Showing 33001 words to 34100 words out of 34100 words
Chapter 12 - A Jininsa Yake Book 3 Zulaihat Sani Kagara
shi yasa
Ubangiji ya halasta shi.
Haka kawai ta dauki bakin kishi ta dorawa
kanta, daga nan ne za ta fadawa hallaka.
Allah ya kiyashe mu.
Zarah ta kamo hannun ta, suka runtse,"Kin yi
gaskiya amarya, shi yasa na ke wa Allah godiya
da yasa ke ce abokiyar zama na." Ta yi
murmushi,"Ni din Antina? Na fi kowa farin cikin
samunki. Allah ya k'ara hada kan mu, ta yadda
yayanmu zai ci gaba da samun kwanciyar
hankali.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Tafi suka ji ana yi ta bayan su.
Duk suka waigo,yayan na su ne a tsaye yana jin
su. Ya zagayo suna dariya ya tsaya gaban su, ya
ce,"To a matsa min in zauna." Suka ware ya
zauna tsakiyar su." Allah ya kamaku, ashe zama
ku ke kuna gumalta ko? Zarah ta kama baki,
"Lah!
Allah mai halitta, jaba ta dubi bakin mijinta.
Gulmar me kuma a mu ka yi ta ka?
Ya kamo kunneta. Nusaiba na kwasar dariya, ya
ce,"Ita jabar 6ata dubin ta ba ne? Ta ce,"Oho."
Ya k'ara murdawa, ta yi k'ara. Nusaiba ta kamo
na shi ta ce,"Allah sakar min Antina, ko ni ma in
cire na ka. "Ya saki ya dube ta,"I see, kun hada
kai ko?
O.k, yayi kyau, ke ba zan ta6a ba, kin zama
yangwam!
Amma ke, za mu hadu."
Duk suka yi dariya.
Ya rungumo kafadansu ya sake fadin,"Allah ya
yi maku albarka, kun zama abin alfahari na, kun
zama jigon rayuwa ta.
Na kuma gane rayuwa shirin Ubangiji ce,
mutane da yawa suna samun dama, amma sai
su ki amafi da da damar har ta wuce su, daga
baya su zo suna cizon yatsa.
Allah ya ba mu ikon amafin da damar mu."
Suka nisa suka amsa da Amin.
Kowacce ta dora kanta bisa kafadar gefen sa.
Suka yi shiru na 'yan dakikai.
Cikin shirun ne suka ji kamar suatin T.V, a wani
sashi na gidan. Naseer ya ce ,"Wai ba duka
yaran nan sun taifi makaranta ba?.
Eh mana."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Ya mike yana fadin,"Ga sautin (Game) can ina j?
Duk suka mike suka bi shi sashin yara. Ameer
ne ya kuke yana buga Game na tseren Polo,
sautin T.V ya rage can k'asa, yi yake kamar zai
tashi sama, sbd kwaikwayon yadda dawakan ke
gudu. Naseer ya lalla6o ya cafke kunnansa, a
tsorace ya waigo manyan idanuwan nan na sa.
Suka kara yo waje tamkar Naseer a zamanin da
yake shagalinsa a filin sukuwa.
Bai tanka masa ba, yai ta jan kunnan sa har
falo, sai su Zarah ke ta faman salati suna
fadin,"Amma dai Ameer Allah ya shirye ka!
Ya tsaya ya k'are masa kallo, kafin ya ce,"Kai ne
babba, amma babban kwabo? Kullum da kai ake
complain! To zan kwashe Game din tunda shi ke
hana ka zuwa makaranta! Yayi sukuiti yana
kumbura.
Nusaiba ta zungure shi, "Maras kunya, sai anyi
magana, ya rink'a cika yana hura hanci, wa ka fi
zuciya? Come on wuce ka dau ko jaka Lado ya
kai ka! Zarah ta kamo shi,"Wuce mu je, ka
dauko jakar, kai ba ka ganin kannin ka sun tafi?
Ta raka shi ya dauko jaka. Nusaiba na ta fada,
ta fita ta kira Lado Direba, yasa shi a mota zai
wuce da shi."
Nusaiba ta zauna kusa da Naseer ta ce,"Ameer
sai addu, ace yaro baya maida hankali a karatu.
Sai game din tsiya? Shi yasa ban so ka kawo
masu wannan sabin Game din ba."
Ya ce,"Zai bari ne." Zarah ta dawo ta zauna inda
ta tashi,"Ameer kenan an dai tafi ana ta
kunci,"Nusaiba ta ce,"Ai kin ji Babansa ya ce zai
bari ne, amma complain din Ameer yayi yawa,
ko makarantar kuka suke da rashin maida
hankalinsa, ga masifa, ni na rasa irin sa."
Ya ce,"Ni kuwa in na kalle shi, dariya yake ba
ni." Kin ji ko Antina? Ta ce,"Ya dai kamata ka sa
baki, ka yi masa fada sosai, kafin ka bar garin
nan, kila ya fi jin na ka. Ameer yan aikin gidan
nan bai kyale ba, haka 'yan kanninsa. Aliyu
kadai bakin sa ke ceton sa da yake duk gautan
ja ne.
Baba na da Alhaji kuwa, sai dai su yi kuka su
share hawaye, balle kuma 'yan matan."
Ya kama kai, ya ce,"Wayyo Abba na, duk
wannan laifin shi kadai? Wai ba yarinta bace?
Nusaiba ta ce,Yarinta? Me yasa............
Ya katseta,"Ya isa! A yimin shut up nace! Rashin
jin nan fa kowa yayi shi, ke kin yi, ke ma kin yi.
Ni ma na yi."
Nusaiba ta ce,"Oho, ashe abin gado ne, ta
6angaranka, amma mu ba muyi rashin jin kin
zuwa makaranta ba."
Yayi 'yar dariya ya ce,"Yan rainin wayau, kun
cika ni da , kamar ban san sirrin kowacce ba."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Zarah ta gyara zama ta ce,"Ai sai ka
fadi"Yalla6ai, mu na ji." Ya dube ta, ya ce,"Ke fa
kullum ki na like bayan taga, ki na zuba ihu,
hawaye sharaf-sharaf, majina har baki. Da an
tambaye ki menene? Sai ki ce kudin (Break) dina
ne suka 6ace."
Ya fadi yana kwaikwayon muryart har da
shashshekar kuka.
Ya juya kan Nusaiba,"Ke kuma ai Abba ya gaya
min da zarar Direba ya fito da mota, zai kai ki
makaranta, sai ki ce kashi ki ke ji."
Ni din?
Zarah ta ce,"Ke ma ki ka tsaya tambayar sa. Ta
figo filon kujera. Nusaiba ma ta dauko na ta,
suka rufe shi da duka.
Me zai yi ba dariya ba, yana fadin,"Mugaye,
k'arya na yi.........?
Na kwashe 'yan biro na da takarduna na bar
gidan, don ba zan iya ceton Naseer ba.
Tsokanar fada A JININ SA YAKE!!! ,
saboda haka ALHAMDU-LILLAH, na gaji da
shari"a.
Idan kuma akwai ma iyawa, to Bismillah!
Jah-Jah na can yana dakuwa a hannun zaratan
matan sa.."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
afuwan bakujini da wuriba sakamakon wayata
tadan samu matsala, daga bayakuma nadanyi
rashim lafiya, your prayer is needed pls
Zaharaddeen Shomar
Whatspp 08168575100