Showing 15001 words to 18000 words out of 25987 words
Chapter 6 - Yan Kungiyar Asiri Book Complet by Mrs Sadauki
shi ya yi dariya fita.
Zahra na fitowa ita ma Bintu ta shiga ta yi wankan,sannan suka shirya suka tafi islamiyya.
Ko da suka sauko tuni har Halilu ya sayo wani teddyn da murna Zahra ta ɗauke shi ta na cillawa
sama.
“Wai sai yaushe Mama za ta dawo?” Bintu ta tambaya.
Zahra ta ɗan tsaya da abin da take sannan ta ce “Sati ɗaya ta ce”
“Ciwon ƙafa ya ƙi ci ya ƙi cinye wa kamar wacce aka asirce” Bintu ta faɗa cike da damuwa.
“Zato zunubi ne” Zahra ta faɗa.
“To Malama na ji,yanzu dai zan kwanta”
“Ana shirin yin magrib ɗin?” Zahra ta tambayeta,ko dubanta ba ta yi ba balle ta bata amsa haka
ta yi kwanciyarta ba ta jima ba bacci ya ɗauke ta.
Sai bayan sallar isha'i Bintu ta tashi agajiye.Wanka ta fara sannan ta yi sallolinta ta fito ta ci
abinci sannan ta wuce wurin su Zahra da suke karatu ita da Habiba.
Washegari
Kamar yadda Kawu Mansur ya yi alkawari hakan ce ta kasance.Tun da safe ya tashi direba
suka je Joal,sai dai ga mamakinsa duk uban sammakon da ya yi akwai uwanda suka riga shi.Ko
wane cikin gizner sai ƙamshi ke tashi,da Kawu ya ga alhazzai sai da ya raina kansa.
Haka suka yi ta jira da ɗaiɗaya ake shiga har layi ya zo kan Kawu Mansur.
Kansa ya fara shigarwa ya buɗe baki da niyyar yin sallama sai kuma ya yi shiru sakamakon
aljannar duniya da ya gani.Ɗakin tarben client ɗin kai kace fadar Sarkin Makka tsabar haɗuwa
da kyau.
Can bisa wata kujera ya hangi wani baƙin mutum a zaune ya hakimce hannunsa riƙe da wata
ƙatuwar lula mai haske .
Muƙut! Ya haɗiye wasu yawu kafin ya ƙarasa,da hannu Mohan ya yi masa nuni ya na mai cewa
“ba a kallon cikin idona muddin ka na son tsira da ganin ka”.Kawu Mansur ya zauna kan capet
ɗin a gabansa,ya wani sunne kai.
Mohan ya ci gaba da cewa “mi ke tafe da kai?”
Kawu ya yi gyaran murya ya ce “dama aiki nake son ayi min kan wata yarinya....” kafin ya ida
Mohan ya ce “ta na da taurin kai ne,sannan duk da ƙarancin iliminsu na addini mahaifinsu ya
koyar da su yadda ake riƙe Tauhidi shi yasa bokan ka ya gagara aiki a kanta.Amma tunda ka zo
nan komai ya wuce ”
“Ina son a aika mata baƙin aljani wanda zai hanata shaƙat har sai duk dukiyar da ke hannunta
ta dawo gare ni” Kawu Mansur ya faɗa.
Mohan ya ce “ba ma tura aljani haka kawai sai da sharaɗin aure”
Kawu Mansur ya ɗago,da sauri ya mayar da kansa zuciyarsa na bugawa saboda ganin
kamannin Mohan ya canza daga nan bil'adama sak.
Cikin rawar murya ya ce “kamar ya aure?”
“Na ɗaura masu aure da aljanin,zai rinƙa amfani da ita kamar yadda ma'aurata ke yi har su haifi
yara” Mohan ya basa amsa ya na mai kallonsa.
Kawu Mansur ya washe baki ya ce “ai hakan ya yi don ina so a ƙarshe ya haukatar da shegiya”
Mohan ya ce “ƴar ɗan uwan ka ce ko?”
Kawu Mansur ya gyaɗa kai,Mohan ya ce “ok ka na iya tafiya”
“Ba ka faɗa min nawa zan bayar ba”
“Sai in na gama aiki ake biya”
Kawu Mansur ya fito zuciyarsa fara tasss.....
