Showing 12001 words to 15000 words out of 28231 words

Chapter 5 - Hamshakiyar Uwa Book Compelet Halima Mashi

lafiya ina kwana? Yace "Lafiya lau ya lura na fita hayyaci
na yace "Ki daina damuwa ba wani abu bane, jiya da naje gurin maman Ogana shine ta ce
tana son ta ganki wai yau ko gobe, ni kuma ina tunani nasan baza a barki kije ba,shine na zo in
tambayi Abba da kai na, ko Allah zai sa ya yarda." Nace wai gaskiya ko da kuɗin ka a gidanmu
hatta Umma baza ta bari ba bare kuma Abba, kan wannan maganar ma sai kaga an fasa auren
nan,ka bata haƙuri kuma zata fahimta tunda itama Uwa ce kuma abinda ke faruwa a zamanin
nan kowa ya sanshi.Kuma ka faɗa mata bamu daɗe ba.

Ya ɗan yi shiru, can ya ce "Baby akwai matsala ne, za a iya samun cikas in har baki je ba,
saboda ita ta zata mun daɗe domin na jima ina ce mata ina da budurwa, kuma zata sanar da
mai gida cewa ban kai ki ba, kuma maigidana shine jigon bikin nan,sai ki ga kan wannan yabar
maganar nan inje ga wata to abin da nake tsoro kenan." Na zuba mishi ido cike da zargi,kodai
cutar da ni zai yi ya dage haka,ƙila ma sai da yaga fitar Abbanmu sannan ya zo dan ya yaudare
ni. Nace Humm Yaya ka yi haƙuri gaskiya ni kai na na soma zargin wani abu, dan Allah kar ka
cutar da ni wallahi ina son ka da gaske... "Cutarwa kuma Amira? Me zai sa in cutar da ke kuma
meye ribar hakan idan nayi? Ba ɗan iska bane ni ban taɓa zina ba ko lokacin da ina saurayi,
kuma bazan fara a yanzu ba. Ko zan yi Baby ai ba zan yi da matar da zan aura ba." Na sauke
lumfashi Yaya bazan hana zuciyata yin kowane irin hasashe ba,sai dai in ƙi gaskata abinda ta
hasaso. Ka yi haƙuri ko ƙanwarka ce in ka mai da abin a kan ta zaka ga ba za ka amince da irin
hakan ba. Ya sunkuyar da kai "Kin fini gaskiya ko ta wane fanni Baby amma taimakon da za
kimin ciki harda sana'a ta. Mahaifiyar maigidana mace ce mai kirki da mutunci,ta ɗauke ni
kamar ɗanta. To tana da irin nata ƙa'idojin dan Allah ki taimakawa mijinki." Zuciya ta ta soma
tunanin munafurtar iyayena, amma ta Yaya kuma wane tabbaci ne da ni kan cewa bazai cutar
da ni ba? Ya sake katseni "Nasan haka rashin kyautata ne musamman ga iyaye amma
sadaukarwa a soyayya ibada ne, kuma ɗan gyaran babbar ɓarna yin ƙaramin kuskure ba aibu
bane. Wallahi ki yarda da ni Rabi'atu wallahi ba zan cuce ki ba." Na zuba mishi ido wata
ƙaunarshi na ke ji a zuciyata ga tausayin shi kamar inyi kuka. Na sauke a jiyar zuciya. Yaya
Aliyu ban taɓa yi wa iyayena ƙarya ba, kuma ban taɓa munafurtar su ba, zan sadaukar kan so
da ƙauna,zan munafurce su so ɗaya a yau kuma zan musu ƙarya, amma karka maida hakan ya
zama nadama a gurina ka tabbatar da kyau tata maka zato da na yi. Na shirya sai ka tsara min
yadda zan yi duk abinda kake so batare da sanin iyaye na ba.
Ya sauke wata ajiyar zuciya "Alhamdulillah! Kina da ƙawa wadda za kuje tare domin ki ƙara
samun mutsuwa?" Na girgiza kai, ba ni da ƙawa. Yace, "To Jamila fa? Kiyi magana da ita
matsayin ta na 'yar uwarki zata iya fahimtar ki sai kuje tare, matsalar ina zaki ce zaku?" Na ce
Yaya komai zai faru da ni ni ce mai son ka don Allah banda Jamila. Yayi 'yar dariya kirata nace
kibar wannan a hannu na zamu yi magana anjima a wayar Umma sai dai muje gobe kenan.
Yace yauwa daidai ke nan gobe bamu cika fita kasuwa da wuri ba,insha Allahu zan kira muyi
magana. Mukayi sallama ya ce in shiga gida kafin nan ya wuce.
Jamila tana shara na shigo ta dube ni,"Lafiya Yaya Baby naganki sukuku haka? Nazo na leƙo
naga saurayin ki da safen nan. Nace Umma bata tashi ba? Tace e kinsan sai gurin shaɗaya
zata farka, na nufi ɗakinmu na dubi Jamila na ce,zo. Ta saki tsintsiya ta shigo cike da fargaba
tana faɗin wai ya fasa ne Yaya Baby? Na ce zauna, muka zauna kan katifa, na ce Mahaifiyar
maigidana ce ke son gani na, in ba haka ba zata bashi wata,kuma inya bijire zai iya rasa
aikinsa. Jamila tace "To kije mana." Nace baki da hankali su Umma baza su bari ba, shine nike
tunanin yadda za ayi ki raka ni batare da sun sani ba,sai muce zamu je gaida su Baba kinsan
Abba zai yarda sai muje gidan daga can sai muje mu gaida su Baba ɗin ko? Jamila ta ce haka
ne, amma kafin lokacin islamiyya zamu dawo gara ke maraja'ar sauka kuke yi." Na ce ba
damuwa,zan faɗa masa, amma sai mun ji ta bakin su Umma. Bayan Isha'i ya kira ni na faɗa
masa duk yadda muka yi,kuma na faɗawa Umma ta ce mu tambayi Abbanmu. Yace "Na gode
sosai,amma ita Baba ɗin wacece? Nace ita ce ta riƙe Ummanmu har ta aurar da ita bayan
rasuwar mahaifiyar ta,kuma mun jima bamu je ba,tana son mu sosai. Yace Ni ma ya kamata

