Showing 9001 words to 12000 words out of 19801 words

Chapter 4 - Tawa Ta Sameni 3 by Halima k Mashi .pdf

ni ba?

menene wanda kike so ba zan iya miki ba gaya min?
nace ok daman wannan ne? to dan Allah kayi hakuri
dama ba wai zanyi wani abu da kudin bane saboda
kawayenmu na makaranta da suke zuwa shi yasa ina
son na dan ringa basu na mota kuma Babana yace kar
na tambaye ka kudi na tambayeshi, to amma kayi
hakuri ba zan sake ba kaji?na kawo maka abincin?kaji
don Allah um ni ya zuba min ido yana kallona na kifta
idona na baka a baki?na fada ina dubanshi ya harareni
na runtse idona sai hawaye na tashi zan shige bedroom
ya jawoni jikinshi to na hakura yi shiru kinga zaki bata
min kwalliya baki bari nace kinyi kyau ba, nayi lamo
kan jikinsa yayi mani magana cikin kunne tashi ki bani
abinci my Dear tashi,na tashi nayi ina yar shgwaba ta
na soma bashi abinci yana ci bayan ya gama ne muka
tarkata sai master bedroom kai yaynmu karshene ya
iya soyayya mai ban mamaki daran ranar ya min
abubuwan da na san yes ni mace ce kauna zalla mai
tsayawa a rai.
Washe gari sai ga Haj Yaya ta kuma zuwa lokacin ma
baya gida tana ta masifa har ya dawo tace su tattara
su koma England tunda yace jira yake ta haihu ai ta
haihun yace Haj kinga dan bai yi kwari ba don Allah ki
bari ko wata yayi tace yayi acan dole suka bari akan
sati maizuwa zasu tafi wannan satin dai mun kwashe
shi ne cikin soyewa,bana manta ranar lahadi ana gobe
zasu tafi ba kowa sai ni kadai yaynmu ya tafi ya kai
Anty Mimi gidansu sallama ina zaune a falona abin duk
yabi ya dameni yanzu in yaynmu ya tafi shikenan ko
sai yaushe zai dawo oho?banji shigowar mutum ba sai
ji nayi an kama min gashi ta baya zan yi ihu sai naji
yaynmu yace ke sarkin tsoro ni ne tunanin me kikeyi ne
ban rufe ba nace tunaninka mana in ka tafi ko sai
yaushe oho?ya zauna zanzo da zarar na samu sukuni
tunda na dade,nasan zan dan kwana biu dama sun
dameni da waya karki damu mun gama magana da Alhj
gobe Haj Maska zata zo sai ki gyara mata dakin kusa
da kicin ko,nayi shiru duk ya damu na kula so yake
yaga na daina damuwa ya jawoni yana min wata
magana cikin kunne na mike nace a'a yace ni ko?nace
eh ya kai hannu zai kamo ni na ruga ya biyo ni muna ta
zagaya kujerun babban falon na gaji inata dariya na
fada kan doguwar kujera ya zauna a jikina nace wayyo

