Showing 15001 words to 18000 words out of 19801 words
Chapter 6 - Tawa Ta Sameni 3 by Halima k Mashi .pdf
ya saki jakar yana kallona ni
ko na juya na kuma juyawa a gabanshi nace nayi?ya
rungume ni gami da fadin zaki kashe ni da salon gayun
ki big gal,ina sonki nima na kankame shi nace nima ina
sonka guy,muka nufi cikin gida,rayuwa kenan koda
sunan wasa ban taba zaton yaynmu zai zama mjina ba.
sai bayan babbar sallah muka soma shirin zuwa gida
don bikin yaya Kabir Amira kam anyi nata, ban so bana
nan ba sai dai alkawarin zanje yola gurinta
Mun fita dan yin tsaraba kudin da yaynmu ya zube min
har tsoro ya bani, nayi kwalliya cikin suit riga da wando
na sa karamin hijabi mai tsayawa iya wuya yayanmu
yace kinyi kyau sai dai ba in sadaukar da jikinga ga
wasu, canja, dole na sa siket da riga na jeans blue,yace
saka abaya na saka yace kai itama tana nuna jiki sai
dai muje na ringa kareki nace kai yaynmu ka cika
kishi,yace na ji ba komai. Mun yi tsaraba sosai sannan
mun zaga sai gurin sha biu muka dawo,a cikin jirgi ina
lafe a jikin shi kamar mage yace saura yan mintuna mu
sauka a kano nace to waye zai kaimu KD?yace akwai
jirgi da zai je daidai sanda zamu sauka sai mu shiga,na
ce amma gidan su mMama zamu ko?yace a'a gidanmu
zamu nace kai yaynmu kai guy kaga nayi missin din
maMama,yace kada ki bata bakinki nace to ai da Aunty
Mimi ne can kuke sauka sai ynxu na tuno da Aunty
Mimi har gabana sai da ya fadi saboda tuno su da
nayi,dana manta da yan matsaloli yace naji kinyi shiru
ne ko da nike sauka a gidan dan saboda ke ne in ganki
kawai amma ke sai ki boyewa ganina na dago ina
dubanshi saboda ka ganni yace tabbas nace dama
kana sona ne?yayi murmushi gami da kara rungume ni
tsam! Kamar yanda kike sona muka yaudari zukatanmu
ke ban san hujjar ki na kin gaya min ba amma ni
hujjata na riga na cika baki gurin abokina bana son su
min shakiyanci shi yasa naso kiyi karatun in kin girma
sai in nuna ina sonki ,sai gashi kin nuna aure ki keso
kika sa hankalina ya tashi(confession tym)karshe
sanda na samu lbr sa ranar ku da Adams naje Umara
na roki ubangiji ya bani ke, ya amshi adduata cikin
sauki ya bani ke lokacin da na soma yanke kauna da
samunki,na kara shigewa jikin shi nace nima sonka
nake guy tamkar raina yace kar ki rainani kar ki ga
rashin girmana nace yaynmu ba raini tsakanin mu sai
ma girmama da ka kara a idona.Muna ta hira har muka
iso, muna mota nace yanxu yayanmu gidan ka zamu
wuce?yace kina ganin zan yarda nayi missing dinki?
