Showing 6001 words to 9000 words out of 25987 words
Chapter 3 - Yan Kungiyar Asiri Book Complet by Mrs Sadauki
tagumin.
"Har kun taso?"
"Eh Mama" su yi gamon baki suka amsa mata.
"To ku je ku yi wanka ku ci abinci"
"Mine ne ke damun ki Mama?" Zahra ta tambaya.
"Babu komai kawai zuciyata ce nake jin ta yi min nauyi babu daɗi sai ƙunci" Mama ta faɗa
kamar wata sakarya.
"Zai wuce Mama ki yi ta addu'a "
Ɗakinsu suka wuce ko wace ta yi wanka ta saka kayan shan iska.Su na cin abinci su na
hira,Bintu ce ke bata labarin barkwanci da kuma na ban tsoro ita kuwa baiwar Allah Zahra har
tsoratar take.
Da Abba ya dawo sosai ya yi wa Bintu faɗa ,kafin ya haɗe su da Zahra ya yi masu
nasiha.Mama na daga gefe ta bi ayari ta yi shiru kai kace sabuwar musulunta.
Washegari
Ƙauyen Djifer Abba ya yi sammako.Daidai ƙofar gida ya parker motarsa sannan ya fito ya shiga
bakinsa na shirin yin sallama ya ji ƙafarsa ta yi wani girrr.
Halilu da ke tsaye ya na wankin kifi ya ga komai sarai ya ce "ka shigo mana Baban Twins "
Abba ya haɗiye wasu yawu dakyar sannan ya shigo,"babu kowa gidan?"
"Baba da Inna sun tafi gona,Habiba kuma ta na ɗaki ta na yi wa Tsohuwa tausa" Halilu ya basa
amsa.
Abba ya sake matsawa ya yi sallamar da ya so yi tun a bakin ƙofa,aka amsa sannan ya shiga.
Mahaifiyar tasa wacce suke kira da tsohuwa ya gaida bisanin ya yi zaune,Habiba ta gaishe shi
ita ma ta na fitowa waje.
"Ga ruwa nan a langa ki kai masa ya sha"
"Halilu daga zuwansa ?"
"Na ci uwarki ki ɗauka na ce"
Habiba na zumɓurar baki ta ɗauki ruwan wanda ainahi boka ne ya bado su ta kaiwa Abba .Cike
da ladabi ta ce "an kwaso hanya ga ruwa nan Abba " ta ajiye a gabansa ta fita.
Abba ya ɗauki ruwan ya sha kaɗan ya ajiye.Ya na nan zaune sai ga Inna matar Kawu ta
shigo,gaisawa suka yi ya na mai tambayarta "ina Yaya Mansur ɗin?"
"Ya shiga banɗaki yanzu ya fito"
Kawu Mansur kuwa ya na gun Halilu da ke faman gasa kifi sai barbaɗa magani suke su na hira
ƙasa-ƙasa.
Abba da ya gaji da jiran shigowarsa ya fito ya na mai kiran sunansa.Kawu Mansur ya haɗe rai
kamar bai taɓa dariya ba,sannan ya zo suka gaisa da ƙanen shi.
"Ina dawowa gida aka ce min har ka tafi,shi ne na zo na ji in lafiya?" Abba ya faɗa .
"Hum! Ta ga dama ta baka dama ka zo?"
"Don Allah Yaya ka bar wannan maganar ai dai gani na zo ta ƙorafi ta ƙare"
Kawu Mansur ya ɗan washe baki tare da rungume Abba ya ce "har na ji daɗi ƙanena,Habiba
shimfiɗa min tabarma can gidin bishiya mu yi hira ni da ƙanena "
Ganin murmushi kan fuskar Kawu Mansur sai Abba ya ji wata irin nutsuwa.
Kan tabarma suka zauna su na hira ,kafin Halilu munafiki ya kawo hasashen kifi babba da
ƙarami "Baban Twins wannan ne naka ,Baba kai kuma ka yi haƙuri ka ci wannan tunda kullum
ka na ci" cike da munafurci yake faɗa tare da ƴar dariya .
"Babu komai ka basa har da nawa ɗin,ka je ka ƙara kamo wasu sai ya tafi da shi can gida"
cewar Kawu Mansur ya na kishingiɗa.
