Showing 15001 words to 18000 words out of 21753 words
Chapter 6 - Auren Jinsi Book 1 Halima Abdullahi Shuaib Ummu Basmah
tace lallai kuwa kinyi kuskure da baki fara kiran sunan mahaifiyar ki da
wadannan sunan ba ....ita tafi dacewa dasu....... Mom ce da jikinta yafara sanyi domin wani
tunanin datakeyi ko nasmat taji abinda sukayi ranar ne....... Gun salmah takara Sa tace kiyi
hakuri da halin da yar uwarki ke ciki.... Kinji dukkan tsananin yana tare da sauki..... Waye ta
bata miki rai ne a airport.... Mom daga saukata wata banza tazo take cemun.... Dad ne yamata
sign da ido alamun yin shiru.... Dan yasan idai taji maganar hankalinta tashi zaiyi..... Kirane ya
shigo.... Wayar ta... Da wata bakuwar number.... Gaban ta ya fadi.... Tace nashiga uku... Waye
kuma yasamu numbers Dina bayan ban raba ba........ Kin dauko tayi dad ne yace kije ki dauka
mana bakyau wulakanci.... Kuma baki San waye ma ba.... Watakila yazama important kiran.......
Bandan ranta yaso ba tayi hanyar waje..... Tana picking.... Taji muryar da bata sake tunanin jinta
bat.....salmah yayi... Amma ta kasa amswa.... Sai rufe ido kawai.... Dan ko a mafarki taji wannan
muryar tabbas zata gane ballatana kuma muryar jalal data zama mata ruwan sha..... Magana
yakeyi amma shiru..... Kashe wayar tayi gaba ki daya.... Ta shigo fuskar ta tab da hawaye......
Ba wanda ya kulla da yanayinta sai dad.... Yasan me kiran... Domin ruwa baya tsami banza......
Nasmat dataki yin shiru tace dad inada question dayawa.... Kuma kamun promise indan naji
sauki zaka amsa mun ko kai yada mata.... Yace to kiyi shiru ko....... Kizauna da antynki barin
Kai mom gida kafin ayi salmah ko.... Gyada me kai tayi dan nasmat akwai shagwaba...... Suna
fita ba wanda yace ma wani ufan acikin su.... Salmah na tunanin jalal..me yadawo dashi cikin
rayuwar ta bayan ta shafe babin shi.... Ita kuma nasmat na tunanin rayuwar su... Yadda zata
kare da bakin painting da mom ta musu... ...
Salmah tayi nisa cikin tunanin ta tace Anty salmah dan Allah kiyi hakuri kinji..... Daga mata
hannu kawai tayi... Nasmat saukowa tayi kasa inda antynta ke zaune tayi kneeling tace pls my
Anty am sorry for the disrespect... Tace is OK... Rungume tayi sukayi ta kuka.... Can nasmat
tace anty dan Allah waye.... JALAL.......
Typing......
By:H.@.S
[3/1, 12:26 PM] H.@.S頎柬己頎柬几:
AUREN JINSI.
28-2-2018
Typing.... 76 to 80
Dedicated: HANAN ABUJA.
Gaskiya yar uwa nagode da abun arziki... Yaba kyauta tukuici ne... Allah ma yace
indan yabaka ka gode masa sai yakara ma.... Indan kuma ka kafurce to lallai ya tanadi azaba
me tsananin..... Hanan naji dadi kuma nagode.... Allah yabar zumunci yaraya miki zuri'arki....
Yakareki daga sharrin masu Shari.... Allah yasaka da alkhairi...頎卷礉頎卷礉頎卷礉頎卷礉頎卷礉頎卷礉頎卷礉
Hajiya kema sakonki ya iso gareni... Nikam ba abinda zance sai fatan alkhairi... Allah
yasaka miki da alkhairi... Allah ya raya miki iyalanki.... Allah kuma yabar ki... Da me house.... A
dade anayi sai gaskiya....頎卷礉頎卷礉頎卷礉
Fans kuma naji dadin yadda kuka mun jiya gaskiya ba abinda Zan iya cewa sai
Alhmadulillah..... Nagode sosai.... MARWANATU..... ina ji dake kema nagode da kuwalarki..
yabaki abinda kike nema duniya da lahira......
HOME OF MY QALAM WRITER'S ASSO.
Ku kasance tare da alkalamina.... Dan fadakarwa , illimatarwa.... Game da nisadantarwa....
Daga yar mutan jasawa....
