Showing 18001 words to 21000 words out of 28231 words

Chapter 7 - Hamshakiyar Uwa Book Compelet Halima Mashi

zan iya
bacci in aka É—aura mana aure kuwa? Mamaki ya hana Shamaki magana,duk da cewa shima fa
yana jin wata ƙaunarta a zuciyarsa wadda bazata misali ba. Ta katse mishi tunani da faɗin
lokacin walimar tamu za a saka ko? Yace ban sani ba gaskiya haka dai nace su tambayar min."
Nace Kaga Yaya, asa hakan wallahi na yafe lefen, kuma kayan ɗàkin ma zan faɗawa Umma ba
takura ko? Yace "Sai ki iya faÉ—a mata haka baza ta ga cewa kinyi rashin kunya ba?" Nace to
wai me na ke yi ba daidai ba? Tun jiya ake cewa wai na canza ina ta zumuÉ—i, kuma ni ina jin
wani sonka ne bansan ya zan fassara maka abin ba. Ina samun nishaÉ—i da jin daÉ—i ne kawai in
naji muryarka, da na kira baka É—aga ba har kuka fa na shiga ban É—aki na yi, sai ina ji a jikina
kamar zaka fasa. Yace "Gaskiyar magana kin canza gaba É—aya kamar ba ke ba. Nima dai ina
mamaki." Nace to Allah ya sa dai su amince shine damuwata. Yace "Ya maganar walimar ku?"
Na yi É—an jim sannan nace tana nan, amma gaskiya dai zaka zo min ko,duk da masana cewa
kana cikin shirin biki lokacin ai na san zaka so ka ga karatu na. Yace in sha Allah zan zo sannan
karki saka a ranki cewa dole sai lokacin da muka ce, in basu yarda ba dole mu jira lokacin da
suke ganin ya fi." Na ce Ni fa damuwata kada ka zo ka ce ka fasa, wallahi zan iya mutuwa har
lahira. Yace Baby in kinga na fasa aurenki wallahi na mutu ne,matsawar ina numfashi bazan

fasa ba. DaÉ—i ya rufe ni, nace Allah na gode maka. Munata tattauna batun soyayyarmu na ga
Abba ya zo ya shiga gida. Ya ce bari inje in sallame su, ki koma gida zan dawo nace to. Na
shiga gida don inji yadda suka yi. Anan na samu Abba yana ba Amma labari ya zauna genen
tabarmar da yake kai har Jamila ta kawo masa abinci. Yana faÉ—in "Wato Salamatu Allah ya
amshi addu'armu ya kawo wa Jamila mijin ƙwarai ba sai mun bincika komai ba sun wanke shi
tas. Limamin Unguwarsu inkinji yadda ya ke yabon sa abin zai baki shi'awa ga neman na kansa
ga alheri duk sun yabe shi,ƙanin mahaifiyarsa da ƙanin mahaifinsa banda albarka babu abinda
suke sa masa. Kuma sun nemi alfarma ko za a sa aure tare da walimar saukar su nace a a
saboda yanayi shima kar ya takura kansa muma haka, amma sai suka dage kan cewa gaskiya
yana buƙatar aure sosai kafin nan da azumi. Sanna duk abinda ake dashi bashi da wata
matsala akai wa yarinyar. Na ƙara kaso kunne inji me Umma zata ce. Sai naji tace, Gaskiya a
sa shekara ya yi haƙuri dan shekara kwana ce Abban Baby, bikin 'yar fari ba mu yi mata komai
ba ai sai mun shiga bakin duniya. Ban san lokacin da nace Umma zai fasa inhar aka sa
shekara,ni dai gara lokacin da yace É—in dan in ya fasa mutuwa zany.... Saukar ta kalmi da naji a
fuska ta shine ya tuna min cewa bai kamata in tsoma baki a zancan aurena da mahaifana su ke
yi ba. Na lalle su dan in gane waya jefe ni,sai naga ashe Umma ce, sai huci take ta rasa abin
faÉ—i dan takaici. Shi kuma Abba ya sunkuyar da.kai, sai suka bani mamaki, domin a magabata
banga wani abu na tashin hankali ba, na faÉ—a musu abinda ni nake so ne, kuma dai su iyayena
ne wazan fadawa halin da zan samu kaina in an fasa. Sallamar wani yaro ce ta ratsa shirun da
gidan ya yi kamar mutuwa ta gifta, Abba ya amsa sai yaron yace "Ance Baby ta zo." Na tashi
da sauri na shuri takalma sai da na kai bakin soro sai na waiwayo dan naji a jikina ni suka bi da
kallo dama na zargi haka. Na fita ina tunanin ko dai na kuma wani laifin ne? A fili nace garama
amin auren in tafi tunda har sun soma gajiya da ni. Na isa gunsa ina faɗin yau Jamila ta ƙi
kawo mana tabarma. Yaya sun tafi ke nan? Ya ce "Sun tafi." Nace amma sun faÉ—a maka komai
yadda aka yi? Yace "bakiji ba da Abba ya shigo?" Na ce Banji matsaya ba a maganar na saka
musu baki Umma ta jefe ni sai kuma suka yi shiru. Yace "Subhanallah! Me zai sa ki saka
bakinki cikin managarsu?". Na ne Yaya Shekara fa Umma ta ce, kuma kai nasan baza ka
shekara bada matarka ba. Yace Banda haka Yaya nima ba zan iya ba. Yace "Baby bai kamata
ba kina saka baki a maganar manya. Hajiyata tana da zafi in kinje kina mata irin wannan za ku
samu matsala wanda hakan zai kawo matsaloli a cikin zaman aurenmu. Ni kuma bana son a ce
ni da ke mun rabu, saboda akan Hajiya zan iya komai. To gaskiya in kina son mu daidai ta ni da
ke, to sai kin sawa bakinki linzami in manya suna magana babu ruwan ki." Na sunkuyar da kai,
insha Allahu na dai na. Nima jiya ne suka fara wannan kukan da ni,amma bana yi, ko yanzu a
maganar ka kaÉ—ai suke cewa na canza. Ni kuma banga canjin ba. Ya ce "Nima na gani dan
haka ki dawo kan hanya. Nace to, amma kai ai zamu iya tattauna maganar aurenmu ko? Ya ce
"Sosai ma kuwa." Nace to yanzu faÉ—a min yadda aka tsaya. Yace Abba sunce za su yi shawara,
domin shima Wan Abba cewa ya yi tunda na ce abinda ake dashi a kawo ki ba matsala to na shi
ganin gara a yi bikin kawai. Shine aka ce a shawarci Ummanki. Nace to Umma tana kiran
shekara. Yace Allah dai ya zaɓa mana mafi alkhairi. na ce ameen. Yace "Ni ma dai ya kamata
in tafi, da har zan wuce, sai kuma nake tunanin ban muyi sallama ba." Nace yanzu sai yaushe?
Yace, "Bazan sa lokaci ba gaskiya tunda an bani ke. amma kowane lokaci za ki iya gani na. Zan
bada waya a kawo miki saboda za mu ke yin magana akai akai. Nace "To É—an Allah kar ka
manta da Ni kaji. Ya yi yar dariya sannan ya yi ƙasa da murya, ashe zan mantà kai na. Ina

