma ba nazo inji laushin katifa ai gashi ta haƙura ta fuce tasan duk tujararta na fita hhhhhhh
gaba da gaban ta aljani ya taka huta



majina uwani ta face ta haɗa hannuwanta biyu tace

"IYA dan girman Allah ki haƙuri ki taso mu tafi ,

wata uwar ɗirga sukaji a lamun abu buwa sun sauka tuni hanjin cikin uwani ya cure gu ɗaya ta
fara zare idanuwa domin ba baƙin magana IYA ta ja musu da ta taso da duk haka bata faru ba

"wani irin ƙugi su kaji guggugug wata ku bil adama kuna da taurin kai na baku dama ku fita
ƙunƙi gashi ni har naje chaina na dawo kuna zaune ,


zaro ido IYA tayi ya dafe ƙirji daman tun zuwan uwani da ta bita Allah sarki ashe sona uwani ke
yi oni lami na shiga ukku yau sai ta Allah tace


*"UWANI* in kin sami kuɓuta ina bin matar me gari naira hamsim kuɗin daddawa ki amso kiyi
min sadaƙar ashirin da biyar sannan ki gina min masallaci da raguwar kuɗin tun huri na keso in

iya sa'alun amma sakalci na ya hanani

yanzu da tayi min rana ina zuwa ƙabari ana tambayata in amsa kuka tasa domin ba haka ta so
ba taso abar mata jiran duniya ,

zuba mata ido uwani tayi da alama IYA ta fita hayyacinta bata san me take faɗa ba yanzu har
yaje chaina ya dawo ji tayi fa a radio ance ba ƙasar da takai chaina nisa

"ɗazu na ƙafa muku sharaɗi kun bujere min to zaku rufe idanuwan ku har sai wani daran yayi
sannan ku buɗe in kuka ƙus kura kuka buɗe to fa rundunar aljani gushshu zatayi sama daku
sannan ki faɗawa labahani ƙar ya sake ya ƙara fita waje da sunan bara sai de yaji anyi sama
dashi bashi ba dawowa,
"To mun gode ,


tuni suka rufe idon su suka fara laluban ƙofa ruge ruge suka shi ga yi ganin uwani ta bangaje
IYA ba ta luraba yasa IYA ta fusgota ta dawo da ita baya tayi wuf ta futa gani take in ta ƙara
second ɗaya rundunar aljani gushshu zata yi sama da su


Ganin iya ta futa yasa itama ta fita a guje har ta buge da garo ɗakin uwani suka shiga suka cure
gu ɗaya hakama malam ya zuba ta gumi dan ko shakka babu yasan fatalwar gimbiya ce ta zo
musu ba mala'ika ba duk abin da ake yana ji har da hana shi bara

duban mero yayi duk ta fita hayyacin ta sai surutai take allah ya rufawa saminu asiri da yau be
ƙwana a idan nan ba

da ya ƙwana da dashi wannan rundunar gushshu zata haɗa domin ai ba zasu bar shi ba
saboda kajin mutane da yana sakat a garin nan kullum cikin cin kaji yake suma harya sammu
su




*WANNAN KENAN*



"wallahi momcy duk abin da zan ja hankalin sa ina yi amma wallahi a banza anya kuwa yana da
lafiya?,

YUSRAH ki nutsu ki gano abin da baya so da wanda yake so shine fa amfanin zaman ki kenan
a gidan wallahi na ƙwaɗayin dukiyar gidan alhaji ƙura kin san kaf ƙasar nan ba na biyun su a
ƙuɗi da mulki ke ce wacce zata zamo silal dawamar mu a daula kinsan a kullum sai naji ɓakin
cikin hajiya turai saboda mahaifin mu ya fi son ta shiyasa har ya bawa bilal auran ta lokacin da
na gane haka wallahi har ƙwanciya nayi a asibiti ƙarshe sai ya haɗani aure da mahaifin ki
wanda bashi da wata shahararriyar dukiya dan haka wallahi ko zan yawo tsirara sai na rusa
hajiyan turai akomai


