Showing 39001 words to 42000 words out of 76655 words

Chapter 14 - Idan Bake Book 1 Complete Naima Sarauta

ƙoƙarin shi na son shiga part ɗin nasa ba tare da kowa ya gansa ba. Yaje corner kenan yaji ance.
"Yaa Sheikh" Khalil Ahmad Sarki ya faɗa yana murmushi hannun shi riƙe da gorar ruwa. "Yanzu nake shirin zuwa can gida muji yadda al'amarin bikin zai kama, nasan dai bikin Yaa Sheikh dole ba events ba D.j" Sheikh ya ware idanu da kyau yana bin Khalil da kallo. Khalil ya ce "na ƙosa naga matar Yaa Sheikh, nasan dole ta zama Malama kamar haka, Wow! Ga Yaa Sheikh ga Malama what a beautiful couples wlh dole love yaci ƙaniyar shi"
Yaa Sheikh ya ɗauke Idanunshi tare da kama hannun Khalil Ahmad sarki suka nufi hanyar ƙofa Khalil ya ce "Ya dai kamata ka fito tun ɗazo Mai martaba ya shigo" har lokacin Yaa Sheikh bai ce komai ba, yana zuwa bakin ƙofa ya tura Khalil waje tare da rufo ƙofar ya murɗa key. Khalil ya dinga dry daman ya lura zan can damun Yaa Sheikh yake yana mmkin yadda baya ƙaunar ai masa maganar mace?. Ya juya inda yabar su Abba Hakimi yana zuwa ya ce "Abba Hakimi ai ga ɗan naka can ya gudu part ɗin shi" Abba Hakimi ya ce "Za mu yi faɗa dakai yanzu Ibrahimul-khalil" Khalil ya yi murmushi ya ce "Nikam ina ruwar gida Momi ne?" Abba Hakimi ya ce "Tana can tana kayan buɗe baki na Aliyu, ƙosai da kunun gyaɗa"... "Ah! Lallai aikin lada take kenan" Mai martaba Ahmad Sarki ya kalli Ishaq-Hakim cikin kamala ya ce "kira Sheikh" da mutumtaka ya ce "To ranka ya daɗe Allah yaja kwana" kafin Ishaq-Hakim ya miƙe El-bashir wanda tun ɗazo yake hakimce saman kujera ya miƙe cikin nutsuwa hannu cikin aljihun suit ya nufi hanyar fita Abba Hakimi ya bisa da kallo yana nazartar yanayin yaron wanda baya son haɗa inuwa da Yaa Sheikh gaba ɗaya. "El-bashir kada kai nisa" cewar Mai martaba. He just nods his head and quickly leave the parlour. Bayan sallar magrib Yaa Sheikh na zaune a ƙawataccen parlournsa gabansa ɗauke da kayan buɗe baki, inibi yaci sai ƙosan da yake mai zafi ya yi laushi sosai sbd ƙwai da aka zuba cikin haɗin, hakan yasa ya ɗan saki jiki ci ƙosan da kunun gyaɗar. Yana jin gine da jikin kujera yana kallon Aljazzera yaji Sallamar Abba Hakimi shi ne kawai ke shigowa kai tsaye cikin part ɗin na shi, ya gyara zama sosai yana mai amsa sallamar ta Abba Hakimi. Bayan Abban ya zauna ya dubi Yaa Sheikh ya ce. "Aliyu haydar" Yaa Sheikh ya ɗaga kansa gaba ɗaya tare da kallon Abba Hakimi da yake faɗin "Jibi ɗaurin auren ka, ya ya zakai da uwar gidan naka kafin amaryar tazo?"
"Uuuu...uu... Uwar gggg gida? Am am amarya?" Ya faɗa yana kallon Abba alamar rashin fahimta. Abba Hakimi ya lura da gaske Yaa Sheikh bai gane ba ya ce "Yarinyar da aka ɗaura maka aure da ita a can Yola? Ka tuna?" Tab yakan manta abubuwa amma wannan abun ya zama abu na farko da ya yi saurin mantawa da shi. "Ina jinka,ina so muje can rugar tasu ne" magana zarar bunu cikin rashin sani Yaa Sheikh ya ce "Uhm bani da labarin hakan Abba, idan akwai auren ma zan kunce shi yanzu...


*Don Allah kada a fitar😒 littafin IDAN BA KE na kuɗi it's 500 via this account 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank. Via evidence 08119237616.


