Showing 12001 words to 15000 words out of 25987 words
Chapter 5 - Yan Kungiyar Asiri Book Complet by Mrs Sadauki
da zai saka kaf ma'aikatana da su kansu ahalin gidan su dinga shakkata da
mugun tsorona”
“In dai wannan ne babu matsala an gama”
“Yauwa sannan ina son ka haɗa ni da wannan malamin Mohan”
“Sai wani sati mai zuwa yake dawowa ” boka ya basa amsa.
Kuɗi ya basa kafin ya koma gida,shi kuwa boka tun a daren ya fara aiki...
★JAPON
Da sassarfa Bobby ya iso gare ta,“Salut!” ya furta ita ma ta mayar masa da “Hi!” ya ɗan
murmusa bisanin ya tara mata hannu.Sai da ta kalle shi da ƴan ƙananan idonta bisanin ta saka
nata hannunta.A hankali suka fara tafiya hannunsu sarkaye da na juna,Bobby ne ya ce “kin zo
kin tsaya kamar wata baƙuwa” “Eh to mice ce ? Ban san kowa ba a nan sai wanda ya gayyace ni kuma shi ne nake kira”
“Kenan ni ba ki sanni ba?” Bobby ya yi mata tambayar ya na mai tsayawa da tafiyar,ta kalle shi
cikin ido kafin ta ɗan girgiza kai.Ya kama haɓarta ya ce “yauwa ko ke fa! Sunana Bobby ke
kuma fa?”
“Sabitry”
“Jolie nom! Nice name” ya furta daidai nan suka shigo ɗakin show ɗin.
“thank you”
Wurin zama suka samu suka zauna,sai ƙoƙarin kiran lambar Fadeel take yayin da shi kuma
Bobby ke ɗan baza ido ya na kallon masu rawa.
Muryarta ya ji “Tu veux danser?/Ka na son yin rawa ne?”
Ya ɗan yi murmushi ya ce “pourquoi pas? Surtout avec une charmante comme toi/mi zai hana,
musamman da kyakkyawa irin ki”
“ok allons-y” ta faɗa tare da tashi tsaye,Bobby ya miƙe shi ma tare da jan hannunta suka fara
yin rawa irin a hankalin nan su na kallon juna cikin ido.
“An taɓa faɗa miki ke ɗin kyakkyawa ce?”
“Hum! In ma ba a taɓa ba ai ga shi kai ka faɗa”
“Gaskiya ki na da kyau, musamman idon ki am...da kuma laɓan ki” Bobby ya faɗa ya na mai
ƙura ma lips ɗinta ido,Sabitry ta ce “Allah sa dai wannan zancen naka har zuci yake”
“Don mi?”
“Saboda dayawan maza mayaudara ne, musamman in su na son kwantawa da mace”
Bobby ya ɗan saki murmushi ya ce “ba cewa na yi ina son ki ba fa! Kawai na ce ki na da kyau”
“Daga ƙarshe kalmar so ɗin ce za ta biyo baya”
“Shikenan mu yi dai rawar,ko kin gaji ne?”
“In na gaji mi za ayi?” ta tambaye shi idonta ƙur cikin nasa.
“Eh to! Na kai ki ɗaki ki kwanta”
Wata dariya ta yi ta na mai kai hannunta kan fuskar shi ta ce “wai gaske? Hutun zan yi ko kuwa
dai?” sai maƙe masa ido ɗaya.
Bai ce mata komai ba ya ja ta zuwa wani ɗaki,kai kace wata matarsa haka suka holewarsu.
Bobby ya dubi Sabitry ko ƙyaftawa bai yi,“ya dai irin wannan kallon?” ta tambaye shi.
“Ina mamaki ne kawai yadda ki ka jure min” dariya ta shiga yi kamar mahaukaciya kafin ta ce
“Wai da gaske,halan budurwar ka raguwa ce”
“No matata dai”
Da sauri Sabitry ta dubi hannunsa sai ta ce “ya aka yi ban ga zoben aure ba?”
“Sai nan gaba za mu yi aure ” ya bata amsa.
Sabitry ta ɗauki jakarta dama tuni ta kimtsa ta tashi ta fita,Bobby ya yunƙura zai tashi wayarsa
ta ɗau ruri.
