Showing 3001 words to 6000 words out of 24906 words

Chapter 2 - Dani Da Mijina Book Compelet

01 Sep 2026

257

marairaicewa tace baba Dan Allah baba kajanye maganar auren nan
Ran baba ya baci yace maganar auren nan dole ne saboda haka kitashi kibani guri
Cikin matsanancin kuka afra ta tashi taje dakin yaya affan tayi sa a kuwa ta iskoshi tana xuwa ta
xube gabanshi tana kuka tana roqonshi
Dan Allah yaya affan kaje kabawa baba haquri wallahi komai nakeyi nadaina wlh idan akayi
auren nan xan mutu Dan Allah, ,,
Ya katseta da cewa
Ni amfada maki sonki nakeyi ne to kisani nima banasonki bana qaunarki mexanyi dake yar
qwailarki ni nafi qarfinki kuma idan har akayi auren saina gyara maki xama Dan sai kinyi Dana
Sanin xuwa duniya kuma kitashi kifitar mun daga daki bana son ganinki
Hankalin afra inyayi dubu ya tashi a duniya babu Wanda take tsoro kamar yaya affan idan har
yana gida bata wani sakewa to inaga sunyi aure tashin hankali ihu ta saki a dakin tana kuka
Ran affan ya qara baci ya hasala ya isa inda take ya damqi lallausan gashinta yayi mashi
mugun riqo itako sai ihu takeyi kamar tasaki fitsari saida yaga dama ya saketa da kanshi aiko
yana sakinta taje dakinta a guje tafada kan gado ta bude wani sabon kuka

Afra tana fita shima affan yaji ranshi yayi mugun baci yarasa meyake damunshi qarshe yaje
toilet ya dora alwala ya tada sallah

A bangaren shirye shiyen biki yakeyi Dan har mutanen xamfara babu Wanda bai saniba baba
da kanshi ya bada sadaki dubu hamsin xa a daura aure assabar ta sama yakama saura kwana
goma kenan Amma a bangaren amaren kuwa kowa yanajin haushin kowa

Umma tayi fushin harta gaji ta sauko itama ta fara shirin biki amm taje ta samu baba ta roqeshi
a daura aure Amma tarewa saita gama karatun ta baba yace bashi xata tambaya ba affan xata
tambaya saboda shiyake da iko da matarsa ranta ya baci Amma bata nunaba tace babu komai
xan roqeshi Bayan tafito dakin baba dakinta ta koma sannan ta aika sagir qanin affan din tace yaje yakira

mata affan
Bayan yan mintuna saiga affan ya durqusa gabanta yace
Umma gani
Umma tace dama ba wani abu bane akan maganar auren nan ne tunda alhaji ya nace sai anyi
auren nan ba yanda xanyi Amma afra baxata tareba sai tagama karatun ta
Affan yayi qasa da kai tabbas bayason afra amma yanda umma take nuna fifiko tsakanin affan
afra abun yayi yawa ai kamata yayi ta tambayeshi idan ya yarda taci gabada makaranta ba
waita yanke hukunci ba saboda idan anyi auren shiyake da iko da ita
Umma ta katse mashi tunani da cewa
Naji kayi shiru ?
Umma Kibari xan tambayi baba duk yanda mukayi dashi xan fada maki
Umma tace bance katambayeshi ba ansa nakeso kabani yanxu kaga afra yarinya ce duka
14years all Dan haka saita gama makaranta
Affan yayi murmushi cikin ranshi yace nagane abunda kike nufi umma a fili kuwa cewa yayi
babu komai da kaina xan nema mata makaranta Dan xan canxa mata makaranta xuwa
bourding skul
Umma taso tayi mashi gardama akan cewa yabarta inda take Amma sanin halin affan xai iya
cewa baxata cigaba da makarantar a gaba daya idan tayi mashi gardama shiyasa tace to yanxu
wace makarantar xaka Maida ita ?
Affan yayi kamar mai naxari yace ina son xan kaita G G S S JIBIYA saboda makarantar tanada
kyau sosai
Umma tace haba affan jibiya ai tayi nisa
Affan yace umma can nakeso kuma can xataje
Umma tace to allah ya bada sa a
Yace amin sannan taci gaba da yimashi yan nasiha da shawarwari

