Showing 18001 words to 21000 words out of 25987 words

Chapter 7 - Yan Kungiyar Asiri Book Complet by Mrs Sadauki

samun
lafiya in Allah ya so.

Domin samun wannan littafi 400 kawai za ki biya na saka ki group +22795045822
[23/07 à 14:41] MRS SADAUKI : *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*



```MRS SADAUKI```✍

FCWA ☀️


*Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban
buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take
+22795045822.
*Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa
kuma arashi ne*


*Page 15_16*

```Assalamu alaikum jama'a,ina yi ma kowa fatan alkhairi saboda yawan ƙorafin cewa babu kuɗi
a yanzu a rage mana.To zan bayar da book one a free na *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI* book 2
kuma za ku biya 200 kacal ga masu buƙata su yi min magana pc.
Katin MTN ko transfer,ƴan Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 200f```

Jikin Bintu ya fara yin wata irin kyarma, kamar ranta zai fita haka zuciyarta ke wani bala'in
bugawa.Ƙiiii! Ya rinƙa janta har suka isa wani ɗaki,daidai nan hasken ya dawo ya kuma sakar
mata baki.A wahalce ta juyo ta dube shi,Kawu Mansur ne tsaye ƙiƙam ya na aika mata wata
muguwar harara bisanin ya yi gaba ya ɗauko wata system. “Ki buɗe matakan tsaron da ke ciki,PA ya tabbatar min ke ɗaya ce ki ka san sirrin ubanki” Kawu
ya faɗa cikin bayar da umarni.
Bintu ta haɗiye wasu yawu,tsoro take ya yi mata wani abu hakan ya sa jiki na kyarma ta fara
buɗe duk wasu abubuwan da ke da code.Ta ɗago hawaye sai zuba suke yi mata,cikin rawar
murya ta ce “na buɗe” Kawu Mansur ya wangale baki ya na mai ɗauke system don shi bai san
komai ba da ya shafi boko.

“Fice ki ban wuri ki ka wani tsaya ki na kallona da shegun idonki” ya daka mata tsawa.Bintu har
tuntuɓe take wajen fita,direct ɗakinsu ta wuce ta na mai fashewa da wani marayan kuka.


Hankali tashe Zahra ta farka daga bacci,“lafiya mike damun ki?”

“Kawu Mansur ne shikenan duka dukiyar mahaifinmu zai kwashe” ta faɗi haka cikin kuka.
“To mine ne na kukan? Kin ga don Allah ki bar zancen dukiya,ina ce dai wanda ya tara ta ma ya
mutu ya barta balle mu da gado ne za a bamu” Zahra ta faɗa ta na jawo Bintu a jiki,ita kuwa sai
kuka take kai kace yanzu aka shaida mata mutuwar Abba.


Washegari da kumburar fuska Bintu ta tashi tare da matsanancin ciwon kai.Halilu ya shigo har
ɗaki domin dubata,ta wani yi banza da shi .
“Mene ne ya saka ki kuka? Zahra ta ce min ba ki da lafiya” ya furta ya na mai zama bakin bed
tare da ɗan jan zanen da ta rufa da shi.
“Ka je ka tambayi maci amanar ubanka” ta faɗa sautin muryarta bai fita sosai.Halilu ya rumtse
ido jin furucinta,“mi shi Baba ɗin ya yi miki? Na san dai ba zai dake ki ba”
“Don Allah ka fita ka bar ni ban son surutu”
“To ki tashi ki sha magani”
“Ban sha”
“Don mi?”
“Saboda jikina ne ba na uban wani ba”
“Bintu ni ki ke zagi?”
“In akwai fiye ma da haka zan yi”
“To na ji! Amma ki daure ki sha maganin,ko kuwa na kai ki asibiti ”

