Showing 57001 words to 60000 words out of 76655 words
Chapter 20 - Idan Bake Book 1 Complete Naima Sarauta
ya samu peace of mind kwana biyu yana stressed kansa da yawa. Kiran sallar farko a kunan Yaa Sheikh da Halisa domin zamanta wajan mother ta saba da tashin asuba, a hankali ya nufi bathroom tare da sakarwa kansa ruwa mai zafi kana ya yi alwala tare da yin brush, cikin zafin nama ya shirya cikin kyakkyawar shigar shi wacce ya saba, farar jallabiya ya ɗora hirami a kan shi, bakinsa ɗauke da aswaƙ ya nufi Masjid Malik wanda shi ke gabatar da jam'i a can, bayan idar da Sallah ya yi karatu wa jama'a kamar yadda ya saba.
7:00 ya shigo gidan da mmki yake jin parlour ƙamshi mai daɗi, yana ƙoƙarin shigewa part ɗin shi ta ce "Jamɓanduna?" Jin fillatanci yasa ya fahimci ba Zahrah bace amanar shi ce kuma ƴar riƙonsa, ya juya tare da kallon ta, tana cikin wata duguwar riga mai kyau plush pink sai baby hijab a kanta, kai ya ɗauke ta ce.
"Anti Zahrah ba ta shi ba, ni tun ɗazo na tashi ina ta kallo" shi dai bai ce komai ba ya shige part ɗinsa tabi bayan shi da kallo kafin ta juya zuwa kollon girke-girken da ta keyi.
Yana shiga part ɗin sa ya zauna saman kujera, tare da kiran number Umar-khan babu jimawa ya ɗauka a nutse ya ce "Ka yi komai, kada ya shige kwana biyu a nemi gurbin karatun" yana faɗin hakan ya kashe wayar, tare da kiran wata number mgn ɗaya ya yi ya kashe..
Halisa na zaune taji telephone line na ƙara ta miƙe sauri daman Umar-khan ya faɗa mata yadda ake amfani da ita, tana ɗagawa taji ance "Mrng maaa, the breakfast is ready Yaa Sheikh na jira" Halisa ta ce "Kika ce me?" Ta ce "Abincin Yaa Sheikh ya kammala kina magana da ɓangaren kitchen, yanzu maid zata kawo" Halisa ta taɓe baki tare da komawa ta zauna, babu jimawa wata mata mai fararen kaya ta shigo ɗauke da tray da butar shayi ta ce "Mrng Maa ga shi Yaa Sheikh na jira"
Halisa ta amsa tana miƙewa tsaye Zahrah ta fito cikin kayan barci da alama ko sallar ba tai ba, ta kalli matar ta ce "lafiya?" Tai mata bayani ta ya mutsa fuska ta ce "Ok daman ita ce mai aiki bata ta kai, ki sama mini breakfast mai kyau yanzu" matar ta juya Halisa ta riƙe tray Zahrah ta ce "Sai ki fara aikin ki tun yanzu, kije ki kai masa breakfast ɗin ki dawo ki shirya mini kayana a wardrobe" Halisa ba ta ce komai ta juyawa zuwa inda taga Yaa Sheikh ya nufa, bakinta ɗauke da sallama bata sani ba ko ya amsa ko bai amsa ba, yana zaune kan kujera ta ƙarasu har inda yake ta tsuguna ta ce "Ga shi wai" ya gyara zama yana tsiyaya tea ɗin tare da kaiwa bakinsa. "To kai iya wannan kake sha ne? Ko nayi maka abinci?" Da idanu kawai yake bin gefen fuskarta da kallo ta gyara zama ta ce "Mother ta ce kai mijina ne" ya ware idanu da sauri yana binta da idanu, ta buɗe baki zata sake magana caraf ya saka hannu tare da kame bakin.....
08119237616
Paid book
Not edited
"Shiru" ya ce yana sakin bakin tare da mai da Idanunsa kan glass cup ɗin da ya tsiyaya tea aciki. Ta tura baki gaba ba tace komai ba duk da irin ƙaiƙayin da bakin yake mata, haka nan taji kamar ana mintsininta akan Halisa yi magana cikin sauri ta ce.
