Showing 1 words to 3000 words out of 28231 words
Chapter 1 - Hamshakiyar Uwa Book Compelet Halima Mashi
*HAMSHAƘIYAR UWAí ¾í·•í ¼í¿»*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_KuÉ—in Karatu 600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
_Godiya ta tabbata ga Allah maÉ—aukakin sarki mai kowa mai komai,tsira da amincin Allah su
tabbata ga annabi Muhammad(S.A.W)._
_Kamar yadda na fara lafiya,Allah ka bani ikon gamawa lafiya,Allah ka bani ikon faÉ—akarwa
gwargwadon iyawata,Ya Allah ka yafe min duk wani kuskure da hannuna zai rubuta,Allah ka
bani ladar faÉ—akarwar._
*DOKA*
_Ban amince wani ya É—ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare
da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Free Page 1*
Kan shi a ƙasa bayan ya zube a gaban ta gwiwoyin sa suna ƙasa tamkar mai neman gafara. A
hankali ya furta Hajiya Barka da dare.Ta É—ago kai daga kan TV da ke nanne a bango cikin wata
ƙatuwar ma'ajiyar ta bango guda. Ta maida kanta gare shi ta na nazarin fuskar shi, sannan ta
dubi yarinyar da ke zaune a ƙasa tana shafa mata man zafi a ƙwauri ta ce, "Azima ta shi ki je ki
kwanta." Cikin sauri yarinyar ta miƙe ta re da faɗin sai da safe Hajiya. Allah ya tashe mu lafiya,
Hajiya ta furta a hankali. Ta maido kallon ta ga gareshi sannan ta soma magana cikin isa
"Shamaki zauna da kyau Allah ya yi maka albarka." Ya ce Ameen Hajiya. Ta ce "Bisa dukkan
alamu ka ga wadda ta yi wa ranka, ko dai birgewa ko kuma ta baka shi'awa, faÉ—a min wani abu
dangane da ita."
Ya sake gyara zama bai yi mamaki game da kalaman mahaifiyar ta sa ba,domin ita mace ce
mai tsananin basira tare da karantar É—an Adam, in har za ku yi zaman minti talatin da ita ba ko
shakka zata iya zayyana maka abubuwa da dama daga cikin É—abi'u ko halayyarka. Sannan
babu abinda tafi saurin ganewa irin ka yi mata ƙarya. Ya ce Hajiya so ɗaya na ganta zata je
Islamiyya na tsaya zan yi mata magana ta ja tsaki ta wuce, maimakon in fusata sai kawai na ci
gaba da bin ta a baya bata sani ba har ta shiga makaranta.
Na san cewa kamar shidda sun ta so na koma sai ban ganta ba, yau na bi ta layin da na ganta
cikin sa'a sai na hange ta a wani shago tana siyayya,na jira ta gama na bi bayan ta na ga
gidansu yanzu ina neman iznin zuwa ne in Allah ya sa an bani izni.
Hajiya ta yi shiru kamar ba zata ce komai ba, zuwa can ta ce "Je ka kwanta amma kafin hakan
ina son ka yi sallar istikhara da safe ka zo ka kuma bani wannan labarin da ka bani." Ya miƙe a
hankali tare da faÉ—in na gode a tashi lafiya. "Allah ya maka albarka." Ta furta tare da É—aukan
goran ruwa a gefen ta ta buÉ—e da zumar sha. Firgigit ya farka ya na kallon É—ayan sashen da take kwance, mafarkin yana dawowa a zuciyar
sa, babu ko shakka sai ya yi wanka domin ya cimma hakan a mafarkin sa, bai taɓa samun
hakan ba duk zaman gauran takar sa, kila gara lokacin da ya ke saurayi farkon balaga. Ya yi
addu'a a sallar sa, domin bai samu zuwa Masallaci ba sakamakon makara,ba zai iya tuna
lokacin da ya rasa jami'in sallar asbahi ba. Ya jima kwance jikin sa lankwas wanda yin hakan ba
al adarsa ba ce. Sai ya ji kamar wani ɗan zazzaɓi ya na sarfatar sa. Cikin hakan ya ji ana
kwankwaso ƙofarsa, ya tashi zaune sannan ya bada iznin a buɗe. Ta turo ƙofar ta na sanye da
kayan makaranta, Azima ce. Ta ce"Yaya Shamaki Hajiya ta ce in duba ka." Ya ce ki sanar mata
ina zuwa. Ya miƙe ya ɗauki jallaiya bulu mai gajeren hannu tasha aiki da sirfani mai ruwan zaiba
ya saka.
