Showing 27001 words to 28231 words out of 28231 words

Chapter 10 - Hamshakiyar Uwa Book Compelet Halima Mashi

daga tambayoyin da Hajiya tayi min a ranar farko da na kwana
ɗakin na bata amsa tace gaskiya banyi aure ba, tace yarinyar ta gama bin mazanta ta ɗora
mata karan tsana,wanda hakan ya janyo nima naji na tsane ta. Haka ta rayu da mu duk da bata
rasa komai ba amma tana yaye Meema ta zaɓi ta bar gida kamar na mu mai cike da daula, ta
koma gidan iyayenta duk da cewar suma ba wai talakawa bane. Haka nan na sallame ta Hajiya
ta sa aka haɗa mata da goma ta arziƙi kamar dai yadda kuka sani. Kinji ɗaya. Ita kuma Maman
Mubina kunsan daga girki a nan aka fara samun damuwa, domin da Hajiya ta yi min irin
tambayoyin da tayimin a daren farko da muka kwana sai na faɗa mata irin abinda ta ke
buƙatar ta ji, don haka sai tace to bisa al'adarta za a haɗa komai na girki ta fito ita ce zata ciyar
da ƙawayen Hajiya da sauran "yan biki da girkin da ta yi da hannun ta. Sannan tazo ta zuba wa
kowa da kanta. Wai manufar haka a ga ko ta iya girki,in kuma ta iya a gurin zubawa a gani ko
marowaciya ce ko kuma zata iya jan ragamar gidan a matsayin ta na matar jigon gidan. In baku
manta ba,itama anan aka soma samun matsala. Wadda ta zama kullum cikin faɗuwa a duk
wata jarabawa da Hajiya ta yi mata. Bisa ga wannan dalilin itama ta ce ta gaji dole na sallame
ta kamar yadda Hajiya ta bada umarni. Ya numfasa ta ƙarshe Maman Anisa. Ta tsallake
maganar girki da wani budurci domin ita Hajiya sai da ta tsaya ta tabbatar ban yi mata ƙarya
game da daren farko ba.Sannan Maman Anisa ta iya girki da kayan ƙwalam na fulawa ina ji a
jikina za mu zauna na har abada da ita domin ta iya duk wasu dabaru na riƙe zuciyar miji, to sai
Hajiya ta hango aibun wannan kular da ta ke bani, tace ni ne jigon gida kuma ni ne sirrin gida
babu wani dalili da matata zata san komai na gidan dan haka in tsuke baki na kar ta na jin
komai daga gare ni. Haka na yi wa Hajiya alƙawarin ta dai na sanin komai, to amma na kasa
daina faɗa mata musamman in ta sani farin ciki na rasa labarin da zan bata kuma ni labarin
kasuwa nafi sani. To Hajiya ta zafafa akan hakan kuma ita bata nemi saki ba,Hajiya ta nemi a
sahale mata tare da bata tukwaici irin wanda aka ba 'yan uwanta na baya. To Ni kunji damuwa
ta Yarinyar nan da zan aure na ɓoye mata ko ni waye, 'yar talakawa ce, kuma ƙarama ce bata
kai shekarun Matana na baya ba. Sannan wata babbar matsalar ina yi mata wani irin so wanda
bazan iya fassara shi ba. Ta kai bani da control ɗin kai na game da ita, har yaran Kantina su
Hassan sun fara yi da ni akan soyayyar ta. Bana son mu samu wata damuwa da Hajiyata amma
nasan zata yi ƙorafi game da soyayyar Baby. Haka ga matsalolin farko dana lissafa muku, ba
lallai yarinyar nan ta na da wannan budurcin ba kuma hakan ba yana nufin ta bi maza ba ne,
likitoci sunyi bayani zai iya tafiya da kanshi sakamakon cima da wasanni na makaranta tsalle
tsalle da guje guje to in aka yi wa yarinyar hukunci da cewa ta bi maza ai bamu yi mata adalci
ba. Wannan shi ne kukana. Maman Umar ta numfasa ta kalli sauran ta ce "Ni a nawa ganin