SARAUTAR MARUBUTA

Surry da mamakin kaifin bakin Halisa Danejo Rome ya gama cika mata zuciya,domin yarinyar ƙwarai ta shayar da ita mamaki, alamu sun nuna da gaske take dukkan maganganun da take. Surry ta ƙara gyara zama ta ce.
"Ok sai ki shirya biyanmu dukkan kuɗin da muka kashe, kama daga kuɗin aiki, magani, kuɗin gado, dana abincin da kuke ci?" Bakinta har kumfa yake wajan faɗin.
"Aradu babu inda zani ina tare da Dadata ku bakwa abu saboda Allah ne yanzu ba lada zaki samu ba?" Surry da ranta ya fara ɓaci da abin da Halisa keyi wanda yake gab da shirin ruguza mata nata tsarin na ganin ta kai Zahrah ƙasa ta ce "To ba mu yi niyyar samun ladan ba, idan ba zaki iya biyan kuɗin ba, dole kije ko na kira ƴan sanda" Halisa na ƙoƙarin magana Dada ta kalleta tare da watsa mata harara cikin sanyin murya ta ce.
"Ki manta da ita, tunda tai al'ƙawari dole taje duk da nima bana so, amma babu yadda za a yi ƙila hakan shi ne alkairi" murmushi ya bayyana saman fuskar Surry ta ce "Ai alkairi ne ma, zaki mamakin Halisa aikatau ɗin data samu mai kyau kuɗi sosai za a bata" Dada ta jinjina kai alamar gamsuwa.
Halisa banda tura baki gaba babu abin da take,duk abin ta bata iya musu ki jayayya da maganar Dada maganar ta kamar yankan wuƙa take. Surry ta miƙe tana duban Halisa ta ce "Ki tabbatar kin fara aiki da kayan nan kamar yadda na nuna miki?"

"To sannu Dada" Surry ta hangame baki cikin ranta al'amarin daɗi yake mata, Zahrah zata zauna da daidai ita wacce bata da tsoro sam cikin lamarin ta. "Ni kike haɗawa da Dadar taki?" Halisa ta ce "Eh Aradun Allah, naga ita kawai ta isa ta bani umarni na bi" Surry ta kasa cewa komai tayi waje abinta bayan ta ajjiye musu kuɗin mota na komawa can Rugar Rome.
Dada ta sauke numfashi tana kallon Danejo ta ce "Bakin ki babu linzami Danejo?" Ta tura baki ta ce "Ni ban san wani linzami ba, kin fi so aita cutarmu kina kallo, wai Dada waye Baffa ne?" Dada ta ɗaga kai da sauri kanta na sarawa zuciyarta na harbawa da ƙarfi najin tambayar na Danejo kamar daga sama. Halisa ta ƙara cewa "Dada waye Baffa mai yasa komai nasa sai a ƙwace mana shi?" Dada tai shiru har lokacin kallon Danejo take, irin kallon meke damunki ɗin nan? Me ya sa kuma kike tambayata wannan babbar maganar mai shirin tarwatsa zuciyata. "Do Allah Dada yau ɗaya ki faɗa mini waye Baffa a cikin Rugar Rome? Kuma....,"
Kyakkyawan marin da Dada ta saukewa Danejo shi ne ya taimaka wajan haɗiye sauran tarin maganganun da su ke maƙale a saman harshenta, cikin faɗa Dada ta ce.
"Hande en boni Danejo, banshe kada ki sake maganar Baffa? nashe ki barshu da Allah duk wanda suka ƙwace naggenku" Sai kuma ta fashe da kuka ganin yadda fuskar Danejo tai jajir saboda marin da tayi mata sai huci yarinya take alamar zuciyarta na kusa.
Dr ya turo ƙofar room ɗin hannunsa riƙe da file tare da kallon Danejo dake kuka ya ce "A'a yau mai akaiwa ƴar fillo ne?" Bakinta na rawa ta ce "Ba wanda suka kawo Dadata bace wai mijinta zai..." Kafin ta ƙarasa Dr ya ce "Ƴar fillo bari na fara duba Dadar taki yau dai kuka ya ƙare Dada ta samu lafiya" nan da nan ta washe bakinta tare da goge idon kukan kamar ba ita aka daka ba. Ta tsaya gefen Dada, Dr ya fara dubata cikin nutsuwa yana gamawa ya ce.