jikina ba zai iya kwanciya ba in har bake.Muna isa
gidanmu yaya Kabir yasa an gyara mana gidan tsaf,
Aunty Mimi bata gidan nayi mamaki ban tambaya ba
bayan munyi wanka mun ci abinci da mama ta aiko
mana sannan muka fito sai gida.Munyi murna da ganin
juna na shiga gurin Haj Yaya ta tamke fuskarta ko
kallona batayi ba, na kari gaisuwata na tash,i da
daddare muka koma gida.Haka akayi bikin yaya
Kabir,mun hadu dasu Mami mun rungume juna,Mami
tana da tsohon ciki ta ce kai Iman me yaynmu yake
baki ne?kinyi kyau kin zama big gal ga wani class na
musamman da kika kara nace Mami kinyi fa gsky Nasir
yana kula mana dake,muka shiga dakinsu Jamil,a nan
take bani lbr rigimar yaynmu da Mimi, tayi mamakin da
nace mata ban sani ba dan yaynmu bai gaya min
ba,nace gsky naga bai taba kiranta a waya ba tun da
muka je,Mami tace ki tashi tsaye ki dage da adduoi dan
an ce suna nan suna shiga bokaye don su rabaku,wai
kema da asiri aka aure ki wai duk abinda yayanmu ya
ma Aunty Mimi ba yin kanshi bane asiri ne, nace su dai
sun kasa gane kaddara, Mami na san ina son yaynmu
so daya tak amma ban taba tunanin zan aure shi ba
dan na san cewa koda wasa niba ajin shi ba ce,to da
da yake Allah ya kaddara da aure a tsakaninmu ana
saura kwana uku biki Adams yace ya fasa Allah ya sani
ban taba shan wani abu ko zuwa gurin wani dan
yaynmu ya aure ni ba,Mami tace na sani kin san abinda
mutane yakeyi,zai dauka haka kowa yake, tace saima
kin ga Mimin duk ta rame, nace sun sa kansu a uku ni
ban ma ganta ba,Mami tace tana nan ban ganta ba sai
a gidan amaryanan muka hadu,gabana yayi mugun
faduwa amma na dake tana ganina ta tafi,Dady ma
gurin mamanta na hange shi.Zaune yaynmu yake a
gaban Haj shi tana yi mashi fada akan abinda yayi wa
Mimi ta kawo kara har da cewa yau din nan nake son
kaje gidansu ka bata hakuri ta koma in ba haka ba zaka
sha mamaki zaka ga yanda zanyi maka, ai ka bata min
rai na karshe ka daketa sannan ka tafi abinka ba waya
ba aike,yace yo ya take so ne haj? Ya Mimi take so
dani ne? baki fa san abinda take min ba banda ke Haj
da kike tsakaninmu da tuni ta koma gidansu ta koyo
tarbiya in dai tana son zama dani,ya cigaba ke kanki ki
dubi jikina wannan zuwan nafi kiba yarinyar nan da kika
tsana tafi kula dani fiye da yanda ba kya zato gashi
tana bin dokata tare da girmamani duk abin da nake so
tana min fiye da yanda na bukata sannan.....ta daka
mishi tsawa kai!.....ni dai na gaya maka in ta maka ina
ruwana?ni dai nace kaje ka mai da Mimi yace ai bani
nace ta tafi ba tace bana son wani kwane kwane, kaje
ka maida ita yace shi kenan baru inje wanka,Bansan
abinda ake ciki ba ina gida na gama gayuna yaynmu ya
shigo nayi sauri na tashi na tare shi ina fadin yaynmu
ina ka shiga ne?yace naje gida hadamin ruwan wanka
nace ina zaka? Ba ka yi wanka dazu ba yace to ai ynxu
tadi zanje na rungume shi nace gaya min gsky?ya sha
mur ana wasa da maganar aurene?Na fada kan kujera
nayi shiru ya zauna kusa dani tashi big gal kar tace ta
fasa aure in shiga uku, nayi kicin a zatona da gaske ne
nace cikin shagwaba ni ba zan hada ruwan wanka da
za'aje tadi ba na turo baki gami da cewa to menene
bana maka?gaya min na dinga yi maka kaji?na fada ina
dubanshi sai ya fita yana fdin to ni bari naje na hada
nayi ina nan zaune sai gashi cikin tattausan yadi milk