Duk Abun nan da akeyi afra nacan kwance babu lafiya xaxxabi mai xafi ya rufeta ba a saniba
saida umma shiru sannan tace affan naji afra shiru koxakaje kaduba ta umma tanayin haka
Dan su Saba kuma su shirya a matsayinsu na ma auratan sati na sama
Affan kamar baxaijeba amma tunda umarni na mahaifiyarshi ba yanda xaiyi dole yaje
Aiko yana shiga dakin yaga kamar babu kowa gashi kuma cikin duhu saida ya kunna wuta
sannan ya hangota can qudundune da bargo sai rawar sanyi take cikin sauri ya isa inda take ya
yaye bargon yajishi da dumi yataba jikin afra kamar garwashi da sauri ya dago kanta xafi rau
idanuwanta a rufe daukar jarirai ya mata da sauri ya kaita gurin umma Umma tana ganinshi hankalinta ya tashi tafara kuka tana cewa lafiya affan meya sameta?



*yawan comment yawan typing*

*taku ummu Meenal*
[9/4, 4:29 PM] Aysha Galadima: *❤❤❤DANI DA MIJINA❤❤❤*

❤❤❤

*NA MRS SADEEQ (Ummu meenal)*


*DEDICATED TO AYSHA GALADIMA*


*Short story*

*page 21-25*


*WANNAN SHAFIN NAKUNE ❤ DANIDA MIJINA FANS*❤


Umma tana ganinshi hankalinta ya tasha tafara kuka lafiya affan meya sameta?
Shikanshi affan baesan meyake faruwa da itaba saboda haka bashida ansar da xai bata
Can yayi qarfin hali yace umma bara nakira baba yaxo da mota aje asibiti
Umma tace hi sauri kakirashi kada afra ta mutu
Kafin affan ya kira baba afra ta farfado tana fadin
Ruwa ruwa muryanta duk ta dushe da alama taci kuka harta qoshi
Umma cikin sauri ta dauko pure water tafasa tabata aiko tasha ruwan sosai ahankali ta koma
kan cinyar umma ta kwanta ita kuma umma tasa affan ya dauko mata towel tana sawa cikin
ruwa tana dafawa afra cikin ikon Allah xafin xaxxabin ya tafi
Shi kuma affan sai kiran wayar baba yakeyi Amma bai samuba daga qarshe ya tsaya yana
kallon soyayya tsakanin umma da afra affan yayi murmushi cikin ranshi yace umma ko kinaso
ko bakiso saikin rabu da ita nan da kwanakki kadan xataje makaranta
Ita kuma afra barci ta koma abunta sannan umma tace mashi Naga kamar jikinta da sauqi
tunda tasamu barci kaje kasiyo mata magani idan ta tashi saita sha
Haka ya fita da niyyar siyo magani akan hanya ya hadu da wasu abokanansa suna ganishi suka
fara
Ango ango
Cikin mamaki yace waya fada maku ni ango ne
Aliyu daya daga cikin abokanansa yace
Aini wlh baba ya burgeni da yayi maka haka ace kayita xama babu aure yanxu ko da yayi maka
haka aiya kyauta
Affan cikin jin haushi yace idan banyi aure ba ina ruwanka kai bakayiba
Aliyu yayi dariya yace affan bakasan ni imar da take tartare da aure ba shiyasa amma yanxu
ranar da aka kaimaka mata washe gari idan munxo xamuga canji
Affan yace Dan Allah kubarni da maganar auren nan ni wlh ba a son raina xanyi auren nan ba
duk daga baba ne
Aliyu yace affan waiko bakada lafiya ne