Yana fitowa falonsa Meema ta na shigowa ta nufeshi da gudu tana faÉ—in "Dadi! Ya sa hannu ya
É—aga ta sama ya sata a jikin sa tare da faÉ—in Mamana Ina Mubina ina Anisa? Ta nuna mishi
hanyar É—akinsu tare da faÉ—in "Suna ciki Rahin tana shirya su." Ya lakaci kuma tun ta ke fa? Ta
ce "Ni'ma yanzu za 'a shirya ni." Ya dire ta to maza kar ku yi latti ki tafi a shirya ki. Ta ruga da
gudu. Shi kuma ya nufi sashen Hajiya.
Tana zaune a kan sallayar ta ƙafafun ta a miƙe sanɓal ta rufe kanta da hijabi na alfarma
ƙamshin ta na tun fil"azal ya na tashi tana riƙe da carbi tana lazimi. Ya samu gefe ya zauna
zama irin na girmama wanda ka ke gaban shi. Ya kalle ta cikin darajawa tare da faÉ—in Hajiya ina
kwanan ku? Ta sauke numfashi cikin ƙasaita, sannan ta amsa da "Lafiya lau Shamaki, me ya
same ka yau ba ka je sallar asbahi ba?" Ta yi tambayar cike da kulawa. Ya sunkuyar da kai,
jikina yau na tashi babu daɗi sam, kuma sai na makara. "Me ya biyo bayan neman zaɓin da ka
ba Allah ajiya! Ka ji wata damuwa game da yarinyar ko kuma Allah ya haska maka wani
al'amuri a cikin baccin ka?"
Ta jeho masa tambayoyi. Shamaki ya ce eto har zuwa yanzu ina jin ƙaunar ta kuma na yi
mafarkinta. Ya sunkuyar da kai domin ba zai iya bada labarin mafarkin ba. Hajiya ta ce "Ina
sauraron ka." Ya sa hannu ya shafa fuskar sa sannan ya saci kallon ta ta tsira mashi ido,ba ko
shakka so ta ke yi sai ta fahimci ko zai mata ƙarya. Ya ce cikin wani yanayi muka haɗu Hajiya
Allah dai ya kyauta.
Ta yi É—an murmushi da alamu ta fahimci ina ya dosa. Shike nan, ka sake bani labarin da ka bani
jiya game da yarinyar. Ya gyara zama ya zayyana mata komai kamar jiyan. Ta numfasa tare da
faÉ—in shike nan ka je ka fara bincike a kanta kafin ka je gurin ta. Sannan kar ka manta. da
sharuÉ—É—a na akan duk wata mata da za ka aura. Bana son ka sake sakin mace daga guda
ukun nan da ka yi, amma ka sa a ranka matan ka huɗu ne in Allah ya ƙaddara ina aɗdu"a. Kaje
ka shirya yau kai zaka kai yaran ka makaranta domin tun jiya suka nemi alfarmar hakan.
Sannan in kaji zazzaɓin zai matsa sai ka sha magani, duk da nafi zargin zazzaɓin na soyayya
ne. Ta kai ƙarahen maganar da 'yar dariya irin ta manya cikin ƙasaita.
Ya shafa kanshi tare da yin murmushi mai sauti,ba ko shakka zolayar sa Hajiya ke yi.
