Showing 1 words to 3000 words out of 12378 words
Chapter 1 - Tuzuru Book Complete By Mrs Sadauki
[18/12 à 08:14] Mrs SADAUKI í ½í²«: *TUZURU*í ½í¹Š
```Love
and
romantic story```
```MRS SADAUKI í ½í²«✍í ¼í¿»```
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️*
_______________________
*PAGE 1&2*
MARADI ADS
A hankali ya ke saukowa daga matakala hannun shi riƙe da hullar kakin soja wadda tayi machin
da tenue shi ta sojawa.Fuskar nan a murtuƙe kamar tsohon kunun da aka dama ba'a sha
ba,dogo ne fari sol mai ƙirar ƙarfi ya na da saje baƙi siɗik wanda ya ƙawata doguwar fuskar
sa.Ƙaton ƙirjinsa mai manya muscules kawai in ka kalla ya isa ya firgitaka saboda yanayin
yadda ya buɗe yayi faɗi ƙwanjinsa tamkar za su fasa riga su fito.
Gaban mahaifiyar shi ya zo ya tsugunna ya sunne kai ba tare da ya kula ƙannan sa da suke
jero mashi gaisuwar Barka da safiya ba.
Ɗan ɗagowa yayi kalleta jin tayi shiru ba kamar yadda ta saba mashi ba,ido ya rausaya uwanda
suke blue kamar na mage can ƙasan maƙoshi yace "please"kawar da kai tayi kafin ta ɗora
hannunta bisa sumar kan shi wacce ba ta dayawa sosai amman gyaran da ta ke sha yasa tayi
kyau da sheƙi "Allah ya tsare ka a duk inda kake"shine abinda datijuwar matar ta faɗa miƙewa
yayi tsaye ya na sauke ajiyar zuciya kafin ya ɗora hullar sa a kai ya na daidaita mata zama.
Kallon ƙannan na sa yayi uwanda duk suka ƙame waje ɗaya su na numfashi sama-sama tsabar
tsoro,kai ya jinjina masu alamar ya amsa gaisuwar da suka yi masa kafin ya fice.
Da sauri Faruk ya tarbe sa haɗi da sara mashi kafin ya buɗe masa mota ya shiga,gate man ya
buɗe porte Faruk ya fita da mota a slow har sai da suka hau titi sannan ya fara sharara gudu
kamar zai tashi sama.
Babu jimawa suka kawo compagnie ɗin wacce ta ke birjit da sojoji ta ko ina,shigowar motar shi
ne yasa sojawan ƙara daidaita tsayuwar su haɗi da ƙamewa kamar wasu tsuntsaye.
Cike da ƙasaita ya fito lokacin da Faruk ya buɗe masa mota,tafiya ya soma irin ta jaruman maza
duk in ya taka sai ƙasa ta amsa saboda yanayin ƙirar sa ta samudawa.
Office ɗin da aka tanadar dominsa Faruk ya buɗe kafin ya bashi gu ya wuce,wani dadaɗan
ƙamshi ne ya bugi hancinsa wanda ya sa shi lumshe ido bai shirya ba.Office ɗin ya fara bi da
kallo yadda aka ƙawata sa fiye da kullum yau ma ƙamshin daban ne,faux du fleureí ¼í¼¹ ɗin da ya
gani tsakiyar teburin shi ya bashi mamaki a zuci yace "yaushe kuma aka za wannan?"taɓe baki
yayi ya samu gu ya zauna takardu ya jawo domin dubawa sai dai tunanin Mami ya faɗo masa a
rai yadda ta ɗaure fuska ta canza ma shi sam bai ji daɗin hakan ba.
Baya yayi da kujera ya na mai lumshe ido tare da sauke wani huci,Faruk ya turo ƙofa ya shigo
hannunsa riƙe da coffe.Bisa table ya ajiye kafin yace "ya dai?"ɗagowa Général Waleed yayi ya
dube shi kafin ya ɗan harare sa bai tankasa ba ya ɗauki Coffen ya fara kurɓa, murmurshi Faruk
yayi yace "ɗan gaban goshin Mami yau kuma wa ya taɓo ka?"sai da ya gama shan Coffen
sannan ya dubi Faruk yace "da farko dai kai ne na biyu kuma Mami"ya ƙare zancen da kwaɓe
fuska kamar wani ƙaramin yaro.