inje in gaisheta wata rana nace gaskiya ne. Yace "Wace unguwa take?" Nace Kurna ta ke, yace
"To ba matsala gobe kamar ƙarfe nawa zaku fito?" Na ce kamar shaɗaya Ummanmu ta farka a
bacci mu kuma mun gama aiki, ya ce haka yayi zan zo amma sai dai in tsaya can gurin ƙofar
fanfo sai ku zo mu wuce." na ce to. Bayan mun yi sallama na damu sosai yadda zan ha inci
iyaye na amma sai wata zuciyar tace khairan insha Allah. Abba yana cin abinci Jamila ta ce
Abba zamu samu kuɗin mota gabe muje mu duba Baba tunda ta yi zazzaɓi nan Ummanmu
bata samu zuwa ba muma haka, yace to zan sama muku, daga nan kwa bata labarin saurayin
na Baby kar taji daga sama. Umma tace aiko aji murna gurin Baba,bata da burin da ya wuce
auran Baby. Ni dai duk tausayinsu nake ji domin na ha'ince su.
Washe gari Abba ya bamu na mota sannan ya bamu ɗari biyar ya ce mu bata. Umma kuma ta
bamu Naira ɗari ta ce mu sai mata goro. Jamila dama ta saƙe wayar Umma sai da muka fita
ƙofa muna gefen babban titi sanna nace Jamila yanzu yaya za ayi Yaya yasan mun fito? Ta ciro
wayar Umma ta miƙo min tare da faɗin "Taimakon farko." Na karɓa tare da faɗin na shiga
uku,in Umma ta nema fa.? Jamila tayi dariya wa ke kiranta banda Abba sai kaɗan daga dangi,
ƙila har mu dawo ba a kira ba, in ma an kira zamu ɗaga muce tana gurin mu. A zuciya ta nace
in ma munga zai cutar damu sai mu kira Abba. Na kira shi na ce mun fito ya ce to ku samu keke
kuce Janbulo ƙofa ta biyu ni sai zan jira ku a daidai BUK tsohuwa. Muka ce to.
Cikin sauri yake shiri tun jiya ya sanar da Hajiya cewa su Rabi"a za su zo yau da misalin
shabiyu saboda islamiyya ta ce Allah ya kawo su, dan haka ta soma duk wani shirinta. Sun
sake kira shi da suka zo inda ya kwatanta musu,sai yace Kuɗan jira,ko da yake ba mai
adaidaita sahun mu yi magana." Na bashi ya yi masa kwatance ya ce ya gane,sai yace ya bani
wayar,na amsa sannan yace zai kawo ku kusa da gida sai mu ƙarasa. Mun tsaya kusa da wata
baƙar mota sai kiranshi ya shigo kune kuka tsaya yanzu naɗan leƙa ko zan ganshi ina fadin e
mune. Sai naga ya buɗe motar ya fito yazo yace wannan motar tace ku biyomu. Na ce to cikin
fargaba. Gaban wani damfareren gida muka tsaya ga wani ƙaton gate kamar ƙofar kasuwa, dan
ƙareren masallacin da na kalla a jikin gida kuma fentinsu iri ɗaya shine ya sa na ɗanji sauƙin
fargaba. Mai gadin ya buɗe,naga anyi masa magana daga motar sai ya nufo gurin mu yace da
mai keke ya shiga. Muka shiga hamshaƙin gidan mai keke yace ashe zan shiga gidan Hajiya
ZEENA a rayuwa. Nace kasan ta ne? Yace e mana masu ZEENA Foundation ina ne ba'a san
su ba a ƙwaryar Kano.Har muna haɗa baki gurin faɗin muna jin tallolinsu a Radio muka tsaya
nace nawa ne kuɗin? Yace bari Alhaji ya bani nan gidan ai ba 'a rowa. Nace Alhaji baya nan
wannan yaro shagon sa ne. Daidai lokaci da Yaya yace Amira,na waiwaya, ya yafito ni da
hannu naje gurin sa yace nawa ne kuɗinsa? Na ce yaƙi faɗa, yace to tsaya nan ina Jamilar
kirata bari inje gunsa. Nace Jamila zo,ta fito shi kuma ya nufi gurin mai keke,abinda yake gudun
shi ya faru,mekeke ya soma faɗin ranka ya daɗe ina gaisuwa Shamaki ya ciro kuɗi bai ƙirga ba
ya bashi tare da faɗin jeka Allah ya tsare. Shiyasa ya yanke shawarar ƙin jiransu domin tabbas
mutane za su gane shi kuma komai zai fallasa.Ya shiga gaba ku zo muje.


