Showing 9001 words to 12000 words out of 21490 words
Chapter 4 - Mutuware Gidan Hawa Complete Book Mrs Sadauki
Momah ” na amsa.
“Ayodele ke ɗin ta daban ce,dole ki dinga taka tsantsan duk da ina da yaƙinin ababen bauta ba
su taɓa bari a cutar da ke ba,domin su na tare da ke a ko ina amma ki dinga kulawa ba ko ina
ba ne ake zuwa” Momah ta sake faɗa ta na mai kallona cikin ido.Kai kawai na jinjina mata
bisanin na wuce ɗaki,kaya na cire na yi ɗaurin ƙirji na je na yi wanka . Ina tsaka da cin dambun shinkafa da Moma ta girka kiran A'ishah ya shigo,gabana sai da ya
faɗi a take duk abin da ya faru da ni ya dawo kaina,hakan yasa har kiran ya katse ban ɗauka ba
. Lokacin da na biyu ya shigo kuma a daidai nan maƙociyarmu Asabe ta shigo ta na rangaɗa
sallama.
Na amsa mu na gaisa wa,Momah ma ta fito .Godiya ta zo ta na ta faɗa mana yadda lamarin ya
kasance da Zeinab nan muka yi ta hira kan Mayu da illolinsu.Sai bayan ta fita ne na duba
wayata ,har zan maida kira kuma sai na fasa na tsunduma zancen zuci ‘tabbas da walakin goro
cikin miya! In babu rame mi ya kawo zancen shi? Mine ne na biyana har toilet? Babu shakka
akwai abin da ya saka a abincinmu,to shi kuma restaurant ɗin da ya zama kamar ɓatan wata?
Hummm! Zan nutsu,na ankare komai sai na gano gaskiyar lamarin’
Abincin ma sai ya fita raina,tashi na yi na fiddo fararen rigunan da nake saka wa na likitanci na
wanke su tasss bisanin na kwanta ina yin bacci don jiya mun sha aiki sosai.
Tamkar a mafarki na ga wasu mutane masu fararen kaya sun zagaye ni,idona sun min nauyin
da ba zan iya ware su duka ba amma tabbas ina iya ganin abin da ke gabana.Kaina na ji an
fara shafa wa yayin da sauran kuma ke yin hira cikin wani Yare wanda in ba zan manta ba shi
ne na taɓa ji Momah ta yi.Cikin wannan yanayi na lula duniyar mafarki,yau ma kamar kullum
sanye yake cikin kayan ƴaƴan sarakuna ya saka kayan yaƙi,daidai ƙugunsa kubai ne mai ɗauke
da takobinsa.Gefensa kuma masu tsaron lafiyarsa ne a tsaye cikin shirin yaƙi akan duk wanda
ya kawo masu farmaki.Murmushi yake sakar min ya na kallona daga nesa, cikin izzar da ban
san yaushe na same ta ba na fara takawa izuwa inda yake muna facing juna.Da sauri na
lumshe ido sa'ilin da ya tsaka ɗan yatsansa manuni ya dangwala min jininsa a goshi a nan take
wani sanyi ya luluɓe ni yayin da kuma nake jin shigar wasu lamurran da ba zan iya fassara su
ba su na ratsa ɓargo da tsokar jikina.
“Ayodele? Ayo....” a kasalance na buɗe idona na zube su kan Momah wacce ke faman jijigata
da kiran sunana.
Ta sakiya wata nauyayyar ajiyar zuciya bisanin ta ce “daga yau kar na sake ganin kin yi bacci a
daidai lokacin da tartatsin rana ke tsakiya ban so”
Dakyar na iya buɗa baki na ce “don me?”
“Lokacin babu wata albarka a cikinsa ,bacci ya haramta ga al'ummar Victoria Falls ”
Da mugun sauri na ce “su waye kuma al'ummar Victoria Falls ? A wacce ƙasa ce? Mine ne haɗi
na da su?”