zaka kasheni yace to kin yarda?nace na yarda pls ya
dagani ya dorani a jikinshi hannuwanshi yasa ya balle
maballin gaban rigata ya sa baki yana aikin....kungane
dai,na kuma kwacewa zan gudu yace pls kinga daga
yau bana nan zanyi missing dinshi nace to sai ka
goyani yayi dariya yace to zo hau ya duka na dane ya
sulmiyoni ya kwantar kan kafet ya cire min rigar gaba
daya ya soma sarrafa albarkatun kirjina shi dai yana
son wannan abu daran ranar mun raya shi kan gobe
zasu tafi..
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Washe gari sai da hankalinshi ya tashi ganin yanda duk
na tada hankalina ynxu iman in kina wannan kukan kike
son na tafi?ko ban fada miki ba kinsan kina da matsayi
mai girma a gurina karki damu wata rana dake zamu
tafi sannan ga waya ko yaushe zakijini ki dai kular min
da kanki shi ne nafi so ina share hawaye nace shi
kenan,ni na hada mishi kaya suka fito har gurin mota
na raka su,Anty Mimi sai wani jin kai takeyi,ta shiga
gaban mota zai shiga ma zaunin dryva dama ina kusa
dashi sai na rike mai hannu da hannuwana guda biyu
hawaye suka sake zubo min ya juyo ya rasa me zai ce
yace jeki ki dauko hijabinki mu saukeki a gida in su Haj
Maska sun iso sai ku dawo tare nace to,baya na shiga
mun isa gida ta gaida su Haj Kulu da Shuwa ta shige
dakin Haj Yaya,ina jin Anty Mimi tana ce mata wai ni na
tsaya shagwaba yana biye min da yanxu sunyi nisa dan
haka da ina gaisheta bata amsa min ba sai na dawo
dakin Mama, nan na samu yaynmu yana gayawa Mama
wai don Allah ta lallashe ni duk na damu, Mama tace
kaima ka daina biye mata kuyi tafiyarku zata
warware,yace game da kudin amfanin ko abinci komai
na hannun Kabir, nace mama ni fa da jamila zamuje
can game da makaranta sai ya ringa zuwa daga cen
mama tace badani ba tana min yan aikace aikace na
hada rai kamar za sa ihu yaynmu ya dubeni sai kuma
ya dubi mama yace maman sagir kiyi hakuri su tafi
mama tace ka daina biye mata Abdulrahman akwai

abinda nake hangowa wanda ita bata hangoshi ba, yace
to ko dan kwana biu ne Mama tayi shiru sannan tace
da tayi kwana biyun zan aiko a dakko min yarinyata, ya
dan rusuna yace mun gode ya dubeni bari na shiga gun
Hajiyata,mama ta nufi kicin, ina nan zaune ina jiran shi
muyi sallamar karshe ashe ahi yayi gaba dan kar na
mishi kuka, sai dai waya yayi min wai sun wuce nace ni
kaima haka ko,yace sorry zan kiraki amma sai mun
sauka lfy,nace Allah ya tsare min kai yaynmu yace na
gode kanwata sai kin jini,ni ce na fara kashe waya ina
gaida su Haj Maska suka amsa sai da muka yi magriba
muka ci abinci sannan yaya Kabir yazo
daukamu,maimakon ka bari sai bayan ishai sannan
kazo yace a'a zanje tadi bayan isha'i, Jamila tace yaya
Kabir gidan Anty Zee zakaje yace kwarai can zani
Jamila nace kin san tane tace yaya ne ya kaimu ni da
Sagir da Kamal,Haj Maska tace ai gara ayi auren,Kabiru
yace to Haj kwanan nan ne.
Na gyarawa Haj Maska dakinta katifa biyu ne a dakin
sai kafet sai gurin aje kaya, babban falo muka zube
munyi kallo bayan isha'i sannan muka shige dakin Haj
Maska, nan muka kwanta katifa daya ni da Jamila ita ta
kwanta dayar,bayan na rufo kofata.cikin dare naji
wayata nata ringin na tashi na san yaynmu ne dan na
sa mishi ringin din shi daban,cikin yanayin barci nace
yaynmu yace iyen ba kice ke barci ma kike?nace to ya
zanyi yaynmu yace ban san nayi kewarki ba sai da
nazo kwanciya gsky nayi missn dinki a lot nace gara
kai ga maman daddy nan, ya juya ya dubi mimi da taki
ko kissing dinta yayi wai tana kishi sai ynxu ya san da
ita,sai yace min mmn daddy jego takeyi nace to ynxu
ga shi gari ba kusa ba bare nazo gareka yace me zan
samu ynxu?nace komai ma yace kiss kafin ya karasa
fadi na mishi yace Allah ya bar min ke kina cikin aikina
haka mukayi ta hira har asuba sannan mukayi sallama
dan haka da nayi sallar asuba sai na koma barci.Goma
na tashi da zazzabi na sha panadol jamila ta mana
Break har ina mata jinjina nace Jamila mama tayi
kokari har kin iya girki?ai ko ina cin dankali sai amai,jiki
yaki ko da yaynmu yayi waya ban sanr dashi halin da
nake ciki ba Jamila ce tayi wa Mama waya, da yake
komai namu yana hannun Kabir sai Mama ta mishi
waya, sai da yazo ya dauki Mama suka zo gidanmu ko