Daddy ne,ya na ɗagawa ko magana bai yi ba Daddyn ya ce “Bobby duk rintsi ka nemo yarinyar
nan da ka kwanta da ita,in kuma ku na tare kar ka bari ta gusa gani nan tafe” ƙittt ya kashe
wayar,zuciyar Bobby ce ta fara dakan tara-tara.
*Uwanda suka shirya za su iya fara yin payement don free page na dab da ƙarewa 400 ne kacal
za ki biya kuɗin karatu book na ɗaya da na biyu ,ki tura ta wannan account ɗin*
3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank
Sai ki turo min da shaida biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin mtn,ƴan Nijar kuma
carte Moov ko airtel ta 400f.
MRS SADAUKI
[20/07 à 17:10] MRS SADAUKI : *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*
```MRS SADAUKI```✍
FCWA ☀️
*Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban
buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take
+22795045822.
*Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa
kuma arashi ne*
*Page 11_12*
Da mugun sauri Bobby ya fita,duk da bai san taƙamaimai mine ne ba amma ya san Daddy ba
zai kiransa kan banza ba.
Cak ya tsaya ganin Sabitry na fizge-fizgen ƙwatar kanta gun Kameel da ya yi mata wani mugun
riƙo.
“Mais lâche moi! Ka sake min hannu!” shi ne abin da take ta faman faɗa,kowa na ɗakin taron ya
tsaya cak ya na kallonsu.
Muƙut! Bobby ya haɗiye wasu yawu bai ma iya furta komai ba.Fadeel da ke can gaban Camera
ya ga abin da ke faruwa ya fito da sauri,can ɗakin suka koma su duka.
“Sabitry dama duk abin da ki ke da tsafi ki ke amfani ban sani ba?” Fadeel ya yi mata tambayar
ya na mai dafe goshi.
Kameel ya ce “Allah ya yi sa'a ta na fitowa na ci karo da ita,ba don haka ba da shikenan ta saka
rayuwar abokinmu cikin cakwakwali”
“Wai don Allah mine ne ke faruwa,kaina ya ɗaure! Daddy ya kira ni ya ce kar na bari ta gusa ku
kuma ku na wani zance”Bobby ya tambaya ya na son samun haske.
“Bobby wannan yarinyar da ka ke gani muguwa ce,za ka iya kiranta da BOKANYA kai
tsaye.Duk ƙarfi da juriyar da aka ce ma ta na da to tsafi ne,da zarar ta kwanta da namiji babu
shi ba zaman lafiya sannan ƙarfin jikinsa za ta dinga tatsa su na saffara abubuwan tsafinsu”
Kameel ne ya basa amsa.
Bobby ya yi masa wani kallo irin kamar ban gane ba, wannan ya saka Kameel ci gaba da cewa
“ni ma na fahimci haka ne saboda ƙarfin iko da nake da a duniyarmu” kafin wani ya sake
yunƙurin yin wata magana aka turo ƙofa.
Daddy ne,fuskarsa ta yi jawur.Wani gigitacen mari ya ɗauke Sabitry da shi wanda ya saka ta
faɗuwa ƙasa wanwars ba ta shirya ba.Gashin kanta ya cakumo ya ɗagota sama,kuka ta fara ta
na basa haƙuri.Bakinta ya taɓe ya saka yatsansa manuni wanda yake ɗauke da zoben tsafi a
ciki.Kamar yadda gashi in ya shiga cikin ruwa ko mai yake yin sama haka wani baƙin hayaƙi ya
fara fita daga bakin Sabitry ya na shiga zoben Daddy.Can ya yi yarɓi da ita ya na mai cewa “Ƴar
iskar yarinya! Ke kin yi kaɗan ki taɓa rayuwar yarona wanda tun kafin ya zo duniya nake kula da
duk wani motsinsa saboda mugayen mutane irin ki” ya gama faɗa ya fita.
Jiki babu ƙwari Sabitry ta fice,yayin da su Kameel kuma suka samu kujeru suka zauna.