Affan yayi murmushi yace kafi kowa Sanin lafiya ta Lau saboda idan sha awa na yatashi kai
kake siyo mun magani
Aliyu yace ai yanxu matarka itace maganinka
Affan yace kai mexanyi da wannan yarinyar afra ce fa xan aura
Dariya sukayi gaba dayansu
Affan yace wannan yarinyar tayimun qarama ai sai inraba biyu
Dariya suka sake gaba dayansu


Ana saura sati daya biki mutanen xamfara sukaxo harda yayyen amarya da abokanan arxiqi
aunty Asma u harda guxurinta na kayan mata sai dai umma ta hana abata a cewarta sai
lokacin tarewa yayi
Afra kam tasha kuka harta godema Allah shima affan ya barwa Allah komai tunda dai ba fasa
auren xa ayiba

Maganar kayan daki babu abunda aka siya sai lokacin tarewa yayi tunda yanxu karatu xata
cigaba dashi bayan daurin aure
Ranar jumma a abokanan affan Sunxo har gidansu affan Sun iske gida ya cika da mutanen biki
da qyar sukasamu suka shiga dakin ango Sun sameshi kwance ko tunanin me yake Oho
Aliyu ne ya dauko wata baqar leda ya bashi
Affan yace menene wannan?
Kayan daxakasa kaje daurin aure ne
Affan ya hade rai yace Kaga malam ni anfada maka xan tsaya sa wani sababbin kaya ne ni qila
daurin auren baxan samu xuwa ba
Dariya sukayi abokanansa sannan shima affan yace
Ana daura aure xata kama gabanta Dan makaranta xataje ni kuma xanje bautar qasa

Ranar assabar misalin qarfe goma sha biyu dubban mutane suka shaida daurin auren affan da
afra akan sadaki dubu hamsin inda ango yasha manyan kaya babu laifi ya dan saki fuska
Amma a cikin ranshi ko kadan baya murna da wannan auren
Ita kuma afra tanajin labarin an daura aurenta da affan ta fara kuka sosai tana fadin nabani an
daura mun aure da mugun mutum yau nashiga uku wlh baxan xauna dashiba tunsu aunty
fatima suna bata haquri har Sun gaji Sun fara yimata fada
Aunty Asma'u cewa tayi
Afra bawai affan baya sonki bane halinki ne bayaso idan kin gyara halinki sai kiga kun xauna
lafiya
Afra taqara fashewa da kuka tace ni banason Shi
Duk abunda takeyi affan yanajinta saboda masu karatu kunsan gidansu daya
Ran affan ya baci da kalamanta bawai Dan tace bata sonshi bane jin haushi a'a wai shi take
kira da mugu lallai xataga mugunta
A hankali ya qaraso inda take yace
Ke nikike kira da mugu ?
Tayi shiru saita turo Dan madaidaicin bakinta

Bata saniba ashe su aunty fatima sun bar dakin lokacin daya shigo
Aiko gabanta ya fadi tayi saurin tashi da niyyar fita ya riqo hannunta yace
Ina xakije
Dakin umma
Affan yace ni kike kira da mugu ko?
Afra tayi shiru idanunta suka fara cicciko da hawaye
Ba tambayar ki nakeyiba? Waye mugu?
Nanma tayi shiru
Affan yace to tunda kince mun mugu xakiga mugunta baxakici gabada karatunki ba kuma sati
na sama tarewa
Afra ta xaro idanuwanta ta dafe qirji tace
Dan Allah yaya affan kayi haquri wlh baxan sakeba Dan Allah
Murmushi yayi Dan dama wasa yakeyi mata
Bani kike cewa mugu ba
Natuba baxan qara ba Dan Allah tasaki sabon kuka afra kenan kuka baya mata wahala


