Showing 18001 words to 21000 words out of 21490 words

Chapter 7 - Mutuware Gidan Hawa Complete Book Mrs Sadauki

baya ,dakyar na iya miƙe wa kan ƙafafuna na juyo ina
fuskantar shi.Namiji ne dattijo wanda ya ba shekara saba'in baya ,shi ne ya jawo ni yayin da
sauran tsofin da suka haɗa maza da mata suka yo gaba. “Yau dai asirin ki ya tonu,shegiyar yarinya ashe mayya ce ke shi ne kika fake da sunan ceto
kike.Wancan Kambun maitar da kika rufe shi muke so ki tono kafin Sarkin Mayu ya ƙara so ” ya
faɗa ya na mai yin nuni da inda na rufe Kambun Kunkuru.

Banda haske babu abin da wurin yake ,wanda a bayyane yake kowa na ganinsa har da normal
mutane.A daidai wannan lokaci ba zan iya yin wani dogon tunani ba ballantana na samo mafita
,duk ma ba wannan ba halin da Momah ke ciki shi ya fi ɗagan hankali.

Tsofin unguwarmu sai zagi ne suke a gaban jama'a, miyagun kalamai wanda duk mai zuciya ba
zai iya jura ba.Sosai na yi mamakin dalilin da yasa ban ji sarawar kai ba ,saɓanin sauran lokuta
da nake harzuƙa na ɗauki ɓoyayyar fuskata.
A na haka har Sarkin Mayu ya iso,sosai na yi mamaki ganin mutumen nan da muka taɓa
haɗuwa cikin taxi.Bayani suka fara yi masa,shi kuma yayi kamar bai taɓa gani na ba tare da
umarta ta “je ki haƙo abin da kika ɓoye”
Sai a lokacin na juya na dubi Momah,jiki a sanyayye na duƙa na buɗe ramen tare da ciron
Kambun Kunkuru.Haskensa ya ƙara yawaita kan lokacin da yake cikin ƙasa,Sarkin Mayu ya
karɓe shi ya na cewa “kin ji kunya ƴar ƙanƙanuwar yarinya da ke amma kin zama muguwa
mayya kawai” da mugun sauri na rumtse ido ina jin hawaye na min zuba.
Mutane ne suka fara suratai akan sai mun tashi mun bar masu unguwa,zagi kam ya fi cika buhu
babu kalar baƙar maganar da ba a faɗa wa Momah.Ita kuka ni kuka,Sarkin Mayu ya ƙara
ɗaukar magana inda yake cewa “na baku nan da awa ɗaya kacal ku tashi ku bar nan ko kuma
na sa a ƙone ku da ranku”
Jama'a suka ɗau ihu,da mugun sauri Momah ta shiga gida na take mata baya.A ɗaki na tarar da
ita ta na gangamar kaya,rasa abin da zan ce mata na yi kawai sai na faɗa jikinta ina kuka.
“Kukan mi kike? Ina ce ke kika saya mana wulaƙancin da kuɗin ki,tun ranar da kika zo da abin
nan sai da na ce ki mayar mai shi abinsa amma kika yi kunnen uwar shegu da ni” ta ida faɗa ta
na mai ture ni na yi baya.
Daga inda nake ina jiyo hargowar mutane sai juya suke mana cikin gida tare da zaginmu.Cikin
ƙanƙanen lokaci Momah ta haɗa kayanmu,dakyar da siɗin goshi muka samu mu ka isa bakin

hanya.Ɗaiɗaikun mutane ne kawai ke tausaya mana,ciki kuwa har da Asabe don a gidanta ma
Momah ta kai ajiyar sauran kaya.



A wannan wunin mu ka bazama neman haya sai dai kamar abun tsiya ba mu samu ba,sai a
wata unguwa mai ƙarancin mutane kamar za a fita gari shi ma ɗaki ne ciki guda.A haka dai mu
ka share mu ka zauna bayan Momah ta kwaso sauran kayanmu.






