Showing 6001 words to 9000 words out of 34100 words

Chapter 3 - A Jininsa Yake Book 3 Zulaihat Sani Kagara

ta."Suka
dungoma cikin dakin, shiru suka yi suna kallon
ta kawai, don kar su yi surutu ta farka. Sun
kusa minti 10 a tsaye, sannan suka fito dan
koridon. Naseer ya baza darduma, suka
zazzauna. Ya koma gefe ya zauna, suka ci gaba
da tambayar sa yanayin jikin na ta?
Ya ce,"Da sauki, an gode Allah, amma ko dazu
ta sha kuka, kuma ta k'i magana, abinda ma ya
sa ta barci ke nan."
Antin Jordan ta goge kwalla, ta dubi
Alhj,"Gaskiya yaya idan babu wani ci gaba a fita
da ita waje kawai." Ya ce,"Wannan maganar na
rai na, akwai iiya kwanakin da na dibarwa
Likitocin nan din ne, idan sungaza, zan dauke
ta."
Ta ce,"Wannan tashin hankali da yawa yake." Ya
ce,"Jarabci ne, mun gode Allah, muna rok'onsa
sauki.
Kai Naseer ka yi ta hakuri, ka ji?
Ya ce,"Hak'uri na mu ne duka Abba."
Haka suka kasance tare, jama'a na ta zuwa
kamar kullum. Koda ta farka. Naseer ne kawai
ya shiga, ya kai mata Bebi. Allah da ikon sa
babu kuka, sai hira kamar ma ba ita ta sharari
kukan dazu ba.
Yayi mata burosh, ya bata Tea, ta sha. Abin
yana ta 6a Antin Jordan mmk har ta

tambaya,"Yanzu ina shiga, sai ta fara Ihu?,
Ummi ta ce,"Ko za ki gwada ne?
"Don daukan alhaki? Na gan ta ta taga, ya isa.
Allah ya yaye mata."
Ta ce,"Amin. Kwananta 7 ta koma Jordan.
Ranar da ta tafi, ranar Kausar ta iso da mijinta.
Bata 6ata lokaci ba, ta fadawa dakin, kanta ta yi
ta rungume ta sa kuka. Wani ihun da Nusaiba ta
yi, dole ta sake ta, tana kallo, jiki na rawa. Ta
runtse ido, tana zagi tana fadin.
"Ban son ganin su. Ban son ganin su! Naseer ya
rirrike ta. Mijin Kausar ya fito da ita, me za ta yi
ba kuka ba. Haka ta fada jikin Ummi, tayi ma
isar ta. Naseer kuwa da kyar ya shawo kan
Nusaiba tayi shiru, ta daina zage-zage. Ba
karamin Huashi Kausar ta bata ba, sbd ta6a tan
da tayi.Yini guda masifar da ta rink'a yi
kenan,"Wata munafuka ta zo ta cakume ni za ta
kashe ni! Sai bayan la'asar tayi barci. Kausar ta
je gun ta, tayi mata addu'o'i. Hawaye na zuba.
Da yamma lilis suka koma Kaduna.
Haka Kausar ta tafi da bak'in ciki, a duk lkcn da
ta tuna hawaye, ke zubar mata.
(Allah sarki Nusaiba

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100



Ajininsa yake 3-02
Posted by ANaM Dorayi on 08:53 PM, 20-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______



Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi


------------------------------------------------------------------------------------------------


To shi kenan ya wuce." Ya kamo ha6ar ta, yi
dariya,"Yi dariya 'yar gidan Abba!

Ta fado kirjinsa, tana murmushi.

Ya rungume ta, ya runtse ido, wasu kwalla suka
yi masa caa, fadi yake a ransa, "Son ki ya kama
ni Nusaiba, ki yafe min don Allah.". (Hhhhhhh,
Anzo gurin, ammafaaaa...uhm! Maji ma gani)




Bai ko san ta kici-kicin tashi ba, sai da ya ji tana
kira,"Abba!

Ka shake ni!

Ya hanzarta sakin ta, yana goge kwallah. Ta bi shi
da kallo,"Wash!

Ka wani matse ni Abba, ai sai in mutu."Ya tashi
ya bata wuri, ya shige bayi ba tare da ya ce
komai ba.