Ya ɗan rusuna. zan yi yadda ki ka ce insha Allahu Hajiya. Sanna ya miƙe ya nufi ciki. A mota
tare da 'yan yaran sa mata su uku, Meema da ke zaune a gefen shi ta ce "Dadi za ka dawo ka
É—auke mu?" Ya dube ta sannan ya girgiza kai, Bazan dawo ba Mamana zan tafi kasuwa ne fa.
"To zaka raka mu har ajin mu?" Ya kai hannu ya shafi kanta me zai hana zan raka ku in kuna
so. Anisa ta sako hannuwan ta daga can baya ta shafo kumatun sa, Dadi muna so 'yan ajinmu
suna cewa basu taɓa ganin Babana ba. Mubina ta ce Nima haka Dadi za ka raka mu kowa
ajinta. Ya ce to shike nan sai mu fara kai Anisa ita ce Smaller ko sai mu kai Mubina, sai in kai
Anty Babba ko Meema? Cikin jin daÉ—i ta ce e Dadi na.
Sun yi kamar yadda suka tsara da 'ya'yan na sa sannan ya ciro kuÉ—i ya raba wa malaman
sannan ya tafi suna ta godiya sannan ya kama hanyar kasuwa.
Tun da ya zauna a ofishin sa da ke babban reshen manyan katunan sa wato Zeena Galary da
ke ƙatuwar plazarsa mai suna Gidan Zeena a babbar kasuwar kwari da ke Kano. Dukan
yaransa na katin sun fahimci ya na da 'yar damuwa, kasancewar ba haka ya saba zuwa ba. Shi
kansa tunda ya ke bai taɓa samun kansa cikin wannan yanayin ba game da matansa da ya
aura a baya. Ko matarsa ta fari bai ji irin abinda ya ke ji a wannan lokacin ba. Yana jin in bai fita
ya nemo yarinyar nan ba kafin yamma akwai matsala.
Suna idar da sallar Azahar ya cire agogo da zobe da duk wani abu da zai nunashi a mai kuÉ—i,
ya fita ya saka salifan da ke ƙofar banɗakinsa na ofishin ya fita ba tare da ya yi wa kowa
magana ba, ya je titi ya tari É—an sahu ya hau tare da faÉ—in kaini ÆŠan a gundi. Dai dai bakin
lungun ya tsaya ya ciro kuɗi Naira ɗari biyar ya miƙa masa sannan ya sa kai cikin lungun, shi
dai ÆŠan sahu ya ciro canji ya É—ago kai ya ga baiga Alhaji ba, cikin jin daÉ—i ya yi tafiyar sa.
Na siyo gawayi ina sauri zan dafa mana taliya 'yar murji ni da ƙannai na kasancewar Umman
mu bata nan taje awon ciki. Na taka dakalin ƙofar gidanmu sai naji ance "Salamu alaikum. Na
waiwayo sai naga wani Mutum wanda wanda ba zan iya siffanta shi a take ba. Na amsa
sallamar ina jira ya min tambaya domin dai ƙila wani gidan yake nema a lugun namu. Ga mamaki na sai naji ya ce "Zan iya magana da ke?" Me zai hana.Na bashi amsa ba tare da
na fahimci me ya ke nufi ba. Ya ɗan ƙara matsowa ya dafa bangon gidan mu ya soma magana
"Sunana Aliyu amma anfi sani na da Shamaki, kusan kwana uku baya na ganki kuma gaskiya
ba wata kwana Ni ina son ki!" Na É—an ja baya da sauri domin ban zaci inji haka daga gare shi
ba,hasali ma ni ba a taɓa furta min kalmar so ba,dan haka sai na rikice ina sake kallon shi. Ya
ce ,"Na ga kin firgita da gaske na ke yi." Zan shige gida ya ce "Tsaya mana ya kamata ki bani
amsa ko da rashin amincewa ce." Na ce abinci zan dafa wa ƙannai na suna jin yunwa. "In dawo
anjima da dare?" Ya tambaye ni da sauri. Na sake duban fuskar sa, nifa bantaɓa zance
ba,bansani ba ko Abban zai bari. "To ki tambaya in sun dawo amma zanzo anjima É—in." Na ce to
shike nan.
