Showing 6001 words to 9000 words out of 9822 words
ne wai? Ku yi sauri ku fita don ga ƴan uwanku Mayu can tuni sun fara
leƙowa kamar uwanda suka san da shirin ku"
Ba su ɓata lokaci ba suka fita,direct gidan Mai Gari suka nufa.
Ba su wani sha wuya ba don dama ba ta ƙofa za su bi ba.
Rashin sa'ar Mai Gari shi ne da ya kwanta bakin ƙofar ɗaki,kamar wasu aikaki haka suka fara
kiciniyar fitar da kurwarsa daga cikin gangar jikinsa.
Sun yi nasarar fito da ita amma a wahalce saboda Mai Garin ma ba zaune yake ba,ya na da
bokayansa.
Tamkar wata sallah haka Mayun ƙauyen ke ƙetara katangu su na kame kurwar ƙananan
yara.Mutanen da ke zube kan titi kuwa sai Hamdullah.
Washegari
Bayan na tashi daga nanauyan bacci na yi miƙa.Wuyana kuwa tuni ya ƙage,fitsarin da ya cika
mini mara na fara tafiya na fitsare a kewaye sannan na fito tsakar gida na wanke jikina babu
sallah balle salati.
"Inna? Inna?" Na fara kiran sunanta shiru babu amsa, wannan ya saka na shiga ƙurya
ɗaki.Tasss abin da ya faru da ni daren jiya ya dawo mini a kai,kusa da akwatin na ƙarasa na a
tsorace na buɗe shi sai dai wayam babu komi.
Na ja wata ajiyar zuciya ina cewa "duk ta ƙare Inna ta canza ma Macijinta ma'ajiya,to mage da
ƙadangaren fa?" Na tambayi kaina ina tunani can kuma na baiwa kaina amsa "ƙila ƙadangaren
ya shige akwati ita kuma mage na jin yunwa ta biyo sa,haka nan ma ne!"
Ihun da na ji a ya karaɗe ƙauyenmu ya saka ni fitowa da gudu ina leƙawa,mutane na gani su na
gudu izuwa hanyar da za ta kai ka gidan Mai Gari .
Ni ma na bi bayansu ina cewa "wlh ba a bani labari"
Cirko-cirko mu ka yi a ƙofar gidan Mai Gari,bokaye ne wasu ƴan ƙauyenmu ne wasu kuma na
ƙauyukan maƙwabta.
Ɗaya daga cikinsu ne ya fara bayani,da wannan abun mai ƙara sauti "duk wanda ya san shi
maye ne mu na son ganinsa a ƙofar gidan Mai Gari in ba haka ba jikinsa zai faɗa
masu.Dayawan mutanen ƙauyen nan Mayu ne,jiya maitar ku ta motsa duk jama'ar da ku ka
kame kurwarsu ba su ishe ku ba shi ne har da ta Mai Gari .To ku sani kurwarsa ta fi ƙarfin ku
doli ku maido ta ,sannan bayan haka za mu shimfiɗa doka mai tsanani"
Wani abu da ya bani mamaki shi ne yadda wasu mutane ke ware kansu ,ciki kuwa har da
Salame ita ce kawai zan iya shaida wa ita ma don ta na abokiyar Inna .
A gaban idonmu aka fiddo Mai Gari wanda yake kwance bai cikin hayyacinsa.Ɗaya bayan ɗaya
haka suka yi ta ƙetara shi amma Mai Gari bai tashi ba.
Bokan nan ya sake magana ya ce "doli da sauran Mayun da suka ɓuya,a nan ƙauyen wa ku ke
zargin maye ne amma bai zo ba"
Daga inda nake tsaye na waro ido a zuci nace 'goggo Mairo!' na fara dudubawa ko zan
hangota,sai dai yadda mutane suka yi cunkoso ban ganin tarin Mayun dukkansu.
Ina tsaka da dube-dube mu ka haɗa ido da Salame,gabana ya faɗi ganin ta na nuno ni da
yatsanta.....