Fadeel ne ya ce “ban taɓa sanin da tsafi take aiki ba,sai yau.Shi ma ɗin don yanzu ina cikin
ƙungiya ne”
“Kenan in mutum na cikin ƙungiya ya na iya gane duk wani mai amfani da asiri ko tsafi?” Bobby
ya tambaya.
“Eh sosai! Da ace Kameel bai ganta ba da shikenan ” cewar Fadeel.
“To ai ni ma ina cikin ƙungiyar ko?” Bobby ya faɗa,a tare suka kece da wata irin dariya bisanin
Kameel ya ce “kai fa dutsen Barclay bai karɓe ka,wanda kuma shi ne yake babban jigon
ƙungiya ”
“Sai nan gaba sannan ka shigo sawun mu ka ƙara haƙuri ”
Bobby ya ɗan taɓe baki ya ce “ni fa ban wani damu da harakar tsafi ba,kawai don ban son
baiwa Daddy kunya ne”
“Ko ma dai mine ne mu je mu yi shagali” cewar Fadeel tare da miƙewa,su ma suka mara masa
baya.
Bobby wuri ya samu ya zauna kawai,sosai ya yi mamakin ta yadda aka yi har Sabitry ta ɗauki
hankalinsa alhalin shi duk matan duniya su da maza duk ɗaya suke a wurinsa in ka fidda Anita.
Ya lumshe ido tare sakin murmushi,a hankali ya furta “ina son ki Anita ” bugun zuciyarsa ne ya ji
ya amsa.
Sosai aka yi shagali aka cashe bisanin duk kowa ya kama gabansa.
Bobby na zuwa gida Daddy ya tarbe shi da pasport ɗinsa wanda tuni an yi masa VISA .
“Ga shi gobe in Allah ya kai mu jirgin ka zai tashi zuwa Pakistan,na yi magana da mutumena ya
yi bincike kan Anita ya gano inda take.Lambar wayarta da address ɗinta duk a wajen shi za ka
samu” Daddy ya faɗa ya na miƙa masa pasport ɗin.
Wani tsallen murna Bobby ya yi,ya rungume mahaifinsa sannan ya shiga sumbatarsa ya ce “na
gode sosai Daddy bari na shiga ciki na haɗa kayana”
Mamy wacce ke zaune kan salon ta ce ,“My Prince tuni na haɗa maka komai ya na cikin trollyn
ka,fatana kawai ka more rayuwar ka.Ina son ace ko da ka ke dawo wa ƙasar Japon ace kai da
Anita kun yi saka zoben alƙawari in son samu ne ma ace da Baby a cikinta”
Dariya duk suka shiga yi, Daddy ya mirza sumar kan Bobby ya ce “to ka ji dai don haka ka sa
himma! Je ka yi wanka ka zo ka ci abinci”
“Ban jin yunwa,zan dai huta ne don na gaji sosai” Bobby ya faɗa ya na mai haurawa sama
passeport ɗinsa a hannu.
Bayan ya yi wanka ya shiga group ɗin su na WhatsApp ya shaida wa abokansa.A nan ne shi
ma Kameel ya sanar da su za su koma Senegal shi da mahaifinsa.Fadeel duk sai ya ji babu
daɗi sam sai babu yadda za su yi....
★SENEGAL
Sai da Kawu Mansur ya danne zuciyarsa sannan ya bar su Twins domin su ci gaba da
karatunsu.Habiba wacce ta fita daga boko tun primary malami ya ɗaukar mata ya na koya mata
a gida,sannan kuma ɗaya ɓangaren Zahra na koyar da ita.
Sosai ta maida niyya wannan ya saka,Kawu biya mata kuɗin makarantar ita ma sai dai irin ta
ƴan gayu ce mai masifar tsada.
Ranar farko da Habiba ta shiga aji,sai ta zama banban da sauran.Duk da dai kowa uniforme ce
a jikinsa amma duk ƴan matan sun sha kwalliya sun zubo gashi,wasu gashin doki ne ma amma
banda ita.
Yadda ta ga ana kallonta ya saka ta gane bai rasa nasaba da burkiɗeɗen hijabin da ke jikinta.