Tace anty waye.... JALAL .... Gaban salmah ne yafadi.... Amma ta dake tace a ina Kika
samu sunan jalal... Kuma.... Ban San ko waye ba... Tace Anty nasan bakya karya... Amma yau
kina so kifara kenan..... Naji kuna waya dad ranar.... Kuma wayar na hands free take.... Naji me
kike cewa.... Dan Allah I want to know little about him.... Nasanki da kamal ba jalal ba... Amma
duk lokacin da zakiji wani Abu gameda... Jalal zuciyarki na rawa idanunki na fitar da ruwa....
Dazu nasan dashi kuka yi waya... Tunda naga har kin kashe waya kuma bakya marmarin...
Kara kunnata........ So pls Anty..... Tell me something about him..
Salmah guntu hawaye ta goge.... Tana mugun tausayin kanwarta... Allah yarabaki da
kadarra irin ta wa....zaunar da ita tayi kusa da ita... Tace Zan baki labarin jalal amma...abisa
sharadi daya.... Dan naga alama nasmat acikin hayyacinki kike ....dan duk wanda zai iya
wadannan tamboyoyi to nidai aguna lafiyar shi kalau.... Dad ma ya biye miki saboda shagwabar
ki.... Amma nifa bazan iya ganin kina muzanta mun mahaifiya ba bazan dauko ba... Ga dukkan
alamu kin dade da yin watsi da ita a matsayinta na mahaifiya ba.... So what ever... Kome kika ji
Kika ganin tare da ita kisani ita mahaifiyar ki ce... Kuma ita ce sila data kawo ki duniya....
.....safiya dake sunan mahaifiyar Alhaji gareta..... Kisani duk duniya zaki iya canja komi amma fa
banda iyaye.... Kuma zaki iya siyan komi amma banda iyaye domin kuwa basu da kasuwa.....
Ina so kisani.... Iyaye amana Allah yabasu zai tambaye su game da Mu muma kuma zai
tambaye Mu akansu..... Kinga kowane sashi an bashi amana...... Allah yana cewa kulkum r茫'ee
wa kullkum m茫sul.....dukkan mu kiwo aka bamu ....kuma zamu kasance abbaben tambaya......
Allah yana cewa a cikin alqur'an me girma..... Adi'ulllaha wa'adiul rasullu... Wa aullu illim
minkum..... Nasmat kina da saninki iya gwargwado.... Amma kina nema ki jefa kanki cikin
halaka......
Lallai nasan kome Kika ji nasan babban ne ....kuma bana fatan jinshi..... Amma ai kamar
yadda iyaye nmu suke indan munyi Abu ba daidai ba... Suke mana fada haka muma indan
sunyi ba daidai ba.... Zaki iya afani da wata siga ko dubara da Allah yabaki.... Wajen musu
nasiha.... Da kuma nuna musu kuskure.... Amma ba saikiyin fushi da su ba ko kin muzanta su....
Wanda Allah yagaya mana yadda zamu zauna dasu.... Yace kar da muce musu tir... Kuma kada
Mu hantare su Mu gaya musu magana me daraja..... Amma ke kin take saninki kin bi rudin
shedan...... Nasmat ba wai na zaunar dake bane dan namiki dadin baki ki janye gudurinki aa....
Sai dai ina tuna miki fushin Allah akanki ne......wanda Allah ya tanadi azaba Kala Kala.... Akan
masu. Kinyi ma iyaye azaba.... Kuma tunda ga duniya baza su ga abinda suke nema daidai
ba..... Kamar yadda nace miki Zan baki labarin jalal.... Sai kin mun alkwari bazaki kara kallon
banza wa mom ba.... Kuma bazaki kara mummunan magana akanta ba...... Idan har kin mun
wannnan alkwari to.... Ki miko mun hannunki......
Nasmat ta dade a durkushe tana kuka saboda kalar nasihar da nasmat ta mata gabadaya
jikinta yayi sanyi.... Duk abinda salmah ta fada gaskiya.... Amma abun mom din nasu da yayi
muni amma zatayi iya kokarinta...Wajen dagewa da adu'a Allah yaraba mom da wannan hali tun
kafin dad din su yasan abinda ake ciki....... Mikawa salmah hannunta tayi.... Suka rungume
juna..... Suna kuka salmah ta dago ta.... Ta share mata hawaye itama nasmat ta share ma
salmah hawaye.... Tace antyna in Allah ya yadda na daina.... Zan cigaba da adu'a Allah ya
sautata mun wannan Abu aciki raina.... Amma antyna mom na bukatar adu'armu sosai.... Abun
yayi muni dan Allah Anty kidinga sata a adu'a kinji.......
Tace naji kema ki dinga adu'a kuma indan mun koma gida kije kinemi yafiyarta.... Kinji gyada
mata kai tayi tace insha Allah zan aikata.......