Bintu wacce tun shigowarsa ta rufe ido,ta yi saurin buɗe su ta na kallonsa kafin ta ce “kai a su
wa?”
“Mijin ki” Halilu ya bata amsa,ita kuma ta ja dogon tsuki bisanin ta juya masa baya.
Fita ya yi ya sawo maganin ,cikin kofi ya jiƙa shi sai da ya narke duka sannan ya yi wa Bintu
ɗuren shi.Duk yadda ta so ta ƙwaci kanta hakan ya cuttura saboda ƙarfin namiji da mace ba
ɗaya ba.Babu jimawa gumi ya fara keto mata,a sannu ciwon kan ya fara sauka.Ta ja ajiyar
zuciya ta na mai sake yin lamo a ƙirjinsa don har yanzu bai saketa ba. Tafin hannunsa ya kai kan goshinta ya goge zufar,ta buɗe idonta masu kama da mai jin bacci ta
saka su cikin nasa.Ya ɗan hura mata iska ya ce “ya jikin?” ta turo baki ta na hararen shi.Halilu
ya ɗan ja ajiyar zuciya ya ce “Bintu ban so ki na tayar da hankalin ki akan dukiya,na yi miki
alƙawarin ba zan taɓa bari ta salwanta ba.Ni ke nake so,ban damu da wasu kuɗi ba don haka
da zarar na kammala karatuna duk wasu abubuwa za su dawo ƙarƙashin kulawata kin ga
shikenan sai na mayar miki da komai”


Da sauri ta yunƙura tare da janye wa daga jikinsa,“bakin ku haɗe kai da mahaifin ka.Kamar ku
na jiran mutuwar Abba duk ku ka dawo gidanmu alhalin babu wanda ya ce ku zo.Mama ba ta
lafiya amma tsabar mugunta ta Kawu a gabanta yake cutar da mu, wannan ya saka ta
gwammaci ta koma zaman asibiti.Na tsane ku dukan ku ban son ku,ban san ma ya aka yi mu
ka haɗa alaƙar jini da ku ba”

“Kenan ba ki yarda da ni ba? Ko kuwa soyayyata ce har yanzu ba ki gamsu da ita ba? Bintu
dube ni cikin ido”
Ta ɗago suka haɗa ido,sai kuma ta yi saurin sunne kai saboda ba za ta iya jurar kallon cikin su
ba har wata zaiba-zaiba take gani da kuma wani abu mai kashe jiki.
“Ina son ki,kuma in sha Allah babu wanda ya isa ya cutar da ke ciki kuwa har da shi Kawun” jin
furucinsa ya saka ta sake dubansa ya jinjina mata kai.


Wani ɗan sanyi ta ji ya ratsa sashen zuciyarta,duk da ba ta yarda ɗari bisa ɗari ba amma ta
yarda da soyayyar da yake yi mata.
“Lilu....” sai kuma ta yi shiru,shi kuwa wani murmushi ne ya ƙwace masa ba ƙaramin daɗin
sunan Lilun nan yake ji ba.Cikin zaƙuwa ya ce “mine ne Bintuna?”
Sai da ta yi ɗan jimmm sannan ta ce “da gaske ka na sona? Sannan za ka iya zama da ni a ko
wane irin ƙuncin rayuwa?”


Sai da ya riƙo tafukan hannunta sannan ya dube ta cike da kulawa ya ce,“Babu wani hali da
Bintu za ta shiga wanda Halilu ba zai zauna da ita ba,da ace za ki zama kuturwa,makauniya
kuma kurma to ki saka a ranki ɗigo ɗaya na soyayyar da Halilu ke yi miki ba zai ragu ba”
Bintu ta zumɓuro baki ta na wani hararen shi,ya tambaye ta “mi na yi kuma?”
“Sai wani kiran kan ka kake da sunan ubanni,kawai ka ce Lilu ya fi kyau da daɗi” cike da yarinta
ta yi maganar,wanda hakan ya saka shi yin dariya har sai da haƙoransa suka bayyana.
Bintu ta yi kasaƙe ta na kallonsa,ba ta taɓa sanin ya na da kyau ba sai yanzu,sai kuma ta kawar
da kai.


Halilu na shirin yin magana Kawu Mansur ya shigo ɗakin.
“Uwar mi kake yi nan? Ke kuma ki tashi ki yi shirin makaranta don ubanki tunda ba kuɗin banza
na zuba ba”Kawu ya faɗa ya na hararenta.



“Kawu ba ta da lafiya ne,yanzu nan ta sha magani”cewar Halilu .
“Ka je can falo ina son ganin ka,ke kuma na baki minti goma ki shirya ” Kawu na gama faɗa ya
fice.