Ina girki ina tunani, duk da mutumin ba yaro bane amma naji ya birgeni, sannan kalmar so da
ya furta a gare ni ta zama baƙuwa a gurina, dole ma in amsa masa ko na shiga sahun
'yammata da ke zance a lungunmu bayan wasu ma na girme su nesa ba kusa ba. Shekaruna
ashirin da haihuwa jarabawar kammala Sakandire muke yi, a Islamiya ina ajin sauka, amma
ban taɓa samun wanda ya ce yana sona ba ko da sunan wasa ba. Na sha kallon kai na a
madubi duk da ban kasance fara me shegen kyau ba,na tabbata ba za a sakani a layin munana
ba, kuma dai dai gwargwado ina da hankali da kamun kai. Cikin wannan yanayi na gama girki amma sai na kasa ci, haka a Islamiyya yau sai tambayata a
ke yi lafiya kuwa. Domin na zama shiru sai tunani, in har iyayena sun laminci in yi soyayya da
shi ba shakka zan ji daɗi domin har na fara jin cewa na ƙosa in sake sauraron muryar shi.
Bayan magariba Umma tana zaune kan tabarma ta idar da salla ta na cin É—ata, na zauna kusa
da ita na ce Umma ɗazu wani mutumi ya zo ƙofar gidan nan wai gurina ya zo. Ta ɗago kai da
sauri "Me ya ce miki ?" Na ce wai yana so na, nace sai in na faÉ—a.a gida. "ÆŠan ina ne?" Ta
tambaye ni, na ce wallahi bansani ba, ya ce dai zai dawo da daren nan. Tace Allah ya sa dai na
gari ne,dama ranar nan sai da Umman su Fati ta gwaɓa min magana wai an saka ranar Fati ita
dake suyar awarar dare, masu zuwa haddar Kur'anin dare shiru. Kuma nasan ta gwaɓa min
maganar ne saboda na ce ta hana Fati yin dare sosai a gurin tuyar awara wani lokacin har
shaÉ—ayan dare take kaiwa Abbanku in ya zo sai ya yi ta faÉ—a. Wai an bar yarinya gurin daga ita
sai yaran nan maza marasa kunya. Na ce ai yanzu faÉ—ar gaskiya ta zama matsala Umma. Ta
ce haka ne ke dai ki kula da kanki in ya zo ki fita ki saurare shi in kuma Abbanku ya dawo kafin
lokacin zan faÉ—a masa.
Jamila ƙanwata ta matso kusa da mu tace Umma Yaya Baby ce zata fita zance? Na ce to sarkin
tsegumi. Umma ta ce "Menene a ciki in kin faɗa mata, Jamila ai ƙawa zaki maida ita,na faɗa
miki komai ki ke yi tare da ita shekarunta sha bakwai fa yanzu." Na kalleta nayi murmushi tare
da faɗin to ƙawata baƙo zan yi. Ta ce Allah na gode maka mu ma Allah ya sa ayi biki a
gidanmu. Umma ta ce "To kije kiyi wanka ki gyara jikin ki." Na ce har sai na yi wanka kuma, na
yi da safe fa. Jamila ta ce, au da me ki ke nufi, haka zaki je kina zufa? Na tashi na je na É—ebi
ruwan sanyi abinda bana wanka da shi amma dan zumuÉ—i na faÉ—a banÉ—aki na yi wanka aiko ina
ta atishawa, cikin zuciya ta kuwa fargaba ce tana saƙamin ko ma dai ba zai zo ba.