mugun sonki Baby. Cikin farin ciki nace ina sonka Aliyuna. Sai kuma naji kunya na saka hannu
na rufe fuskata. Muryar Abba naji yana cewa "Malam Aliyu bari in baka saƙo ka faɗawa
magabatan na ka.". Aliyu ya ce to shiga gida sai kin ga saƙon na ce to ka gaida su Hajiya da su
Anisa. Na laɓe a soro ko zanji me za su faɗa amma banaji. Dole na shige ciki Umma harta
kwanta na leƙa ɗakinta ina yi mata sannu, ko dai ta yi banza da ni, ko kuma ta yi bacci. Na fita
na je na saka tuwo na É—ebi ruwa a kofi na shiga É—akinmu na zauna ina ci. Jamila ta shigo da
shirin baccin ta, tace Yaya Baby ki sa su Jafar su yi fitsari in kin gama, yau duk ni na yi aikin ki a
gidan nan." Na ce me kika yi nawa da zaki faÉ—i haka?" Ta ce "Ni na tace gasara kuma na
kammala komai." Na yi 'yar dariya. Ni da zan tafi ma gidan mijina daga can zan ke zuwa ina
miki akin? Jamila ta yi gialala ta na kallona,sannan ta ce, gaskiya Yaya Baby abinki ya soma
wuce tunani, kuma ko a jikin ki. Na kalleta Ni Kuma ke kike bani mamaki, ko da yake na miki
Uzri bari ki faÉ—a soyayyar za ki gane abinda ya same ni. Tace haka É—azu ki ka yi ta rera wakokin
soyayya a gidan nan ke da ko wani ya yi waƙa sai kin masa wa'azi." Na suɗe robar ina lashe
hannu, na ce duk ba wannan ba, faÉ—a min abinda su Umma suka yanke da na fita. Abba ya
tsorata da yadda ki ka yi,Ya ce Umma ta yi haƙuri ayi bikinnan a haka yadda ki ke yi ya nuna kin
matsu da aure,abinda aka samu a kai miki. Daƙyar Umma ta yarda domin har abin sai da ya kai
su kamar za suyi sa'insa, daga bisani Abba ya lallasheta. Amma tana ciki da ke,zaku gauraya
da safe. Na É—anyi jim har ga Allah ni banga abin laifi ba amma dole in ke yin shiru dan in samu
zama lafiya. Na dubi Jamila wadda ta kwanta tana ƙokarin rufa. Na ce amma ya suka yi
matsaya a ƙarshe. Ta ɗago kai zakiji a bakin Umma da safe, shawarar da zan baki kuma ita ce,
ki bawa Umma haƙuri, sannan ki daina magana sam in ana zance.Na miƙe tare da faɗin zan
kula sosai. Da safe Umma bata amsa gaisuwa ta ba,to nan ne fa hankalina ya tashi na soma
kuka ina bata haƙuri, tace haƙurin me zaki ba ni, ni a su wa ɗanwake a Otal ba dai ɗa namiji
bane Baby Allah ya bada sa'a." Na ce Umma wallahi ni fa bansan me zance miki ba ne, kiyi
haƙuri na tuba don Allah.Abba ku yi haƙuri ni ban san cewa ba a magana ba. Ya ce tashi kije ki
yi aikin ki ta haƙura. Na fita ina sharɓen kuka. Ina jiyo Abba yana baiwa Umma baki, tare da
nuna mata cewa ƙuruciya ce,kuma mu godewa Allah Salamatu da ya bamu yara masu kamun
kai da nutsuwa, duk tsukunnan yaban su ake Allah ya sa musu albarka karki fusata Allah shine
mai rufin asiri abar auren a lokacin da aka sa shi. A ranar wani matashi ya yi sallama muna
Islamiya anci sa'a Abba yana gida . Suka gaisa yace Aliyu ne ya aikoshi da saƙo ya baiwa
Amira. Abba ya amsa waya ce sabuwa a kwali sai layin da kuma kati wanda ya ce ace in ta
saka ta kira shi. Abba ya ce to insha Allahu za a bata, taje islamiyya. Na yi murna sosai lokacin
da muka dawo. Umma ta ɗan saki jiki harma ta karɓi wayar ta sa albarka. Tace ki kula irin
wannan ta shafawar ba wuya ta fashe. Na ce to. Na saka layi na sa katin na shiga É—aki na kira
wata Number É—aya daga cikin lambobin da ke jikin wani kati da ya sako a ciki kwalin. Wani ya
É—auka, nace Aliyu nake nema. Yace mai gida baya nan ya yi tafiya. Nace Shamaki fa na ke
tambaya? Yace nima shi nake magana ya tafi China É—azu. Na ja tsaki sannan na kashe waya,
ina faÉ—in Ni Aliyu na ko filin jirgi baya zuwa bare wata China. Na sake É—akko katin don in duba
wata Number. Sai naga ya yi wa wata lamba alama da biro a ƙasa ya rubuta ki kira wannan
layin. Cikin sauri na saka na kira. Ya É—aga "Baby zan kira ki kinji?" Na ce to Yaya na gode, ina
jira fa ka kira ni fa. Yace karki damu. Haka dai abubuwa suka ci gaba da tafiya,
iyayena suka tada hankali gurin neman kuÉ—in da za a yi min kayan É—aki aure saura sati uku da
'yan kwanaki. Umma ta sanar da Baba har Kurna taje,Baba tace Allah ya sa hakan ya zama