zama ba na iyawa yaya Kabir yace mu je Asibitin da
yaynmu yayi Family Card Garkuwa Hosp, nan muka je
bayan likita ya dubani sai ya bani gado yayi ma su
Mama bayanin ina da shigar ciki sai dai yana bani
wahala,sati na daya a hosp amma su Mama sun hana a
gayama Yaynmu don sunce bai dade da tfy ba, sai dai
duk san da ya kira sai Haj Maska ta dauka tace ina
barci,ranar da aka sallameni ya kira ina kwance akan
gadona na dauka a wahalce nace yaynmu......ya
katseni ke ba wani yaynmu me kike nufi da kin daukar
wayata nace bari kaji wlh ya katseni dama na kirane in
kin ga dama kin dauka ince maki kin kyauta sai dai
dadin abin ba ke kadai gareni ba bare abin ya dameni
sai ya kashe wayar,ni ko da yake bani da lfy ban damu
sosai ba.tun daga ranar bai sake kirana ba nima ban
nemeshi ba,yau lfy gobe ciwo har muka shiga wata na
biyu da rashin lfyr rannan da jiki yaki sai da aka kuma
mai dani Asibiti na sha ruwa leda uku,Kamar daga sama
sai gashi yayi min waya na dauka nace yaynmu ka
huce ne?dan Allah kayi hakuri ka saurareni yace ina
jinki nace sanda kake nema na a waya bani da lfy ina
hosp sati na daya su Akhj sunki a sanar da kai don kar
kace zaka dawo gashi baka dade da tfy ba ynxu ma ina
gadon asibiti yau kwanana uku kuma yau za'a
sallameni,sannan duk tsawon kwanakin da ka dauka
kana fushi dani bani da lfy da sauri yace wanne irin
ciwo ne?nace nima ban sani ba sai dai ka tambayi
yaya Kabir ko Doc din yace to zaki iya jina ko wanne
lokaci mukayi sallama, cikin tashin hankali ya yiwa Doc
waya bayan sun gaisa Doc ya sanar dashi ciki gareni
sai dai yana bani wahala,washe gari na fito wanka
kenan sai na samu mutum a bakin gado,yaynmu ne
zaune ya zuba tagumi da sauri na isa gareshi nace
yaynmu yanxu kazo?ya dubeni hannuwanshi ya bude
naje na shiga jikinshi yace Allah sarki babyna duk kin
rame sai farin ciwo ko?na sunkuyar da kaina yace ina
Haj Maska nace tana dakinta ya su Dady yace suna
gaisheki nasan dai ya fada ne nace bari na samo maka
wani abun yace a'a gurin likita zamu koma dake shirya
na shirya nasa gyale wai nasa hijabi na cire gyalen
nasa hijabina.
Muna zaune gaban likita yace ma likita yana so ne a
cire min wannan cikin da sauri na dube shi ban gane