Da mamakina sai na ga Momah ta rikice,abin da na lura ma kamar suɓutar baki ce ta yi.“Ki na ji
Ayodele mu bar wannan maganar,ke dai kawai ki kiyaye abin da na ce.Am...na ce ... Ki taso na
koyar da ke saƙar hannu” duk a rikice take,ni kuwa na zuba mata ido.Lokacin baya babu yadda
ban yi da ita kan takoya min saƙar hannu ba ta ƙiya,amma yau sai gashi yau take son koyar da
ni.
Fuskata na wanke,na gyara zama ta fara nuna min yadda ake fara aza zaren farko na
Foundation ɗin sannan a fara zarga wa gabanin ta miƙo min ƙarafan saƙar.
Abu guda ya ban mamaki yadda na iya tafiya da takun saƙar kamar wacce tun can farko na
taɓa koyon ta ,Momah na daga gefe ta ƙure ni da ido .Ko shakka babu ta zurfa sosai cikin
tunani duba da yadda na yi mata magana sam ba ta ji ba.Ganin haka yasa na je na fara cika
bokiti da ruwa,“oh! Har kin gaji?” na tsinkayo muryarta, murmushi kawai na sakar mata bisanin
na ɗauki bokitin ruwan.
Ina kai soso fuskata na ji wani irin uban raɗaɗi tamkar na zuba barkono ,da sauri na wanke na
fito direct ɗaki na shiga na ɗauki madubi.Ɗigon ja na gani a goshina mai ɗauke da wani ƙaramin
tauraro.Shiru na yi ina daɗa kallonsa,“Momah???” na ƙwala kiranta ,ta na shigo wa na ce,
“Dubi wannan abun mine ne? Zafi yake min”
Cike da kula wa ta ce min “ki jira har ranar da kika cika shekaru ashirin da biyu duk zan yi miki
bayani”
Na turo baki gaba na ce “ni dai ki faɗa min yanzu”
“Ke ban fa son sakarci ,wai haihuwata ma kika yi da za ki tsare ni da tambayoyi ? To ban sani
ba” ta na gama faɗa ta shige ƙurya ɗaki.
Yadda na matsa wa kaina sanin mine ne har Allah yasa na tuna da mafarkin da na yi,wato na
masoyin ɓoye.Har ban san lokacin da na saki murmushi ba,cike da nishaɗi na shirya cikin riga
da wando na fita ƙofar gida.
FATIMAH
Tun lokacin da ta ci abincin da Mansur ya saya masu a restaurant take jin wani mugun sauyi a
jikinta.Tamkar wacce ba da lafiya haka ta samu wuri ta kwanta,wani irin tsoro da shakkar
saurayin ƙawarta take ji ba tare da ta san dalili ba.Ummarta har tambayarta ta yi abin da ke
damunta amma ta ce babu komai.Ta rufe kanta cikin ɗaki kawai ,domin wani irin son kaɗaici ne
ya zo mata.Wayarta ta ɗauka ta tura ma Nasir saurayin ta text ,duk da ba ta son shi haka ta ji
ra'ayin kula shi.Da wannan ta ɗan rage faɗuwar gaban da take ji,har ta samu ta ɗan saki jiki.
A can ɓangaren A'ishah kuwa haka ta kira Mansur ta shaida masa ta yi ta kiran Ayodele amma
ba ta ɗauka ba.Har ƙasan ransa ya ji mugun daɗi don dama ya na tabbacin fatalen da ke kan
hanya kawai sun isa su kasheta da tsoro.
Washegari
A asibiti duk muka haɗu,ko kaɗan ban yi ma A'ishah maganar kiranta da ban ɗauka ba hasali
ma ban so wata doguwar hira ta haɗa mu.
Ina ƙoƙarin saka wa wata mata tiyon fitsari A'ishah ta matso kusa da ni,ta ce “jiya Mansur na
tambayar ki” sai na yi shiru kamar ban ji ta ba,ta sake maimaita min sai na ce “ki jira har mu fita
mana,ki duba sauran patients ko akwai wanda ba a yi masa aiki ba ” na yi tunanin na rabu da
ita kenan amma mu na fito wa ta sake tara ta da zancen “jiya sai da ya tambaye ni ,sam bai ji
daɗi da bai baki kuɗin taxi ba”
Na ce “ba komai ana tare,ki tuna min don Allah zan baki kuɗin anko sai ki sayo min”
“Ok to babu matsala,amma Mansur ya ce min abokansa sun shirya party kin ga ya zama dole a
sake fitar da wata ankon ”
“ A'ishah yanzu fa babu kuɗi ba lallai kowa ya iya sayen har anko biyu ba”
“Zan yi masa magana to,ƙila su abokan su saya maku”
“Hum!” kawai na yi,bisanin na ce “wai ita Fatimah ba za ta zo ta kama aiki ba ne?”