Abba kuwa a duniya babu abin da ya fi so kamar kifi wannan ya saka babu jira ya fara ci,ya ce
"a'a Yaya wannan ma ya ishe ni" jin haka ya saka Mansur ɗaukar nasa shi ma ya bi bayan
Halilu suka koma can bayan gida su na ƙyalƙyata dariya.
Tsohuwa ta fito waje,"tsabar mugunta a gasa kifi shi ne ba za a ban ba?" Ta faɗa ta na tako a
hankali.
Abba ya yi saurin raba wa biyu ya bata rabi, tsohuwa ta fara ci ta na saka masa albarka.
Kawu Mansur ya na dawowa ya ga kifi a hannun tsohuwa da mugun sauri ya ƙaraso ya na
cewa "Tsohuwa ba dai kifin ne ki ke ci ba?"
Abba ya ce "Ni na bata ya na ga hankalin ka duk ya tashi?"
Kawu ya haɗiye wasu yawu ya ce "a'a babu komai"
Sai marice lis Abba ya koma can gida.
★JAPON
“Kar ku ji tsoro ai dama haka ne ƙa'idar dajin da zarar ka shiga yake rufewa ” Bobby ya faɗa ya
na saka masu murmushi bisanin su ci gaba da tafiya.
Kameel ya yi ihu ya na mai dawowa tsakiyar su Fadeel.
“Lafiyar ka?”
“Wlh ji na yi kamar an taɓa kafaɗata” Kameel ya faɗa .
“Ku Afirka wa Allah ya yi ku da shegen tsoro,mu uku ne kawai to wane ne ya taɓa ka ɗin?”
cewar Fadeel cike da masifa.
“Oho! Dai ina na nan tsakiyar ku ba zan gusa ba,dama ku da Aljannu banbacinku kaɗan
ne”Kameel ya faɗa ya na wani riƙe rigar Bobby shi da ke gabansa.
Duwarwatsu ne ta ko ina yayin da gayen ya yi kore tsanwa shar,dajin tsit ba ka jin komai sai
kukan tsuntsaye da kuma sawun sawayensu. A haka har suka shigo tsakiyar dajin inda yake
mai faɗin gaske."Ƙwaƙwaƙwa! Tsutsutsu! Tsitsitsi!" Kawai ke tashi kamar ana ruwa.
Kameel ya ɗaga kansa sama,ido huɗu suka yi da wani tsuntsun mai manyan ido ya tattakura ya
fasa ƙara ya na cewa “wayyo! Aljani! Aljani! Ku duba ”
Su ka kece da dariya Bobby ya ce “mujiya ce fa! ” Fadeel kuwa ƴar bangar Kameel ya yi sannan
ya ce,“haka ake aljani? Mtsw! ”
“Ku biyo ni wannan ita ce hanyar shiga kusurwar dajin inda bishiyoyi ke magana” cewar Bobby
ya na mai yin gaba suka take masa baya,Kameel sai waige-waige yake a haka har suka iso
ƙofar shiga NOIRA wanda yake tamkar kogo.
Yau babu mai gadi,Bobby ya fara shiga sannan Kameel a ƙarshe Fadeel .
“Hiiyihiyi! Zhumm!” haka kogon ya fara ɗaukar wannan sauti bisanin ya fara juyawa kamar
majaujawa.
Mutane masu fararen shiga suka fara ketowa ta ko ina su na dariya,wacce sautinta kawai ake ji
amma ba a ganin fuskokinsu sai ƙwarangwal.
Abin da bai kashe Kameel ba, lokacinsa ne kawai da bai yi ba.Wani uban tsalle ya yi ya ɗale
jikin Fadeel wanda shi ma a tsorace yake.
Bobby ne ya fara magana “kar wanda ya cutar da su abokaina ne,kar ku matso kowa ya tsaya
inda yake” ya na maganar ne idonsa na ɗaukar wani irin haske .
Da sauri duk suka fara ja baya,domin hasken ba ƙaramin cutar da su yake ba.
“Kar ku ji tsoro ina tare da ku” Bobby ya faɗa wa abokansa,“Bobby ka fitar da mu don Allah
zuciyata za ta tsinke” Kameel ya faɗa ba tare da ya buɗe idonsa ba.