*ummu meenal
[9/4, 4:29 PM] Aysha Galadima: *❤❤❤DANI DA MIJINA❤❤❤*

❤❤❤

*NA MRS SADEEQ ( ummu Meenal)*



*DEDICATED TO AYSHA GALADIMA*


*short story*

*page 26-30*


*MASOYA NA A DUK INDA KUKE INA GODIYA SOSAI DA MASU SON NOVEL DINA DA
MASU YIMUN MAGANA A PRIVET DUK INA GODIYA*

*TUKWICI GAREKI AYSHA*


Haka akayi taron biki lafiya dukda dai ba wani taron akayiba saboda cewa akayi sai a tarewa xa
ayi taro
Amarya afra ta rame dama gata ba qiba gareta ita yanxu tunda an daura aure burinta ta cigaba

da xuwa makaranta kada affan ya hanata dan tasan ba qaramin aikinshi bane
A bangaren affan kuwa yanacan dashida abokanansa sai xolayarshi sukeyi tun baya tanka
masu harya fara maida masu
Affan yace ni cikin satin nan xan kaita makaranta a huta danni ko ganinta banasonyi
Bello daya daga cikin abokin affan yace haba malam ai dai yakamata kabari ka angwance a
daren yau koba hakaba ya tambayi sauran abokanansu
Aliyu yace a a qara ta tafi tun yanxu saboda idan ya tare yaji yanda aure yake ai saiya tauye ma
yarinya haqqinta yace baxata cigaba da karatunba
Affan duk firan da sukeyi yanajinsu haushi ya hana yayi magana


Yaune affan yaxo da transfer na makarantar afra yana fadawa umma angama komai ko yauma
xata iya xuwa G G S S JIBIYA
Umma tace bangane ko yau xata iya xuwa ba ina kayan provision?
Yace umma bansan me take buqata ba kitambayeta
Umma tace ni xan tambayeta kenan daukarta xakayi kuje ta xabi abunda takeso
Affan yace umma taje dai ta siyo tunda ba mota gareni ba
Dan bakada mota shine baxakaje ku hau napep ba
Ran affan ba haka yasoba Amma babu yanda xaiyi dole ya amsa mata
Umma to tashirya anjima xamuje Mu siyo umma tace to Allah ya kaimu

Umma ta tashi taje dakin afra ta sameta tana sana an kuka umma tace haba afra wai har yanxu
baxaki daina kukan nan ba saikin jawa kanki ciyo
Afra ta dago manyan idanunta da suka koma ja saboda kuka tace umma banason auren nan
Dan Allah kice ya sakeni...
Umma ta rufe mata baki da hannunta tace kul na hanaki daga yau karki qara cewa affan ya
sakeki kinsan babu kyau mace tace mijinta ya saketa
Afra ta rushe da sabon kuka tarasa ina xatasa kanta
Kishirya anjima xakuje kuyi siyayyan xuwa makaranta
Umma dawa xamuje ?
Da mijinki
Umma basai munje tareba kuma banason ya siya mun komai ke nakeson kisaya mun
Umma tayi murmushi cikin ranta tace bakyason abun hannun affan Amma kinason nawa lallai
wannan qiyayyar tayi nisa
A fili kuwa cewa tayi a a afra affan shine wajibi ya siya maki baniba ita dai afra shiru tayi
Sai bayan lah asar sannan affan ya fito yacewa umma shidai ya shirya umma tace to kaje
kagani ita ko ta shirya
Da kamar baxaijeba kuma saiya tuna mahaifiyarshi ce
Dakinta ya shiga ya sameta xaune da alama bata dade da gama sallah ba daga qofar dakin ya
tsaya yace
Kifito mutafi
Ko kallonshi batayiba tace to
Nifa banida lokaci kina wani to idan xaki tashi kitashi kinma ci albarkacin umma

