Showing 21001 words to 21490 words out of 21490 words

Chapter 8 - Mutuware Gidan Hawa Complete Book Mrs Sadauki

akan sanin tarihina kasa wa na yi.Bayan mun gama cin
abincin dare na ce “Momah wai mine ne sunan Abbana? Na ga ko lokacin da na yi makaranta
Ayodele kawai ake kira na” shirun da ta yi ya saka ni ci gaba da cewa “ko dai shegiya ce ni
banda uba?” “Da ubanki Ayodele! Jarumi mai zubar da maza ko a fagen yaƙin wasa.Ke ɗin sauraniya ce
ɗaya tamkar dubu,a kaf cikin ƴaƴansa maza da mata,manya da ƙanana ke ce ƴar baiwa”
Momah ta faɗa wanda a ƙarshe sai da ta saki murmushi.
“To ya na ina? Mi yasa ba mu rayu a tare ba?”
“Don na tseratar da ke daga uƙubar da ababen bauta ke shirin tsoma ki yasa na gudo” ta bani
amsa ta na mai kallon cikin idona, ta ci gaba da cewa “ko da na ji kin ambaci sunan Lassey na
fahimci lokaci ya yi da za ki san tarihin ki,sai dai fa ba komai zan sanar da ke a yau ba sauran
sai ranar birthday ɗin ki” Cike da jin daɗi na matso, Momah ta saki murmushi wanda a cikinsa ina iya hango tsantsar
farin ciki wanda ban san mi ya wanzar da shi ba sai dai na fi alaƙanta shi ƙila ta na son
mahaifina irin sosai ɗin nan.

Sai da ta jawo ni jikinta kamar wata ƙaramar yarinyar,kaina na kan cinyarta hannunta kuma na
shafa ƙananun kitson da ta yi min.

Momah ta ce “kamar yadda na shaida miki ke sarauniya ce to mahaifin ki shi ne Sarkin Victoria
Falls inda ya gaji sarautar ne a hannun Yayarsa na manta sunanta ”
Da mugun sauri na ce “ Déborah ” ambaton sunan ya saka ƙwan lantarkin ɗakinmu fashe wa ji
kake ɗuuuu.
Momah ta zabura ta miƙe tsaye,“wa ya faɗa miki sunanta? Wa ya ce miki ana ambaton sunanta
a ko ina? Da na ce miki na manta a tunanin ki gaske manta war na yi?” Momah ke faɗa cikin
wata irin murya wacce ba ita na santa da ita ba,idonta kuwa wani irin haske suke fitar wa kamar
an kunna glov har wani canza kala suke. Jikina ne ya ɗauki rawa ainun, musamman da ƙofofin gidanmu suka fara yin wata irin buga wa
su rufe kansu su buɗe ji kake faaa-faaa!
Rufin ɗakinmu kuwa kamar zai kware har ɗaga wa sama yake,wata da ban manta inda na ɗora
ta ba na lalubo tare da ƙoƙarin kunna fitila ita ma ta yi bindiga ta fashe har ɗiyan hanjinta da
garin batirinta na ji a hannuna.
Tashin hankali,gobarar gemu Momah ta canza Yare ta shiga suratai.In ba gizau idona ke min ba
wasu fararen siffofi ne ke faman shigo wa ɗakinmu tamkar duniyar fatale.........




A nan kawo ƙarshen free page,duk wacce ke so ta biya 500 ta akwatin nan 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki tura shaidar biya ta WhatsApp +22795045822



MRS SADAUKI NIJAR

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login