400 ne kacal za ki biya domin karanta littafi na ɗaya da na biyu na wannan littafin wacce ta
shirya za ta iya tura kuɗinta ta wannan account ɗin
3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank
Sai ki turo min da shaida biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin MTN na 400,ƴan Nijar
kuma carte Moov ko airtel ta 400f
[22/07 à 07:37] MRS SADAUKI : *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*
```MRS SADAUKI```✍
FCWA ☀️
*Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban
buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take
+22795045822.
*Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa
kuma arashi ne*
*Page 13_14*
Tamkar daren sallah haka Bobby yake ji.Tun da ya sauka a filin jirgi Léo ya zo ya tarbe shi ya
kaisa can inda zai zauna.Cikin shiga irin ta ƴan Pakistan ya shirya har da wani ɗora farin rawani
akai,sai kuwa ya yi kyau sosai.
Léo ya miƙa masa duk wasu takardu masu ɗauke da bayanai kan Anita ,sannan ya ce “ka kula
da kyau kamar yadda na shaida ma mahaifiyar Anita musulma ce,mahaifinta kuma Kirista ne
don zan iya ce maka ma kusan kowa ya san shi a garin nan saboda yawan wa'azinsa da kuma
taimakon da yake raba wa al'umma”
Bobby ya saki ɗan murmushi ya ce “kar ka damu Léo duk zan kula,salamu aleykum! Shi ne
gaisuwar musulmi ko? ” Léo ya jinjina kai alamar eh,Bobby ya ci gaba da cewa “Mohamad shi
ne wanda suka fi so duk duniya,saboda shi ne shugaban annabawan su” Léo ya ce
“annabawan mu dai! Ya na gaban Annabi Musa ” Bobby ya ɗage kafaɗu ya ce “sunan fa ina Bayahude ne ,amma da za ka yi min tambayoyi kan
annabinmu ban sani ba” Léo ya ce “don mi?” “saboda ni ban yarda da ko wane irin addini ba”
Bobby ya basa amsa ya na mai ɗora baƙin gilashi a fuska ,da sauri Léo ya cire shi ya na mai
cewa “no! Kar ka saka shi” “ok mu je ka ajiye ni”
Harabar hotel ɗin suka fito,Léo ne ya tuƙa su har zuwa wani haɗaɗen gida mai zagaye da
furanni.
“Ka sauka ka ƙwanƙwasa,zan jira ka a nan”cewar Léo .
Bobby ya fita daga mota ya je ya yi knowking ,an kai minti biyu kafin wani ya buɗe alamu sun
nuna dai mai gadi ne.
Bobby ya yi masa sallama bisanin ya tambaya “wajen Anita na zo” Cike da wata irin murna ya
buɗe masa gidan.
Bobby ya sa kai,mai gadin ne ya yi masa iso har cikin falon wanda ba ka jin komai sai sautin TV
ta na waƙoƙin Mohamed zain na larabci.
“Assalamu aley...” saurar sallamar ce ta laƙe a maƙoshinsa ganin Anita ta fito daga wani ɗaki
ƙugunta ɗaure da towel, ta na girgiza kai jiƙaƙen gashinta sai yawo yake.
Cak ta tsaya ta na kallon Bobby ,tun daga fararen fartun ƙafarsa har zuwa fuskarsa wacce ya
fidda ma gashin baki ya bar saje kawai.
Fuuu ! Ta koma ɗakin da fito,Bobby ya fara kiran sunanta “Anita? Anita?” amma ba ta saurare
shi ba.
Bai yi wani tunani ba ya bi bayanta,ya na shiga ya ganta tsaye ta baiwa ƙofa baya.
Ya ja wani dogon numfashi bisanin ya ida takawa dab da ita,kamar mai rawar sanyi haka
hannunsa ke kyarma wajen ɗora shi kan ƙunta ya juyo da ita .
Hawaye ne ya gani cikin idonta su na shirin zubowa.“Ki yi haƙuri in zuwana ya ɓata miki rai,laifin
ruhina ne da ya kasa sukuni saboda rashin ki a kusa da ni” cikin sanyin murya ya faɗi haka .