“Kanta ke ciwo ta na can baya wurin ƙofar emergency ”
Da sauri na kewaya ta bayan na sameta a kwance kamar ba likita ba.“Fatimah?” na kira
sunanta,ta buɗe ido dakyar ta dube ni ai ban san lokacin da na yi zaune ba na ɗauko kanta na
ɗora a cinyata.
“Mine ne taƙamaimai abin da ke damun ki?”
Murya na ɗan sarƙe wa ta ce “ A'ishah ce sai hirar mijin da za ta aura take yi min,ni kuma
wallahi mugun tsoronsa nake ji.Ban so ko kaɗan ana kiran sunansa” shiru na yi na ɗan wani
lokaci bisanin na ce “yaushe kika fara jin tsoron nasa?”
“Jiya”
“Bayan kun dawo daga restaurant ko kuma kafin mu je?”
“Bayan mun dawo” ta ban amsa ta na wani irin tari,na lumshe ido ‘ tabbas zargina ya zama
gaskiya.Saurayin A'ishah ba mutumen kirki ba ne,to amma wace iri ce ɓoyayyar fuskarsa? Ban
sani ba!’ na faɗa a zuci tare kuma da tunanin mafita.
Can dubara ta faɗo min na ce “Fatimah a Addinin ku ba a sanar da ku yadda ake karye asiri
ba?”
“Mi ya kawo zancen Addini kuma?” cewar Fatimah don na santa sarai,ba tun yau take guje duk
hirar da za ta kawo banbancin Addinai ba.
“Ke dai ki ban amsa” na sake faɗa,ta ce “eh an sanar da mu mana,gaba ɗaya Alkur'ani waraka
ce akan dukkan ko wace matsala”
Ta na gama faɗa min na ce “ok jira ni” sai na sauke kanta kamar yadda na tarar da shi tun farko
bisanin na koma can ciki.Direct office ɗin Dr Haleema na nufa,mace ce mai matsayi babba
sannan ma'abociyar Addini ga ta kuma da sauƙin kai ba ta hantarar na ƙasa da ita.
A zaune na tarar da ita ta na duba wasu takardu ,da murmushi ta dube ni ta na mai cewa
“Ayodele dama ke ce ke buga ƙofa? To zauna”
Na zauna tare da gaisheta bayan ta amsa na ce “Dr don Allah a Musulunce wane abu ne ina
nufin addu'a ko kuma magani wanda yake saurin kare asirin da mutum ya ci”
Cike da kulawa ta ce “sanamaki! Ganye ne mai matuƙar amfani wurin kare tasirin asirin da
mutum ya ci ,in an tafasa shi sai a yi addu'a cikinsa a sha”
“A ina zan same shi don Allah?”
“Wurin masu sayar da ganye ko kuma Islamique center,mike damun ki Ayodele?”
“Babu komai Dr na gode,jira ina dawo wa”
Ina fito wa daga office ɗinta na je na shiga ɗakinmu inda na aje jakkata,kuɗi na ɗauko sannan
na fita bakin hanya.Na samu mai taxi na yi masa bayanin inda zai kai ni,wata cibiyar sayar da
maganin musulunci ya kai ni.A can na sayo sanamiki mai kantin ya haɗo min da zuma,sannan
na dawo asibiti. Tun daga nesa nake hangen Dr Jaleel ya na masifa,ina zuwa ya ce “daga ina kike? Wa ya baki
izinin fita?”
“Ka yi haƙuri matsala ce ta ujila ” na furta ina mai sunne kai domin yin ladabi.
“Su majinyatan da kika bari fa? In wata matsala ta faru ki sani a bakin aikin ki” nan ya shiga yin
min masifa kamar wata ƴarsa kafin yayi gaba.