Jim kadan ya fito, ya wanke fuskarsa, kwance ya
same ta, ya matsa gabanta ya ce,"Hirar ta isa
haka, ki yi barci ki huta." Ta amsa da ka, ya
duk'o ya sumbace ta, ya ja mata mayafi. Ya ja
kujera ya zauna, ya sauke numfashi,"Allah ka ga
iya kokarin da na ke yi. Allah ka taimake ni
yarinyar nan ta sami lafiya.

Ta ce,"Ka kwanta mana Abba." Ya ce,"Zan
kwanta, ke dai yi barcin ki." Ta rufe ido.

Tare da gyara kwanciya.

Da asuba ya fito bayi da alwalar sa, ya shimfida
sallaya, yayi sallah. Ya jima yana addu'o'i kafin
ya jiyo motsin ta.

Ya waigo yana kallon ta, ta tashi zaune, tayi mika
tana salati. Ta kalli can, ta kalli nan, bai ce da ita
k'ala ba.

Ta k'ura wa Bebin da ke barci cikin (Net)
ido.

Ta dago kai ta dube shi, suka yi ido 4.

Yayi murmushi, ya ce,"Kin ta shi?

Fashewa tayi da kuka, ya taso da sauri ya zauna
gefen ta."

Nusaiba, ke Nusaiba, za ki fara koke-koken nan
ko?


Tayi shiru tana tunaniin Antin ta.

Hawaye na ta ambaliya.

Ya rik'o ta, ta kwace jikin ta, kuka take tana
k'arawa.

Ya ce a ran sa,"Na shiga 3, yau kuma da kukan ta
tashi." Ya matso, ta matsa. Ya ce,"Ni Nusaiba, ni
ki ke gudu? Bata kalle shi ba, balle ta ce wani
abu. Ya sake matsowa, ta matsa. Ya ce,"Shi
kenan, bari in yi tafiya ta, in tafi ko? Ta amsa eh,
da kai. Ya ce,"Tabd'i! Da magana yau,"Cikin
ransa.Ya rasa yadda zai yi, dole ya sa mata ido,
tayi ta kuka. Can kuma ta tashi ta fito koridon ta
zauna, bisa kujera. Shi ma ya biyo ta nan ya
zauna, yana gadin ta.

Jim kada ya ji kukan Ameer.

Ya mike ya ce da ita,"Ga Ameer can ya tashi, in
kawo shi ya sha? Ta kyale, bai ma ishe ta kallo
ba, ya shige ciki ya dauko shi, ya tsugunna
gabanta,"Yauwa, 'yar gidan Abbanta kenan, dubi
Bebin mu kuka yake yana jin yunwa, dan ba shi
ya sha." Ta dauke kai, tamkar bada ita yake
magana ba.

Abu fa ya gagara, dole ya dauko wa Ameer fida
ya tura masa, yayi ta tsotson ruwa da
glucose.

Kullum karfe 7 nan take masu. Alh.Basheer suna
nan zaune kuwa, sai ga su.

Naseer ne ya fara hango su, ya mike ya nufo
su.

Su ma tsayawa suka yi cak, ganin Nusaiba a
zaune wajen.

"Yaya dai? Alh.Basheer ya tambaye shi, yayin da
Ummi ta kar6i Ameer a hannun sa.

Ya ce,"Ai yau ko Ameer ta k'i ba shi nono.

Kuka kawai take yi,"Ya ce,"Likita ya zo?

Ya ce,"Ka tsaya nan, kai kuma koma gun ta, bari
in nemo Likitan." Ya koma wajen ta.

Alhj ya zaga ya wuce, ita kuwa Ummi ta
lafe.

Jimawa kadan suka dawo da Likita. Abin ya ba
Naseer mamaki daya ga Lkita ya zo, ya tsaya
gabanta bata zage shi ba.

Ya ce,"Nusaiba, tashi mu shiga ciki, mu yi wata

magana." Kai tsaye ta mike ta wuce. Naseer ya
saki baki, shi ma ya taso ya biyo su. Ta zauna
bakin gado, ya jawo kujera ya zauna ya
ce,"Kukan me ki ke yi?