Anita ta kai hannu ta goge hawayen da suka yi nasarar zubowa kan kumatunta sannan ta ce
“Bobby mi ya sa? Na yi kewar ka sosai! Na yi ta jira da tsumayen zuwan ka shiru sannan ba ka
taɓa bani address ɗin ka ba .Har makaranta na je amma abu ɗaya suka faɗa min kai ɗan asalin
Israel ne....” kukan da ya ci ƙarfinta ne ya sa ta yin shiru.
Bobby ya jawota ya manna a ƙirjinsa ya na bubuga bayanta,haɓarsa ya ɗora bisa kanta ya ce
“Je t'aime pour toujours ! Ina sonki na har abada!” Anita ta ɗan ɗago kanta suka tsura ma juna
ido,a sannu a hankali suka dinga matsa fuskokinsu har Bobby ya yi nasarar sunkuyowa ya fara
kissing nata.
Sumbata ce irin ta an yi kewar juna,zuciyoyin su har wani bugawa suke da sauri.
Anita ta yi saurin janye wa ta na mai cewa “Bobby koma falo ina zuwa” ya girgiza kai haɗi da
jawota ya ci gaba da kissing nata.
Anita ta ƙara yin nasarar janyewa ta ce “Bobby Maman ta kusa dawowa daga aiki please ka
koma falo” ba don ya so ba ya dawo nan falon ya zauna.
Kamar minti biyar Anita ta fito sanye cikin doguwar riga blue.Ta yi kyau sosai,ta sakar masa
murmushi ta na mai buɗe frigine ta ɗauko masa ruwa ta tsiyaya a kofi ta basa.
Bobby ya karɓa ya sha,face da shi ta zauna suka fara taɓa hira.
Maman ce ta shigo falon bakinta ɗauke da sallama ,Bobby ya yi saurin amsawa da “wa'aleykum
Salam ya Ummi!”
Maman ta saki murmushi ta zo ta zauna,suka fara gaisawa yanayin shigar Bobby ta zata
musulmi ne.Sosai ta ji daɗi,“Anita ki kawo ma baƙon abinci mana” cewar Maman.
Bobby ya ce “Alhamdullah ! Ban jin yunwa”
“Masha Allah! Bari na bar ku to” Maman ta faɗa ta na mai wuce ɗakinta.
“Maman na son musulmi,burinta kullum na auri ɗan addininta.Alamu sun nuna ta yi zaton kai
ma ka na sallah ”
“Shi yasa na yi bincike kafin na tawo”
“Hum! Haɗuwar ku ta gaba doli ta gane kai ba ka da ma addini,don sai ta yi ta ma tambayoyi”
Bobby ya waro ido ya ce “ki ce tsugunne ba ta ƙare ba an saida Kare an sayi Biri”
Anita ta yi dariya ta ce “sosai kuwa don haka faɗi gaskiya tun yanzu”
“A'a zan yi tunani a kai” hira su ka dinga yi bisanin Bobby ya fito.
A waje ya tarar da Léo ashe bai tafi ba ya na nan dai zaune cikin mota.Har sai da suka hau titi
sannan ya tambaya “Ya ne? Babu dai wata matsala ko?”
Bobby ya furzar da huci ya ce “eh to! Babu sai dai fa doli na koyi wasu abubuwan na musulmai
muddin ina son in mallaki Anita ”
“Ai babu wani wuya zan nemo malami” da haka suka isa hotel ɗin,Bobby ya fita daga motar
yayin da shi kuma Léo ya yi tafiyarsa.
Wanka ya yi sannan ya yi commande ɗin abincin da zai ci,ma'akaciyar hotel ɗin ce ta
kawo.Bobby ya gyara zama ya na ci ya na taƙila waya har ya gama.Kiran Léo ya shigo,“ka
shirya ƙarfe tara na dare zan zo na ɗauke ka zuwa inda za a koyar da kai” shi ne abin da ya
faɗa ,Bobby kuma cike da murna ya amsa da “okay!”
★SENEGAL
Lokacin da Kawu Mansur ya dawo gida ya tarar duk su na cin abinci.Duk gaishe shi suka yi
banda Bintu da ta kawar da kai gefe ta na mai ci gaba da harakar gabanta.