️️️
[6/16, 19:58] Ummi Tandama: *HAMSHAƘIYAR UWA*

*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan
number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare
da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_


*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*


*Free Page 6*


Muna shiga ƙofar da ya buɗe wani ƙamshi ya bugu hanci mu wanda baza mu iya tantance
ƙamshi abinci ne kona turare ba, na raɗawa Jamila cewa ki kama kanki sosai. Ta ɗaga kai
alamun taji. Mun isa wani falon da na zata nan ne sai muka ga ya ƙara buɗe wata ƙofar,muna
shiga wani falon ne na alfarma da ya ɗara wancan. Ya nuna mana kujera,ku zauna a nan ku
jira in faɗa mata.
Ya shiga wata ƙofaar, da sallama Hajiya ta ɗago ta dube shi,tana riƙe da wani ɗan littafi na
addini,a hannunta ya je ya tsugunna,ga su sun iso na ce bari in sanar da ku. Ta aje littafin "Su
shigo mana, ya ce amma Hajiya sai dai fa bance nan ɗin gidanmu bane,zan sanar da su Juma
yanzu don Allah kar su yi wata alama da zata nuna cewa ni ɗin na gidan ne. Hajiya ta ce
"Kasan ban iya ƙarya ba,amma zan iya hikima. Yace hakan ma ni ne da godiya Allah ya ƙara
nisan kwana. Ya nufi gurin su Juma a kicin ya faɗa musu cewa kar su nuna cewa shi a gidan ya
ke, gaban baƙin nan da za su shigo. Juma ta ce "To Allaji uban ɗamina. Ya zo yaje falon da su
ke zaune,ya ce ku zo muje. Ya dubi Baby,"Dan Allah zan nemi wata alfarma a gurinki," Ta me?
Ta tambaya cikin sauri da faɗuwar gaba. Yace duk abinda Hajiya ta tambaye ki dan Allah ki bata
amsa ta gaskiya, kuma karki fusata. Nace To,,Yaya insha Allahu. Gabana ya tsananta faɗuwa
bansan dalili ba, muka cusa kai cikin falon ƙamshi sanyi da laushin kafet ɗin da na taka shine ya
ƙara sani a fargaba. Ko ban ɗaga kai na kalli ko ina ba,nasan falon na alfarma ne, na kalli inda
aka amsa mana sallama kyakkyawar dattijuwa mai matuƙar kama da Yaya sai dai ita fara ce
tas,kuma kamala da isa da bunƙasa sun bayyana kansu a gareta. Ta bimu da kallo tare da furta
sannunku da zuwa cikin maganar hakiman mata. Yaya ya tsugunna a gaban ta ta gefen dama

yana faɗin Hajiya ga su nan. daidai lokacin da ta nuna kujera tana faɗin ku zauna mana. Sai na
zube ƙasa kusa da ita kamar yadda na ga Yaya ya yi Jamila ma tazo muka fara gaisheta cikin
mutuntawa. Ta zuba mana ido,cike da mamaki ta ce, "Shamaki naga wasu 'yan tsintsayen
yara,raino za kayi ke nan? To wacece a cikin su. Ya nuna ni. Na sake sunkuyar da kai. Tace to
madalla. Ya miƙe tare da faɗin "Ina dawowa Hajiya. Tace to ba laifi." Wata Dattijuwa ta shigo da
sallama muka amsa tare da gaisheta,ta amsa cikin fara'a tace Hajiya komai an kammala. Ta ce
"To ku kawo musu abinci da na taɓawa." Wannan Dattijuwa tare da wasu mata biyu suka shiga
jera kayan marmari da kayan fulawa dangin cincin harda alkaki,sai kuma can ga kaji da wata
shinkafa ƙamshi kuma tuni yawuna ya tsinke amma ko kallon gurin banyi ba, ta ce "Ga abinci
sai kunci ko?" Jamila ta kalle ni wadda nasan ta ƙosa ayi mana ta yi,da ido na nuna mata 'a 'a