Ta ce,"Antina ta mutu ko?Ya ce,"An gaya miki
bata mutu ba, Antin ki na gida." Ta runtse ido
wasu hawayen suka tsunke mata, ta sa hannu ta
share. Ya ce,"An ce kin ki ba Bebin ki nono,
saboda me? Haka za muyi da ke saboda Allah?
Ta dube shi da kyau ta ce,"Doctor ka yi min wani
taimako don Allah, lambar Abba na zan ba, ka
kira min shi." Idanuwan Naseer suka k'ara yo
waje, ya koma da baya da baya ya fito waje. Shi
kuwa Likita k'ara tsura mata ido, ya ce,"Abban
ki? Ta ce, eh. Ya ce,"Ina zuwa." Ya leka yayi kiran
Alhj da hannu. Ya taso daga inda yake zaune ya
zo. Likita ya kamo hannun sa, ya shigo da shi a
hankali. Kan ta na duke ya ce,"Wannan Abban
naki ki ke nema? Tana yo ido hudu da shi, ta
mike hawayenta suka yawaita, ta ce,"Abba! Wani
tsananin farin ciki ya kama Alhj, dole kwalla suka
cika idon sa, ya ce,"Bebin Abba! Ta rugo da gudu
ta rungume shi. Tuni Ummi ta fado dakin ta hade
su ta rungume, kuka suke saboda murna. Haka
Naseer ke sharar kwalla. Amma ya rasa abinda
zuciyar sa ke sakawa game da wannan al'amari.
Tabbas Nusaiba ta warke, to me zai biyo baya?
Da alamun zai shiga magana, yanayin da ta
nuna. Yayi ta maza ya shigo. Alhj Basheer ya
rungume shi, suna wa juna barka. Likita ya fita,
ya bar su cikin farin ciki da murna maras
misaltuwa.Bayan sun natsa. Ummi ta dubeta,
duk ta rame ta ce,"Sannu Nusaiba, Ubangiji Allah
ya k'ara karewa." Ta ce,"Amin. Ta miko mata
Bebi ta ce,"Kin ga Bebin da aka ciro miki? Ta dan
dube shi, tayi murmushi , ta dauke ido,"Na gan
shi Ummi ta. Kwalla suka taru fal a idonta, ta
kasa shanye su, sai da suka zubo. Abban ya
rungomu kafadunta, ya ce,"Yi hakuri daina kuka,
komai ya wuce Insha-Allah." Ya ce,"Allah ya
yarda Abba. Bari in yi sallah." Ta mike ta wuce
bayi ta jima bisa sallaya, tana yi wa Allah godiya
daya dawo mata da rayuwarta dai-dai. Ta dawo

gefen gado ta zauna kusa da Abban ta. Ya jawo
ta jikin sa, ta dan numfasa ta ce,"Abba lokaci yayi
da zan gaya maka wata magana, ina fatan za ka
gafarce ni." Naseer na jin haka, ya mike ya bar
dakin. Abba ya ce,"Babu komai Bebina, gaya min,
me ke da mun ki? Ummi ta sa masu ido tana
kallo. Ta k'ara gyara zama ta ce,"Na san za ka yi
mamaki, idan na gaya maka cewa tun aure na da
Naseer, babu kwanciyar hankali tsakani na da
shi. Ai kuwa Alh ya sha mamaki, ba shi da kadai
ba har Ummi da take zaune. Ya kara dubanta,
baki sake, ya tambaya, "Saboda me? Ta
ce,"Abinda na fahinta,"Abba, shine ya kar6i aure
na ne kawai don ka cika masa ido, ba zai iya ce
maka a'a ba. Amma a hakakin gaskiya Naseer
baya so na, kuma ya nuna min kiyayya, ba don
Antyna na tsaye ba, ina ganin wuyar da zan sha,
ba 'yar k'arama bace.

------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Shi yasa na ke son ta, domin tayi min komai,
kuma tayi iyakar kokarinta wajen jawo hankalinsa
zuwa gare ni, sai dai haka bata samu ba, saboda
babu sona a zuciyar sa." Ransa ya 6aci kwarai, ya
ce,"Me yasa tuntuni ba ki gaya min ba? Ta
ce,"Saboda kai ne Abba. Ba na son wani tashin
hankali ya shiga tsakanin ku. Kuma ina ganin ai
ya girmama ka ne, tunda ya kasa fitowa fili ya
nuna maka baya so na. Shi yasa na yi ta kokarin
zama da shi shekara daya da rabi, sai da Allah ya
kawo rabon wannan Yaron, sannan ya shiga daki
na. Daga baya na yi tunanin bai kamata mu