Ya dubeta ya ce “ke ba za ki gaishe ni ba ko? ” duk da ta san da ita yake amma ba ta juyo ba.
Zahra ta ƙyafito ta da hannu “Bintu Baba na yi miki magana ” “ke wai mene ne? Ban son takura”
cewar Bintun ta na mai tashi ta nufi bedroom.
Kawu ya yi murmushin mugunta ya na jin burinsa na daf da ya cika.Wayancewa ya yi ya ce “
Allah ka shiryi Bintu duk yadda nake son yarinyar nan ta zama kamar ƴar uwarta ta ƙi,iskancin
nata sai ƙara gaba yake kamar wacce sheɗan ya yi wa fitsari akai” ya na gama faɗa ya wuce
ɗakinsa.
Ɓangaren Bintu zuciyarta har tafasa take tsabar takaici.Ƙululun baƙin ciki ya turniƙe mata
wuya,kan bed ta yi tsalle ta faɗa ba tare da kakaɓe shimfiɗar ba ko ambaton Allah.
Lummmm! Wani sanyi ke ratsa gangar jikinta,sam ba ta damu da yanayin ba har sai da ya nune
mata jiki ta koma liƙis.Kasa ta yi wa duk wata gaɓar jikinta sarƙa,kanta kuwa kamar mai mura
haka ta ji ya kume wuri ɗaya ya zama ɗingimeme.
Haka kawai idonta ya fara fitar da hawaye,a haka wani bacci marar daɗi ya yi awon gaba da
ita.Mafarkai ta fara na namun daji bisanin Kare ya dinga biyar ta da gudu har ya samu nasarar
cizonta a ƙafa.Firgigit! Ta tashi ta na mai dafe kai wanda zuwa yanzu mugun sara mata yake ga
kuma idonta har rufewa suke tsabar wani baccin da take ji.
Zahra ta shigo ta na mai cewa “ƙarfe tara fa har ta gota ko ba za ki je makaranta ba?”
“Bacci nake ji” cewar Bintu kamar za ta yi kuka.
“Ki tashi ki yi wanka zai sake ki”
“To jira ni kar fa ki tafi ki bar ni ” Bintu na gama faɗar haka ta tashi ta shiga toilet.
Bayan ta fito ta saka uniforme suka wuce islamiyya.Sam ba ta jin daɗin karatun kawai dai haƙuri
ne take har aka taso.Ko da suka zo gida ba ta yi wa kowa magana ba ta shige ɗaki,wani baccin
ta yi.Ba ta farka ba sai da Zahra ta tashe ta don yi sallah zhur.
Da kwandon masifa ta nufi ƴar uwarta,“tsabar baƙin ciki mutum na bacci ki zo ki tashe shi? Ina
ruwan ki don ban yi sallah ba ke dai ba kin yi ba?”
Jikin Zahra ya yi sanyi,sam ta kasa gane kan ƴar uwarta a yau.Haka ta fita ta barta, Bintu kuwa
rasa abin da za ta yi kawai sai ta fashe da kuka.Sai da ta yi mai isarta sannan ta je ta yi
wanka,dakyar ta gabatar da sallar ta fito falo.
Abinci ta zubo ta rakuɓe can gefe ta fara ci kamar mayunwaciya.Duk kowa sai da ya yi
mamakin yadda Bintu ta ci plate biyu na abinci har da hauda madarar bido.
Da lokacin makarantar marice ya yi,ƙememe ta ƙi zuwa nan ta shiririce wajen kallon tv.
Da dare,sun yi shirin bacci Zahra ta dubeta ta ce “Bintu don Allah ko za ki faɗa min abin da ke
damun ki? Gobe Kawu ya ce zai kai mu gun Mama ban so ta ga wannan canjin da ki ka samu”
“Babu abin da ke damuna,kawai na yi kewar iyayena ne.Kin ga ni bacci nake ji sai da safe”
Bintu ta faɗa ta na mai juya ma Zahra baya.
Ita ma a doli ta kwanta ta na saƙe-saƙen zuci.