*Wanda suka shirya yin payment na MACIJIN CIKI za ku iya farawa 500 complete* WhatsApp
number +22795045822
[27/08 à 11:12] MRS SADAUKI í ½í²«: *MACIJIN CIKI..*í ¾íº±
```gajren labari```í ¾íº±
MRS SADAUKI í ½í²«✍️
SADAUKARWA ga S REZA
FCWA ☀️
*Page 5*
Da sauri na duƙe ta yadda Salame ba za ta ganni ba.Ina duƙu-duƙu zan tsere kawai na ji an
sarɓo hannuna,na zabura na miƙe tare da ƙoƙarin ƙwatar kaina sai dai inaaa tuni Asabe ta kai
ni tsakiyar fili.
Duk hankalin mutane ya dawo kanmu,tuni na fara zubar da hawa ita kuwa Salame sai faman
cewa take "ita ma wannan cikin ayarinmu take doli ta yi ƙetara"
Ina kuka ina ƙari aka saka ni doli na ƙetara Mai Gari,duk da na san ni ba mayya ba ce amma
banda zaɓi doli na yi.
Wani irin baƙin ciki ya turniƙe ni haɗi da tsanar Salame.Da ace na san za a ƙaƙaba mini sharrin
maita da wlh ba zan je ba .Ina komawa gida na tarar da Inna kwance ta na bacci,kan jikinta na
faɗa ina mai fashewa da matsanancin kuka.
"Lafiya? Mi aka yi?" Shi ne abin da Inna ta ce lokacin da ta tashi.
Baki na rawar kuka na ce "ba goggo Salame ba ce ta mini sharrin maita yanzu a ƙofar gidan
Mai Gari"
Inna ta bugi ƙirji "ke mi? Ke ce mayyar?" Ta faɗi haka ne tare da tashi tsaye,sai kuma ta ci gaba
da cewa"ina Salamen take? Ko ta na can har yanzu?" Kai na ɗaga mata.
Cikin sauri Inna ta doshi gidan Mai Gari har ƙura ke tashi sama kai kace Giwa ce .
Mutane tuni sun fara watsewa sakamakon Mai Gari da aka mayar cikin gida.Tun daga nesa
Salame ta tsinkayi Inna Asabe, wannan ya saka ta saurin ƙaraso wa ta tari gabanta.
"Ya ne kin ji zafi ne don na saka ƴarki ta yi ƙetara? Hhh! Na yi hakan ne don kowa ya san ke ma
mayya ce kawai raina masu hankali ki ke da sunan ke bokanya ce.In kuma ƙarya nake sai ki
ƙaryata ni ta hanyar fiddo macijin ki ya yi magana" Salame ke faɗar haka ta na wani riƙe ƙugu.
Inna Asabe ta ce "ko ma dai ni mayya ce ban taɓa lashe Ɗan kowa ba,kin ga kau alhamdullah
ke kuwa fa mutum nawa ki ka sanƙame ma kurwa?"
Salame ta ce "Asabe sanin kan ki ne ni na fi gaban ki raina mini hankali,shi jinin da ki ke tsotse
ma mutane mine ne naki ne?"
"Na je na tsotsa,ai duk muguntata ban kai ki ba tunda ni ba na kisa iyakata na sha jini ta yadda
mutum ba zai mutu ba ke kuma fa?"
Kafin ta kai ga bata amsa ne wannan bokan ya iso gare su "ya aka yi ne?"
Salame ta ce "ita ma wannan mayya ce"
Ya juya ya dubi Inna Asabe su na haɗa ido da ita ya ji wani shock ya ja shi,kallon tsaf ya yi ma
Inna a baɗini ita ɗin mayya ce sai dai a zahiri duk wanda ya san maye zai iya ƙaryata hakan
saboda ita ba ta yawo da kambun maitar ta .
"Ina kurwar Mai Gari wacce ki ka ɓoye?" Ita ce tambayar da ya yi ma Asabe , ita kuwa wani
murmushi ta yi sannan ta ce "in kai bokan gaskiya ne ka bincika da kan ka sai ka nemo inda na
ɓoyeta tunda har ka yarda ni mayyace" cike da gadara ta faɗi haka kuma sam babu tsoro a
tattare da ita. Boka ya buɗe baki zai yi magana kenan Inna Asabe ta yi amfani da ƙarfin tsafinta ta liƙe
muryarsa sai ga boka ya koma maganar kurame.