zauna muna cutar da juna ba, shi yana jin haushi
na, ni ma ina jin na shi. Sai na same shi a daran
da wannan abin zai faru, na yi masa magana.
Abba cewa yayi idan na k'ure shi, zai 6atacciya,
dole in koma gidan mu, har d'an baya so, ya bar
mana...................!!! Tana shiru. Ummi ta
cafe,"Ina, inda kuma yayi karya kenan. Ai ba mu
kai masa ke da Da ba." Alh.Basheer yayi shiru,
zuciyar sa na tafasa, abin kamar a mafarki yake
ganin sa, domin ko alama bai ta6a mafarkin
Naseer zai ci amanar sa haka ba. Ya dubi Ummi
ya ce,"Har hada mata kayan ta mu tafi." Ta mike
tana fadin,"Ashe ga damuwar da ta kusan hallaka
rayuwarki Nusaiba, kenan. Yayi wa kan sa. Kuma
sai Allah yayi miki sakayya." Nusaiba ta kada
kai,"Ba haka bane Ummi ta, ba laifin sa bane,
kar ki manta soyayya, gamon jini ce, laifin sa 1,
shine daya danki amanar da ba zai iya rikewa
ba."Alhj ya ce,"Duk laifin iyayen sa............ Tayi
saurin katse shi."A'a Abba, iyayen Naseer ba su
da laifi kuma ina mai tabbatar maku yadda ya
yaudare ku, haka ya yaudare su. Ba su san komai
ba a game da zaman mu. Sun rike ni tamkar 'yar
cikin su. Idan na ce ga abinda su kai min, na yi
masu karya, sai Allah ya tambaye ni. Abba, rokon
da zan maka daya ne, don Allah, don son Annabi
kar ka k'ullaci kowa akan maganar nan, ni ce
baya so, to ka dauki 'yar ka. Ai shikenan, an
gama magana." Ya ce,"Haka ne Nusaiba, ki yi
hkr, ni ma na gane kuskure na, ni na jawo miki
duk abinda ya same ki." Ta ce,"Ban ta6a ba ka
laifi ba Abba, ba kuma zan ta6a ba ka ba. Ai kai
alheri ka k'ulla, sai dai ka san a wannan zamanin
ba kowa yake son ayi masa za6in abinda ya
kamace shi a ruywar sa ba. Ya fi son abinda
ra'ayinsa ya ba shi. Ka ga kuskuren da aka samu.
Ina alfari da kai Abba na, kuma ko a yanzu ka
sake za6a min miji. Wallahi zan aure shi. Bai san
lkcn da ya rungume ta, ya fara kwalla ba. Haka
Ummi ke ta share hawaye, tana sawa Nusaiba
albarka. Ta mike ta shiga hada kaya. Hayaniyar
hama'a suka jiwo gaba daya jama'ar Naseer ne.
Zarah ma kayan barci ne ajikin ta, ta dora zani ta

sa hijabi. Suka doro cikin dakin. Zarah na
fadin,"Amarya!Ta zaburo da gudu, "Antina! Suka
rungume juna, sun sha kuka, sai da Umma ta
raba su ita ma, ta rungume ta. Daga nan ta
matsa ta gaida kowa. Su Malam Balarabe, Malam
Umar. Ya gaisa da Sageer da amayar sa. Bayan
an gama gaishe-gaishe. Malam Balarabe yasa aka
yi addu'a, kowa ya shafa. Aanan suka lura babu
Naseer tun shigowar su. Inna ta fara
magana,"Jama'a wai ina dan Inna ne? Malam
Umar ya ce,"Kai wai dama babu Naseer a wajen
nan? Sageer ya amsa,"Ai kuwa baya wajen nan,
tunda muka zo? Malam Balarabe ya ce,"Ah to ina
ya je? Ya fadi, yana kallon Alh.Basheer. Ya
ce,"Gaskiya ban san inda ya je ba. Kuma dama
ina son ganin ka, idan ba za ka damu ba." Ya
ce,"Bismillah Alhj, ba damuwa." Suka fito waje,
yayin da Zarah da Nusaiba ke like da juna suna
maida yadda abubuwa suka faru. Alh.Basheer ya
kebe da M.Balarabe, ya kwashe bayanin da
Nusaiba tayi masa kaf, ya gaya masa. Tun da ya
soma magana, gaba daya jijiyoyin jikin Malam
Balarane suka tsinke, jiri ya fara dibar sa. Allah
yasa a zaune suke, da babu abinda zai hana shi
faduwa. Tabbas ya san Naseer baya son auran
nan, aka yi shi, amma ko alama bai ta6a sanin
rashin mutunci da wulakancin da ya rinka
aikatawa ba. Ya jima kafin ya ce,"Alhj wannan
magana ta ban kunya, kuma Wallahi tallahi ban
san komai a game da zancan ba. Nusaiba bata
nuna mana ba, balle ta furta da bakin ta. Don
girman Allah ka yi hakuri Alhj. Ya ce,"Ai magana
ta k'are, tunda baya son ta, ni ina son abata
kuma zan tafi da ita, ba tare da 6ata lkc ba.
Amma D'a, ban sako mata shi cikin gara ba, sbd
haka nan za ta aje shi ko ya kashe ko ya bar shi
da rai, duk ya rage nasa. A karshe, ka gaya masa
na gode. Allah ya saka da alkhairi. Kan
M.Balarane yayi gingirinn! Kunya kamar ya nutse
kasa. Idanuwan sa suka cika da kwalla, ya rasa
me zai ce wa Alhj? Kawai sai ya juya ya dawo
dakin, gaban kowa ya daga murya ya
ce,"Nusaiba, don me za ki min haka???Akan me