sannan nace, Alhamdulillah Hajiya mun ƙoshi. Tace aikuwa dai ba a zuwa gidana afita haka
dole sai anci wani abu, kuma ansha wani abu. Nace To na tashi na ɗakko robar ruwa na dawo
na zauna,ta ɗakko wani ɗan faranti da dabino manya jajir tace, "Ci wannan tunda duk can
bakiga abinda zaki iya ci ba." Duk da dabino bai fiya damu na ba, sai na saka hannu na ɗauki
guda ɗaya na soma ci sannan na buɗe ruwan na kurɓa. Ta kalli Jamila ke jeki can kici duk
abinda ki ke da shi'awa a can. Ta tashi taje ta zauna kusa da gurin sai ta ɗauki alkaki. Hajiya ta
dube ni. "Ki cinye dabinon tas tunda kin ƙi cin komai." ban yi magana ba. Na dai kuma ɗaukar
wani. Tace "Ina ne asalin garinku?" Nace Ummanmu 'yar asalin Sumila ce, shi kuma
Babanmu ɗan Rano ne. "Kece ta nawa a gidanku?" Nace ta fari ce ni sai wannan ƙanwar
tawa."Ai ƙanwarki ce! Ina ƙawayenki kike tafiya da ƙanwarki?" Na sunkuyar da kai, bani da
ƙawa ita ce dai mu ke komai tare. Ta ce "Ya yi kyau haka,bayan ita kina da wasu ƙannai?"
Nace akwai biyu maza ƙanana ne. Ta ɗanyi shiru, can tace, "Ina sauran dangin ku suke?" Na
Babana unguwarmu ɗaya akwai kuma wansa da ƙaninsa da kuma ƙannensa mata duk suna
unguwanni suna aure, dangin Ummanmu kuma suna Kurna. Ta ce "Madallah. Amma iyayen ki
sun kyauta da suka bari kuka kawo min ziyara duk da cewa ba wata magana mai ƙarfi taje
musu ba ." Yadda ta yi wannan maganar sai naji kamar habaici, sai nace, Ai basu san zamu zo
ba, gaida Kakarmu zamuje shine muka biyo. Na kalli Jamila wadda ta zuba min ido kamar ta
kai min duka dan haushi nasan tunanin ta me yasa zan yi wannan maganar, ni kuma nasan
dalilina na faɗin hakan. Hajiya ta yi ɗan tsam tana kallona, sai ta yi ɗan murmushi ke nan
ƙarya ki ka yi wa iyayenki ko? Kin yi wa iyayen ki ƙarya wazai sha?" Na sunkuyar da kai, kamar
shirin Film sai naga hawaye sun soma ciko idanu na, cikin shashshekar kuka nake faɗin ban so
yin hakan ba, kuma abin ya dame ni, dole inna koma in nemi gafararsu amma Yaya ne yace shi
yana son in zo in gaishe ki, shine muka fake da zuwa gidan kakarmu. Jamila ta ce Innalillahi
Yaya Baby meyasame ki haka?" Nasan haka zaki yi wallahi ba zan zo ba, ta aje ballin alkakin
dake hannun ta ta koma gefe cikin fushi. Hajiya ta yi ɗan murmushi "To ai kamar ba a yi wani
abin kuka ba ko?" Na numfasa ban kyauta musu bane shi kuma Yaya zai ga kamar ban ɗauke
shi da muhimmanci bane. Na kalleta bayan na sauke ajiyar zuciya. Ta ce "To shi Yayan da kike
faɗa wanene?" Cikin mamaki na tsura wa gefe ido, tsabar rainin hankali ne, ko kuwa dai da
gaske bata fahimci wa nake nufi da Yaya ba.Na numfasa wanda ya kawo mu. Ta taɓa baki, "Au
wai Shamaki ne Yayan? Kuna da wata dangantaka ne ta kusa ko ta nesa?" Na girgiza kai,
babu, kawai bazan iya kiran sunanshi ba ne kai tsaye Hajiya. Na soma ƙosawa da tambayoyin
ta ko ita ce uwar shi ai bazata min Wannan maganganu ba. Wata zuciyar ta ce shi yasa ya baƙi
haƙuri tun kafin ku shigo. "Menene matsayin karatun ki?" Wata tambayar ta kuma katse