Salame ta waro ido saboda ta yi mamaki sosai ashe duk inda ta ajiye Asabe ta wuce nan,da
gudu ta bar gun.
Inna Asabe ta dube shi cikin ido ta na cewa "don duk Mayun Ƙauyen nan sun ji tsoron ka shi ne
ka ke tunanin ni Asabe haka nake kamar farar kura? Mtsw " ta ja tsuki tare da yin tafiyarta.
Can ɓangaren Mairo da Bintoto kuwa su na can wani ƙauye.
Cikin gidan tururuwa suka ɓoye kurwar Mai Gari sannan suka tsaya gadinta ,su na jiran
mutuwar mai Gari.
Daga cikin ramen su na iya jiyo huci na raɗaɗin azabar da yake ji.
"Za ka ci ƙwal ubanka ne tunda ka shigo gonarmu,wato ka shirya korar duk wani maye da ke
ƙauyen ka? To za mu gani in daga can lahira za ka aiwatar da nufin naka" Mairo ke faɗa ta na
hararen gidan tururuwar.
Bintoto ta ce "yawuna sai tsinkewa suke na matsu ya mutu ,mu sha daɗin mu"
"Hhh! Ni fa saboda ƙarfin tsafinsa ne zai sa na ci naman Mai Gari in ba haka ba miye na ci a
jikinsa"
"Ya ne za mu baiwa Salame ko ya ?" Bintoto ta tambaya .
Mairo ta harareta ta ce "tunda har da ita mu ka sha baƙar wahalar ba"
"Mairo mai Gari ya bar motsi,fiddo mana kurwar"
Mairo ta kai bakinta kusa da hudar ramen ta fara karanto wasu launukan tsafi sai ga kurwar Mai
Gari ta fito.
A fannin maita ko tsafi,ana iya raba gadon mutum na muguntarsa.Haka su Mairo suka raba na
Mai Gari su biyu ko wace ta haɗiye nan take suka ji sun ƙara ƙarfi a duniyar mugaye,bayan sun
gama suka dawo ƙauyen su direct gidan Inna Asabe suka nufa.
Ina zaune kan tabarma ina shan fura abokan Innata suka shigo ko wace ido ya yi mata ja kamar
an saka barkono.
"Ke ina uwarki?" Goggo Mairo ta tambaye ni,ban bata amsa ba na ci gaba da shan furata don ni
idona ma na baƙin cikin ganinta.
Sai goggo Bintoto ta ce "Tuwalle ina Innar ki?"
"Ta fita tun ɗazu" na bata amsa.
"Mu tsaya jiranta har ta dawo,bari na shiga banɗaki na yi fitsari" cewar Bintoto ta na mai ɗaukar
buta.
Sam ban ga tawowarta ba kawai dai na ga wata innuwa ta rufe ni,na ɗago kai mu ka haɗa ido
da ita wani koren haske ya fito daga idonta ya shiga nawa.
Ban taɓa sanin akwai raɗaɗi da azaba ba a duniya sai yanzu ,sam na kasa yin ihu
kuma.Tsawon minti ɗaya kafin ta sake ni,na mirza idona ina mai sake kallonta da sauri na
sunkuyar da kai saboda yadda idonta ke da mugun rikitarwa.
Inna ce ta shigo ta na cewa "yaushe ku ka dawo?" Bintoto kar ki cika mini salanga da kashi"
Na ɗaga kai na kalli Inna ina mamakin ta ya aka yi ta san goggo Bintoto na cikin banɗaki.
"Daga ina ki ke?" Mairo ta tambayi Inna .
"Wajen Salame,don iskanci Tuwalle ta saka ta yi ƙetara don sharri"
"Hum! Ina dalilin wannan hali naki,yarinya ƙarama na gama ki da abokan ki? Wlh duk ranar da
ta kawo ƙarata wajen ki sai na cire mata wancan shegen bakin nata" Mairo ke faɗa cikin fushi.
Tuni wani tsoro ya kama ni,sai na ga kamar ta karanci abin da ke zuciyata.Don ina da niyyar
shaida ma Inna abin da ta yi mini ga idona amma yanzu kam na fasa wanda ban san cewa
babban kuskure na aikata ba.