ba ya dubeni ke ba zaki gabe ba ki jirani,suka fita da
likitan da yake dama abokinshi ne yace Maska cire ciki
ba aikin mu bane sannan kayi kuskure da ka fada a
gabanta yaynmu yace Doc Salihu taimakona zakayi
mahaifiyata ta gindaya min doka mai tsanani akan
yarinyar nan sharadin da ta gindaya min tace na zabi
daya na kuma zaba, na farko tace ko in saki yarinyar
nan wanda sakin da zan mata yana nufin barin gidanmu
da mahaifiyata zatayi (wato mahaifina yace muddin na
saki yarinyar mahaifiyata zata bar gidansa)na biyu ko
ta tsine min na kuskura nabar yarinyar ta haihu,a son
ranta kar na kusanci yarinyar kuma ba zan iya ba tunda
ina tsananin sonta na zabi ba zata haihun ba to ynxu
tun bamu je ko ina ba gashi ta samu ciki,Dr Salihu yace
kaima ka san dole ne tayi cikin tunda ba wani mataki
ka dauka ba sannan zaka cutar da ita in har kace ba
zata haihu ba akwai nau'in zalinci,yaynmu yace naso a
dan dauki lokaci ne sannan na san yanda zanyi na
shawo kanta na san bai kamata nabi son rantaba na
saba ma Allah, amma ina son na ganar da ita a
hankali,Dr ya ce gashi ka soma magana a gabanta yace
wannan ba wani abu zan shawo kanta, ni kam lokacin
na kifa kaina a tebir din likita sai kuka nake yi, cikin da
na kwallafa rai shi ne yaynmu yace a cire min ko da
yake ba mamaki tunda dama yaynmu ba wai yana sona
ba an dai bashi ne,soyayyar da yayi ta nuna min don ya
mori albarkatun kirjina ne,ina wannan tunanin suka
shigo yaynmu ya zo gurina ya kamani muka ida
komawa kan wata doguwar kujera,Na dubeshi fuskata
taf da hawaye nace yaynmu ciremin za'ayi yace kiyi
hakuri kinga cikin na baki wahala nace ynxu ai naji
sauki ina sonshi dan Allah a bar min yace ba ki isa
haihuwa ba ki bari sai nan gaba, nace zan iya dan Allah
ku barmin ina sonshi yace nima ina so to amma dole
ne a cire ai bana so in rasaki ne Iman,na dube shi ya
soma ban haushi nace yaynmu kona mutu in dai gurin
haihuwa ne nayi shahada pls kar ku cire min ina son
babyna,sai na ga yaynmu ya daure fuska gami da
hararata gashi in ya sha mur ko kai wanene dole ka
saurara dan haka sai nayi shiru ya kira likitan ta waya
da yake fita yayi ya bamu guri yazo yace to kazo ka
mata inaji ina gani yaynmu ya kwantar dani a jikinshi dr
Saluhu ya danna min Allura har biu sannan yace mu

dan zauna dan tana da karfi ,lokacin duniya ya isheni
na mike nace ni gida zanje sai jiri duhu ya mamaye min
ido na sulale kasa daga nan ban kuma sanin komai ba
sai dai na farka naga Mama da Haj Maska,sai Yaynmu
dake gefen gadon jina nayi sharkaf da lema ko ban
duba ba na san jini ne na soma kuka yaynmu yazo ya
rike min hannu ina ne yake miki ciwo?ban kula shi ba
mama da Haj Maska suna min sannu nace Mama me
yake zuba a jikina?ta dubeni yau me zan gani ni
Habiba?wannan ai jini ne haka jini ya tsinke sai zuba
kan kace kwabo har na fita hayyacina likitan kanshi ya
rude da ganin jinin dake zuba daga jikina ya ma wani
likitan waya yazo sun hadu su biyu a kaina suka ce su
Mama da Yaynmu su fita,Yaynmu hankalinshi a tashe
yama rasa me yake mashi dadi sai safa da marwa yake
yi a kofar dakin tunanin shi in na mutu shine
sanadi,dana sani da nadama kawai yakeyi dan da ya
san hakan zata faru da bai bi san ran Hajiyan shi ba.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Awa daya,awa biyu,har awa hudu basu fito ba sai da
aka kira magriba Mama ta matso gurin shi tace
Abdulrahman kaji masallaci ana kiran sallah yace mmn
Sagir ba zan iya salla cikin nutsuwa ba gara in sun fito
sai nayi tawa,Mama tace ka daure ka je sai kayi addu'a
kaji ko? Haka nan ya tafi ,yana dawowa sai yaci karo
da Dr Salihi,yace yawwa Maska dama kai na fito nema
ynxu mun shawo kan matsalar da kyar sai dai jini muke
so leda hudu zamu duba,yaynmu yace a'a gani ka
gwada nawa in yayi sai ku diba ko laida nawa kuke so
Dr yace biyu zamu diba a naka yaynmu yace Allah duka
za'a diba haka kuwa akayi Mama tayi ta yima yaynmu
fada wai ya zai kwanta adibi jini har leda hudu?yace
mmn sagir mu dai yi fatan samun lafiyarta haka aka sa
min jini hannu biyu sai da na kwana biu bansan inda
kaina yake ba sai da na farka jinin ya kare sai
ruwa.Dishi-dishi nake gani ban san su waye a dakin ba,
hasalima dakin shiru sai karar fanka a hankali idona ya
soma washewa naga Mama da anty Yagana,sai Babana