Miqad bayan ya huta.... Ne dan tunanin salmah ya hanshi sakat.... Tunda yadawo yake
tunaninta ganin jarabarta kawai yakeyi yana murmushi..... Yace nayi mata insha Allah.... Wanka
shi yasha cikin manya kaya idan ka ganshi sai ka rantse ango ne... Iya haduwa ya hadu.... Gun
mahaifiyar shi yaje cikin annashuwa ....tace bunnaya illa aina tazhabul min hazal... Har.....
Dariya yayi yace Ummi na balarabiyya..... Kimun adu'a Ummi.... Tace kullum acikin ma ita
nakeyi.... Allah yamaka albarka.... Kaji dana.... Yace ummina wannan adu'ar ta musamman
ce.... Ta Neman dace ne.... Tace bunnaya kayi isthakar kuwa yace ai dole Ummi.... Sha'anin
Neman aure..... Baisan. Sanda maganar ta kubce mai ba.,.. Dan shi yafi so komi ya kankama
tukunnah......tace Alhamudillah Masha Allah..... Allah yatabbatar mun da alkhairi..... Kace abun
nema yasamu..... Mikewa yayi yatafi.... Cike da farinciki.... Kamar ya riga ya dace ne.....
Basu da nisa sosai dan haka a hankali yake tukin shi.... Kira'ar Ahmad sulaiman na tashi.....
Har ya iso abun shi.... Dake ya nuna card din da aka bashi direct gidan yashiga yayi fakin.......
Gate man ne yasanar da Alhaji cewa akwai bako........ Sai da gaban Hajiya yafadi dataji cewa
salmah ake nema....... A fusace tace kaje kace bata nan..... Dad yace yi tafiyar ka Mallam haliru
kace ina zuwa ko...... Haka ake tarbar bako....... Agidana.... Hajiya kamar ta mutu indan yanxu
akwai abinda bata so bai wuce ace ana son salmah ba......
Typing.......
By:H.@.S
[3/3, 2:54 PM] H.@.S頎柬己頎柬几:
AUREN JINSI
4-3-2018
Typing.... 81 to 85
Dedicated :to my brother....
So fans kun jini shiru jiya hakan yasamo asali ne da rashin lafiyar kanina... Yana hospital a
kwance duk wanda yasamu page dinan dan Allah yatayamu addu'a.... Nagode
Kuma nagode wadanda kuka kira kuka ji dadlli....
home of my qalam writer's also.
Yana daya daga cikin dalilan data sa aka turo salmat karatu waje... Salmah Sam bata da
ra'ayin karatu a waje haka shima dadynsu... Shi yafiso yaranshi suyi karatu agaban shi saboda
gudun lalacewar tarbiyya a wannan zamani.... Cikin kwarewa Mom tasa Alhaji ya turo salmah
karatu waje cewar hajiya hankalinta yafi kwanciya... Kuma ta manta da abinda yafaru da ita.....
Dad na yamike ya aje Spoon din hannun shi yace hajiya ta yakike so ayi ne duk sanda salmah
zatayi bako tun bayan kamal sai Kin nuna ranki bayaso.... Nasan kina tunanin abinda yafaru
abaya ne... Wanda duk wanda ya tuna irin cin fuska da akayi mana zai ji ba dadi amma kisani
ba duka aka taru aka zama daya ba kowa da irin fahimtar sa ko kina so mu dafa salmah
mucinyeta.... Ko uba na auran yar shi ne.... Ko kuma da bakya so wani ya zo gunta ke zaki
aureta ne intambayeki?
Mom kam da zata iya Bada amsar tambayar nan da taji dadi.... Tace haka bazai yuyu ba
amma ina me tabbatar ma abinda yafaru jiya to shi zai faru yau... Kuma duk wanda yace baya
sonka da safe.... Dan Da rana yazo yace yana sonka karya ne.... Amma bana fatan bara ta
dawo bana ina jiyewa salmah.... Dad kafadar mom yadafa yace insha Allah yata bazata kara
dandana irin bakinciki datayi abaya.... Kuma ina ma yara nan kyakyawar fahimta dukkansu ban
ware ko daya acikin su ba..... Salmah mutum daya zata Aura... Dan haka bazan hana kowa
neman auren salmah ba... Mutakar na yadda da addininsa da kuma Dani'unsa.... Ki kwantar da
hankalnki kiyi wa yayanki addu'a dafatan alkhairi.... Bakin ganin ko nasmat ta isa aure ba ma
salmah ba... To me zakiyi dasu dukka acikin gida...... Bayan Allah yace indan Sun kai lokaci
hakkin mu ne muyi musu aure.... So dan Allah ki janye kudirinki.... Ki tayani lallamin salmah....