Hirar su suka shiga yi wacce sam ban fahimta har suka yi tafiyarsu.
Mutuwar Mai Gari ta sauka a maricen yau,tsabar murna ya saka Inna taka rawa ta na cewa
"shikenan yanzu kowa ya samu inci" sai kuma ta shiga ɗaki ta fito ta na mai miƙa mini wani
tandun kwalli "ungo je ki gidan Mairo ki bata wannan"
Tandun kwalli ne a rufe amma ban san ta ya ya aka yi har nake ganin abin da ke ciki ba tare da
an buɗa ba.
Na karɓa,duk da ina jin tsoron Mairo haka na samu kaina da zumuɗin zuwa a can ƙasan raina
kuwa na sha alwashin sai na bi didiginta na gano in mayya ce ko kuwa.
Ina tafe ina kallon baƙin hayaƙin da ke ta yawo cikin tandun kwalli har na kawo gidan Mairo.Yau
dai kam a buɗe yake,ina shiga na ci karo da magenta sai dai wannan ba wacce ta yage ni ba
ce.
Cak na tsaya ina tunanin inda na taɓa ganinta,sai na tuna cikin akwati.
Magen na ƙoƙarin shigewa ɗaki na yi caraf da ƙafarta ta baya,duk yadda na ji ta da nauyi bai
hana ni janta giiiii na cilla a cikin tsari wanda dabbobi ke sha.
Sarai na san da mage ba ta son ruwa shi yasa na yi hakan.Dariya na fara har da ƙyarƙyatawa
ganin yadda magen ke ƙoƙarin fitowa,tsari na ta shigar mata hanci da baki ta na yin kamar za ta
mutu.
Can ta samu ta fito,da gudu ta shige ɗaki ruwa na yi mata tsiyaya.
"Shegiya ke ce na gani ki ka firgita ni a ranar nan ,ni ma na rama" na faɗa a fili,daga can cikin
ɗaki na ji muryar Mairo a shaƙe ta na cewa "Tuwalle shigo mana" ba tare da wani tunani ba na
shiga.
A zaune na tarar da ita kan kujera daga ita sai ɗaurin ƙirji,kanta babu ɗan kwali duk gashinta ya
yi facacaaa da dusa.Sam ban kawo a raina ba ita ce magen sai da ta tsure ni da ido sosai na
hangi baƙin kallon nata,sai kuma na hangi ƙatoton bindin mage baƙi ƙirin sai wani juya shi take.
A siffar mutum take amma kuma bindi ne da ita,muƙut na haɗiye yawu yayin da cikina ya ɗuru
ruwa.
Mairo ta yi wani makirin murmushi ta ce "matso ki bani saƙon"
Jikina na rawa na ƙarasa na miƙa mata,a gabana ta buɗe tandun wannan baƙin hayaƙin ya fita
daga ciki ya shige bakinta.
Ido ta lumshe ta na mai cewa " za ki iya tafiya tunda yanzu kin tabbatar ni mayya ce"
Tsoron da ya shige ni ne ya ɗan ragu har na samu damar yi mata tambaya "to amma mi ya
hana ki zuwa gidan Mai Gari?"
Ta bani amsa da "abin da ya hana Asabe"
"Ita Inna ai ba mayya ba ce" na faɗa cikin jin haushi.
"In ki je ki yi mata tambayar za ta baki amsa"
Na ɗan harareta sannan na fito.Ina zuwa a gida na yi wa Inna tambayar,kallona kawai ta yi ba ta
ce komi ba.
"Kenan da gaske ke mayya ce? Hum! Inna shi yasa ke da su goggo Mairo ku ka ƙi zuwa gidan
Mai Gari"
"Tuwalleeee!" Ta daka mini tsawa,maimakon na ji tsoro sai dai akasin shi.
"Inna ki faɗa mini gaskiya,ni ko mayya ce ke ina sonki haka nan "
"Ita Mairon ta saka ki yi mini tambayoyin? Hum! Za mu haɗu ai"
Daga nan ba ta sake cewa komi ba ta ci gaba da aikinta,ni kuwa fushi na yi don ko abincin dare
ƙin ci na yi.
