Showing 3001 words to 6000 words out of 28231 words

Chapter 2 - Hamshakiyar Uwa Book Compelet Halima Mashi

tambaya. "Baby Ya sunan ki na gaskiya? Saboda ko sunan ki Ni
bansani ba yanzun da na yi sallama da Abba na ji yana cewa Baby." Na ce Amira, amma na
asalin gaskiya Rabi'atu sunan Maman Abbanmu ne, sai ake ce min Amira,Baby kuma
Ummanmu ta ke faɗa min sai kuma ya rinjaya. Ya numfasa. "Ni ma dai Babyn ya fi min daɗi,
amma zan kira kowanne in na so ko?" Na Ɗaga kai alamun eh.
Ya yi 'yar gyaran murya "Baby gaskiya ina son ki kamar yadda na faɗa ɗazu, in har ki na sona
to aure ya kawo ni kamar yadda na faɗawa Abba ɗazu. Sanna bazan ɓoye miki komai ba,ina da
yara uku duka mata,kowacce mun rabu da mahaifiyar ta... Saboda me? Na jeho masa tambaya
ba tare da na sani ba. Ya ɗan yi dim, sannan ya ce "Saboda Allah, kar ki damu sannu zaki san
komai. Ya ci gaba Ni ƙaramin ɗankasuwa ne ina tsare shagon mai gidana a Kantin kwari. Fatan
kin fahimta?" Na ɗaga kai tare da faɗin umm. Take zuciyata ta sare kuma ta soma tuhumarsa.
Mata uku, kuma ba ko ɗaya yanzu, gaskiya ya kamata insan dalili. Ya katse min tunani da cewa,
"Baby ta bakin ki na ke son ji ko kina so na kuma za ki iya aure na? Ni dai komai na ki ya yi min.
Na numfasa cikin sanyi jiki na to gaskiya ni dai bansani ba ko ina son ka domin ban taɓa
samun kaina a cikin shi ba to bansan ya yake ba. Sannan magana aure Allah shine mai
ƙullawa, in har ya ƙaddari hakan zan amsa hannu biyu. Yace "Har yanzu dai ban samu amsa
ba,amma zan baki zuwa jibi, kiyi nazari kuma ki ƙoƙarta ki gano ko kina so na." Na ce, to na
gode kuma zanyi yadda ka ce. "Bani lambar wayar ki zan kira kafin jibin inji wannan sanyayyar
muryar." Na ce sai dai in baka ta Ummanmu, saboda har yanzu Abbanmu bai sai min ba, yace
sai mun gama walimar saukar ƙur'ani. Yace to bani ta ta ɗin, na faɗa masa sai ya yi flashin
yace, "Inkin shiga sai kuyi sebin domin inna kira kai tsaye kinsan ni ne." Nace, to. Yace "Nine
ɗan auta a gurinta, kuma ni kaɗai ne namiji, yayinda huɗu duk mata, Yaya Zainab ce babba,sai
Maryam A'isha da Fatima duk suna aure a nan cikin gari." Na ce masha Allah kaji daɗinka. Ni
kam bani da yaya hasalima ni ce 'yar fari sai ƙanena uku Jamila da Jafar da kuma Habu,sai
wanda za a haifa mana yanzu. Yace "Allah ya sauke ta lafiya dama ina ganin Abba na raya a
zuciyata cewa ƙila ke 'yar fari ce." na ce Ameen, gani ka yi ba tsoho ba ko? Na tambaye shi ina
'yar dariya. Yace "E mana." Shima cikin dariya ya amsa. Nace, haka in 'yan makarantarmu suka

zo sai su ce wai Ummanmu Antinmu ce. Muka ƙara yin dariya tare. Ya ce "To Ni dai bari in zo in
tafi kar dare ya yi sosai,na kalli kekensa nace danma kana da abin hawanka balle ma ka ce
zaka rasa ɗansahu. Yace haka ne." Nace, Ka gaida Hajiya da kyau. Ya faɗaɗa fara'a "Zan
faɗa mata Insha Allahu." Shine ya nannaɗe tabarmar ya tako har bakin soro yana faɗin in gaida
su Umma.