Office ɗin Dr Haleema na sake komawa na nuna mata ,“Ayodele ki faɗa min abin da ke faruwa
mana sannan ba ko wane lokaci ba fa ake shansa”
“Dr Fatimah ce babu lafiya,kuma na tabbata sihiri ne ke ɗawainiya da ita ki taimaka min ki yi min
addu'o'in ciki na bata ta sha don ta galabaita sosai” shiru ta yi,bisanin kuma ta ɗauko moɗar
ƙarfe wacce take dafa Lipton a ciki, da ita ta yi amfani wurin tafasa Sanamakin bayan nan ta
zuba zuma ta shiga yin karatu ciki.Na yi mata godiya na karɓa,inda na bar Fatimah nan na
same ta.Dakyar ta iya tashi zaune ta yi Bismillah ta sha,a nan take zufa ta karye mata.Sai ta
fara sauke ajiyar zuciya bisanin ta ce “Ayodele cikina na murɗawa toilet zan shiga ” da sauri ta
miƙe,na take mata baya har muka isa banɗakin da aka tanada don likitoci.
A wannan wunin tun ina ƙirga adadin da Fatimah ta kewaya har lissafi ya ɓace min, zawayi
kawai take mai ɗan uban wari don ko ni da ke tsaye bakin toilet ɗin ina jin warinsa.A ƙarshe dai
har ni sai da na shiga toilet ɗin don ta galabaita sosai,idonta tuni sun faɗa ta yi zuru.Ganin an
ɗauki sama da minti ashirin ba ta samu wata murɗawar cikin ba,na taimaka mata ta yi wanka
sannan mu ka fito.A ɗakinmu ta kwanta,sai a lokacin A'ishah ta san da ciwon yayi tsanani.Ƙarin
ruwa na saka mata,bayan ta sha lemu exotic baiwar Allah sai bacci.
A'isha ta tsaya tare da ita ni kuma na fita na hau aiki don kusan ban yi komai ba.Sai ƙarfe tara
na dare na nufi ɗakinmu,duk bacci suke.Na taɓa wuyan Fatimah na ji babu zazzaɓi ,na je na
haye gado sai bacci.
“Yaanhun! Uhun ! Uhun!” shashekar kuka ta tashe ni daga bacci,na lalubo wayata na
duba.Ƙarfe biyu ta gota,na ja tsuki tare da fita na nufi MUTUWARE don tuni ruhina ya lamunta
da lamarin da ke faruwa da ni.
Ɓangaren mata na shiga inda ake aje gawa,kwaɗon kawai na taɓa ya buɗe kansa na ja ƙofar
na shiga sanyi AC ya ratsa ni sosai bisanin na yi tozali da wata sabuwar gawa don ko wanka ba
yi mata ba.Mu na haɗa ido da ita ta bar kukan,a gajiye nake hakan yasa nake jin haushin tashe
ni daga baccin da ta yi.
“Sai ki tashi ki faɗa min abin da yasa kika jawo ni izuwa nan” na faɗa ina waige-waige don
neman wurin da zan zauna,sai dai ban farga ba na ji wani hannu ya jawo ni da mugun ƙarfi na
yi baya tare da faɗa wa cikin akwatin mutuwa.....
My book is only 500 duk mai son biyan kuɗin karatunta za ta iya tuntuɓata kai tsaye ta
WhatsApp +22795045822 sai na bata account ɗin da za ta saka kuɗin.
[31/10 à 11:05] MRS SADAUKI : *MUTUWARE ...*♀️
GIDAN GAWA♀️️
Love
and
Horror story
```MRS SADAUKI✍```
Dedicted to Ameera Adam
FCWA ☀️
_________________________
*Promo:* mai ra'ayi zai iya biyan 400 kafin na gama free page a maimakon 500,wacce ta shirya
biyan kuɗin karatunta za ta iya min magana kai tsaye ta WhatsApp +22795045822 sai na bata
account ɗin da za ta tura na gode!