MOMCY yanzu wanne mataki zamu ɗauka naji hajiyan turai tana cewa we waccan shegiyar
yarinyar zata dawo gidan nan


ƙwafa tayi tace


"Uhmm zanyi maganin ta ,



MOMCY ya zanyi ya so ni duk abin da nake kamar baya gani fa


Dariya tayi tace


"YUSRAH yana kula da komai halin su ɗaya da mahaifinsa zai nuna miki kamar besan komai
ba to kisam mummuƙe yake yana lura da komai sannan duk kan wani taƙun kowa yana sa mai
ido amma zanje gun bokana Jibi,


"TO bye,

"Bye,


washe gari 🌅


cikin sauri yake komai saboda yau suna da taron jam'iya gashi sauran ƙwana sittin zaɓe wani
satin za ai primary election za su yi tsare tsaran abubuwa geznar yasa blue black tayi mai kyau
abinka da farar fata yasa black shoe ga rolex black a hannusa hula ya sa me tangaran gyara
babbar rigar sa yayi ya sai ƙamshi yake zab gawa

ɗauki brief case ya ɗanna remote ya kashe komai na ɓangaran sa cikin nutsuwa yake taka
stairs case wayar shi ce tayi ƙara alamun shigowar message be biya ta ƙai ba ya nufi shashin
hajiyan turai duk inda yabi sai sojojin nan sun gaishe da shi amsa musu yake cikin sakin fuska

a bakin ƙofar hajiyan turai ya tarar da sam driver sa sam yace


"good morning sir ,


morning sam

ɗur ƙusawa yayi ya amshi brie case ɗin sa

miƙa mai yayi

Cikin hausar sa mara fita yace

"sir ga sabuwar jaridar c.n trues ,

cak ya tsaya be juyo ba yace


innaje office zan duba ta

"sir is very important ,

juyowa yayi ya amsa shafin farko yaga picture ɗin shi anyi rubutu da manyan baƙi

*SHIN KO KUN SAN DALILIN DA YANA ƊAN TAKARAR SHUGABAN ƘASA AZZAM BILAL
ƘURA YIN AURE* ✍🏻



*Binta yar jagaliya*


*Oum yasmeen yar mutan yakasai*



Zubawa rubutun ido yayi yawa me shirin gano wani abu wato in kana so ka san asalinka shiga

siyasa rintsai don sa yayi a hankali bakin sa ke furta

*HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL*

ba abin da ya ɗaga mai hankali sai we ana zargin sa da yana hurɗa da karuwa shi yasa yaƙi
aure ringing ɗin wayar shine ya dawo da shi hayyacin sa da sauri ya ɗauka ganin mahimmancin
kira yasa dole ya ɗaga yayi shiru


AZZAM kana dawo wa daga taron jam'iya ka biyo jirgi ka tawo akwai matsala duk da alhmdllh
nayi maganin matsalal


to kawe yace mai sukai sallama kai tsaye shiga ciki yayi domin gaishe da hajiya turai sai wanda
ya karan ce shi zai gane cewa yana cikin fushi sosai fuskar sa har ja tayi abinka da farin mutum
cije leɓansa na ƙasa yayi a rasa da me za ahaɗa shi sai da zina rumtsai ido yayi tambas siyasa
mugun wasa ne in baka da juriya ka shigeta sai a haukata ka ba abin da ya tsana ya ƙƴamace
shi irin zina dai dai ta kansa yayi yayi sallama


cikin fara'a ta am samai yace

"lafiya azzam naga yanayin ka ya sauya wannan fa jaridar da ka duƙunƙune ta me ke faruwa?,

risina wa yayi ya ƙaƙalu murmushin dole yace


"hajiya bakomai barka da safiya kin tashi lafiya,

ajjiye chokalin hannuta tayi ta dauki tissue ta goge bakin ta ta miƙe cikin nutsuwa take takowa
inda yake tace