️️️
[6/16, 19:58] Ummi Tandama: *HAMSHAƘIYAR UWA*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko Katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare
da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_


*Free Page 2*

Har tsakiyar dare bacci ya ƙi zuwa min sai juyi na ke akan "yar katifarmu Jamila ta na ta baccin
ta, tufka na ke ina warwara abu biyu ke ɗaga min hankali,menene dalilin rabuwa da matansa?
Kuma komai nasa dole sai Hajiya ta sani? Zuwa yanzu nasan cewa Hajiya dai ba matarsa ba
ce, ko dai mahaifiyarsa ko kuma uwar ɗakinsa. Da safe ina raba mana abin kari awara ce da
koko duk muna tsakar gida harda Abbanmu. Umma ta dube ni,"Ke kuma lafiya duk jikin ki a
sanyaye?" Nace, lafiya lau, kawai yau kasala nake ji. Ta dubi, Abbanmu tace, "Abban Baby
kace ka yaba da saurayin nata jiya?" Ya ce gaskiya Salamatu na yaba sosai, in har sun
dai-daita zanyi farin ciki domin alamu sun nuna shi mai hankali ne.Umma ta ce "To ɗan unguwar
nan ne?" Yace, A a yace min shi ɗan Gama ne can aka haifeshi amma yanzu suna nan haka ko
gurin Janbulo ne, ya ce da ɗan gidan sa a gurin da ya gina suna zaune da mahaifiyar sa. Kuma
yace a kwari yake tsaron shagon wani mai gidansa, amma yace asali su 'yan Gaya ne. Umma
ta ce "To, Allah ya daidaita su.
Ni dai bance komai ba,mutumin ya maƙale a zuciyata duk yadda na auno matsaloli sai zuciyata
ta kawo wani uzri ta wanke shi. Haka nan har naje makaranta na dawo ina tunanin Aliyu