"Nima ina jin yunwa na sha shayin naka?" Cak ya ajjiye tea ɗin daga hannunsa yana ɗaukan tissue tare da goge bakinsa, ta ɗauki shayin daya rage zata kai bakinta ta ji ance "A'a" ta ajjiye cup tana miƙewa tare da bin bayansa, sahun tafiya da yaji a bayansa yasa ya tsaya, tayi saurin dawowa gabansa suna haɗa ido ya ware mata manyan idanunsa masu kaifi ta tura baki ta ce "Na sake magana banga ka riƙe bakin ba ai" Yaa Sheikh ya girgiza kai kawai tare da shigewa bedroom ɗinsa yana ɓoye yanayin fuskar shi. Ta kalli inda ya shiga sai kuma ta juya tana kwashe tray ɗin. A main parlour ta samu Zahrah zaune tana breakfast ga wata maid nayi mata tausa a ƙafa. "Ke zonan" cewar Zahrah Halisa ta dawo ta zauna tana ɗauke kai gefe guda, saboda har yanzu bata mance mari da zagin da Zahran tai mata ba, Zahrah ta ajjiye spoon ɗin hannunta wanda take shan tea da shi ta ce.
"Kai breakfast ɗin sai yanzu? Ko bai ta shi bane" Halisa ta kalle ta sai kuma ta ɗauke kai tana faɗin. "Shi ya ce na tsaya" Zahrah ta ce "Shi Yaa Sheikh ɗin?" Tai shiru ba tare da ta ce komai, tasan indai zatai magana to zata saki layi ne, Maid ɗin ta kalli Halisa da sauri, ai ko ita da tayi shekara da shekaru tana aiki a gidan Yaa Sheikh magana bata taɓa haɗa su ba, infact ko parlourn shi bata san ya yake ba, Ummul ce kawai take kai masa breakfast ita ma iya dining room, sai ya gama yabar wajan take zuwa ta kwashe, idan kuma yini gida zai yi a ranar basa taɓa zuwa part ɗin, Umar-khan ne ke kai masa dinner, bai fiya cin lunch ba sai dinner, anytime yana tare da butar shayi kamar buzu. Mamaki ya cika Maid ɗin jin abin da Halisa ta faɗa wai shi ya ce ta jira? Who is she to him?.... "Whatever, Ke yama kika ce sunanki?" Maid ɗin ta ce "Bara'at" Zahrah ta ce "Ok, duk wani aiki na part ɗin nan, zuwa part ɗin Yaa Sheikh ya dawo hannun wannan yarinyar, idan kun kammala abinci na Yaa Sheikh ita zata dinga kai masa, bana son na dinga ganin wani abu na ba daidai ba, bana son surutu da hayaniya yana saka mini ciwon kai, ko a gidan ubana ban taɓa sanin hanyar kitchen ba, to a nan ba zan fara saninsa ba, kuna gama girki ki bata ta kawo mini nawa" daga Halisa har Bara'at kallon Zahrah suke, suna mamakin ƙarfin ikon nata, duk da cewa Bara'at bata san matsayin Zahrah ba, amma tasan dole da akwai abin da ta taka a gidan... Zahrah ta kaɗa ƙafa tana faɗin "Ku ɗauke idanunku daga kan mijina, daga nesa kuka ganshi ku sauya hanya, duk abin da kuke nema ni zaku faɗawa, koda abin cin gidan ne ya ƙare" Bara'at ta ce "Ok, amma kula da abincin gidan yana wajan Ummul" It's your problem, I just finished planning what I want" ta juya kan Halisa tana faɗin.. "Jeki breakfast ki saman a bedroom" tana faɗin hakan ta shige part ɗinta, Halisa ta bita da kallo a zuciyarta tana mmkin halin Zahrah. Miƙewa Bara'at tayi Halisa ma haka, tabi bayanta har zuwa sashen kitchen, ma'aikata ta gani mata da yawa ko wanne da abin da suke a kitchen ɗin. Da sauri Bara'at ta nufi wajan Ummul tana ce wa "Yau naga abin mamaki Ummul" kyakkyawar matashiyar matar wacce zata iya shekaru 50 zuwa sama ta kalli Bara'at ta ce. "Da akai me Ukkuti Bara'at?" Bara'at ta sauke numfashi ta ce "Wata mata na gani, mai iko da isa, wallahi na tsorata da yanayinta" Ummul tai murmushi tana ajjiye abin hannunta ta ce "Faɗimatul-zahrah bin Umar Farouk, matar Yaa Sheikh" a tare duk suka ce "Matar Yaa Sheikh?" Ummul ta kallesu ta ce "Na manta ban shaida muku bane, sai a haƙuri da juna ko?" Idanunta ya sauka akan Halisa wacce take dube dube duk abin da suke faɗa tana ji amma hirar bata gabanta, Ummul ta girgiza kai kawai, tana mai jin wani abu a ranta, yarinyar tana nan dai babu sauyi a tare da ita kamar yadda yake nuna mata ita a waya. Hawaye ya sakkowa Ummul ko yanzu ta mutu ta yi farin ciki, Aliyu ya samu gefen rayuwar shi kamar yadda yake faɗa mata a koda yaushe.