Komai na ta tafiya cikin tsari, musamman bikin da ya kasance tuwona maina ne.Amayar da
angon duk ƴan uwa ne,sosai abun ya tafi cikin tsari. A'ishah sai rawar kai take,abokanta kuwa
duk sun haɗu wurin kanmu . Fatimah kuwa sai ƙoƙarin kiran Ayodele take a waya saboda
rabonta da ita wajen kwana biyu wayarta ma ba ta shiga,cikin wannan zullumi dai ta yi shagalin
bikin.
Ranar ɗaurin aure tamkar babu gobe haka aka yi abun hauka musamman ɓangaren Mansur da
yake taƙama da Nera.Motocin ɗaukar amarya kaf ɗinsu babu tsohuwa sun jeru rasss sai wacce
ranka ya yi ma za ka shiga.A haka aka miƙa A'isha tamfatsetsen gidan mai kama da aljannar
duniya,duk yadda ta so Fatimah ta tsaya fafur ta ƙi don dama kan babur ɗinta ta je ko kaɗan ba
ta saki jiki da abokan Mansur ba don ƴan magana kan ce sai hali ya zo ɗaya ake abota.


Bayan kowa ya watse Mansur ya shigo tare da abokansa.Kallo ɗaya za ka yi wa gizner jikinsu
ka ga Nera ce ke magana,suratansu suka fara ita dai A'ishah ta na rakuɓe sai da suka matsa
mata ne ta ɗan ɗage mayafinta.Amanar abokinsu suka bata bisanin yayi masu rakiya ya dawo
shi ɗaya.
“Ki sauko mu ci abinci mana” ya faɗa ya na mai jawo hannunta,cike da mamaki A'isha ta bisa
har suka baje kan capet.Ta sha ji daga abokaina abu na farko da ake yi in an kai amarya sallah
ce domin nuna godiya ga Ubangiji,amma sai ta yi masa uzuri da tunanin ko yunwa yake ji shi
yasa.Ba ta kai ƙarshen mamakinta ba sai bayan da suka cika tumbinansu Mansur ya fara aika
mata saƙonnin soyayya har ya kai da ya kusanceta,ko Bismillah ba ta ji yayi ba ballantana wai
addu'a.

Washegari
Tsabar gajiya da ta yi ya saka ta rasa sallar asubah,hasken rana ne ya daki fuskarta ya sa ta
yunƙura ta tashi zaune ta na kallon window.Gefenta kuwa Mansur ne ke ta sharar baccinsa,ta
kai hannu ta na jijiga shi “Ogana ka tashi ka kai ni toilet ka min wanka please ba zan iya tashi
ba” a shagwaɓe take fitar da harufan har ta ci nasarar tayar da shi.

Ya buɗe idonsa ya zuba mata su ,iya kallon da watsa mata kaɗai sai da gabanta ya faɗi.
“Mine ne?”
“Wanka za min ”
“Can a gidanku wa ke yi miki?”
Ras gaban A'isha ya faɗi jin furucinsa sun yi hannun riga da wanda ya sha faɗa mata satin
aurensu.
Dakyar ta ƙoƙarta ta je ta yi wanka ta zo ta gabatar da sallah.Ta na nan zauna har Mansur ya
tashi daga bacci,direct wurin drower ya wuce ya fitar da kaya masu kyau ya saka.
“Ka manta ba ka yi wanka ba fa ” ta faɗa ganin bilhaƙi yake shirin,“uban waye ya faɗa miki
manta wa na yi?” Mansur ya faɗa a zafafe ya na kallonta.
“Ka yi haƙuri ”shi ne kawai abin da ta iya furta wa.
“Ki tashi ki ɗora min breakfast!” ya faɗa ya na mai fesa turare.
“To” ta amsa tare da tashi.Tsabar takaici sai da ta zubar da hawaye ,amma a haka ta haɗa
masa frite da gasashen kifi don ta ga kusan akwai komai.

Kan table ɗin cin abinci ta ajiye bisanin ta wuce bedroom,waya ta tarar da shi ya na yi sai
magana yake cikin ladabi.Da ace mahaifinsa na da rai da to babu shakka za ta ce da shi ne
yake waya.
Bayan ya gama ne ya zo ya rungume ta tare da cewa “har kin gama?” kai ta jinjina masa,“ok mu
je”
Falo suka koma a tare suka ci abincin, Mansur na yi mata hirar soyayya hakan ya kuma ƙulle
mata kai.