Page 6
Kiciniyar fita daga cikin akwatin gawar na fara sai dai ga mamakina wata gawar na gani a tsaye
kan ƙafafunta ta na ƙoƙarin danna ni ciki.Da dukkan alamu akwatinta ne,cikin wata irin murya ta
maso duniya take cewa “ki zauna madadina don Allah na ga ke lamarin duniya bai sha maki kai
ba,ban shirya zuwa can mazaunar fatale da ruhika ba” Idona na ware sosai kan matar, datijuwa ce a ƙalla ta kai shekara hamsin da ɗoriya fara ce
tasss sai tsagen fuskarta na kurmawanci da ya fito raɗo-raɗo.
Tabon goshina ne na fara jin ya na motsi,kamar almara sai gani na fito daga cikin akwatin na
tsaya kan ƙafafuna.
Gawa ta fashe da kuka,cikin tsawa na ce “je ki koma makwancin ki,wato lokacin da malamai ke
yi muku wa'azi kar ku biye ma ruɗin duniya ku na yawon dare amma kuka yi kunnen uwar
shegu da su kuke fita cikin dare farautar bayin Allah.Yanzu kuma da zanzaro ya tonon gidan
Rina gari ya kwaɓe miki za ki neman ki dawo duniyarmu?” Idonta na zubar da hawaye ta shiga akwati ta kwanta wani haske ya fita daga goshina ya
daketa tsit kake ji har esprit ɗin nata ya bar motsi,na maido dubana ga ɗayar wacce ke
shashekar kuka na zuba mata Mayun idona masu masifar kaifi na ce “ ke kuma ina jin ki”
Cikin kuka ta fara yi min bayani “wannan da kike gani mahaifiyata ce,ta ja ni izuwa wani ƙauye
ne don yin shagali ita da ƙawayenta a can suka nemi da ta bada jinina su sha da ta ƙiya ne
hanyarmu ta dawowa mu ka yi hatsari.Kin ga ban mutu ba sun ɗaure ni da azargagi ne,shirinsu
shi ne in an kai ni maƙabarta su je su haƙo ni su tsotsen jini” A ɗan takaitaccen bayaninta na fahimci mahaifiyarta ta na cikin wata ƙungiyar Mayu ce masu
shan jini,sannan duk shekara su na gudanar da bikin ƙara danƙon zumunci inda a dole wata za
ta bayar da kyautar jini daga cikin ahalinta,kamar ɗa,jika ko ƙane.
Kallon tsaf na yi mata,sai yanzu na lura da goshinta da gefen bakinta duk a fashe suke alamun
buguwa.Tunani na fara ta inda zan taimakonta,sai dai na kasa samun mafita don ban san
fuskokin masu son kaita ƙasa ba.
“Ki taimaka min kar ki bari a kai ni maƙabarta da raina ban mutu ba sun juyar da hankulan
mutane ne kawai ake min kallon gawa ” muryarta ta katse min tunani.
Na ja dogon numfashi bisanin na ce “ki na ji na,a halin yanzu banda mafita amma na yi miki
alƙawari zan cece ki ko bayan an haƙa miki kabari ne an saka ki ci to zan zo gare ki”
Fararen idonta ta zuba min uwanda sam ba su da ɗigon baƙin ciki,na jinjina mata kai alamar
tabbatar wa kan ƙudirina.Ban sani ba ko ta yarda da ni ɗari bisa ɗari,amma a sannu na ga
ruhinta da ke dabaibaye da wasu Kambu ya ɗan samu salama.
Sai da na shafi fuskarta bisanin na fito,direct ɗakinmu na wuce sai na tarar da Fatimah a zaune.
“Kin tashi? Ya jikin naki?” na tambayeta.
“Da sauƙi alhamdullah! Na gode sosai Ayodele,haƙiƙa ke ƴar baiwa ce.Da ace musulma ce ke
da tabbas ba ƙaramin gudumuwa za ki bayar ba”
Na sakar mata murmushi na ce “duk Ubangiji muke bauta ! Banbanci kaɗan ne,sannan shi ke
tsara komai iyakacinmu mu yi aiki da baiwar da ya bamu amma komai daga Ubangiji yake”
“Zance na hikima! Anya kuwa ruhinki ba na Musulunci ba ne gangar jikin kaɗai ke ta
Yahudawa?” Fatimah ta faɗa,dariya na yi na canza zancen “ai yanzu dai kin bar jin tsoron komai