Fadeel ya wani cire shi daga jikinsa ya ce “ƙaton banza matsoraci! Buɗe ido ka ga yadda
fatalwa ke tsoron Bobby saboda miracle ɗin da ke fitowa a idonsa”
Kameel ya buɗe ido ya sauke su kan Bobby wanda har zuwa yanzu idonsa ke fitar da haske
kamar wanda aka saka masa ƙwan fitila a ciki.
“Matsafi! Bobby kai matsafi ne?” Kameel ya faɗa cikin ɗaga murya ya na waro ido.
Dirar mikiya NATA ta yi masu ta ɗauke Kameel da Fadeel ta yi sama da su, bisanin ta fara
magana cikin fushi “ka aikata babban kuskure na zuwa da bare a cikin kogon NOIRA wanda
babu mai shigarsa sai wanda aka yi wa wankan TSAFI.Wannan kusurwa ce ta musamman
domin members kawai,don haka zan saka abokan ka gidan Yari in ka na son su to ka kawo
sacrifice ka fanshe su” ta na gama faɗar haka ta jefa su Kameel cikin wata raga da ke can
rataye ga icce.
Bobby ya ɗaga kai ya kalli abokansa sai ihu suke su na neman agaji.
Hasken idonsa sam basa iya yi wa NATA komai.
Murya na ɗan rawa ya ce “Ki yi haƙuri daga yau ba zan sake ba” Nata ta sauko ƙasa ta na mai
komawa ƴar matashiyar budurwa ta ce “a wannan duniyar ba a san kalmar haƙuri ba,jini ake
bayarwa a maimakonta.In ka na so na sauko ma da su to ka kawo jinin ƴan yara biyu da ba su
balaga ba kafin nan da faɗuwar rana” ta na gama faɗar haka ta wani hura masa iska a
fuska,Bobby bai tsinci kansa a ko ina ba sai a waje kusa da inda suka ajiye mota......
[17/07 à 11:26] MRS SADAUKI : *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*
```MRS SADAUKI```✍
FCWA ☀️
*Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban
buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take
+22795045822.
*Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa
kuma arashi ne*
*Page 7_8*
Bobby ya dafe kansa ,ya na mai sake duba yanayin garin da tuni duhun magrib ya fara
ketowa.Tunaninsa ɗaya ina zai samu yara biyun da za ayi sacrifice ɗin? Ya na mugun son
abokansa sai dai sam ya rasa tudun dafa wa.
Keey ɗin motar ma ya na can ga Fadeel ,a hankali ya fara yin tafiya bisanin gundu.
Ya gaji sosai,sai dai yin gudun shi ne mafita gare shi.Sama da minti ashirin kafin ya zo bakin
hanya wacce take tsit tamkar an shareta.
Bobby ya riƙe ƙugu ya na haƙi tare da waige-waige,bai da nisa da dajin AOKIGAHARA ɗin
wannan ya saka yake iya ganin abin da ke faruwa.
Wasu irin gizai-gizai ne baƙi ƙirin suka haɗu daidai dajin kawai sai walƙiya yake.Gaban Bobby
ya faɗi,in ba zai manta ba ya na ɗaya daga cikin abin da Sarkin ruwa ya shaida masa.Da
mugun sauri ya koma,ya fara gudu kamar ransa zai fita har zo hanyar da za ta sada ka da dajin.
A buɗe take,kawai shiga ya yi har ya isa ciki.
Kogon NOIRA ya shiga,ko tako biyu bai yi ba ya ji muryar Nata a bayansa “ina yaran biyu da
aka ce ka kawo?”
Bobby ya juyo suka haɗa ido da ita,muƙut! Ya haɗiye wasu yawu bisanin ya ce “ban san inda
zan same su ba” Nata ta shiga ƙyalƙyata dariya har sai da ƙasa ta amsa bisanin ta ce “Sacrifice
ya zama dolai,ko kum....” ba ta ida kai ƙarshen maganar ba ta ji murya Marlin bayanta.
“Nata ki kawo mana su can gaɓar Teku ”
Da mugun sauri Bobby ya juya ya na ganin mahaifinsa ne ya ji wani sanyi a ransa.Sai dai yadda
fuskar Daddy take kicin-kicin ya saka Bobbyn shan jinin jikinsa.