alkhairi, abinda za ayi yanzu zata sa akama Awakinta guda biyar a saida su, a zo a karɓa a
sai min kayan kicin kuma zata sanar da sauran dangi. Shi kuma Abba an sanar da dangi sun
nuna murna amma da suka keɓe sai ƙanwar Babanmu Saratu wadda dama basa shiri da
Umma tace "Shi Abbana su Babyn da ya kama ya sa rana sati huÉ—u kila ya tanaji kuÉ—in da zai
yi mata kaya da na abinci da za a dafa. Dija tace Nima dai na yi mamaki muna neman
gudunmawar sauka mu bashi, shi kuma ya na tataro aure abinda Allah ya ba ni shi zan bada.
Saratu tace ita matarsa dan hauka gata da tsohon ciki shine ta yadda da wannan gangancin
koda yake ƙila ma ita ce tace a saka dan a ce yar ta ta riga 'yay'anmu aure. Dija tace ko wane
kwashe ne kuma zai ɗebi wannan yarinyar kamar taɓarya oho. Matar waliyin ta taɓa baki tare
da faɗin jiya da na shiga murna ai na ga 'yar da wata ƙatuwar waya wai saurayin ya aiko, shiko
Abban su Zuhra sai rawar kai shi ga waliyyi nace dubu goma dai ya baka abikin Ummi dan haka
sai ka nemi shabiyu kar kaji ance waliyyi ka fara neman siyan gado. Suka sa dariya gara dai ki
faÉ—a masa dan ga sunan riÉ—a riÉ—a duk wadda ta samu shima hidimar ce a gaban sa. Haka suka
yi ta maida zantuka ta re da alwashin zura ido su ga abin da zai biyo baya.
Har kwanaki biyu ina jiran kiran Yaya, Ni kuma inna kira bata shiga. Hankalina duk ya
tashi amma babu dama inyi maganar sai Jamila kawai inna faÉ—a mata sai ta ce bani da aji wai
in jira ya kira ni. Ranar kwana na uku ina zaune a kan tabarma a tsakar gida ina rubuta
sunayen waÉ—anda zan kaiwa katin sauka 'yan uwa da yan makarantar bokonmu. Jamila na ke
kira ta raka ni. Umma tace to kuma yaushe za ki kai na 'yan Kurna? Nace sai mu kai ranar
Lahadi ko asabar tunda bata da Boko sai muje. Umma tace hakan ya yi saura ku kuma zuwa
wani gidan nace imsha Allah babu inda zamu ƙara zuwa. Wayata ta soma kiɗan na ɗauka
da sauri. Sanyin zuciyata, haka na rubuta a lambarsa. Na tashi na shiga É—akinmu. Na É—auka
da sauri. Cikin shagwaɓa na ce sanyin zuciyata shine ka ƙi kazo ko? Yace "My Baby ki yi
hakuri tafiyar gaggawa ta taso min." Nace na kira wata lamba aka ce ka tafi China . Yace a a
Kaduna na je ina can har yanzu aka wasu kayanmu. Nace to Allah ya tsare shiyasa nace ni
Aliyuna ko filin jirgi bana zaton ya taɓa zuwa. Ya yi dariya "Na taɓa raka maigada ba so ɗaya ba
ma. " Nace Allah ya sa kai ma wata rana in raka ka. Yace "Ameen Allah ya sa mu hau jirgin
tare. Na ce ameen. Ya ce "To ya ake ciki menene labari?" Nace wanne zan baka?" Yace "Sabo
wanda ya ke tashe." Na ce kati zan kai in raba na sauka in Jamila ta dawo. "To kuma na bikin
yaushe za araba?" Ya katse ni. Kaga karka wani damu da katin Biki duk kashe kuÉ—i ne,
karatun saukaramu asabar ne ɗaurin aure Lahadi sai a faɗawa kowa a haka. Yace "Taɓ
aurenmu ace ba kati Baby ko bashi ne ni zanci don in buga mana katin biki." Don Allah karka ci
bashi a zo ana sallama da kai. Na faɗa cikin shagwaɓa. Yace "Ai misali na yi.
[6/16, 19:58] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_