Bayan ta dawo gida ta baiwa Zahra labari,“Habiba kar ki biye masu ki ci gaba da shigar da ki ka
saba mana.Kin ga ni da Bintu After dress muke ɗora wa a saman uniforme ko ke ma ita ake
nemo miki?”
“A'a ina son ni ma gashin kaina ya koma dogo har ga baya ”
“Wai kin ɗauka gashin kansu ne? To na doki kuma babu kyawu saka shi”
“Ni dai kam ya burge ne zan shaidawa Baba ya bani kuɗi sai ki yi min rakiya na sayo”cewar
Habiba ta na jin son ganin canjin rayuwarta.
“Ok babu damuwa,yanzu dai mu yi karatun Alkur'ani zuwa dare sai na koya miki lesson”
“Kai na gaji sosai ki bari zuwa dare ni ma sai na koyar da ke”
Zahra ta maraice fuska ta ce “don Allah Habiba ki tausaya ki faɗa min ko da aya biyar ce” ba
don ta so ba ta yi wa Zahra ƙarin karatu kasancewar ita Habibar ta na da ilimin addini.
“Ku zo ku ci abinci,ina Bintu ?” ina ta tambaya ta na mai ajeye trayn abinci a tsakiyar falo.
“Ta na ɗaki,wai kanta ke ciwo” cewar Zahra .
“To ku zo ku fara ci,bari na tasheta ta zo ta ci abinci sai ta sha magani” Inna ta faɗa ta na mai
nufar ɗakin su Bintu.
Tsakiyar gado ta tare da ita ta yi rub da ciki,“Bintu? Bintu?” ba tare da ta amsa ba ta ce “taso ki
ci abinci sai na baki magani” kai ta girgiza ta ce “ban jin yunwa” Inna ta ce “kin sha magani ne?”
ta girgiza kai alamun a'a,da sauri Inna ta fita babu jimawa ta dawo hannunta riƙe da kofin ruwa
da kuma magani amma ƙememe Bintu ta ƙi sha sai da Inna ta je ta kira Halilu wanda a yanzu ta
fara jin tsoronsa.
Fuska ya haɗe cikin bayar da umarni ya ce “ki tashi ki sha” kuka ta fashe ta na mai cewa “ni ba
zan sha ba, chocolat nake so”
Halilu ya dubeta sake da baki ya ce “kenan lafiyar ki lau?” kai ta ɗaga masa ta na shagwaɓe
fuska.
“To tashi ki shirya mu je mu sayo” da murna ta sauka daga bed ɗin ta shiga toilet ta wanke
fuskarta.
Gaban madubi ta tsaya ta shafa mai da hoda sannan ta juyo ta dubi Halilu wanda duk inda ta yi
idonsa na kanta,Inna kuwa dama tuni ta yi tafiyarta .
“Ka fita ina son canza kaya” ta faɗa a sanyaye.Halilu ya maƙe kafaɗa ya ce “a'a ba zan fita
ba,kawai ki canza na yi miki alƙawari ba zan kalle ki ba”
Bintu ta turo baki,zumbulele hijabi ta saka ta yadda ba za a ganin ƴar ƙaramar rigar jikinta ba.
A jere suka fito,su na daf da shiga mota suka ji muryar Kawu Mansur kamar aradu “gidan uban
waye za ki kai min Ɗa? ” a tare suka juyo su na kallonsa.
Bintu ta taɓe baki bisanin ta kawar da kai gefe,“Baba za mu tafi mall ne ba za mu jima ba”cewar
Halilu cike da nutsuwa don yanzu ya ƙara wayewa.
“Ita ta dawo kai ka tafi”
“Lilu wuce mu tafi don Allah rana sai gasa ni take” Bintu ta faɗa a mugun shagwaɓe,wanda ya
saka Halilu tattaro hankalinsa kanta.
Murmushi ne ya suɓuce masa jin da sunan da ta kira shi,uwa uba kuma yanayin maganarta.Bai
san lokacin da ya buɗe mata ƙofar mota ba ta shiga,shi ma ya zagaya ya zauna ya yi wa motar
key suka bar Kawu Mansur tsaye sake da baki.