“Zan tafi wurin aiki,tun ɗazu shugaba ke jirana” ya faɗa tare da miƙe wa tsaye.
“Aiki kuma? A cikin satin aurenmu?”
“To sai aka yi mi? Kin ga ban so sakarci sai na dawo” ya na gama faɗa ya fice. A'isha ta zube
kan salon ta na jin wata irin damuwa na dabaibaye ta,tun kafin aje ko ina auren Mansur ya fice
mata a rai.“Babu wankan janaba ballantana a yi maganar sallah anya kuwa na auru? Mine ne
ma ya hana shi ko fuska da baki ya wanke?” ta furta hawayen takaici na zubo mata bisanin ta
ɓingire bacci.


Hayaniyar ƙawayenta ce ta tashe ta,sosai ta yi murnar zuwan su.Sauran kazar jiya ta ɗauko
masu kafin a hau hira da girke-girke cike da nishaɗin ƙawarsu ta auri mai kuɗi kowacce ta
sasaɓe zane ta ci abubuwa na kayan daɗi ta ƙoshi da za a tafi gida kuwa har da yin tsaraba.




AYODELE

Tun da muka dawo sabon gida Momah ke fushi da ni mai tsanani ,duk uban haƙuri da magiyar
da na ta yi mata kanzil ba ta ce min ba.Hakan ya jefa raunatacen ruhina a cakwakiyar
matsala,na bar cin abinci kan ƙa'ida,na kashe wayata aiki ma sam na bar zuwa.Amma hakan
bai sa Momah ta tausaya min ba. Kamar kullum wuraren ƙarfe takwas na dare na fito ƙofar gida na yi zaune,unguwar tsit take ko
tsuntsu babu.
Wani mutum na ga ya bi ya wuce ta gaban ya nufi wani ɗan gangare,na bi bayansa da kallo
kawai ina mamakinsa don yau kusan sau uku kenan da ina ganinsa.
Zuciyata ce ta raya min na bi bayansa,kamar aikaka haka na miƙe har da haɗa wa da gudu na
take masa baya.Mun yi tafiya mai ƴar nisa bisanin na tsaya,domin ya kai wurin da ke da
tsananin duhu ba zan iya shiga ba.
Idona ne ya sauka ga allon sanarwa mai ɗauke da sunan MAƘABARTA,gabana ya bada ras!
‘Ko shakka babu irin mutanen nan ne masu haƙo kabari don yi aikin asiri ko tsafi’ na faɗa a zuci
ina mai ƙara ɗan yin gaba ina ɗigirgire ko Allah ya sa na hango wani abu.Daga bayana na ji an
dafa kafaɗa,da mugun sauri na juyo muka haɗa ido a take hanjin cikina suka hautsana......




Ban jin daɗin jikina ina barar addu'ar ku
[31/10 à 11:05] MRS SADAUKI : *MUTUWARE ...*‍♀️
GIDAN GAWA‍♀️️