da Alhj, sai kuma Malam. Nakai dubana kusa da kaina
Yayanmu ne daf dani da ganin shi yasa komai ya dawo
min sabo a raina nace abin da kake so shi yake
wahalar da kai,hawaye suka shiga yimin zarya sannan
ne yaynmu ya gane na farka da sauri yace Iman kin
tashi ne?ya kamamin hannu su Mama suka zo suna
min sannu gami da yiwa Allah godiya,wasa wasa kwana
na sha daya,Yau monday na fito wanka ina zaune a kan
gado yaynmu ya shigo Mama da Haj Maska suka fita
bayan sun gaisa ya dubeni Iman ya jiki?nace da sauki
fuskata babu walwala yace iman ki min afuwa na san
nine sanadin sakaki cikin wannan halin amma ki min
hakuri bana son rasa ki ne shi yasa,ni dai shiru na
mashi nasan duk dadin bakine yake min yanxu na gane
in mutum yace baya sonka tun farko ba zai taba sonka
ba,sai dai wani abu to shima yaynmu na gane
albarkatun jikina kawai yake so ba wani ni ba dama
nasan ni ba ajinshi bace shishshigi nayi
Ya tabani Iman tunanin me kikeyi ne?na zame na
kwanta hawaye ya soma min zarya abin da yafi bani
haushi yanda har ynxu zuciyata take matukar son
shi,har ynxu son na nan ba zan iya fdama wani ainahin
abinda ya sameni ba,Likita ya shigo bayan dube dubene
aka sallameni sun yanke shawarar Mama ta wuce dani
gida don haka gida muka tafi shi kuma yaynmu su
babana suka ce ya koma,ranar da zai tafi ya shigo
tunda na gaishe shi ban kuma magana ba, ba yanda
baiyi ba in yi magana naki daya matsa min sai na sa
kuka, ya kifa kanshi akan gwiwoyinshi na dube shi duk
ya rame a raina nace duk kai kaja ni ynxu don son da
nake maka zanci gaba da zamada kai baya ga haka da
sai dai ka sakeni ya mike to Iman na tafi sai kin jini a
waya ko motsi banyi ba bare na tashi nace Allah ya
kiyaye hanya yadan dubeni sai kuma ya tafii,Tunda ya
tafi kullum zai min waya sau uku,amma daga gaisuwa
bana kuma magana har mama ta gane sai fada take
min tanacewa ai ba shi ne ya dora min ciwon ba in
kuma cikine ai Allah ke badawa dan ya zube sai na
zargi mijina.Na warke sarai jikina ya dawo nayi kiba
mama tace na koma dakina nace nidai tunda Haj Maska
ta koma Maska sai su yaynmu sunzo zan
koma,watanshi uku da tfy suka dawo saboda zuwan
watan Ramadan nan da sati daya, ina falo ina kallo naji

ana masu oyoyo duk da son ganin yaynmu da zuciyata
takeyi sai naki tashi,dakin Haj Yaya suka yada zango
sai daga baya yaynmu ya shigo dakinmu, na dube shi
kullum dai yana nan dan gaye dashi jikin nan sumul,
yace gimbiya ina gajiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login