"Azzam ni na haifeka dan haka kome zakai ka ɓoyemin abin da ke zuciyar ka ni me iya karantar
shine ta idonka ko fuskar ka azzam kai ka ɗe muka haifa duk da haka mun baka tarbiya ta gari
mun hane ka da yin ƙarya me yasa yanzu xaka fara alhalin fusƙar ka ta nuna ? ,


ƙasa yayi da idanuwan sa jikin sa yayi sanyi ya miƙo mata jaridar amsa tayi ta sami gu ta zauna
ga banta ne ya waɗi tayi shiru na wasu sakanni kana tace


"ɗaukaka bata zuwarwa mutum ta cikin sauke dukƙan wata nasara tana zuwa da ƙalubale ba

kowa ne zai yarda da wannan zancan ƙazafi ne duk wanda yayi maka nasan ubangiji ba zai
barsa ba ɗana ƙar ka sa komai a ranka Allah yayi albarka ya dafa maka ,


sosai nasiyar mahaifiyarsa ta shige sa tambas duk wanda yayi sa'ar uwa ta gari ya dace yace



"hajiya zan tafi taron jam'iya sannan zanje kura baffa na nemana,


okay Allah ya tsare


"ameen yau muzamfar zai dawo na barmai komai na kasuwanci na kafin komai ya dai dai ta,


"To allah ya rufa asiri ya buɗa,

"Ameen ya allah,


miƙewa yayi zai tashi yaji ance



yaya ina ƙwana



be juyoba ciki ciki ya amsa yayi gaba abinsa


haɗiye wani yahu me ɗaci tayi tayi zaman daɓaro a ƙasa kai kace yar borice zuciyar ta tayi wani
irin baƙi dan ma Allah ya temake ta hajiya turai ta shiga ɗakin ta sallamar ramlat taji da sauri ta
ɗago kai tana jifanta da wata iriyar harara

Mayafi ramlat ta cire tayi ɗamara tace


"wallahi kinsan ni bana ɗauƙar raini ko ? dan wallahi yanzun nan zanyi ƙasa ƙasa da ke banza
ƙaruwa ,

cikin zafin nama yusrah ta ɗaga hannu zata mare ta haseena ta tare tace


"ƙarya a kai miki ai yusrah baki ga komai ba sai ance miki yau an daura aure na da yaya azzam
,


Ramlat da zuciyarta ta kawo har huya ta ɗauki takalmin ta ta bugawa haseena abaki tana huci
tace


"wallahi kaf cikin ku ni ya azzam ya dace ya aura saboda ni daga dangin ubansa nake kufa yan
karan ƙaɗa miya banza ye kawe,


dariya yusrah tayi ta tafa hannaye ta rangaɗa buɗa tace


"anayi muna jin daɗi ku gama haukan ku ni zan aure shi,


sosai bakin haseena ya fashe yana zub da jini dafewa tayi ta zuba uwar ƙara da sauri hajiya
turai ta fito tace



"lafiya haseena ramlat yusrah me ya same ki haseena ?"

yusrah tayi carab tace


"faɗa sukai ita da ramlat ta sami gu ta zauna ta kurɓi lemo ta sa earpon a kunnanta tana bin
waƙa,

hmmm ni ba zuwanku gidan nan shine matsalata ba aa faɗa kuke ace har yanzu baku girma ba
ko wacce a cikin ku da tayi aure da tuni da ƴa'ƴanta wallahi yanzu nan zan ƙira azzam yayi
maganin ku nasan beyi nisa ba


Haseena tace

hajiya ɗan allah kiyi haƙuri insha Allah ba zamu ƙara ba

Ramlat kuwa sai hura hanci take domin tare suka tashi da azzam ya bata shekara ukku saboda
shi taƙi yin aure yanzu haka tana aiki a asibitin kura ta ɗauki hutu ta tawo nan gu ta samu ta
zauna tace


hajiya ki haƙuri insha allah ba zamu ƙara ba yaran nan ne basu da kunya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0