"Allahamdulillah, jiki ya samu, yanzu zan baku takardar sallama, tare da magani sai ku tafi gida" Shatu ta fara tsalle zasu gida. Cikin ƙaramin lokaci aka gama musu komai Sai da Dada tai Faɗa kafin Danejo ta ɗauki kayan da Surry ta bata suka nufi gida.

Zahrah na zaune ana gyara mata tulin gashin kanta sai kiran number Surry take taƙi shiga tai tsaki, tana ƙara danna wani kiran Surry ya shigo ta sauri ta ce "Heyy what's going on, see me here stop calling" ta faɗi Maganar tana shigowa cikin bedroom. Zahrah ta miƙe ta ce "Wai ina kika je? I have been trying to call your number amma yaƙi sai yanzu yake shiga, from where?" Surry ta zauna ta ce "Kin san kayan dinner ɗina bai zama ready ba, naje wajan tailor meye kike ta ihu ne?" Zahrah ta juya ta kalli Make up artist dake tsaye ta ce "Excuse us please" ta ce "Sure Maaah"
Zahrah ta kalli Surry da kyau ta ce "Surayyerh gabana faɗuwa yake, ina jin tsoron a gane ina da ciki Wallahi, ina mutuwarsa son Yaa Sheikh kamar rayuwata, kullum cikin fargabar ranar da zata zo wacce zai haɗa gangar jikinsa dana ƴar fillo, I'm scared Surry" wani shu'umin murmushi Surry tayi daman tasan tatsuniyar gizo ba zata shige ta ƙoƙi ba. "ko fasa tafiya da ƴar fillon zaki ne?" Zahrah ta waro idanu ta ce "Idan ban tafi da ita ba ya ya zan yi? Kina ganin ya ce idan bai saman matsayin mace ba zai sakeni, wlh ina son shi ba zan bari nayi wani abu wanda bai dace ba, dole zan tafi da ita, kuma dole ne ya kwanta da ita a matsayin ni, sai dai i have a plan ba zan bar ƴar fillo haka ba, dole nayi mata baƙin fenti" gaban Surry ya bada sauti sai ta share ta ce "Ya kamata kam, ƙila plan ɗinmu ɗaya me zaki yi mata ke?" Tai murmushi ta ce "sirri ne, muje lokacin na tafiya Finally Aliyuna zai zo na kansa, har imagine nayi hugging nasa nake" Surry ta ce "Uhm" kawai tana barin bedroom ɗin.

Misalin 12 hall event ɗin ya cika da ƴan mata da kuma samari D.j ke tashi kamar zai fasa hall ɗin, amarya Zahrah ta sha ado cikin wata pink ɗin gwon gaba ɗaya half ɗin ƙirjinta yana waje. Yaƙe kawai sbd rashin ƙarasuwar ango Yaa Sheikh da bai ba gashi friends ɗinta sai tambaya suke kowa ya damu da yaga wanne mai tausayin ne ya auri Zahrah?.
Sautin Algaita da suka ji a can wajan hall ɗin ya sanya Surry ta shi da sauri ta nufi wajan, manyan motoci ne guda wajan huɗu sabbi dal sai ƙyalli suke. Fuskar Surry ta sauya launin lokaci guda ta gane Yaa Sheikh ne da friends ɗinsa. Ta kasa motsawa wani abu na cakar zuciyarta, tana tsaye taga wasu matasan samari ko wanne da fararen kaya har ƙasa sun rufe musu ƙasa ko takalmin su ba a iya gani, motar ƙarshe wacce ta kasance da Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu wani saurayi ya buɗe ta, cikin nutsuwa ya fito shima yana sanye da fararen kaya mai Alkyabba rigar har ƙasa tana jan ƙasa. Ya ɗago kai a nutse suka haɗa idanu da Surry tayi saurin ɗauke idanunta bata taɓa ganin ƙwayar idanu mai tarwatsa zuciya irin ta Yaa Sheikh ba. Cikin sauri ya juya zuwa hall ɗin labari tuni ya isa kunnen Zahrah farin ciki ya lullube zuciyarta. Mc ya fara sanar da zuwan ango Zahrah ta tasu tunda Yaa Sheikh ya ganta sau ɗaya bai sake ganinta ba, domin ba ita yake nema ba a yanzu. A haka suka jera har yanzu wajan zaman da aka tanadar musu, lokacin zuwa lokaci idan Zahrah ta haɗa idanu da Yaa Sheikh sai ya sakar mata murmushi abin mamaki haƙura biyu kacal take gani a cikin bakin nasa, ta dai daure. Lokacin da akace su tasu zuwa filin hall ɗin idanunta ya sauka akan ƙafar shi da rigar ta zame, wani irin zaro ido tayi gabanta ya faɗi jikinta ya hau rawa sbd ganin kofato da tayi maimakon ƙafa, ta ɗago kai da sauri suna sake haɗa idanu ya buɗe mata bakinsa mai ɗauke da haƙura biyu. Wani ihu ta fasa a wajan tare da sulalewa babu numfashi. Surry da sauran friends sukai kan Zahrah ba tare da sun lura ba ango da abokan shi suka ɓace daga wajan.