yayi kyau sosai na tashi da sauri na fisge key din
motan na ruga uwar daki da gudu na wurgashi bayan
gado ya biyo ni big gal ki bani key dina na shiga toilet
na kulle na gaji da jira ya tafi.Ina girki duk raina a
jagule na son ko wacce yarinya ce zata so yaynmu dan
ba irin mazan da za'a kisu bane shi kam wancan
lokacin yana gidan su Aunty Mimi, bayan ya faka da
mota sai ya kira ta a waya sau uku tana tsinkewa
sannan a na hudu ta dauka yace ke ana miki waya kin
ki dauka kar ki raina min hankali fa,tace gidan bakonka
ne da ba zaka shigo ba?ta kashe wayar yayi kamar ya
juya sai kuma ya fasa dan ya tuno da Haj, yasa kai
cikin gidan tana zaune a falo ddy yana barci a kan
carpet,Haj Laure tana waya,ba wanda ya amsa mishi
sallamar da yayi ya sami guri ya zauna,Mimi tski kallon
inda yake a karshe ma sai ta tashi tayi ciki abinta ya
dubi Haj Laure yace momy ina wuni? fuskarta a
murtuke ta ce lfy lau ,yace momy nazo ne mu tafi gida
da Mimi, tace eh da yake babyn wasan yara ce Mimin
dole kace haka to ba zata koma ba sai naji dalilin duka
da kana son ka tafi da gimbiyar taka ai ba sai ka
daketa ba in kace ba zaka bita ma ya isa yace momy
kar ki tsaya dawo da abin daya wuce kuma zagina fa
tayi ai ko kina gurin kya ce na ladabtar da ita tace
karya ne kace ta zage ka, kai dai kaje kaida Allah batun
komawa kuma ba zata koma ba, yayi shiru yana tunanin
yanda zaiyi shi dai yana son cika umarnin Haj shi ne
yace momy kiyi hakuri dan Allah ba zan kuma ba jin
haka sai tayi zaton aikin Malmin nasu ya cine,dama
yace da kanshi zai zo yana bada hakuri kuma komai
suka ce yayi musu zai yi masu,koda Haj Laure ta tuno
da wannan kuma ta ga abinda ya faru(yana bada
hakuri)sai tace mishi ko zata koma tana bukatar
kudaden da zatayi gyaran daki,yace ba matsala zan
bata tace to sai ka aiko da kudi in an gama gyaran
gidan ta koma yace shi kenan zan zo anjima ko gobe
na kawo,ya fita ranshi a bace ya tafi,yana mota Haj shi
ta mishi waya wai ya dakko Mimin?yace sunce sai
anyu mata gyaran daki ta ce sai ka bata ko nawa take
so tunda ita yar rukon taka wa ya san kudin da ta
samu a gurinka, yace ai nace zan bada tace to shi
kenan,bayan ya kashe yayi tsaki gami da cewa an
auran matsala
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Zaune nake cike fam tamkar zan fashe,yaynmu ya tafi
tadi Aisha n Adams tai min waya sama sama muka yi
hira saboda bana cikin hayyacina,na jefar da wayr kan
kujera ina tsaki na dubi agogon bango awa uku kena da
fitar shi lallai tadi yayi kyauzya shigo da sallama da
kyar na amsa mishi ya zauna gami da fadin big gal bani
abinci nace au bakaci a can ba?to nima ba zan baka ba
ya tuno yanda suka rabu sai ya yi murmushi dan Allah
big gal kar ki min haka ina jin yunwa kar na kara fusata
nace ina da abinci amma ba zan baka ba kuma ka
daina ce min big gal tunda yanxu ka daina sona,ya taso
yana dariya yana fadin to ai yarinyar ma tace bata sona
na mata tsufa,na dubeshi idona tam da hawaye nace
kaine za'ace baa sonka bayan kana da kyau da kudi?ya
jawoni jikinsa gaskene wai bata sona nace mata tazo
taga biga gal a gidana nima na fasa,da na kula
tsokanata yake sai naje na kawo miasi abinci.Rigima
kala kala na dinga mishi yana lallashi gami da
zolayata,ya basu kudi masu yawa amma har ynxu suna
nan suna ja mishi rai a cewar su sai sun ja mishi aji