Kujera Faruk ya ja ya zauna yace "to faɗa min mi nayi?dan dai ita Mami na san gatanar gizo ba
ta wuce ta ƙoƙi"hararar wasa ya kuma yi mashi kafin yace "wace gatana kuma?"Faruk yace "ta
aure mana,ka san fah abun na damun Mami dan jiya ma mun yi zancen sannan ya kamata kai
ma ka yiwa kan ka ƙiyamul laili ka girma ka ƙosa tun ka na cikin sahun samari yanzu har ka
zama *TUZURU* duk sa'anin ka sun yi aure"kai Général Waleed ya dafe yace "aure?aure,aure
dai?"Faruk yace "Yes !"tashi yayi tsaye yace "ni fah ba auren ba ne ban so a'a raini ne ban so
yarinya ƴar ƙarama ta rinƙa baka ordre mtsw..."ya ja wani tsuki ya na girgiza kai ya cigaba da
cewa "sam ba zan iya ɗaukar iskanci ba"dariya Faruk yayi yace "ai babu macen da ta isa ta
dubi mon général ta raina sa ina sam hakan ba mai yiyuwa ba ne,ko mu da mu ke Mazan ya mu
ka iya balle wata aba wai mace?"murmushi Waleed yayi yace "ɗan iska yau dai ka dawo a
matsayin abokina shiyasa har kake gaya min magana son ranka"Faruk yace "eh toh kai ɗin ne
akwai wuyar sha'ani dan wani zubin tsoron ka ma ni ke ji"
Kallon shi Waleed yayi yace "shiyasa tun da aka bani kai a matsayin mai min hidima na so na
canza ka wlh sam ban son risinawar nan da kake min"Faruk yace "to ya zan yi ?a bakin aikina
fah ne"Waleed yace "no banda in mun na gida please ka bari in mun zo nan"kai kawai Faruk ya
jinjina kafin ya ɗauki kofin da ya shigo da shi ya fita.
Takardun masu son permission ya fara dubawa kusan rabin su duk yayi rejeté dan wasu na
neman izinin zuwa wani gun ba tare da babban dalili ba wanda kuma haka rauni ne ko kuma
shagala cikin aikin soja.
Ya na gamawa ya tattara takardun ya maida gefe,Faruk ya shigo ya ɗauki takardun ya na cewa
"Momy tayi dambun shinkafa tace na faɗa maka ko a kawo ma?"miƙewa yayi yace "no sai dai
mu tai can mu ci tunda babu wani aiki ka ga nayi zumunci"da ƴar dariya Faruk yace "ai
kuwa"kafin su fito.
***Gao
A gajiye ta ke tafiya cikin yashin da ya tuje sakamakon manyan motocin da suke zaryar
wucewa,kallo ɗaya za ka yi mata ka san ta kwaso yunwa da ƙishi yadda jajayen laɓanta suka
bushe.
Tafiya ta ke duk illahirin jikinta na motsawa kasancewarta ƴar lukuta mai ƙiba mai manya
mazaunai da dukiyar Fulani.Ƙofar ta tura ta na mai shiga gidan bakinta ɗauke da
sallama,amsawa Momy tayi ta na duban ƴarta ta tace "Nabeela yau ma ƙasa kika tawo?"a
shagwaɓe tace "Eh Momy ba doli nayi tafiyar ƙasa ba ko na samu wannan ƙibar ta rage,dube ni
fah ki gani yadda na ke kamar wata Hajiya í ½í¸†"dariya Nabeel yayi wanda ya ke can gefe ya na
wanke babur ɗin shi yace "Allah kuwa gwara haka shiyasa na bar ɗaukar ki a babur ɗina kar ki
fashe min taya"cike da jin haushi ta fara bubuga ƙafafu ta ce "wlh sai na hau kuma koya zan yi
ta yadda zan rinƙa hawa in ba ka nan"dakatawa yayi da wankin babur ɗin yace "wai a hakan za
ki hau babur?tab ai ina ga ke sai dai mota shiyasa na ke yi maki sha'awar auren mai kuɗi"Momy
ta karɓe zancen da cewa "a'a Nabeel kar na kuma jin ka saka mata mummunar aƙida ta sai mai
kuɗi Allah ya bata mai kyawawan halaye dai tayi aurenta ta huta"Nabeela tace "amen Momy
can wadda ya sake gani sai ya ce mata lukuta"ta faɗa ta na mai buɗe frigo wacce ta ke a waje
cikin rumfa,ruwan sanyi ta ɗauko cikin tasa ta sha ta na mai sauke ajiyar zuciya kafin ta shige
ciki.