tunanina Muna jarabawar kammala Sakandire zamu gama jibi. "Kina da burin ci gaba?" insha
Allahu in har Yaya ya amince kuma yana da halin hakan ina son ci gaba da karatuna. Ta yi ɗan
murmushi Ki daina kiranshi da Yaya ki faɗa mishi wani sunan ko dai ki kira shi da sunan sa. Na
yi shiru cikin mamaki. Ta nuna min ɗan farantin Dabino. "Akwai buƙatar ki cinye wannan
dabino." Na kalla na ci guda uku. Sai naji kamar zan zargi a wani abu a cikin dabino. Nace ya
ishe ni ne Hajiya ban cika cin dabino ba. Ta maida kallon ta ga. TV kamar ba zata kuma
magana ba, na kalli Jamila ta min alamar wai inzo mu wuce.

"Islamiyya fatan dai kina zuwa?" Mu ne zamu yi sauka a makarantarmu nan da sati uku. Na
bata amsa nima kamar ina jiran tambayar. Sai na ga ta kalle ni, daidai lokacin Shamaki ya Turo
ƙofa tare da sallama. Ya kalle ni sannan ya tsugunna a ɗaya gefen na Hajiya yana mata sannu
da hutawa. Ta amsa a ƙasaice ba tare da ta kalleshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login