A cikin mota Halilu sai surutu yake zuba mata kamar Akun kuturu,har suka isa mall ɗin.Kai kace
wata Baby haka ya ɓata kuɗinsa wajen saya mata kayan maƙulashe da kuma wani ƙaton Teddy
pink.
Lokacin da suka dawo sun tarar Kawu Mansur na ta balbalin masifa kamar zai tadi gidan.Ko
kaɗan babu tsoronsa a fuskar Bintu ,ido cikin ido suke kallon juna da ita.
A zuciye ya kifa mata mari ya na mai cewa “shegiya mai ido tsakar kai,ke ga ƴar iska wacce ba
ta samu tarbiyya ba.Dama ta ya ya barewa za ta yi gudu ɗanta ya yi rairafe.Amma zan yi
maganin ku ke da munafukar uwar ki” ya na gama faɗa ya sa hannu zai karɓe ledar
hannunta,da sauri Halilu ya tare shi ya na cewa “Bintu shiga ɗaki gani nan zuwa” Idonta sun yi ja amma ba ta yi kuka ba,wata uwar harara ta banka wa Kawu bisanin ta wuce
ciki.
Zahra ta bi bayanta,falon sai ya rage Kawu da iyalansa.
“Baba wannan abun da ka ke sam ba ka gyara min,ka yi kowa sanin irin mugun son da nake yi
wa Bintu .Da ya ya na yi na samo soyayyarta? Aiki na yi tuƙuru babu dare babu rana sannan na
samu ta fara saurarena,amma shi ne kake rushe min ginin da na tsara”
“Halilu rufe min bakin ka,mahaifin ka ne fa.Kuma ai ba ka fi shi sanin daidai ba,abin da ba ka
sani ba rabin dukiyar Marigayin Ayub Bintu ce kawai ta san inda take sannan akwai takardun da
doli sai ta saka hannu sannan su zama mallakinmu.Ko ka yi tunanin banza yasa har yanzu ni
ban fito da mugun halina ba? ” Inna ke faɗa ta na matsowa kusa da Ɗanta. Halilu ya ce “ni dukiya ba ta gabana Inna ,wlh na fi son Bintu fiye da duk komai na ƙyalƙyalin
duniyar nan.In kuka kwantar da hankalin ku ni nan da kaina zan karɓo komai,ya kuke gani in na
aureta?”
Kawu Mansur wanda takaici ya rufe da sauri ya yi gaba,ɗakinsa ya shiga .In akwai abin da ya
tsana to ya na bayan zur'ar Ayub ,ba don gudun zargi ba da guba yake zuba masu duk su mutu.
Safa da marwa ya fara ya na tunanin malam Mohan da aka ce masa gobe zai shigo
Senegal.Kamar wani zararre ya fara magana shi ɗaya “zan yi maganin ki,gobe in Allah ya kai
mu ƙarfe bakwai na safe a Joal zai yi min! Hum! Haba! Duk za ku ci ubanku ”
Halilu kuwa ɗaki ya bi Bintu nan ya tarar su na rigima ita da Zahra akan teddyn da ya sayo.
“Lilu wai ita ma sai an saya mata ko kuma ta toye shi” Bintu ta faɗa ta na dariya har dimple ɗinta
ya lotsa.
Halilu ya dafe goshinsa ya ce “oh! Shaf na manta da komai iri ɗaya ku ke yi,Bintu laifin ki ne
amma in sha Allah da dare zan sayo mata”
Sai a lokacin Zahra ta saki ranta, toilet ta shiga don lokacin makaranta ya kusa.
Halilu ya zauna kusa da Bintu ya ce “ina sonki sosai” ta dube shi da sauri yanayin fuskarta na
canzawa.Ya ja dogon numfashi ya na shirin kamo hannunta ta yi saurin tashi,“zo ki zauna babu
abin da zan yi miki ” ya faɗa ya na mai kafeta da ido.
Ta maƙe kafaɗata haɗi da turo baki gaba ta ce ,“ni dai don Allah ka fita”
“Don mi?”
“In dai ka na sona ka fita”
“Hakan shi zai sa ki yarda ina son ki?” kai ta gyaɗa masa da sauri shi kuma ya miƙe,ta gabanta
ya wuce ya yi ƙoƙarin yi mata kiss a goshi ta ture