Wanka tayi ta canza kaya zuwa riga t-shirt da zane, kitchen ta shiga ta zubo abinci ta fara ci.
Chaîne ta canza ta kamo Tauraruwa tv inda suke haska wani Film na sojoji,cike da jin daɗi ta
sauka ƙasa ta na mai ƙara volume.
Nabeel ya shigo ya zauna kan kujera mai zaman mutum ɗaya yace "albishirin ki?"ba tare da ta
juyo ba tace "goro" hararta yayi yace "a hakan zan gaya maki albishir ɗin kin wani ƙurawa tv
ido?"juyowa tayi ta fuskance sa tace "to ina jin ka"
Sai da yayi wani murmushi sannan yace "jiya Faruk ya kira ni zuwa compagnie ɗin su ai kuwa
na ga mutumen ki"da sauri tace "wa?mon général ?"dariya ya sheƙe da ita har da riƙe ciki ita
kuwa taji haushi ta kai masa duka tureta yayi ya ta faɗi ai kuwa ta taso ta jibge sa shi ma da yaji
haushi ya sharara mata mari plate ɗin da ta ci abinci ta buga masa ta yo waje a guje ta na ihu ta
na kiran sunan Momy idonta duk sun rufe saboda hawayen da suke zuba,gijibbb taji ta gabji
wani ƙaton abu tayi tangal-tangal za ta faɗi kuma taji an taro ta....
[18/12 à 13:32] Mrs SADAUKI í ½í²«: *TUZURU*í ½í¹Š
```Love
and
romantic story```
```MRS SADAUKI í ½í²«✍í ¼í¿»```
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️*
_______________________
*PAGE 3&4*
"Ya Salam !Waleed ya furta jin dukiyar Fulaninta bisa fafafaɗan ƙirjinsa kuma alamu sun nuna
ba ta saka bra ba ta yadda har yaji taushin su sun shiga ƙirjinsa sun ratsa ɓargon sa.
Cikin yanayin ruɗu da tsoro ta ɗan buɗe idonta sai ta ga kakin soja kawai sai ta ƙara shigewa
jikin sa ta na cewa "Ya Faruk ka cece ni wlh duka na zai yi"ta fashe da kuka saboda zafin marin
har yanzu bai sake ta "Innalillahi wa'inna iley raji'un"kawai Waleed ke maimaitawa a zuci duk ta
ruƙunƙumesa hakan ya sakar masa kasalar da ya kasa taɓuka komi balle yayi ƙoƙarin cireta
daga jikinsa.
Nabeel kuwa ya na can ɗaki dafe da goshi ya na fitar da jini shiyasa ma bai biyota ba,wani irin
fincikota Faruk yayi daga jikin Waleed ya na cewa "ke ba ki da hankali général ɗin ne kika
cakume haka"jin muryar Faruk ya na ambaton général yasa kukanta tsayawa cak ta na mai
waro ido kallo ɗaya Waleed yayi mata ya ɗauke kai ya na mai shiga falon dama can Faruk yace
ya wuce kafin ya shaidawa Momy zuwan su wacce ta ke ɗakin Abba ta na gyara.
Tun da ya shigo idon sa ya sauka ɗigo-ɗigon jinin da ya zuba ƙasa,ya ji ransa ya ɓace matuƙa
allura soja ta motsa a nan take ya gane da Nabeela ce ta fasa mashi kai.
Ƙarasawa yayi gun Nabeel wanda ya duƙe ya dafe gun da jinin ke zuba da hannu,wani tissu
mai ɗan tsayi Waleed ya fiddo ya ɗaure mashi.
"Nabeelaaa"Waleed ya furta da wata irin murya wacce hatta Faruk sai da ya ɗago ya kalle
sa,jiki na kyarma Nabeela ta koma bayan Faruk ta laɓe dama shigowar su kenan.
Wani kallo ya yiwa Faruk wanda ya sa shi saurin janyewa Nabeela ta bayyana sai kyarma ta ke
dan tsoro,"ki goge wannan jinin sannan ki zo ina neman ki"Waleed ya faɗa cikin bada umarni ya
na sake taken fuska.
