Showing 9001 words to 9822 words out of 9822 words
ƙaranci ban sake
sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na tsince ni kan shimfiɗata.
Duk abin da ya faru ne ya dawo mini akai,sai dai kash ƙwaƙwalwata ta kasa ɗauka balle har
zuciyata ta gamsar da hankalina kawai sai nace mafarki ne nake .
Sai dai ba aje ko ina ba na gaskata lamari.Bayan na dawo daga banɗaki na shiga ƙurya ɗaki da
zumar neman Inna ,ban kai ga buɗa baki na kira sunanta ba na yi tuntuɓe da wutsiyar MACIJI
gudar ƙatuwa har sai da na yi tangal-tangal zan faɗuwa ƙasa .
Da taimakon bindin na faɗa kan gangar jikinsa,a hankali kuma ya warware bindinsa.
Zuciyata sai faman bugawa take,duk a tunanina macijin Inna ne sai dai ashe abun ya wuce
haka.
"Tuwallena ni ce Innar ki,kar ki ji tsorona saboda ke na gwammaci na zama macijiya akan na
bari a cutar da ke" muryar Innata ce amma baki da gangar jiki na MACIJI ne da ita.
Ta na maganar ne ta na wani shafar fuskata da bindi,ban san mi yasa na ji duk tsorona ya
gushe ba.Ƙila sanin ita ɗin garkuwata ce ba za ta bari wani ya cutar da ni ba balle kuma ita ta yi
wannan gangancin duk da zamantowar ta macijiya.
Na rungumeta ina kuka na ce "Inna don mi yasa ki ka zama mayya? Mi ya sa? "
"Ba son raina ba ne Tuwalle,ni ma gada na yi gun mahaiyata.Je ki yi mana girki na fara jin
yunwa"
Na ɗan ɗagata ina kallon idonta da ba su da kyawun gani,na ce "Inna shikenan yanzu ba za ki
sake komawa mutum ba?"
"Zan koma sai lokaci ya ya yi" ta bani amsa.
"Yaushe kenan?" Na sake tambayarta.
"Sai in kin girma sosai a lokacin zan rikiɗe na dawo mutum saboda ƙarfin ikon ki"
Ba tare da na fahimci mi take nufi ba na tashi na fito waje na ɗora mana ɗumame.
Bayan na gama na zuba shi a cikin kwano na shiga ƙurya ɗaki.Da hannuna na rinƙa baiwa Inna
macijiya abinci a baki har ta ƙoshi.
Mu na nan zaune sai ga Bintoto,ba tare da wata doguwar hira ba ta ce "Asabe ya kamata mu
bar ƙauyen nan kafin a yi mana tonon silili,tuni an ɗora sabon Mai Gari kuma tsanani ne da shi"
Na kalli goggo Bintoto a zuci nace 'oh ! Ita Inna ba ta haɗiye ta ba kenan?'
"Ni ma na yi tunanin haka amma kin san ba zan tafi a haka ina macijiya ba,doli sai an samu
wajen da za a ɓoye ni "Inna ta faɗa ta na wani kaɗa taɓaɓen kanta.
Goggo Bintoto ta fiddo wani ɗan kwagiri irin wanda tsofi ke ɗaurawa a ƙugu don zuba kuɗi,sai
dai wannan shi azargagi ne da shi.
"Ga inda za ki shiga nan" ta nuna mata,Inna ta ce "to babu matsala gobe sai mu tafi, yau za mu
haɗa duk komi namu"
"To gwara ku fara tun yanzu don garin hadari ne da shi" cewar goggo Bintoto ta na mai yin
tafiyarta.
Bayan fitar ta ne Inna ta faɗa mini abubuwan da za mu tafi da su,ni kuwa duk na haɗe su wuri
guda.
Ruwan sama suka fara zuba kamar ga bakin ƙwarya an ɗauki dogon lokaci bisanin a tsagaita.
Kamar mai jira haka na fito tsakar gida tare da nufar hanyar da za ta kai ni ƙofar gida.
Wani kuka ne ya ja hankalina,na fara waige-waige har idona ya sauka wurin da na taɓa ganin
Inna duƙe ta na rufe wani abu.
Daga nesa a inda nake tsaye ina iya hango yadda can ƙarƙashin ƙasa yadda wani abu ke ta
bada kalolin wuta sai haske yake.
Ƙafafuwana har ƙaiƙayi suke wajen saurin isa,na duƙa tare da sa hannu na fara tonon ƙasa
wacce ta jiƙa ta yi taushi.Ina tono har na isa ga wani ɓawan ƙwai fari sol wanda ya ɗan yi huda
ƙadan.
Ko kafin na ida cirosa wani ɗan jaririn MACIJI ya fara fito da kansa,ba tare da jin tsoro ba na yi
masa tarba mai kyau kan tafin hannuna.
Ɗan mitsitsi ne sosai,jikinsa kori da baƙi ne .A hankali nake ware idona ina sake kallon shi,na
shagala sosai sam ban farga ba har ya huda jijiyayar hannuna.
A gaban idona macijin nan yake kurɗa jijiyar hannuna har ya shige duka,ruf hudar da ya shiga
ta rufe sai dai a saman fatata ina iya hango ƙyallinsa ,ina kuma jin yadda yake tafiya cikin jikina.
Wani abu na fara jin ya na mamaye ni kamar wacce ta sha ƙwaya,idona kuwa har wani yaji na ji
su na yi.Kafin wani lokaci hannuna ɗaya ya rine ya yi baƙi haɗi da ɗaraba-ɗaraba kamar jikin
MACIJI .
Duk mai son complete sai ta biya 500 katin MTN ko transfer,wacce ta shirya sai ta yi mini
magana ta WhatsApp +22795045822