Bara'at ta ce "Ummul wace ita kuma wannan?" Ummul ta ce "Masu gidan ce" "Masu gidan kuma?" Cewar Suhaima Ummul ta ce "Ina nufin mai aikin Zahrah ce" ta kalli Halisa da kyau tana mai sakin murmushi ta ce "Sunanta Halisa, ƴar uwar Zahrah ce an bawa Yaa Sheikh riƙon ta amana ne, zatai amfani da sunan Halisa bin Sheikh Aliyu haydar Aliyu" Halisa ta ƙarasu wajan Ummul da sauri fuskarta ɗauke da kyakkyawan murmushi ta kama hannun Ummul ta ce "Laa kema kin sanni ashe, kuma kin san anyi...." Ummul tayi saurin rufe bakin nata tana cewa "Ba'a yin surutu a ɗakin girki, Bara'at akwai tray tana shirya breakfast ki bawa halisa" Bara'at ta ɗakko tray ta bawa Halisa ita kuma ta ce a kitchen ɗin zata zauna ta ci.
Bayan ta gama cin abincin Ummul ta miƙa mata farar madara mai ɗauke da zuma a ciki, batai musu ba ta amsa "Nima ina son na iya girki sosai, ina son yi wa Yaa Sheikh girki mai daɗi" Ummul tayi kamar bata ji zancen na Halisa ba, taci gaba dayin aikin gabanta tana son a akai gidan ciyarwa Yaa Sheikh abincin akan lokaci.
Zahrah na tsaye a gaban mirrow anci uwar kwalliya sai ƙarinin mai take, wayarta dake ringing ta ɗauka ganin sunan Deen ta ce "Uhm maye daman nasan babu mai kirana sai kai" daga cikin wayar ya ce "Ba wannan zaki tambaya ba, fara duba number" da sauri Zahrah ta duba number da mmkin take kallon number ta Saudiya ce,what does that means? Ya katse mata tunani da faɗin "Ki daina mamaki na riga ki sauka a Madina, ke kawai nake jira, don't make any mistakes nazo da maganin da ki ke buƙata, ina son ganinki" The surprise of his behavior prevented Zahrah from speaking. "Wallahi ki san yadda akai ki ka zo, ko ki ganni a gidanki" yana faɗin haka ya kashe wayar babu jimawa ya tura mata address ɗin inda yake, Zahrah ta dafa kai da sauri kuma ta juyawa zuwa ɗaya bedroom ɗin nata a nan ta samu Halisa tana shirya mata kaya a wardrobe, zama tayi ta ce "Ke kin fara menstrual?" Halisa ta ɗauka gyaran kayan take nufi kai tsaye ta ɗaga mata kai alamar eh. Juyawa tayi ta nufi part ɗin Yaa Sheikh.
Fitowar shi kenan daga Library room ɗinsa, ya zauna sanye da wata tattausar Jallabiya a jikinsa hannunsa cikin sumar kansa, cikin nutsuwa ya gyara zama akan duguwar kujerar da yake kai hannunsa riƙe da Cup yana shan green tea wanda Ummul ta kawo masa da kanta, speaking calmly ya ce da Khalil.
"Uhm surutu dai" Ta cikin waya Khalil ya saki dariya ya ce "Ya muke da matarka? Allah ya nuna mini ranar da zata barbabaɗa tana ɗauke da cikin Yaa Sheikh, koda yake kace baka son ta ai, auren dole akai maka" Yaa Sheikh yaja idanu ya rufe yana jinsa fresh sbd barcin da ya yi, cikin son dakatar da Khalil ya ce.