Shamaki.
Da dare muna 'yar hira da Umma, ta tambaye ni da cewa "Ni ko Baby mutumin nan ya yi miki
kina ganin cewa zaki iya aurenshi?" Na ce to Amma Ni dai ina ta waswasi. "Game da me?" Ta
katse ni da tambaya. Na ce aurensa uku duk sun rabu da matan, 'yayansa uku duka mata
kuma duka sunan mahaifiyarsa ya saka, sai ina jin tsoro ko mahaifiyarsa ce bata barin matan.
Umma tace "Karki fara lamarinki da zargi, tabbas dole ki damu game da rabuwa da matansa,
shawarar da zan baki shine ki sa hankalin ki sosai ki gano raunisa da fushin sa, ta haka zaki iya
samun zaman lafiya da shi. Baby a irin tarbiyyar da nake baku ina sa rai ko mutum yana fidda
wuta ta baki dan bala'i za ki iya zama dashi, haka duk wata kissa ko kisisina, ko shirka bai
kamata kiji ɗarba." Na yi 'yar dariya haka ne Umma.
wayar Umma ta yi ringin Jamila tace Yaya Baby lambar jiya ce da kika ajiye. Gabana ya faɗi
harda juyawar ciki,take naji banɗaki kawai na ke son shiga. Na amshi wayar na shige ɗakin
Umma ina jinshi yana sallama, sai da na zauna sannan na amsa sallamar da wata murya da
bansan ina da itaba. Na gaida shi,ya amsa na tambayi Hajiya da yara,yace duk suna lafiya.
Yace, "Shine ko ki kira ni kiji ya naje gida jiya." Na ce to kayi haƙuri amma gaskiya na so in kira
ka sai kuma na yi tunanin kar kana kan Kekenka kuma in tsaida kai, har kuma bacci ya ɗauke
ni. Ya numfasa "To na amshi uzrin ki, amma ya kike gani zuwa yanzu a zuciyarki ta kuwa fara
sona?" Na kwanta tare da ƙara manna wayar a kunnena. Ba zan iya tabbatar da haha ba
Yaya,sai dai ka faɗamin yaya son ya ke ko zan gane.
Ya yi yar dariya. "Bani labarin bayan rabuwa kin tuna da ni? Sau nawa? Kina tuna hirar mu?
Wacce a ciki?" Na numfasa, gaskiya na tuna ka sosai amma ban lissafa dadin ba. A hirar mu
dai nafi tuna batun auren ka guda uku,sai in ji fargaba. Yace, "Alhamdulillah Baby kin fara so na,
karki damu da maganar matan da na rabu da su, ko tunanin dalilin rayuwar mu, zai fi kyau ki
maida hankalin ki akan irin rayuwar auren da za mu yi. Zanzo gobe,ki tanadi labari mai daɗi da
za ki bani." Nace,to Insha Allahu Allah ya taimaka a gaida Hajiya. "Zan faɗa mata." "Yaran ki
fa?" Cikin sauri na ce agaida min su don Allah, koda bansan sunayen su ba. Ya ce "Haka ne
ban faɗa miki ba, dukansu sunansu Zeena." Kamar yaya na tambaye shi cikin rashin fahimta.
Yace Ƙwarai kuwa duk sunan Hajiya suka ci, amma kowace da laƙaninta Babbar Meema, mai
binmata Mubina sai ƙaramar su Anisa." Na sauke ajiyar zuciya, gaskiya abin ya birge ni kuma
har naji ina son in gansu. "Karki damu ke da 'ya'yanki kuma ke ma zaki haifa mana wata
Zeena ɗin ko?" Kunya ta sa na yi saurin faɗin sai da safe, na kashe wayar sannan na yi
rigingine a gadon ina jin farin ciki gami da fargaba. Dole in yi magana da Umma.

Kamar kullum ya zauna a gefe yana jan carbi yana jiran Hajiya ta gama addu'o'inta kafin ya
gaida ita kuma su yi 'yar hirar da suka saba. Bayan ta kammala suka shafa tare, ya matsa
gabanta sosai ya rusuna ya gaishe ta. Ta amsa tare da kai hannu ta shafa masa kai tana faɗin
"Allah ya albarkaci rayuwarka, da ta 'ya'yanka, ya yi albarka a cikin neman ka, ya albarkaci
abinda zaka samu. Allah ya tsare ka daga dukkan sharri mutum ko Aljan da duk wani abinƙi."
Shi kuwa yana ta maimaita ameen. Bayan sun kammala sai ta gyara zama sannan ta ce,
"Jiya Maman sani ta zo game da maganar abincin sadaka na ranar juma 'a wasu abubuwa sun
ƙare, na ce ta lissafi kamar yadda aka saba, kuma ina son wannan karon za'a saka sunan
mutum ɗari a kayan salla yara marayu, sai mu ba Zeena Foundation dama su nemo yaran da
suke dace da buƙatar tallafin nan a ba su. sannan ɓangare kayan ɗaki Amina ta. Kawo sunan