_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo evidence ta wannan
number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya É—ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare
da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_


*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*


*Free Page 8*


Abubuwa sun kankama lokaci yana ta ƙaratowa Munafinci ba ga maƙota ba ba kuma ga dangi
ba. Umman su Fati har gida ta zo wai Allah ya sanya alkhairi amma harda cewa Umma ashe ku
da tanajin ku,auren Fati sai bayan Babbar salla mu masu ƙaramin ƙarfi. Umma tace Allahn da
ya kawo mijin a lokacin da masu gori suke gori shine zai kawo abinda zamu kai mata. Ina jinsu
Umman su Fati aka wuce ana borin kunya. Umma tace Allah kai zaka yi mana wannan lamari
Allah ka taimake mu. Sauran kwana huÉ—u walimarmu kwana biyar kuma a É—aura mana aure.
Yaya ya aiko min da katan Lemo guda biyar wai na walima a daran ranar ne ya zo gurin Abba
ya nemi alfarmar a É—aga aurenmu zuwa wani satin. Walimarmu da sati É—aya kenan. Abba yace
ba damuwa, ya shiga ciki ya sanar da Umma sannan ya ce in fito. Mun gaisa yake faÉ—a min wai
gyaran banÉ—akin gidan za'ayi shine dalili. Na ce to Allah ya kaimu, amma banso haka ba,yace
kamar yau ne. Yanzu ki faɗa min me da me kike buƙata a gurina. Na dube shi, kamar na me?
Yace "KuÉ—in lalle da pati ko baza ki yi ba?" Nace zanyi amma kana da kuÉ—in ne? Yace Inkinji
makaho yana cewa a yi wasan jifa ai ya taka dutse ne ko? Ki lissafa min duk abinda ki ke so na
biki zan miki daidai ƙarfina." Nace to kana son mu kira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login