"Wallahi ba auren dole bane, ni na zaɓi matata It was completely my plan..." Katse wayar ya yi jin yana faɗin abin da mai shirya ba, tare da rufe kansa. Tsaye ya ganta a kansa babu sallama ya ɗauke kai kawai yana ci-gaba da danna waya tare da duba abubuwan da Umar-khan ya tura masa.
Ta zauna kusa da shi tana cewa "My Excellency baka fito ba har yanzu hope lafiya?" Kai kawai ya jinjina mata ba tare daya kalleta ba, ta haɗe jikinta da nashi tana cewa "Daman nace ina neman permission zamu shopping da ƴar fillo" har lokacin idanunsa yana kan waya bai ce komai ba. Ta shafi fuskar shi tare da cewa "Ba jimawa za mu yi ba kaji My Excellency" Jotter ya ɗauka da pen ya yi rubutu kana ya ajjiye mata a gefenta haka kurum yaji harshensa ya harɗe baya jin yin maganar. Ganin ƙoƙarin rungome shi take son yi ya ɗan miƙe tsaye, yasan cewa hakƙinta take nema, kuma yasan girma da ƙarfin hakƙi amma ya zai? He's not interested at all, baya son Ubangiji ya kama shi da wannan laifin.
Tabi bayan shi da kallo, tana ji a ranta dole ne ma tayi gaggawar aiwatar da burin dake ranta, Yaa Sheikh ya dawo hannunta sai yadda tai da shi tayi imani da Allah idan ya zo hannunta shi da wata ƴar mace kuma har abada, ba zai iya kallon kowa a matsayin mace ba dole sai ita, What is the solution? where will she start and what will she do now.
"You can go,
Ina buƙatar gyaran part,
With food" shi ne abin da ya rubuta mata a jikin Jotter ɗin, ta duba kenan dole mutum ɗaya ya tsaya, ita gasky ba wani gyaran ɗaki da zata iya, bayanta ciwo yake idan ta yi,kuma bata saba ba. Fita tayi ta samu Halisa a main parlour a kwance barci ya ɗauke ta tunda ta farka da asuba bata koma ba, gashi tai aiki ta gaji sosai bata san barcin ya ɗauketa bama sbd kallo take. Tana zuwa ta fisgo ƙafar Halisa zuwa ƙasa ta faɗo daga kan kujerar, a tsorace ta ce "Hande en boni me na yi Anti?" Zahrah ta ce "Ai hutu kika samu kenan? Ai babu ranar da zaki huta, zaki ta wahala har abada, kije ki gyara part ɗin Yaa Sheikh, ki kai masa lunch zan fita unguwa" kanta a ƙasa ta kasa cewa komai, tana zaune a parlourn Zahrah ta fito cikin wata duguwar riga ta yana mayafi hannunta riƙe da hand bag, kamar yadda Zahrah bata kulata ba itama bata kula ta ba. A compound ta ci karo da Umar-khan yana fitowa daga mota hannunsa riƙe da takarda. Ya ce "Evening" ta share sa, ta nufi wajan wani da alama shi ne drivern gidan.
Kai tsaye Umar-khan gidan ya shige ya samu Halisa zaune kanta a ƙasa tana gyangyaɗi ya ce "Matar Malam" tai saurin jan mayafin abayar ta ɗora a kanta tana yi masa murmushi ta ce "Ina yini?"
"Lafiya, barci a nan kuma? Yaa Sheikh ɗin yana ciki?" Ta ce "Ban sani ba" ya jinjina kai ya ce "Ok bari na duba, kije ki kwanta mana" ita dai ba tace komai ba ya nufi Part ɗin Yaa Sheikh barci yaci ƙarfinta, ta kwanta nan ƙasan carpet.
Umar-khan ya zauna bayan ya gaida Yaa Sheikh ya ce "Na cike komai na makarantar, gobe aka bada izinin ta fara zuwa, Mother ta ce komai cikin gaggawa take buƙata" ya miƙawa Yaa Sheikh file ɗin takardun Halisa bai amsa ba, sai tsare Umar ɗin da idanu da ya yi, Umar yana fahimtar shirun na Yaa Sheikh hakan ya sa ya ce.