gami da sashi ya sakeni yaje ya basu hakuri bisa
tursasawar mahaifiyarsa nan suka rufe shi da masifa
ita da uwarta bai tanka ba sai da suka gama sannan
yace ni dai ina baku hakuri ne tazo mu tafi,Haj Laure
tace sai ka je ka saki wannan matar taka! Ya mike da
sauri Momi me kike fada?tace nace ka saki Iman, yayi
mata duban kinyi kadan sannan yace Momy ki sake
sabon tunani in har sai na saki Iman Mimi zata koma
gidana to ta zauna dan ko mutuwa da ina da yanda
zanyi da ba zan bari ta dauki Iman ba,zan iya rabuwa
da kowa a ciki harda ku da dai na rabu da Iman, ya
wuce fuuu!!yana fadin in ta ga dama ta dawo in kun ga
dama kar ta dawo, yatafi ya kashe dukkan wayoyinshi
dan ma kar a kirashi.Ina kishingide ina tunanin maganar
Babana da ya ce inyi tunanin irin kasuwancin da zan
fara a bani kudi, sai naji an rungumeni ta baya da sauri
na tashi yaynmu ne yayi wata wawuyar ajiyar zuciya
nace guy lfy?yace sonki ne naji yana son ki ne naji yana
son faso min zuciya ya fito waje, dadi ya kamani nace
guy nima ina sonka ina tuna wata rana zaka iya min
halin maza ka sakeni sai in ta kuka,yace big gal auran
mu yafi auran zobe karfi ya shafi zoben hannuna tun
wanda ya bani yace ki kalli cikin zoben nan me zaki
gani na tsura masa ido(AA)nace AA ne a ciki yace to
Amina Abdulrahman for ever zaki gani cikin zoben ta
baya,kafin na kuma magana sai naji bakinshi cikin nawa
ya mantar dani duniyar da muke.
Mimi ta kalli haj Laure tace gaky momy nifa zan koma
gidan baban Dady tunda kin ga an samu wancan
maganin yayi yazo duk abinda muka ce yayi ni kuma
Iman in shiga ba sai in san yanda zanyi waje da ita baz
Haj Laure tace shikenan tunda kin dage ai sai ki koma
dan dama ni nufi na in karbar miki yanci,da sanyin
safiya munyi lako lako ni da guy dina muna kari sai
mukaji sallama tun kafin su gama shigowa muka gane
su su Anty Mimi,ne nan da nan na ga yaynmu yayi kicin
kicin da rai ya ajiye kofin hannunshi ya ja tsaki, nice na
amsa musu sallamar su gami da gaishe su, basu amsa
min ba sai suka nufi dakin Yayan mu ya yi dakin nima
nayi nawa dakin.Sun danyi fushin su da juna na kwana
biu suka shirya, sama sama take min magana nima
bata gabana, kwata kwata kwananta uku yaynmu yayi
shirin tfy, Haj shi taso ya tafi da Mimi sai yace shi ba
zai tafi da kowa ba saboda wani club zasu siyeshi
kuma bai san yanda abin zai kaya ba, tunda ya tafi ta
tsiri yawo kullum ba ta nan,ni dama ban cika fitowa ba
tunda abinci kowa nashi yake yi,yana kirana a waya
musha hirar soyayya ya sanr dani wani club sun
sayeshi miliyoyin kudi, kafin wata uku kowa ya san
yaynmu yayi kudi gidan su ma ya sha gyara
musamman dakin Hajrshi da dakin Alhj, motoci uku ya
sai musu. Muma ya soma gina mana namu gidan a
malali na gani na fada, tsarin gidan ma abin fda ne sai
da ya turo da kudi kabiru yake gabatar da komai
,yanuwa da abokan arziki aiken kudi da tufafi kowa sai
sa albarka yake.Ranar da zaizo bai fada ba zuwan
bazata yayi,ni kadai ce a gidan Aunty Mimi an tafi
yawon bin bokayen da aka saba, lokacin ko tunanin shi
na keyi sai naji ana kwankwasa kofa cikin faduwar
gaba na bude dan bansan kowane ne ba ina budewa
sai naga yaynmu ban san san da na daka tsalle na
dane ahi ba shima cikin murna ya rungumeni muka
shige cikin daki ya sauke ni akan kujera yace me ya
same ki ne big gal?kinyi wani ciwo ne?naga kin rame?