Sumi-sumi Nabeela ta ɗauko bokiti da ƙaramin towel ta jiƙa shi da ruwa ta goge gun da kyau
sannan ta je kusan Waleed wanda ya hakimce bisa kujera su na gaisawa da Momy cike da
girmamawa.
"Lafiya ki ka zo kika yi ma mutane tsaye a kai?"cewar Momy ta na kallon Nabeela,da ido ta yiwa
Momy nuni da Waleed "minene ke ba ki iya gaisuwa ba ne?"baki ta zunɓuro sai kuma tayi
saurin maida shi ganin irin kallon da ya watso mata "ina wuni?"ta furta baki na rawa kawar da
kai yayi gefe ya na mai ɗaukar spon ya saka cikin dambun da Faruk ya aza mashi bisa hannun
salon "koma can ki kama kunnuwan ki ko kuma tsallon kwaɗo"ya faɗa murya a dake ya na kai
lomar farko baki.
Kallon Momy Nabeela tayi ta marairaice sai kawai Momy ta miƙe ta fita ma,Faruk kuwa cikin
zuciya ya ke dariya ya na kuma jin salon ogan na sa na kuma burge sa dan shi a ko ina soja ne
in ya an yi ba daidai ba doli ya zartar da hukunci.
Nabeela na matsar ƙwalla ta kama kunnuwanta ta fara sama da ƙasa,duk in ta tashi ma'ana ta
duƙa haɗi da tashi sai ta kalli Waleed wanda ke cin dambun shi hankali kwance lokaci zuwa
lokaci kuma ya na kallon tv.
Ruwa masu sanyi ya sha yayi gyatsa tare miƙe ƙafa ya ɗan kishingiɗa jikin salon ya na mai
lumshe ido kamar bai barci ganin haka yasa Nabeela tsayawa ta na mai sauke ajiyar zuciya
ganin kamar zai waigo ta cigabaí ½í¸¹
Sai da ta kwashe sama da 30mns sannan yace "stop!"ai da gudu ta ruga ɗakinta ta na mai
fashewa da kukan da ya ke jin sa har cikin tsokar zuciyarsa.
Tashi yayi zaune ya na duba agogon hannun sa kafin ya miƙe ya fita Faruk na take masa
baya,bakin ƙofa ya tsaya ɗan guntun murmurshi kan fuskarsa yace "Momy zan wuce,dambu
yayi daɗi sosai na gode sai kuma in mun dawo wani lokaci"ya ida maganar ya na ɗan sosa
bayan ƙeya Momy tace "eh tunda kun ƙi tsayar da matan aure ai doli ku rinƙa santin girkin mu
yanzu ina hullar kan ka?"saurin shafa kai yayi yace "laaa Momy kin ga fah na manta sam"Faruk
na dariya ya koma ciki ya ɗauko masa suka yiwa Momy sallama suka fice.
Gida ya aje Waleed yayinda Faruk ya wuce compagnie,ya na shigowa duk suka tsaya daga
dariyar da suke sai Jamila ce babbar Yayar su dan ita ke babba sannan Nafissa wacce ke aure
Mashi sai Waleed wanda shi kaɗai ne namiji , sai A'isha da kuma Auta Amal.
"Ah!ah ka ga Mazan fama soja tuwon ƙaya miyar allura ashe da rabon zan gan ka?"cewar
Jamila ta na dariya,a shagwaɓe ya zauna kusa da ita ya na cewa "anty yaushe kika zo?shine ko
ki kira ni ?" "Ai ban jima ba dama Mami ta aika kira na tace akwai maganar da za mu yi"ɗan cije
leɓe yayi ya na kallon ƙannan na shi sumi-sumi suka miƙe. Kallonta yayi da kyau yace "maganar mi?"jikin Jamila a sanyaye tace "aure mana,Waleed ka kai
matsayin da ba sai an ce ma ka aje iyali ba yanzu fah shekarun ka kusan arba'in amman ba ka
da niyyar aure why?koko ba ka lafiya ne?"ta wutsiyar ido ya ke kallon Yayar ta sa tun da ta
ambaci kalmar ko bai lafiya yaji wata kunya ta kama shi a nan take kuma moment ɗin da
Nabeela ta faɗa jikinsa ya faɗo masa a rai da sauri ya kawar da tunanin jin kamar yanayinsa sai
canza.