Love
and
Horror story

```MRS SADAUKI✍```

Dedicted to Ameera Adam


FCWA ☀️

_________________________


To alhamdullah wannan ce page ɗin ƙarshe ta kyauta,don haka duk mai son ci gaba da karatu
zai biya kuɗinsa na karatu 500 ta wannan account 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank kafin na saka shi group sai a turo shaidar biya ta WhatsApp
+22795045822

Last free page 10



A'isha na nan zaune cikin halin ƙaƙanikayi Momy ta fito Mansur na bayanta.Kan salon ta
hakimce ta sune ta tare da cewa “ A'isha ruwan gidan ma ba za a bani ba sai na roƙa ko kuwa
ban isa ba ne?”
“Haba Momy ya za ki ce haka? Ai ko ban auren Mansur ke ɗin uwa ce gare ni domin ciki guda
kuka fito ke da Mamana ” cewar A'isha ta na mai tashi da sauri har jikinta ke yin rawa ta nufi
kitchen.
Drinks da abinci ta haɗo mata,ta dire su a gaban Momy sai bayan ta zuba mata komai ne ta
tashi ta shige bedroom.Matsanacin kuka ya kubce mata,ta faɗa kan gado ta rusa shi cincin
ƙarfinta.
Mansur ya shigo,“ A'isha?” ya faɗa cikin sanyin murya kamar ba shi ne ya ga ma yi mata tsawa
ba.
Ba ta daina kukan ba ballantana ta kula shi,ya isa gare ta ya na mai jawo ta jikinsa ya shiga
aikin rarrashi amma ta ƙi yin shiru .Sai da Mansur ya kai ruwa rana sannan ya shawo
kanta,ashe shi ma da walakin wai goro a miya.Buƙatarsa ce ta kawo shi,kuma ko da ya samu
abin da yake so ya bar ta nan. Cike da baƙin ciki A'ishah ta isa toilet,abu ya tare mata goma da gomiya tara.
Kamar wata zararriya ta shiga dukan ruwa ta na cewa “da me zan ji? Wace rayuwa na tsoma
kaina ni A'isha? Wayyo Allahna!” sai ta ƙanƙame dukkan jikinta jin tamkar ana kallonta .
Ƙoƙarin fita daga bawon wankan ta fara,sai dai tamkar wacce aka jone fatar jikinta da bawon
haka ta ji ta liƙe gam.Cincin ƙarfinta ta buga wani uban ihu wanda ya karaɗe duka gidan,sai dai
ko motsin wucewar ɓera ba ta ji ba ballantana Mansur ko Momy su kawo mata agaji.
Dakyar ta ci nasarar fiddo ƙafafunta waje,sai ta ga su yin wani ja ƙau jawur babu kyawun gani
kamar jan nama.Hankalin A'isha bai ida tashi ba sai lokacin da Allah ya bata iko ta tashi kan
ƙafafuwanta.Kaf shap ɗinta ya zube kamar an zuba sukari a ruwa,jikinta ne ya ɗauki wani irin
rawa ganin ƙugunta kamar muciya saɓanin da can farko da take turbakallah. Towel ta saka ta fito da mugun sauri,bayan Momy ta gani ta na mai fita daga ɗakinta ba tare da
ta san mi ya kawo ta ba.
Bakin ƙaton madubi ta tsaya ta na kallon kanta,sai kuma ta ganta normal ba ta san lokacin da ta
saki ajiyar zuciya ba.“Ashe gizau ne ban canza ba” ta furta cikin murna bisanin ta shafa mai da
turare,ta saka kaya sai kuma ta fito falo.
Turus ta yi ta na kallon Momy na yayafa ruwa a duk wata kusurwa ɗaki,ba abin da ya fi bata
mamaki irin sunanta da na Mansur da ta ji ta na ambato.
“In kin gama gulmar sai ki je ki yi abin da za ki yi” cewar Mamy ba tare da ta juyo ba.

‘Ko ya aka yi ta san na fito?’ A'isha ta tambayi kanta bisanin ta wuce kitchen.Girki ta ɗora
,bisanin ta dawo falo ta ɗauki wayarta.Fatimah ta kira,cikin sa'a ta same ta tamkar rariya haka
A'isha ta buɗe baki ta na ba Fatimah labarin abin da ya faru da wanda ma ke kan faruwa ba tare

da ta san babban kuskure ta aikata ba.


Da dare Mansur na dawo wa ya shiga ɗakin Momy,bayan ya gaisheta ne take ce masa “ɗazu
matarka ta kira wata mai suna Fatimah ban san ya suke ba,amma kaf sirrin gidanka ta sanar da
ita na mu'amalar ka da ita .Hum! Ni kuwa cewa ta yi jarababiyar tsohuwa ko amarci ba ku gama