Cike da tausayi ya dubeta ya ce “ki tashi ki shirya kin ji? Ni zan kai ki da kaina ” Bintu ta jinjina
masa kai.Ya miƙe ya fita,ta bi bayansa da kallo bisanin ta je ta yi wani wankan.
Bayan ta fito ta je kitchen ta samu ruwan zafi ta gasa idonta,duk kumburin ya baje.Cikin
uniforme ta shirya,ta zo falo ta yi zaune ta na jiran fitowar Halilu don tuni su Zahra sun tafi.

Daga inda take zaune ta na jiyo sautin muryar Kawu,alamu sun nuna masifar ce da ya saba
yake yi wa Halilu.Ta nan zaune ya fito ransa a ɗan ɓace,su na haɗa ido ya sakar mata
murmushi ya ce “tashi mu tafi” ta take masa baya har zuwa mota.
Shi ya tuƙa ta ya kaita makaranta,a hanya sai hirar soyayya yake yi mata ita dai sai dai ta
mayar masa da martanin murmushi.





HABIBA

Tun da a ka sa ta makaranta ta fara wayewa,don yanzu tsakanin ta da hijabi sai in za ta yi
sallah.Hullar gashin doki kuwa ita kanta ba ta san rabon da ta cireta a kanta ba,kamar ibada
kullum ta na ga kanta.
Ƙawarta guda duk faɗin makarantar,sunanta Mardeeya ƴa ce ga shugaban ministan kuɗi.Abotar
tasu ta samo asali ne tun ranar da ita Mardeeyar ta fara zuwa aji babu wuri sai ita Habibar ta yi
mata nuni da kusa da ita shikenan suka ƙulla ƙawance.



Zaune suke su biyu,Habiba ta dubeta ta ce “yanzu da gaske ba ki iya girki ba? To in ki ka yi
aure wa zai dafa wa mijin ki abinci?”
Mardeeya ta tuntsire da dariya ta ce “na yi miki kalar shiga kitchen? Hum! Ai ni yanzu haka ko
wanka zan yi sai mai aiki ta cika min bawon wanka ta zuba kalolin sabulu da turare.Mijin da zan
aura kuma ba ɗan nan ƙasar ba ne,Balarabe ne a facebook mu ka haɗu da shi”
Habiba ta waro ido ta ce “yanzu yadda ki ke baƙar nan sai Balarabe ya aure ki?”
“Ai sun fi son baƙar fata,ƙarshen week ɗin nan zai zo gidanmu ina gayyatar ki fatan ba za ki ƙin
zuwa ba?” Mardeeya ta faɗa ta na kamo hannuwan Habiba alamar roƙo.
“Zan zo mana,dama ina son zuwa gidan ku ke ce ba ki bani ƙofa ba”
“Ko yanzu ki ke son zuwa sai mu tafi ai ba wani abu ba ne” cewar Mardeeya ta na mai tashi
tsaye,Habiba ta washe baki ita ma ta miƙe.


Inda ake ajiye motoci suka nufa, Mardeeya ta buɗe wata latsetsiyar farar mota ta shiga ,Habiba
ta zauna a gaba.
Cikin slow take driving ta na shan chocolat yayin da kuma bakinta ke bin waƙar Dadjou,a haka
har suka isa katafaren gidan wanda a ƙofaf gidan har da jami'an tsaro.

Aka wangale gate ta cinna hancin motar ciki,ta samu wuri ta yi parking sannan suka fito.
Duk kurin da Habiba take da murnar su ma yanzu masu kuɗi ne sai ta ashe Kawu Mansur
talaka ne in aka auna shi da mahaifin Mardeeya.