Kusan ƙarfe biyun dare amma baccin ya ƙi ɗaukar ta,duk yadda ta so ya yi awon gaba da ita.Ta
juyo ta na mai facing Zahra wacce ita tuni baccinta take.Shiru Bintu ta yi bisanin ta lumshe
idonta,a nan take wata damina ta fara luluɓeta ta na sanyayya fatarta.A sannu a hankali ta fara
shiga duniyar mafarki mai kama da gaskiya. Tsikar jikinta ne ya yi wani mugun tashi, lokaci ɗaya ta fara jin amai yayin da kuma tsoro ke
daɗa aurenta.Ta yi baya za ta gudu kawai ta ji an cirata sama ƙafafuwan ta na yi reto a iska.Ihu
ta fara sai dai alamu sun nuna babu mai jinta don muryata sam ba ta fita.Timmm! Aka saketa ta
faɗi ƙasa,bakinta ya fashe jini ya fara zuba.Mumunar hallitar nan ta ga ta dumfarota,Bintu ta
rumtse ido ta na addu'ar Allah zare ranta ta huta da wannan masifa.
Hannunsa ta ji ya na shafar fuskarta,tamkar garwashin wuta haka tafinsa ke da mugun zafi.A
karo na biyu ta buɗe ido ta kalle shi,idonsa ɗaya da ke can kusa da kumatu ya kafa mata,yayin
da kuma yake wani juya ƙawon da ke gefe da gefen kansa.
Jikinsa duk gashi ne babu kyawun gani,murya na ɗan rawa ta ce “wane ne kai?”
“mijin ki ne?” ya bata amsa cikin wata ruɓaɓiyar murya ya na mai cire kayan jikinta.Tamkar
wacce aka yi wa allurar kashe jiki haka ta gagara hana shi har sai da ya biya buƙatarsa.Ihun da
ta fasa ne ya dawo da ita daga duniyar mafarkinta.Kalle-kalle ta fara bisanin da sauri ta sauka
ta nufi falo don ɗauko ruwa ,tsit kake ji babu motsin komai.Kitchen ta shiga ta ɗauko ruwan
,hannunta har rawa yake wajen buɗe murfin sai dai kash ta na ɗaga butalin sama kamar magie
ruwa ko ɗigo ɗaya babu.
Daga bayanta ta ji motsi,a tsorace ta waiga ta na fitar da wani sauti “haaann” sai dai wayam
babu kowa ta na shirin ajiye butalin ta ɗauki wani sai kuma ta ga ya cika da ruwa da sauri ta kai
bakinta ta shanye su tasss.
Innuwar mutum ta gani,a hankali ta fara ɗago kanta zuciyarta na halbawa sai dai kafin ta yi
tozali da fuskar mamallakin innuwar wutar gidan ta ɗauke ɗifff.Ta buɗe baki da niyyar yin ihu ta ji
wani kakauran hannu ya toshe mata baki tare da cewa “shiiit!”
Masu son ci gaba sai mun haɗe a PAID GROUP,400 ne kacal Hajiya .Ki tura ta wannan account
3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
Talla
Assalamu alaikum,ina masu fama da shafar aljannu ko sihiri to ku matso kusa ga wani book na
musamman da na ware domin wannan matsalolin a cikinsa akwai bayanai daki-daki akan ko
wace matsala sannan da addu'o'in ta.Akwai su a rubuce sannan kuma da wanda za a saurare a
samu waraka bi'izinillahi ta'ala.
*ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI* ƙirƙirarren labari ne mai ɗauke da darussuka,masu cutar hauka,ko
damuwa ko jinnu duk za ku samu addu'o'in ko wace matsala na karatun malumai da suka tsaya
suka zaƙulo ayoyin Allah daga cikin Alkur'ani na dangane da ko wace irin cuta.
Uwanda ba su iya karatu ba za su iya saurare ko kuma su bayar wani ya karanta masu cikin
ruwa.
A cikin wannan littafi na fitar da kalolin asiri uku wanda su ne aka fi samu.
Akwai masu fama da djinn ashiq bayyananne ko ɓoyayye irin wanda bai nuna alama ko kuma
ya tashi.Da yardar Ubangiji shi ma zan yi magana akai tare kuma da karatunsa domin