"Al Aqeeq International School for Girls, Safiya Opens 7:30 ita ce makarantar" Yaa Sheikh ya jinjina kansa tare da miƙewa ya shigewa ɗaki. Wajan mintuna goma suka fito tare da Umar-khan wata Milk ɗin jallabiya ce a jikinsa, sai golden ɗin Alkyabba daya ɗora a kan jallabiyar, ya fito a babban malaminsa sai ƙamshin Roja yake bazawa, yana fitowa idanunsa ya sauka akan Halisa wacce ta cure waje guda tana barci, ya tsaya cak tare da kallon Umar-khan, Umar ya nufi ɓangaren Ummul babu jimawa suka dawo tare, Ummul ta kallesa ta ce "Malam za a fita ne?
Ba kaci abincin kirki ba?" Ya ɗan ɗauke kai zuwa hanyar fita yana faɗin. "Sanyi zai illata ta, a sauya mata waje" sai a lokacin Ummul ta lura da Halisa.
"Tom babu damuwa, Allah ya tsare" ta nufi wajan Halisa ta shiga tashinta tare da faɗin "Matar Malam, matar Malam" ta buɗe ido tana kallon Ummul ta ce "Maza ta shi ki koma ɗaki, a kwai sanyi zai kama jikin ki" ta buɗe ido sosai ta ce "Anti Zahrah ta dawo ne?" Ummul ta ce.
"Fita tayi ne? ta shi lokacin sallah ma ya yi ai muje ko" har part ɗin Halisa Ummul ta shiga, akan idanunta Halisa tai alwala kana tai Sallah. Ummul ta ce "ƙarfe biyar kizo ɗakina, zan nuna miki yadda ake cikakkiyar sallah, na fara karanta miki Alkur'ani, yanzu ki kwanta wajan ƙarfe 4:30 ki tashi ki wanka ki wanke baki, ki sauya komai na jikin ki, kinji ko?" Ta tura baki sosai ta ce "To wannan duk na mene Ummul" Ummul ta ce "zaki sani ne" ta fice daga ɗakin.
Yaa na fita kai tsaye Al Masjid an Nabawi ya nufa sbd wani karatu da yake dashi na musamman, kuma acan yake son yi Sallah ma, da kuma zaman tattaunawa da za su yi da mahukunta kula da Masallaci harami ana son naɗa Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu matsayin limamin masallacin Haramin wanda zai jagorancin sallar Taraweeh da Tahajjud, gaba ɗaya azumi saura wata guda ya rage a fara.
Tamkar uwa mahaifiyya haka Yaa Sheikh ya ɗauki Ummul yana ɗaukan minti goma yana magana da ita, tasan kusan komai nasa kuma tasan da yawa abin da Mother bata sani ba, tunda yafi rayuwa a Madina fiye da Nigeria. Sai bayan sallar issha Zahrah ta shigo a gajiye tana tafiya da ƙyar idanunta ya yi jaa, Halisa ta bita da idanu ganin yadda take tafiya kamar yaron da akaiwa shayi. Duk yadda Halisa tasu taga dawowar Yaa Sheikh bata gani ba, barci ya ɗauketa a Main parlour. Ƙarfe 12:30 ya shigo gidan shi kansa a gajiye yake sosai, ganinta a parlourn ya sanya ya tsaya yana binta da idanu, a hankali ya dubi lokaci sai kuma ya shige part ɗinsa.
Kiran sallar asuba ya farkar da ita, da mmki take bin makeken gadon da take kai da kallo, an rufe ta da wani haɗaɗɗan duvet mai ƙamshi ga laushi an kuma rage ƙarfin a.cn ɗakin, ita dai tasan a parlour ta kwanta waya kawota nan? Ko ita ta shigo da kanta.
Ta miƙe ta nufi toilet yadda Ummul ta koya mata haka tayi, tai wanka da ruwan zafi ta shafe jikinta da Vaseline Intensive Care Cocoa Glow Body Lotion.
Shiryawa cikin Abaya ta ɗora hijab a nutse take duba littafan da Ummul ta bata, Ubangiji ya bata fikirar hadda ce, da yawan lokaci ita abu a kanta yake zama, duk wani abu mai muhimmanci bata wasa da shi. Tana zaune taji saukar muryarsa a kunnanta yana data kabbarar sallah, shiru