Cikin falon kalolin kugerun zama sama da guda biyar,ƙaton falo ne irin sosai ɗin nan.Tsabar
ƙauyanci ya saka Habiba yin tuntuɓe ji ka ke tassss! Ta ture faux du fleure .
“Fatan ba ki ji ciwo ba?” Mardeeya ta tambayeta,Habiba ta girgiza kai a zuci ta ke cewa ‘oh! Ita
ba ta damu da abun da na fashe ba ma’

“Ga ɗakina na nan” Mardeeya ta katse mata tunanin zucin,ta buɗe ɗakin ta shiga Habiba ta
mara mata baya ta na mai cewa “mi ya sa ba a baki ɗaki can sama ba sai a nan ƙasa?”
“Ɗakin Dad da kuma Ya Kameel ne kawai a sama hatta Momy a ƙasa take zaune” Mardeeya ta
bata amsa ta na mai cire takalmin ƙafarta masu tsini.
Habiba na shirin yin magana idonta ya yi tozali da ƙaton hoton wani Guy baƙi suluk,sai dai sajen
da ya ajiye shi ya ƙayatar da fuskar tasa.
“Ya Kameel ne wannan,shi ne babba gidanmu,bayansa an haifi wasu duk sun mutu.Ni ce aka
haifa ta ƙarshe kuma ni ce auta”
Habiba ta waigo ta dubeta,ita kuma ta ɗaga mata gira tare da cewa “Yes! Ko ya yi miki ne ki na
son shi?”
Habiba ta ce “mi zai yi da baƙauya, wannan da ganinsa ƴan matansa ba su ƙirguwa”
Mardeeya ta ce “ai kuwa kamar kin sani ,don yanzu haka maganar da nake yi miki kusan kullum
sai sun zo nemansa.Wasu ma har gyaran ɗaki suke yi masa,akwai kuma masu kwana a gidan
nan duk domin samun soyayyarsa ”


Wani baƙin ciki ne ya rufe zuciyar Habiba wanda ba ta san dalili ba,kawai sai ta taɓe baki ta na
mai ɗan ƙarewa ɗakin kallo.Komai na cikinsa pink ne tun daga bed ɗin har labulaye da kuma
kujeru biyun da ke ajiye.
Takalmi ne kaloli a jere ras a cikin ƴar kwabarsu,haka ma hullunan mèche na gashin doki.Kan
dressing mirror kuwa ba a magana,kai kace wani kantin kayan kwalliya da turarruka.


“In kin ga abin da ya burge ki kawai ki ɗauka” Mardeeya ta faɗa ganin yadda Habiba ta baza na
mujiya ta na kallo.
“Ina son kayan kwalliya ,sai dai ban iya ba”
“Hhh! Ai babu wuya bari na yi wanka sai na nuna miki yadda ake yi” ta na gama faɗa ta shiga
toilet ta fara wanka,babu jimawa ta fito ƙugunta ɗaure da towel fari sol.

“Ki shiga ki yi wanka,sai na yi miki kwalliyar”

“Mardee kar fa aje ayi min ta ƙi yi min kyau”
“Dalla Malama ki shiga kawai ki yi wanka in ba ta yi kyau ba ki ce ni ba Mardee Mohan ba ce” ta
faɗa har da wani buga cinya irin yanda indiyawa kan yi, Habiba ta tuntsire da dariya bisanin ta
shiga ta yin wankan.


Bayan ta fito ne Mardeeya ta tsantsara mata kwalliya,kai kace wata amarya.Cikin kayanta ta
zaɓo wa Habiba wata shuɗiyar doguwar riga.Kamar wata ƴar tsanar roba haka ta fito ta yi tsaf
da ita,hotuna ta yi mata bisanin ita ma ta shirya kanta.
“Yadda ki ka yi kyawun nan ina mai tabbatar miki in mu ka je gidan shaƙatawa sai an samu
kyakkyawan saurayi ya wud da ke!”

“Mardee kar ki sa kaina ya fara hayaƙi mana”
“Allah gaskiya nake faɗa miki ”
“To ina za mu je?”
“Mu je mu sha crème glacée”


Direba ya kai su wajen shan crème glacée ɗin.Su Na zaune su na taɓa hira,Mardeeya sai bata
labarin yadda suka haɗu da Balarabenta take a haka har suka ida suka fito.
Su na shirin shiga mota wani saurayi ya yi saurin ƙaraso wa gun su.Sallama ya yi masu suka
amsa,ya dubi Habiba ya ce “don Allah in babu damuwa ina son lambar wayar ki”
“Banda lamba” ta basa amsa.
“Ba dai za a bani ba,to a sayar min ko nawa ne zan saya”
Ta ɗan saki murmushi ta ce “tukunna dai ban fara riƙe waya ba,karatu nake”
Saurayin ya dubeta,don Habiba ta kai shekara sha takwas.
Ɗan waigawa ya yi,ya ce “in babu damuwa to ku jira na je na sayo miki wayar na kawo miki,don
muddin ki ka suɓuce min na shiga uku”
Ba Habiba ba hatta Mardeeya sai da ta dube shi,haɗaɗen gaye ne irin sosai ɗin nan.