NATA ta ɗauko Kameel da Fadeel uwanda tuni sun fara fita hayyacinsu ta kai su gaɓar Teku
.Daddy na fita Bobby ya take masa baya har suka isa can gaɓar ruwan.
Tuni an cire ma su Kameel kaya an saka su cikin ruwa,Bobby ya yi tsaye kawai ya na kallon
Mohan da Martan.
“Ka matso kusa” Daddy ya umarci Bobby ,a sanyaye ya matsa tare da jerawa layi ɗaya da su ya
rufe ido kamar yadda suka yi.
Kogin na fara yin ruguuuu suka fara karanto ɗalasiman TSAFI.Bobby bai san ta yaya ba amma
samun bakinsa ya yi da rera harafofin.
An ɗauki sama da minti goma sannan kogin ya kwanta.Duk wata ajiyar zuciya suka
sauke,Bobby ya kalle su a zuci ya ce ‘ko mi hakan ke nufi?’
Kameel da Fadeel suka fito cikin ruwa fatarsu na wani irin sheƙi ba kamar lokacin da suka shiga
ba.
Cike da murna Daddy ya rungume su ya na mai cewa “Barka da shigowa cikinmu yarana” ko
wanensu murmushi kan fuskar shi ya amsa ma Daddy bisanin su je ga iyayensu.
Kogon NOIRA suka dugunzuma,aka ci gaba da yi masu sauran tsibace-tsibace.Fadeel ya ɗauki
baƙin tsafi,yayin da Kameel kuma jan tsafi.Bayan sun gama zaɓa aka basu wasu ruwa cikin
wata tsohuwar ƙwarya.Ruwan baƙi ƙirin suke,su na shan ruwa duk illahirin gangar jikinsu ta
ɗauki caji suka fara jin banbanci su na jinsu a duniyar sama saboda pouvoir/can/ƙarfin ikon da
aka basu.
Bayan an gama komai iyayen suka fito.Bobby ya ce “na ji tsoro sosai abokanai na yi zaton zan
rasa ku ne” Kameel ya ce “to ga shi a yanzu mu ma an yi mana wankan shiga mun zama ɗaya”
Fadeel ya karɓe da “a'a fa,abin da na lura kamar mun fi Bobby ƙarfin iko”
“Eh haka ne saboda ni ba a bani ruwa na sha ba sai nan gaba”
“Nan za ku kwana ko kuwa?” NATA ta tambaye su.
“Yanzu za mu tafi”
“Yauwa saboda akwai meeting da za ayi ”
Ko da su Bobby suka fito ba su ga mahaifan su ba.Cikin motar da suka zo suka koma,sai da
suka biya inda suka ci abinci Bobby ya ɗauki motar shi sannan duk kowa ya kama gabansa .
“Bobby?” ya ji muryar mahaifinsa, ya dawo baya ya na amsawa “na'am Daddy ”
“Dube ni cikin ido”
“Daddy ban iyawa,ka yi haƙuri ”
“Mi yasa to ka yi haka?”
“Tsautsayi ne”
“Ka san irin haɗarin da ka saka rayuwar ƴaƴan mutane? Ba don Allah yasa na shiga ɗakin sirri
ba na ga alamar matsala da sai ya ya kenan? ”
“Daddy nace ka yi haƙuri ba zan sake ba” Bobby ya faɗa a shagwaɓe ya na mai ɗagowa ya kalli
mahaifinsa.
Daddy ya ja wani huci ya ce “zan baka wasu ɗalasamai da za ka yi bita kafin lokacin da za a ida
naka rantsawar,ban so a samu matsala Bobby .Abokan ka ga shi nan sun shiga gaban ka,sai
sun fi ka saurin samun matsayi”
“Daddy ni fa ba wani son wannan abun nake ba”
“To ka manta da Anita kawai!” Daddy na faɗa ya miƙe tsaye,Bobby ya ce “No Daddy ina sonta
sosai” murmushin gefen baki kawai Daddy ya yi .
Bobby ya shiga ɗakinsa ya yi wanka,ya canza kaya.Kwnonking aka yi ya bada izini,Janash ce
ta shigo riƙe da tray .Kan ƙaramin table ta ajiye masa ta ce “ga abincin ka nan,Madam ta ce na
tabbatar ka ci sosai”
“Fita!” shi ne kawai abin da ya furta,Janash ta fice da sauri.