tunaninka guy shine ya ramar dani ya kuma rungume ni
tare da yan wasanni yana gayamin yayi missn dina a
lot,bai tambayeni Aunty Mimi ba,na shirya mishi abinci
ina fadin ban san kana hanya ba guy dana shirya maka
abinci na musamman amma gobe kace ma abokanka
suzo lunchn ya ce to shi kenan big gal
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Da daddare na shirya mishi farar shinkafa da miyar
dambun nama,yana ci na ajiye mishoi coke mai sanyi
na gwangwani,ya dubeni tun yaushe Mimi ba ta nan?na
ce dazu ta fita bai sake magana ba, muna tare har
goma bata dawo ba na tsuke cikin riga da gajeren
wando ,albarkatun kirjina duk sun fito,hakika kwalliyata
ta firgita guy,dan na lura ya nuna kwalamar shi a
fili,duk da fitar da Aunty Mimi tayi ta mugun bata mishi
rai sai yace big gal zamuje dakina na ce guy dakinka fa
kace me zanyi a ciki cikin zolaya nake magana yace
lada zaki samo ko ba kya so? nace ina so mana amma
sai dai ka goyani,ya ce abu mai sauki zo ki hau ya
duka ni kuma na dane bayan shi muka fita muna
dariya,mun kai tsakiyar falo sai ga Aunty Mimi ta
shigo,ganinmu ya bata mamaki musamman ma da bata
san yaynmu ya dawo ba,jakar hannunta ta fadi shi ko
guy sai yayi tamkar bai ganta ba ya shige dakin shi,kan
katifa muka fada ya nuna min karshen soyayya dama
gashi tunda ya tafi ko yaushe cikin kitsa kaina na ke
yar borno da yar arab suna kawo min kayan harka ga
na Anty Yagana,Mama ma tana aiko min dana ta a
gefe,rudewa yaynmu yayi ya gigita wane irin abu na bai
min ba haka bayan nutsuwa tazo yace big gal dama
kina bina bashi yau kam wannan rana nasa ta a cikin
ranakun tarihi sannan duk wanda nake bi bashi ko nawa
ne ranar yana tafe na dubeshi sai dariya nake yace au
dariya ma na baki washe gari har tara na safe muna
manne da juna yaki i tashi wai sai nayi barci jiya banyi
barci sosai ba,zan shiga da kaina in hada miki ke dai
Allah yayi miki albarka me zakici?na dauka wasa ne
ashe da gaske guy shine yayi mana break shi ya min
wanka sannan nayi kwalliya muka fita sai gidanmu,can
muka samu Aunty Mimi ina zaton kara ta kawo,kwana
biu mun sha soyayya dan guy karshe ne ya iya tsantsar
soyyaya, Aunty Mimi ta amshe shi suna tafke rigima
sosai har yayi sanadin dukanta,bata dai tafi ba dan ya
ce kuma in ta sake fita bai sani ba ta tafi kenan yace
yana son ya tafi dani ne yana tunanin Hajiyarshi ,amma
zai gwada yi mata maganar da na ga bai kuma
maganar ba har tazo na san ba sa'a.bayan tafiyar shi
na shiga laulayi kin gaya mishi nayi ko ya yi waya sai
dai na daure mu sha hirarraki, ko asibiti naki yarda
naje, nayi sa'a wannan karon ya dde sosai dan sunyi
wasanni,ga na Nigeria da zasu yi na gasar cin kofin
duniya,ni kaina ban san ko wata nawa bane amma har
ya fito,Anty Mimi tunda taga cikin sai hankalinta ya
tashi,suka shiga shige shige sai ga Aunty Mimi wai tana
iya cin komai tayi ta lallashina naki karba