“Ok bari mu shiga mota mu jira ka” Mardee ta faɗa,ya yi murmushi ya ce ya “na gode” wata jar
mota da ke parker a gun ya shiga,su ma suka shiga suka zauna.


“Kin gansa kyakkyawa da shi”

Habiba ta taɓe baki a zuci ta ce ‘ai bai kai Kameel kyau ba’ a zahiri kuwa cewa ta yi “mun dace
da shi ne?”
“sosai ma kuwa”
“Ni kuwa bai kwanta min a rai ba”
“Ki ƙara masa lokaci dai,duka fa yanzu ne kuka haɗu”
Su na nan zaune ya dawo,ya ƙwanƙwasa glass dakyar Habiba ta fita ta karɓi wayar bisanin su

yi tafiyarsu.



★JAPON


Malami na musamman ne ke koyar da Bobby abubuwan da suka shafi Musulunci.Ba wai don ya
yi aiki da su a karan kansa ba ne a'a,kawai dai ya na koyo ne saboda ya ci nasarar samun
Anita.
Sosai ya maida hankali wajen koyon babbaƙu,bai ɗauki dogon lokaci ba ya fara iya tada baƙi
tare da koyon karatun Alkur'ani mai girma.
Shi da Anita kuwa kullum su na maƙale a waya,tun ranar da ya je gidansu bai sake zuwa ba.




Garin yau ya tashi da hazo,luf-luf ko ta ina hadari ne ya gangamu ya yi baƙi ƙirin.Bobby kuwa a
tsanake ya ke ƙara gyara ɗakin nasa saboda ziyara da Anita za ta kawo masa.Flowers ya zuba
kan gado ya rubuta kalmar I LOVE YOU da babban harufa.

Komai ya shirya shi tsaf zuwanta kawai yake jira.Ya na nan zaune ya ji knowking,da mugun
sauri ya je ya buɗe.Anita ce sanye cikin riga da wando ,ta harɗe gashin kanta a tsakiya.
Blue idonta masu kama da na mage ta ƙura masa,Bobby ya ja ya bata hanya ta shigo sannan
ya rufe ɗakin da key.


“Waooo!” ta furta ta na kallon kwalliyar da ya yi wa ɗakin kamar ba hotel ba.Ya rungumeta ta
baya ya ce “Oui je t'aime ! Ina sonki my Ani! ” dariya ta yi ta ce “ni ma ina sonka”

Ya sake ta,ya nuna mata wurin zama ta maƙe kafaɗa ta ce “a samar ƙafar ka zan zauna”
“oh! Hakan ya yi min daɗi” ya furta ya na mai zaunawa ,Anita ta hau kan cinyarsa.
Jus ya zuba a kofi biyu,ya miƙa mata ɗaya ya ɗauki ɗaya.
“Shikenan ka manta da ni,shiru ka ƙi zuwa wajen sati biyu kenan.Maman har sai da ta tambaye
ni ko lafiya ?”

“Lafiya lau,ina nan ina ta fafutukar iya addinin Maman don ta bar min ke” Bobby ya faɗa.
Anita ta ce “Ka na nufin larabci ka ke koyo ko kuwa karatun?”
“Duka biyun”
Ta ƙura masa ido,bakin na ɗan rawa ta ce “dama har haka ka ke sona?”
Ya bata amsa da “Fiye da haka”

Anita ba ta san lokacin da ta yi saurin kwanto shi ba,ta na mai kai bakinta kan lips ɗinsa.Mai son

kuka an jefe shi da kashin awaki! Bobby kamar mai jira ya yi mata kyakkyawan masauki akan
ƙirjinsa....



Wacce ta shirya payement za ta turo 200 kacal ta wannan account ɗin 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo da shaida biya ta WhatsApp +22795045822 ƴan Nijar
carte Moov ta 200f
[24/07

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login