Wanda ake tunanin shi ne Yaa Sheikh suna fita daga hall ɗin ya yi wani ihu tare da girgiza ya rikiɗe zuwa Aljani Prince Bilal. Sauran wanda akace abokan shi ne suma suka rikiɗe zuwa Aljanu.
Cikin wata murya mara daɗi Prince ya kalli Sandu ya ce "Na samu nasarar kashe babana, tsayin kwanaki ina neman matata Danejo amma babu ita, babana ya cuce ni ya sanya na manta kamarta yanzu ko na ganta ba zan san ita bace idan ba zoben dana bata na gani ba" Sandu ya ce "Ai zoben ya fara dacewa mu nema, tunda kace yana wajanta ko?" Prince bakinsa na fidda hayaƙi ya ce "Yana wajanta" hura iska daga cikin bakinsa sai ga wani photo ya bayyana na tambarin masarauta ya nuna musu tambarin ya ce "Duk inda kuka ga zobe mai tambarin nan a hannu wani to shi ne zoben hannun matata Danejo,da zoben da ita a kawo mini su, maza kuje" ɓat suka ɓace daga wajan, Prince ya juya ya kalli hall ɗin da ake partyn kamar zai koma ciki sai kuma ya ɓace ɓat shi ma.
Ƙarfe 2 na daren Asabar ɗin jirginsu Yaa Sheikh ya sauka a Yola International airport, kai tsaye motoci suka ɗakko su zuwa cikin wani haɗaɗɗan hotel, tawagar Abba Hakimi daban, ta Father daban, sai su Saif-wazir, Umar-khan, Ishaq-Hakim, Khalil Ahmad Sarki, El-bashir. Dashi kansa Mai martaba.
Har zuwa lokacin Yaa Sheikh ya kasa yarda wai ɗaurin auren shi aka zo, da yarinyar da ko sanin kamanninta bai ba, kuma bai damu daya sani ɗin ba. Washegari Lahadi aka ɗaura auren Zahrah Farouk da Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu akan sadaki dubu ɗari yadda Abba Hakimi ya bada. Ran Father ya ɓaci shi da ya so a bada dubu ɗari biyar ko miliyan guda.
Abba Hakimi na cikin mutane Saif-wazir ya zo kusa da shi murya ƙasa ya ce "Abba ga motar can ya kamata muje" Abba Hakimi ya miƙe tsaye hannunsa riƙe da sanda yabi bayan Saif-wazir zuwa cikin mota.
Kai tsaye Rugar Bello Saif-wazir ya nufa yana faɗin "Ina Yaa Lee zai kai wannan matar? Wallahi Abba kallon sani nake mata kuma na manta inda na taɓa ganinta" Abba Hakimi yai murmushi yanayin garin Yola na birge shi ya ce
"Saifuddeen ina rabaka da shiga sabgar da bana ka ba" Saif ya ce "da gaske Abba, tabbas na san fuskarta na manta ne kawai" ya faɗi haka yana parking daidai inda suka tsaya last time shi da Yaa Sheikh.
Abba Hakimi ya fito suka jera da Saif zuwa Rugar Bello, kamar yadda yasan Rugar haka ɗin ya sameta suka samu Arɗo dasu Giɗaɗo. Bayan duk sun zauna Saif ya ce "Nasan baka gane ni ba ko?" Arɗo yai jim alamar nazari can ya ce "Gaskiya bai shaidaka ba" Saif ya gyara zama ya ce "mun zo kwanaki ni da ɗan uwana,kuka ce wai ya yiwa wata ƴar fillo fyaɗe har kuka ɗaura masa aure da ita?" Arɗo ya ce "tuh! tuh! Masha Allah na gane shi yana ina? Ina kuma matar tashi nake?" Zuciyar Saif ta buga, ya kalli Abba Hakimi kafin ya kalli Arɗo ya ce.