Barinje in salami bako..... Mom kamar tayi kuka saboda wani kululun bakinciki ne yatokare ta....
Kwana biyun da salmah tayi kullum da tunaninta take kwana .......
Dad gun miqdad yaje a masaukin baki... Miqad yana ganin shi yace sannu abba... Yana
dukar da kai yace abba ina yini.. Abba murmushi yayi yace lfy dana.... Ya rana ya kuma hutu
yace alhmdlh.... Dad zama yayi yace miqdad nasan salmah kazo nema ko.... Ya Asma mai da A
amma kanshi na kasa.... Dama kasamu wani information akanta yace no. Abba amma dai tace
mun ita matar aure ce.... Shiyasa yau nazo inji gaskiyar maganar..... Abba murmushi yayi
saboda agidar da salmah ta dasama zuciyarta yafara tasiri..... Yace salmah ba matar aure ba
ce...... Amma Kuma amatsayin datake yanzu kusan a haka take..... Ido miqdad ya zaro dan
yafirgita sosai ....Dad yace kwantar da hankalinka dana.... Salmah ta gidaya ma kanta wani
shardi na bazata kara saurayi ba saboda wani irin kalubale data fuskanta.... So ni abu daya zan
gayama ni bazan ma yata auren dole ba.... Kayi kokari ka Nemo soyyayar salmah da
hannunka...... Ita mutum ce me saukin kai.... Amma zaka gani da idonka.... Amma yanzu bata
nan tana gun yar uwarta a hospital.... Miqdad ba karamin dadi yaji ba saboda shi duk wani wasu
steps da suka rage ganin su yakeyi Sun fi komi sauki..... Yace Dad dan Allah ka taimake ni da
contact dinta.... Dad baiyi musu ba yabashi dan yasan waye family margayi..... Kuma zai so ya
hada zuri'ar shi da wannan babban family.... Yace Dad amma wani hospital ne yace karka damu
yau insha za'ayi discharged nata..........
A hospital kuwa da salmah da nasmat hirar su sukeyi cikin nishadi da fahimta da kuma
kulawa da shakuwa irin na yan uwantaka..... Tace Anty ranar da mukayi waya dake nake ce
miki yaushe zaki fito da miji musha biki.... Sai naji muryarki ta shake kamar zakiyi kuka......
Salmah tace saboda ni banda saurayi Kuma bana so ma nayi..... Saboda ni bana she'awar
auren yanzu..... Kin gane sis yanzu ba lalle ki fahimci ni ba amma indan nabaki lbr waye jalal da
Kuma kamal zaki tayani yanke hukunci game da soyyya.... Tace to Anty kira Dad yazo ya maida
mu gida..... Tunda anyi discharge dina..... Kunawa tayi.... Taga sako sunata shigowa.... Bata
dade ba wayar tafara ringing..... Kin dauko tayi wata number ce still ta shigo an rubuta My
childhood frnd.... Dariya tayi ta dauka....daga dayan bangaren akace ke kullum sai Kin ja aji ne
before picking ne.... So yakike so ayi.... Wama yagaya miki nashigo 9ja me........ Hmmmm
mutane mana..... Akwai News ne.... Sai nazo ina little din mu ne.... Tace itace ma bata da
lafiya..... Subhallah meya sameta.... Ke fever ne kawai tasamu sauki ma...... Ok Allah yabata
lfy.... Amin
Ina baby mu da kuma oga..... Duk lafiya.... Waike frnd sai yaushe zamu sha bikine.... Tace
yanzu mana.... Kin fiye wasa dayawa... Pls keep juck aside...... Wai ina jalal ne..... Tsaki ta ja ta
kashe wayar.... Mutum bazai taba zama lfy ba batare da an bata me rai ba..... Ke ungo kira Dad
din barin hada kaya kinji.........
Nasmat na searching contact din Dad hannunta ya janyo wani text ya bude..... Karantawa
takeyi..... A hankali taga ansa dan Allah ki taimake ni ki aure ni...... Ni macece amma zan iya
biya miki bukatarki wallahi komi yawan bukatarki dan Allah ki fahmce ni..... Ni me sonki ce.......
Sallati nasmat ta kurma..... Salmah ce ta juyo dan ganin abinda ke faruwa..... Ganin nasmat na
kallon waya kuma tana sallati tana hawaye yasata karasaw gun...... Mezata ganin
Typing.....
By:H.@.S
[3/4, 2:15 PM] H.@.S頎柬己頎柬几:
AUREN JINSI
4-3-2018
Typing..... 86