"Tambayar ka fah na ke"Jamila ta sake faɗa,yamutsa fuska yayi yace "kawai lokaci ne bai yi ba
ku ƙara haƙuri kaɗan"ya na gama faɗar haka ya miƙe ya nufi step ya haye sama.
Maɓalan rigar ya cire sannan ya cire wando tenue ya bar gajeran,toilet ya shiga ya sakarwa kan
shi shower.Yanayin surarta,yadda ƙirjinta ke motsawa a duk lokacin da ta duƙa za ta
miƙe,yadda idonta suke nuna alamar tsoro da yadda ta ke shagwaɓa duk suka faɗo masa a rai.
Wuci ya sauke ya na samun wata erection wacce kusan kullum ya na yawan shiga halin
sha'awa sai dai na yanzu ya banbanta dan har wani zirrr ya ke ji wani abu na yi mashi yawo a
cikin mazantakar sa.
***GHANA
A duƙe ta ke ta na kuka gaban mahaifiyarta wacce ta shaida mata ɗaurin auren da aka ɗaura
mata a yau ita da cousin na ta wanda aka yi itiƙafi kaf Familynsu shine Ɗan da aka fara
haihuwa cikin cousins kuma shine bai taɓa aurawa ba a ƙalla ya kai shekara arba'in da biyu
zuwa da uku. "Fannah haƙuri za ki yi ki rungumi ƙaddarar auren ki dan wani bai auren matar wani,Ali ya daɗe
bai yi aure ba ne ƙila saboda dama ke ce Allah ya ƙaddara za ki wanke sa"cewar Mama ta na
mai ƙara kwantarwa Fannah da hankali yarinyar da ba za ta wuce 15years ba,ido cike da
hawaye ta ɗago ta kalli Mama tace "karatuna fah?"Mama tace "za ki ƙarasa a can gidan sa"ba
tare da Fannah tace komi ba ta miƙe ta shige ƙurya ɗaki ta na kukan takaici na aura mata
gabjejejen *TUZURU* wanda da ace yayi auren wuri da tabbas ya isa haihuwar kamar ta.
Sati guda aka ɗauka ana yiwa Fannah gyare-gyare na amare haɗi da kitso da lalle,tsaf ta fito
tayi sharrr gwanin kyau sai baƙar fatarta ta bada wani kala mai kyau kamar ƴar Ethiopia.
Ta na kuka ta na ƙari haka aka kai ta gida Abbas wanda ya ke ciki ɗaya da falo,ta na nan zaune
tsakiyar gado ya shigo da sallama ba ta iya amsawa ba saboda kuka.
Ledar da ya shigo da ita ya ajiye mata kusanta kafin ya fito falo ya kwanta bisa doguwar
kujera,ido ya rufe ya na jin wani raɗaɗi na taso masa "ta yaya za'a ɗaura masa aure ba tare da
neman shawara ba?yanzu miye matsayin auren su shi da bai taɓa jin wani abu dangane da
mace ba?miye mafita ya fito fili ya faɗa masu bai da lafiya ne ko gwada sa'ar shi zai yi akan ƴar
ƙwailar matar da aka aura masa?"juyi ya kuma yi ya na mai jan tsaki ƙasa-ƙasa "ta yaya zan
buɗe sirrina gun waccan ƙanƙanuwar yarinyar?"ya faɗa a zuci kafin ya miƙe ya koma ɗakin ta
na nan yadda ya barta.
"Keee!"ya furta cikin whisky voice,Fannah uwar tsoro tuni ta ƙara sautin kukanta wanda ba
ƙaramin fusata Abbas yayi ba kawai sai ya hauro gadon ya na yaye maluluɓin da aka rufe ta da
sauri yayi baya ya furta "ya Allah"sakamakon kyawu da zubin hallitar ta da ya gani cikin kayan
da suka matse ta wani abu ne ya fara jin ya na fuzgarsa da sauri ya dafe kai....
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*
[19/12 à 07:19] Mrs SADAUKI í ½í²«: *TUZURU*í ½í¹Š
```Love
and
romantic story```
```MRS SADAUKI í ½í²«✍í ¼í¿»```
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️*
_______________________
Thank you for