Haka ta tashi da hijabin da tayi sallah har sunkai bakin qafa afra ta koma tacewa umma umma
mun tafi
Umma taji dadi a tunaninta Sun fara shiryawa ne tace to adawo lafiya
Dan Allah afra karkiyi rashin kunya kinsan dai da Wanda kuke tare
Batayi magana ba ta juya ta koma qofar gida ta iskoshi yana jiranta
Tafiya sukeyi babu mai magana cikinsu har suka samu napep suka shiga babu mai magana
musamman affan da yayi kamar bada ita yake tafiya ba
A super market afra qin xaban komai tayi itama wai fushin takeyi (nidai nace afra ki sassauta
fushinki kixabi kayan abinci mai rai da lafiya Dan bourding skul xakije)
Shi kuma affan gefe daya ya tsaya yana kallonta Dan shima yasawa ranshi cewa indai afra bata
xabi abunda takesoba to shima baxai daukar mata komaiba ba wai Dan bashida kudin ba aa
idan tana taqama ba ason ranta aka aura mata shi ba to shima ba ason ranshi ya aure ba Dan
haka baxai xauna yana bata lokacin shi akantaba
Haka tagama yawonta cikin super market babu abunda ta dauka daga qarshe ma wajenshi ta
dawo tace tagama yace ina kayan tace ita batason komai
Baiyi mata gardama ba yace to mukoma gida haka suka koma gida babu siyayyar komai

Suna shiga gidan umma ta gansu babu komai tace to ina kayan ?
Affan yayi saurin cewa
Umma munyi siyayya to bayan mungama sai muka hadu da wani kuma a makarantar yake
shine nabashi kayan nace yakai mata makaranta kinga an rage kaya kenan umma tace to
kasanshi ne affan yace sosai ma kuwa umma
Umma tace aiko ya kyauta yanxu saitaji da skull back da uniform
Affan yace hakane umma

Yaune afra xataje makaranta kuma affan shine Wanda xai kaita daga kaduna xuwa jibiya akwai
tafiya Dan haka affan ya anshi motar baba xai kaita
Tunda safe afra take kukan rabuwa da umma ita kuma umma sai lallashi takeyi tana yimata
nasiha
Kiyi haquri afra bafa wani dadewa xakiyi a makarantar nan ba iyaka wata uku ne
Umma yanxu har xanyi wata uku ban gankiba umma baxan iyaba
Umma tace kinsan xan rinqa xuwan maki visitin
Da qyar umma ta kwantar mata da hankali ta daina kuka
Haka suka kama hanyar jibiya tana cike da kewar umman ta
(Su afra haka xa aje makarantar babu provition?)



*ummu Meenal ce*
[9/4, 4:29 PM] Aysha Galadima: *❤❤❤DANI DA MIJINA❤❤❤*

❤❤❤

*NA*
*MRS SADEEQ (ummu meenal)*



*DEDICATED TO

*AYSHA GALADIMA*




*Short story*

*page 31-35*


*NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFIN GA PRINCIPAL DIN MAKARANTAR G G S S JIBIYA
ALLAH YAKAI HASKE A KABARINKI ALLAH YA JIQANKI DA RAHAMA DUK MASOYAN DANI
DA MIJINA YACE AMIN YA ALLAH*



Haka suka isa qofar makarantar babu mai magana cikinsu saida aka kai dai dai qofar
makarantar sannan afra tafara hawaye affan yayi kamar bai gantaba saida tagama kukanta
sannan yace ta sauka afra ta tace
Baxan ganeba bansan kan makarantar ba tana kuka yace ina ruwana bake bakyajin magana ba
har kinsa an daura mun aure dake ko to wlh sai kinyi Dana sanin aure na sauka narakaki badan
halinki ba
Babu musu ta fito cikin motar ta bishi duk inda yaje haka suka kai har office din prinsfar hafsat
mai mutunci basu bata lokaci ba prinsfer tabata class j s s 2 sannan takira wata daliba tace ta
nuna mata hostel din j s s 2
Dalibar ta kalli afra tace muje na nuna maki dama antashi yanxu hostel xamuje afra tace to
Ina kayan naki na taimaka maki afra ta kalli affan sai taji hawaye Sun fara wanke mata fuska
Affan kauda kanshi yayi kamar bai ganta ba sannan tace banida kaya muje kawai
Affan ya tausaya mata sosai daga Sun tafi babu kaya har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0