Wayarsa ya ɗauko ya yi danne-danne sannan ya kara a kunne“Mamyyyy!” ya faɗa kamar zai yi
kuka,can ɓangaren ta ce “ya ne Bobby? Ka ci abinci?”
“Ina ki ka tafi ba tare da na sani ba?”
“Wajen meeting ,ba zan dawo ba sai dare ya yi sosai”
Ya furzar da iska ya ce “okay! Na ji!” ƙittt ya kashe wayar .
Abincin ya ci bisanin ya fara aiki a system ɗinsa,a haka har dare ya tsala sosai a gajiye kwana
ya ɗauke shi.
Ƙarfe biyun dare agogon Japon ta buga,a lokacin da kowa ke kwance ya na bacci su Daddy
kuwa farke suke su na shagalin murnar samun wasu members.
Fadeel da Kameel tamkar wasu sarakai haka aka yi ta gaishe su.Kalolin jus kuwa babu kalar da
babu wanda ainahi ana sarrafa su da jinin bil'adama.
Zoben tsafi aka baiwa kowanensu ya saka a yatsan tsakiya na hagun bisanin taron ya watse.
Washegari
Daddy ne tsaye kan Bobby da ke ta sharar bacci.A hankali ya fara bubuga kumatunsa ya na
kiran sunan shi,Bobby ya yatsina fuska ya na mai buɗe ido.
Daddy ya sakar masa da murmushi,“tashi ka yi wanka ina son kai ka wani wuri”
Bobby ya yi wani tashi da sauri ya shiga toilet,a nutse ya yo wanka ya fito.Cikin suit farare ya
shirya kafin ya je can falo inda Daddy ke jiransa.
“Bonjour la famille !” Bobby ya furta,Mamy ta ce “Morning Babyna” ya yi mata kiss a goshi ya ja
kujera ya zauna,Janash ta yi saving nasu.
Bayan sun gama Daddy da Bobby suka fito,direba ya ja su a mota.Tafiya mai nisa suka yi
kamar za su barin gari bisanin su isa wani ƙaton waje wanda aka yi masa doguwar ƙatanga
kamar ta gidan fir'auna.
Ƙaton gate ɗin aka buɗe,“wooo! ” Bobby ya furta saboda aljannar duniyar da ya gani.Kusan
unguwa guda ce Daddy yasa aka tsara masa haɗaɗen gida mai game da masana'antar shi.
Ma'aikata ne birjit ta ko ina,baƙaƙen fata sun fi yawa sai aiki suke tuƙuru.Duk tsayawa suka yi
su na gaishe da su Daddy,cike da tausayi Bobby ke kallonsu har da mata da ƴan mata.
“Kar ka wani tausaya masu kuɗi suke so,duk yarinyar da ka gani nan to iyayenta ne suka
kawota don yi aiki a biya su ” Daddy ya faɗa ya na mai jan hannun Bobby ya fara zagaye da shi.
“Amma Daddy su matan bai kamata ace su na aikin ƙarfi ba,wai su na ma cin abinci kuwa?”
“Akwai ma'aikatan da kawai aikinsu girki ne,wasu kuma wankin kwanoni.Maleek?” Daddy ya
ƙwala kiran wani saurayi,da gudu ya ƙaraso “ka kai Bobby ko ina na wajen nan ,zan shiga daga
ciki ai ka shirya komai ko?”
Maleek ya ce “Eh yalaɓai tun jiya da ka shaida min za ka zo na shirya komai”
Bobby ya bi bayan Maleek,ya na sake nuna masa wasu wuraren.
Daddy kuwa katafaren sashen ya nufa ,ya na buɗe ƙofa ya hangeta zaune kan gado cikin
shigar kaya shara-shara.Ya lumshe ido ya na jin wani sanyi a ransa, Babyn ta haɗu sosai.Ta na
ganinsa ta fara fari da ido kamar yadda Maleek ya shaida mata don saye zuciyar shugaban
nasu. Daddy bai wani ɗauki lokaci ba suka fara masha'ar shi da yarinyar da a haife ya haifeta.Wannan
shi ne halin Daddy holewa da ma'aikatan shi wanda musamman ya ɗauki Maleek aiki don duba
masa wacce zai rinƙa holewa da ita a duk ƙarshen mako.
Bayan ya gama biyan buƙatarsa