Na idar da sallar Isha'i a É—akin Umma na zabga tagumi gefe ga kayana sabbin na sallar bara da
Umma ta ce in saka. Jamila kuwa ta tasani agaba sai fadi ta ke "Anty Baby ki tashi ki saka
kayan kar ya zo baki shirya ba." Na ce Jamila ni yanzu fargaba ke duka zuciya ta,ji na ke
kamar ya fasa zuwa,kila ma ya canza shawara.Ta ce "Karki faÉ—i haka Anty, shifa ya zo da kansa
tun farko ba ke ce ki ka nemo shiba." Sauke ajiya zuciya ta sun zo dai-dai da sallamar
Abbanmu. Umma ta amsa tana masa sannu da zuwa, muka leƙa muka yi masa sannu da zuwa
ya amsa. Nace to Jamila bari in shirya É—in,ke ki je ki kaiwa Abba abinci. Ta fita tare da faÉ—in
"To."
Ina jiyo Umma ta na sanar da Abba game da baƙon da zanyi,na yi kasaƙe inji me zai faɗa,sai
ga muryar wani yaro ta ratso gidan da sallama. Umma da Abba suka amsa. Ya ce,"Ana sallama
da Abban gidan nan inji wani mutum." Abba ya ce to ka ce ina zuwa. Umma ta ce baka tambaya
ko waye ba,yace Malam Sani ne mun yi da shi zamuje wani aiki gobe,to nasan kan maganar
ne,kinsan yadda rayuwa ta ke yanzu in ka samu aiki ƙoƙari ka ke ka je in ba haka ba sai aba
wani. Ta ce "Haka ne Allah yasa mu dace." Ya ce Ameen bari in dawo yanzu.
Na gama cire rai da zuwan mutumin har takwas da rabi na yi danasani da ban saurare shi a
lokacin ba, na kwance É—ankwalin da na É—aura dan ya soma damu na,nafara ninke shi sai naji
sallamar Abbanmu. Ya na kuma tambayar ina Baby?" Da sauri na amsa gani Abba, ya ce "Kije
baƙonki yana waje yana jiran ki." Gabana ya yanke ya faɗi, na ce to.Jamila ta miƙo min yar
kwalba tare da faÉ—in ga Humra ta Umma ce ki shafa ajikin ki. Na É—an goga na fita da sauri.
Umma ta ce "Baby in kinje fa ki gaida shi ." Abba ya ce haba kema dai yaran yanzu kar suke
kallon kowa. Umma tace kasan wannan ce farkon fitar ta zance dole a tuna mata. Abba ya ce
"Jamila kai masa tabarma. Can na tsaya a bakin ƙofa ina shaƙar ƙamshi turare mai daɗi irin
wanda na ji É—azu, yana can gefe jingina da bango sanye da farar shada riga da wando ba hula
a kanshi, gefen shi ga keke irin mai kwando a gaba na manya ya jingina. Jamila ta shimfiÉ—a
tabarma a kan dakali sannan ta gaishe da shi ta koma ciki. Na taka a hankali na isa kusa da
shi,nace sannu da zuwa Yaya. Basan lokacin da baƙi na ya furta hakan ba. Cikin yanayin jin
daɗi ya amsa da "Yawwa ƙanwata." Na nuna kishi tabarmar Yaya ka zauna. Ya ce to, ya isa
bakin dakalin ya zauna,na tsugunna a gefe ya ce, ,"kema dawo nan ko ki hau sama ko ki yi irin
zaman da na yi." Na zauna sannan na rusuna na gaida shi,ya amsa "Hajiya ta ce in gaishe ki,
na ce ina amsa wa amma, sai kuma na yi shiru. Ya ce amma me? Na ce nayi mamaki ya aka yi
ta sannu. Yace, "Ta sannu tun ranar da na fara ganin ki, tasan na yi magana da ke É—azu, kuma
ta san ina nan yanzu." Na ce Allah sarki to ina gaishe ta in ka koma. Sai da tuni zuciyata ta
shiga fargaba e ko matar sa ce Hajiyar domin daga ganinsa ka san dai yana da iyali.
Ya katse min tunani da