Tamkar yadda ake juya majaujawa haka na fara jin cikina na juyawa,da farko na zata ko yunwa
ce sai dai yadda cikina yake ƙaba ya na ƙara zama ƙatoto ya saka ni ƙwala ihu.
Inna kamar jira take ta tashi,fitila ta haska mini ba ta kai ga tambayata ba na fara cewa "wayyo
cikina Inna zan mutu"
"Innalillahi ! Mi Mairo ta baki ki ka ci?"ita ce tambayar da Inna ta yi mini .
Cikin kuka nace "komi!"
"Kamar ya komi? Ki tuna dai" Inna ta sake faɗa ta na shafar ƙaton cikina.Tsabar azaba ya saka
na kasa yin magana sai kuka,Inna ta sungume ni cikin tsohon daren nan mu ka fita zuwa gidan
Mairo.
Abun mamaki can mu ka tarar da sauran wato Bintoto da Salame.Inna ta shimfiɗar da ni
tsakiyar ɗaki ta na mai cewa "haka za ki yi mini? Na yi miki dare ke kuma ki saka ni rana?
Bintoto har da ke?" A yadda Inna ke yin magana za ka iya jin rauninta.
Mairo ta ƙyalƙyace da dariya ta na cewa "hhhhh! Ai wlh Asabe ban taɓa sanin ba ki da wayo ba
sai yau,tunda har ki ka iya ara mini ƙarfin ikon ki."
Inna ta ce "na ji amma don Allah ki saki Tuwallena ko ma mi za ki yi ki tsaya iya ni"
Mairo ta ce "kin fi kowa sani ban taɓa ɗauka ba na saki,kuma wlh ba zan yi kunya biyu ba"
Salame ta ce "Yauwa ƙawata kar ki saketa ai haka ta yi ta gara ni tare da yi mini baƙar azaba ita
ga mai ɗiya"
Bintoto kuwa cewa ta yi "a'a kar ku ce haka,kar ku manta Asabe kullum ta na ƙoƙarinta a kan
mu"
"Yauwa Bintoto don Allah ki saka baki ta ƙyale Tuwallena"Inna ta faɗa cikin raunin murya.
Ihu na kuma saki ina cewa "Inna shikenan za su kashe ni wayyo cikina zai fashe"
Ban ida rufe bakina ba Inna ta yi wani furuci nan take ta rikiɗe ta zama ƙatoton MACIJI .....
Littafin kuɗi ne katin MTN na 500 za ki biya domin ci gaba complete,wacce ta shirya ta yi mini
magana ta WhatsApp +22795045822
[27/08 à 11:13] MRS SADAUKI í ½í²«: *MACIJIN CIKI..*í ¾íº±
```gajren labari```í ¾íº±
MRS SADAUKI í ½í²«✍️
SADAUKARWA ga S REZA
FCWA ☀️
*Last free page 6*
Zamantowar Inna MACIJI ba shi ya fi ban tsoro ba,a'a yadda ta rinƙa kumbura ta ƙoto ta ƙara
zama gibjejiya kamar icce don har sai da ta kusa taɓo rufin ɗakin.
Duk tsoro ya bayyana a fuskokin ƙawayenta,washeshen bakinta ta buɗe ta na mai zuro shi ta
ɗauke Salame ta fara taunawa kai kace mai cin abinci.
A gaban idona Inna uwa mahaifiyata ta haɗiye mutum.Cikin tsoro goggo Mairo ta buɗe bakinta
ta zaro wani abu sannan ta nufo ni,ta na shafar cikina duk komi ya koma normal sai na ji duk
azabar ta tsaya haka kumburin cikina ya sace.
"Haaam ! " Ta yi wata hargowa ta na mai juyowa saitin mu ni da goggo Mairo.Yadda ta ƙara
wangale ƙaton bakin macijin nan mai ɗauke da zaƙa-zaƙan haƙora ya saka hantar cikina
kaɗawa.Ta sunkuyo kanta yawu na mata zuba,ɗan guntun kallabin Salame ka na iya hango shi
laƙe da haurenta.
Gutsur! Ta gindile kan goggo Mairo da haƙoranta,gangar jikin ta faɗi ƙasa yayin da kuma kan ke
cikin bakinta.Kaina tuni ya fara juya,kafin wani lokaci numfashina ya yi mini