mutum biyu kuma sun gama bincike tabbas yaran mabuƙata ne duk marayu ne na ce taje
gandu su yi magana a Zeena funitures da manajan kamar dai kowane lokaci. Ya ƙara yin ƙasa
da kai cikin girmamawa to Hajiya duk yadda ki kayi dai-dai ne. Ta dubi fuskar shi, "Baka sanar
da ni ko ka tattauna da yarinyar nan ba." Eh na samu ganin mahaifinta kamar yadda ki ka bani
shawara, kuma ya min 'yan tambayoyi kafin daga bisani ya shiga ya turota. "Kamar wace
tambaya ya yi maka?" E ya tambayi unguwarmu sannan ya tambaye ni game da addini da
sana'a da aƙida. Ya gamsu duk da ce masa da na yi ni yaron shago ne, yace buƙatar kawai ace
da sana'ar komi ƙanƙatar ta Allah shine mai buɗawa in yi magana da ita in har mun sasanta ya
bani ita. Hajiya ta ɗan yi jim,sannan ta ce, "Mecece hikimarka ta ɓoye matsayinka? Ya gyara
zama, Hajiya ina son in samu soyayya ta tsakani da Allah bata abin hannu na ba, ina son in
shimfiɗa sabuwar rayuwa ba irin ta baya ba." Ta yi ɗan murmushi cikin ƙasaita ta ce "Wannan
yaro na ne, tabbas akwai hikima cikin abinda za ka yi. Na amince da haka, to ita yarinyar ta
karɓe ka ya kuka yi?". Ya sunkuyar da kai,to har yanzu dai ban same ta sosai ba, na yi mata
uzri yarinya ce sosai yanzu ne zata gama Sakandire su za suyi sauka a Islamiyyar su, haka nan
kuma ni ne saurayin ta na farko. To ta kasa gane ko tana sona. Hajiya ta yi hiru cikin nazari,
sannan ta ce Allah ya zaɓa mana abinda yafi zama alkhairi, za mu ci gaba da addu'a." Ya ce
Ameen ina godiya sosai. Haka suka kasance cikin tattaunawa har zuwa lokacin da Juma ta
shigo ta na jera flas na ƙosai da hankali da wainar ƙwai da na ruwan zafi ga kunun gyaɗa ga
kuma kayan shayi. Shamaki da kansa ya Haɗawa Hajiya Shayi mai kauri kamar yadda ta
buƙata, ya shirya mata komai sannan ya saka abinda kanshi ke so ya shiga ci suna ƙara
tattaunawa.


️️️
[6/16, 19:58] Ummi Tandama: *HAMSHAƘIYAR UWA*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu 600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko Katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare
da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_

*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*

Mamakin kansa ya ke yadda ya ƙosa dare ya yi yawan murmushin da ya ke in ya yi shiru ya sa
yaran kantin suka soma tsegumin cewa maigida ya faɗa soyayya, musun da suka yi ya sa ɗaya
daga cikin yaran mai suna Ɗahiru ya ce bari ya gwada shi. inhar haka ne zai gane. Ya kunna
waƙar Hamisu Breaker ta soyayya. Yaje ya zauna a bakin Office ɗin yana ci gaba da shi'anin
gaban sa. Daga ciki kuwa Shamaki ya yi tsam da ransa yana sauraron yadda mawaƙin ke yin
falsafa akan so, sai kawai ya ƙwala wa Ɗahiru kira, ya amsa ya shigo cikin girmamawa yace
"Gani Alhaji." Wai ku bakwa rabo da jin wakane duk da ita wannan naji ta yi daɗi da ma 'ana,
amma waye ya yi ta ne, tura min ita a waccan wayar in yi wani nazari a kanta. Ya ɗauki wayar
ya fita yaje yana basu labari suna dariya. Ranar haka ya yini jin waƙar. Da yamma ya kira
Malam Bala direbansa ya ce a wanke mota zai fita bayan Isha'i. ya kuma fara lissafin zai bi ta
Zeena Store ya kwashi alawoyi yaje Zeena Factory ya haɗa mata kayan ƙwalam na Snacks.
Kamanta gurin wa zaka kuma wane matsayin kake a idon ta? Zuciyarsa ta jeho masa tambaya.
ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ce sai dai in nemi ɗata ko yalo? Ɗan tsaki ya saki sannan ya
yi maganar da ƙarfi Ayaba da Lemo zan siya. Hassan dake cikin Office ɗin yana rubuta wani
rasit ya ce "Karɓo wa za ayi Alhaji?" Ya dubi Hassan me nace? Yace,"Naji kana maganar Ayaba
da Lemo." Ya yi ɗan tsaki eh da za a karɓo ne amma bari sai na fita sai in siya kawai.