za ki zauna sama da shekaru 2 cikin wulakanci da
bak'in ciki, amma muna tare, ki kasa gaya min?
Ba ki min adalci ba Nusaiba, domin da kin gaya
min da tuni na yanke hukunci, sai dai ya nemi
wani uban, ba ni ba! Kowa yayi tsuru-tsuru.
Nusaiba kuwa tuni ta fara kuka. Ya matsa gadabn
Ummi ya tsugunna." Hajiya ki yi wa girman Allah,
ki yi hakuri. D'a ne ka haife shi ba ka haifi halin
sa ba. Ko alama ban san halin da suke ciki da
matar sa ba. Ga mahaifiyar sa nan a zaune, ko
ita da ke zama tare da su munafikin Yaron nan
bai ta6a barin ta gane wani abu ba, balle ni da
ban zama cikin gida. Maganar tafiya da Nusaiba
kuwa kun yi dai-dai, domin ko ni ne hakan zan
yi. Saboda haka kowa yayi shaida. Ni Balarabe na
tsame hannu na akan komai daya shafi Naseer,
duk abinda ya ga dama yayi rayuwa
ce................ Ya fashe da kuka, jikin kowa yayi
sanyi, matan da ke wajen ma tuni suka soma
taya shi, musamman Umma da ta ji abin kamar
saukar aradu. Sageer ma waje yayi kirjin sa na
bugawa, ga ranar da yake jin tsoron zuwanta,
kullum yana gaya wa Naseer. Amma kunnuwansa
iskar duniya ta dode masa su. M.Umar da Alhj
suka riko M.Balarabe,"Ka yi shiru haka,"Malam
Balarabe, kar zuciya ya kwashe ka, ka yi masa
baki." Ya dube su ya ce,"Ni Naseer yayi wa tijara
haka, Babu komai, rayuwa ce!Ya dubi Umma ya
ce gaba,"Ke dauko masa D'ansa mu tafi, ki kai
masa kayansa, idan ya ga dama ya jefa shi bola!
Malam Umar ya ce,"A' ba'a yi haka bane, duk ku
zauna a sasanta magana. Ai in rai ya 6aci, hankali
ke nemo shi. Alhj ka yi hakuri, mu zauna da
Naseer mu ji ta bakin sa, don girman Allah kar ku
yanke hukunci kai tsaye haka." Alhj ya kada
kai,"Ban k'i taka ba. Amma Naseer ya riga ya
k'are magana, sai dai hukuncin daya yanke ne
ban yarda da shi ba, d'a kan ba na mu bane, na
shi ne. Don haka anan za'a bar shi. Iya magana
kenan." Malam Balarabe ya ce,"Magana tayi dai-
dai Alhj, ku bar masa shi, ya san uwar da za ta
shayar masa D'an shi. Ki dauko shi mu tafi, na
gaya miki, idan kuma ki na nan, ni na wuce! Yayi

waje. Malam Umar ya bi shi. Umma ta dubi
Ummi, ta ce,"Don girman Allah Hajiya kar ku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0