ci ba na zo na tare muku a gida” Ran Mansur ne yayi bala'in ɓaci ,ya tashi da sauri ya fita.Ya na shiga ɗakin ya tarar da A'isha ta
zanzare ta ci uban ado,tuni ya manta abin da ma ya kawo shi ya je ya rungumeta.
Gabanta ne ya faɗi lokacin da Mansur ke ƙoƙarin yi mata kiss saboda wani uban wari da
bakinsa ke yi,warin hammatarsa kuwa ko bunsuru albarka .Amma a haka ta daure suka raya
sunnah,cike da kula wa ya dube ta ya ce “daga yau kar na sake jin kin fitar da sirrina ,ko Momy
ba ta faɗa min ba zan gane wa” A'ishah dai ba ta ce komai ba ,zai lokacin da zai mayar da kaya ta ce masa “don Allah ka je ka
yi wanka”
“Ba zan yi ba” ya bata amsa a takaice.
“Ko brush ka yi”
Mansur yayi saurin juyo wa ya na ƙare mata kallo cikin ido,‘ko dai maganin da na bata har ya
karye ne da har ta ke iya faɗa min magana kai tsaye babu ɗigon tsoro?’ ya yi wa kansa
tambayar a zuci.
“Ka yi haƙuri don Allah ” ta faɗa a ɗan daburce bisanin ta shiga toilet ta yi wanka.


Ɓangaren Momy kuwa shiru har yanzu ba ta ji ihun A'ishah ba ,ta yi zaton shegen duka Mansur
zai lakaɗa mata.Ganin haƙar ta ba ta cimma ruwa ba yasa ta tashi ta rufe ƙofa da key,kayan
jikinta ta cire ta ɗaura wani jan ƙyalle a ƙugu.
A cikin jakkar kayanta ta fiddo wata ƙaramar tukunyar laka mai ɗauke da layu da sauran
abubuwan shirka sai kuma wani bokitin roba fari mai ɗauke da korayen ruwa,nan ta fara yin
surkulle a nan take hayaƙi ya turniƙe ɗakin ba ka jin komai sai hucin narkeken kwaɗo da
kukansa. Ta ɗauki lokaci da dama bisanin ta tsaya,murmushin mugunta ɗauke a fuskarta ta ce “ A'isha
tun da ki ka yi sanadin shigar ɗana ƙungiyar asiri wallahi ke ma sai na gulala miki,sai kin
gwammaci kiɗi da rawarki.Da ni da ke shege ka fasa” ta gama faɗar haka ta buɗe bokitin nan fa
kwaɗon nan ya yi tsalle ya fito kamar mai jira. Shegun idonsa tulu-tulu sai faman juya su yake ya na ƙoto.Ba tare da jin tsoro ba Momy ta shafi
kansa ta na mai cewa “na wakilta ka a matsayin mai ɗaukar fansata,ina so ka fitini A'isha cikin
mafarki da kuma zahiri ka zame mata hawainiya ka na sauya kala kamar yadda aka bani
Kambunka” ta na zowa daidai nan ta furta wasu surkulle a take ya ɓace bai bayyana ko ina ba
sai a ɗakin A'isha.


Ta na zaune kan gado kunnenta maƙale da waya ta na cewa “wallahi Fatimah in faɗa miki har
yanzu ma Mansur ya ƙi yin wanka,ban san dalili ba in kuma na yi magana ya yi fushi”

Can ɓangaren Fatimah ta ce “to ke kamar ba mace ba,ki rasa dubarar da za ta sa yayi wankan?
Kawai ki bari sai ya na kwance ki cika bokiti da ruwa ki zuba masa ai doli ya yi wankan ”
“Katifata ta jiƙe?”
“Ai ta na da leda”
“Ok to zan jarraba na gani” sun yi hira sosai bisanin ta kashe kiran, lokacin ƙarfe takwas na dare
bai gota ba.
A'isha ta sauko ƙafarta ƙasa da niyyar zuwa toilet sai ta ji wani bala'in sanyi tamkar
ƙanƙara,“innalillahi!” ta fusrta da mugun sauri a take kuma ta ji normal .
Toilet ta shiga ,ta hau WC kenan ta fara jin kukan kwaɗo ta saki ihu ta fito a guje sai kuma ta ci
karo da Mansur ya shigo.
Ko tambayarta bai yi ba lafiya take ihu ya zube kan bed,saboda ya gaji sosai ya sha yawo a gari
ko zai samu ƴan mata huɗun da aka buƙata sai dai ko guda bai samu ba.


Baccin da ya fara da ninshari ya saka A'isha da ke can takure saurin dubansa,shawarar
Fatimah ce ta zo mata a kai.Da mugun sauri ta fita waje ta ciko bokiti da ruwa ta malala masa a
jiki.Hargowar da ya yi ya saka A'isha sakin bokitin ta na mai dafe ƙirji.





★AYODELE


Duk yadda na so in danne muradina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login