Nikam kafin Isha'i na shirya tsaf, ba sallah zan yi ba don haka na kame ina jiran zuwansa,
gabana kuwa sai faɗuwa yake ina ayyana yadda zanji idan mun kasance muna hira,ina ta
baiwa kaina shawarar ya kamata ace ina zaɓo kalamai inzan furta masa,sannan kuma kar inyi
masa magana da irin muryar da nake yi wa kowa hakan zai sa in ƙara birge shi. Take na gamsu
da hakan,kuma na yarda shi na musamman ne.
Shamaki ya wahala kafin ya samu kayan da za su nuna shi a talaka,suma dai yadine fari mara
nauyi, yanada mugun tsada amma ba kowa zai iya gane hakan ba sai wanda ya san kaya. Ya
zube wayoyinsa guda huɗu a kan gadonsa, sannan ya saka mai boturan wadda ya sawa sabon
layi domin ita kaɗai a alajihu agogo da zobe na azurfa duk ya zube su. Ya nufi sashen Hajiya. Ta ƙare masa kallo sanna ta amsa gaisuwarsa. Ya ce zanje gurin Rabi a ne kamar yadda na
sanar da ke tun shekaran Jiya. Ta ce "Na fahimta,kaje Allah ya bada nasara,kuma ka ce ina
gaisheta. Sannan ka tabbata ka sami zuciyarta a yau,domin na lura kana matuƙar sonta. Allah
ya yi muku albarka gabaɗayan ku." Ya ce Ameen sannan ya miƙe ya fice da sauri. Ta bishi da
kallo a fili ta furta akwai matsala ya kamu da yawa, ni da nafi son ya samo wadda ta fi son sa
dole inyi wani abu.
Ya dubi Malam Bala yace, in ka isa gurin masu Lemo na ɓawo za ka karɓo. Da suka isa ya rasa
na nawa ya kamata ya siya yace Malam Bala ga dubu biyar su yi kashi biyu. Da aka kawo ya
ga da yawa yace Malam Bala ka dauki kashi ɗaya. Sai da suka gota lungun sannan ya
sauka,yace ka je zan kira ka nan da awa biyu. Ya taka da ledoji biyu a hannunsa ya dawo ya
shiga lungu.
Jafar ya shigo da ledoji suna rinjayarsa, yace Umma wai gashi inji wani mutum wai yace Yaya
Baby taje. Cikina ya juya da sauri na ɗauki buta zan shiga banɗaki, Umma ta ce "Ke dakata
lafiyarki da tun ɗazu kuna zaune sai da yazo zaki tarki shiga banɗaki?" Nace wallahi Jafar yana
faɗa sai naji cikina ya juya, na shige da sauri. Ina jiyo Jamila tana tsaki tana mitar "Yanzu da

wari zaki gunsa?" Na fito na sake shafa turare sannan na fita na samu har Jamila ta shinfiɗa
masa tabarma ta aje masa ruwan fiyawata.
Cikin girmamawa na gaida shi, na kuma tambayi Hajiya da yara. Yace tana gaida ni kuma duk
suna lafiya. Nace shine harda wata ɗawainiya haka? Ni fa karka matsawa kanka a irin wannan
yanayin ba sai ka min wata ɗawainiya ba. Ya ce "Karki damu, ina da halin yin hakan ne, yanzu
ki bani labarin soyayyata. Na ƙosa mu soma musayar ta ni da ke, domin har na soma zama
wawa ina kasa jurewa tunaninki." Nace koda bansan so ba, na tantance kai na musamman ne,
duk wani kai kawo nawa kana zuciyata kuma na kasa gano aibunka, zuciyata tana faɗa min
cewa in maka uzri kuma in amince ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login