"Wannan shi ne babana kuma baban Sheikh ɗin, daman yarinyar baya dawo gida bane? Ai mun kaita asitibi ta gudu" Arɗo ya girgiza kai ya ce "Ayyah shai dake ba a nan Rugar take ba, muma ganinta kawai mukai amma ba ƴar Rugar Bello bace" Abba Hakimi da Saif suka kalli juna kafin Abba Hakimi ya ce "Ikon Allah, yanzu bayan wannan rugar akwai wata ne" Arɗo ya kalli Labo, Labo ya girgiza masa kai, tunaninsu wani taimako za a bawa Fulani a fili Arɗo ya ce "Ai kaf Yola nan ce kawai Rugar Fulani, ba lallai idan ƴar garin bace" Abba Hakimi ya dinga kallon Arɗo yana mamakin wannan bankaura, daga kallon sarkin fawa sai miya tayi zaƙi? Kawai daga ganin Sheikh sai sukai masa bahaguwar fassara a tirɓayar tunaninsu mara kan gado.
Jiki a saɓule Abba Hakimi da Saif-wazir suka miƙe zuciyoyinsu babu daɗi. Bayan sun shiga mota Abba Hakimi ya sauke numfashi ya ce "Abin mamaki,ban taɓa jin wannan kwaɗon ba sai yau" Saif yai murmushi ya ce "Fulanin kenan Abba, yanzu ina zamu nemuwa Yaa Sheikh uwar gidan shi?" Abba Hakimi yana yin murmushi saboda wani tunani daya faɗo masa ya ce "Uwar gidan da baya so? Bari mu buga wasa waye zai nasara? Mai gidan? Ko Amaryar? Ko kuma Uwar gidan da ba a san inda take ba?" Saif ya ƙara sakin murmushi ya ce "Wannan shi ake kira da bikin zuwa ya samu babu zanin ɗaurawa, zan so naga yadda wasan ya zai fara ni ina team ƴar fillo"
A haka suka koma masaukinsu ƙarfe 2 daidai jirginsu zai ɗaga zuwa kano.
Amarya Zahrah na bedroom ɗinta Feedy ta shigo ta ce "Wow Zahrah kinga Yaa Sheikh wlh sai da zuciyata ta buga, na jima banga mutum mai kwarjinin shi ba" Zahrah ta miƙe ta ce "Da gaske Yaa Sheikh ya shigo?" Surry dake shigowa ta ce "Ya shige wai ai, Mimi ta ce ki sakko yanzu Kinga your husband and groom's friends" jiki na rawa Zahrah ta miƙe ta saka babban mayafi kamar ta Allah tana mai rufe jikinta sosai sbd cikin jikinta daya fara tasawa. Yana zaune saman wata haɗaɗɗiyar kujera, yaci dakakkiyar shadda gezner fara tas sai ɗaukan idanu take, ya ɗora Ash ɗin Alkyabba mai adon ruwan zuma, yaci rawani kamar kullum fuskarsa mai ɗauke da saje da tarin ƙasumma wacce tai tsayi sosai ta sauka har ƙasan haɓarsa sai ɗaukan ido take.
Khalil cikin sarki, Umar-khan, Ishaq-Hakim. Sai Oga El-bashir dake can gefe sbd faɗan Your highness gaba ɗaya sun saka kaya iri ɗaya,familyn kowa na ji da kansa wajan kyau.
Zahrah ana karairaya sbd ganin miji ɗaya tamkar da dubu acikin ƙawaye ta kere kowa aka ƙarasa kujerar da Yaa Sheikh yake, cikin ƙasa da murya ta ce.
"Your wlcm My Excellency" idan kujerar da yake kai ta motsa to Yaa Sheikh ya motsa gaba ɗaya hankalinsa baya kanta, barcin dake addabar shi yake son yaje ya rage wanda ya saba yinsa kullum.
Kamar wanda aka tsikara haka ya miƙe tare da barin parlourn, Surry tai Shu'umin murmushi, Zahrah kuma tabi bayan Yaa Sheikh kamar wata jela.
Halisa ce ke kuka kamar ranta zai fita itama Dada idanunta ya cika da hawaye amma bata son tai kuka sbd kada ta karya Jaririyar zuciyar da ƴarta Halisa. "Dada dan Allah kada ki barsu su tafi dani, bana son barinki" Surry dake riƙe da kayan Halisa a wata babbar jaka data zuba mata tai murmushi ta ce "Haba Halisa, ai za a iya kawo ki wajan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login