Hajiya ba ta yi wannan bane domin ta takurawa rayuwarka, tana yi ne domin ta inganta
rayuwarka da mu gaba ɗaya, ka taɓa tambayar dalilin da ka samo suna Shamaki? . Sannan ita
ta ba mu kulawa mai tsanani da lallaɓa rayuwarmu domin ganin mun kai mutuncin mu gidan
miji, in ka fahimce ta to zaka gane dalilin da take yi maka kiwon Azima. Ta fannin rufe sirri ga
mace kuma shima sai inga cewa hakan shima daidai ne, domin kai ne kan komai na gidan
dukkan wata dukiya da muka mallaka kai ne ka san komai,lauyoyinmu ma su kula da
dukiyarmu kai ne suka sani. Duk wani kaya dazai shigo da kuma wanda zai fita sai ka amince
na dukkan rassanmu na jihohi. To mai ɗauke da irin wannan nauyi dole ne ya zama baya cikin
shagala ko wani abu mai kama da ɗauke hankali. Ina fatan kun fahimci me nike nufi. Duk suka
ce haka ne Shamaki ka yi nazarin maganar Maman Umar.

Maman Nana tace kuma gida kamar namu ba zai kyautu ace marowaciya ce matar gidan ba,
akwai hikima cikin gwaje gwajen da Hajiya ta ke yi wa matanka, kuma zaka gane haka nan
gaba. A'isha ta ce "Ya kamata dai ta janye maganar budurci nan saboda dalilan da Shamaki ya
bada gaskiya haka ne, inzan bada misali da kai na, kwanaki Afra ta faɗi a banɗaki har ta yanke
ta gabanta mukaje asibiti damuwata kar dai ya taɓa mata matanci likita yace ko da ya taɓa ba
bu wata matsala ya kuma yi min bayani irin wanda Shamaki ɗin nan ya yi. To in kun kula da
maganar likita kwalbar nan ta yanke wa yarinyar wannan yanar da ake magana to sai aure ya
kai ta inda ake irin wannan al'adar ta ya zata wanke kanta?" Duk suka haɗa baki gurin cewa
babu. Shamaki ya yi zugum yana tunanin amsar da Baby ta bashi, "Ni budurwa ce amma bani
da wani tabbaci akan budurcina." Ya numfasa, daidai lokacin da Maman Iman ta ce "Ina ganin
tun da yanzu duk mun yarda cewa Hajiya ta na kan gaskiya sai dai ɗan gyara kaɗan ta yaya
zamu sha kan hakan?" Shamaki yace Yawwa an zo inda nake son a zo, gyara nake so ya
kasance in nayi aure na yi kenan kamar yadda ku ke da mazajenku. Ba shakka ina son nima in
zama cikakken mutum in kare mutuncina ku sani baya ga karewar Ubangiji matan da suke
kawo kansu gurina da yanzu na canza layi na shiga bin matan banza tunda kuɗi suke buƙata ni
kuma bani da matsalar kuɗi. Suka ce haka ne Allah ya ƙara karewa. Maman Umar ta ce "To ni
a matsayi na na babba a cikin ku kuma wadda in aka samu kuskure a zaman nan laifin zai iya
dawowa kai na ina son in baku dama ku kawo na ku shawarwarin sai in haɗa da nawa sai mu
tunkari Hajiya. Sai dai amma ina son ku tuna wasu abubuwa kafin ku kawo shawara. Wacece
Hajiyarmu? Ya kaifin basirarta yake? Kuma me zata iya amincewa dashi? Ina sauraronku mu
fara da Maman Nana tunda ke ce mai bina sai mu gangara har zuwa Shi Shamakin namu.


*Alhamdulillah a nan na kawo ƙarshen free Pages, waɗanda basu biya ba sai suyi ƙoƙari su
biya dan samun cigaban labarin,zaku turo ₦600 ta wannan account number 0700549935
Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin
Mtn shima ta wannan number 08140004302*

️️️

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login