Showing 9001 words to 12000 words out of 34100 words

Chapter 4 - A Jininsa Yake Book 3 Zulaihat Sani Kagara

yi
wa Yaron nan haka, shi bai san komai ba, ku
tausaya masa." Tayi shiru, ta rasa me za ta ce?
Yadda Alhj ya fusato, babu mai sa shi dukan
D'an nan. Haka Zarah ta rike Nusaiba,"Amarya
kar ki ta fi, don Allah ki taimake ni. Idan ki ka
tafi da wa zan zauna? Suka k'ara fashewa da
kuka. Ita dai Fa'iza ba baki, sai ido. Bata fahimce
komai ba, take ta faman kuka. Alhj ya fice ya bar
su nan, suna ta faman magiya. Jim kadan ya
dawo tare da Likita. Shi dai ya ga ana ta koke-
koke, a zaton sa duk na murna ne, yayi abbuwan
da zai yi, ya gama ya ba su sallama tare da
takardar magunguna da za ta ci gaba da sha na
tsawon kwana 7.Alhj da kansa ya rink'a dibar
kaya yana kaiwa cikin mota, har ya kwashe su
duka. Ya kamo hannun Nusaiba, ya wuce da ita.
Ummi ta biyo bayan su, suka bar Umma da jariri
bisa gado, yana ta faman barci. Ta k'ara fasa
kuka. Inna ta kamota tana rarrashi. Haka Zarah
ke durk'ushe, hannu 2 bisa kai.

------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Daga inda Naseer ke 6oye, yana hango su Alhj
suka zo suka wuce a moTa. Yasa hannu ya goge
hawayen da ke kuncinsa. Jimawa kadan ya hangi
su Umma. Inna na dauke da Ameer, suka shiga
motar da ta kawo su. Direba ya ja suka bar
asibitin. Wasu hawayen suka sake zubo masa,
yayi kamar ya hadiyi zuciya ya mutu. Ya nufi inda
ya aje motar sa, ya shiga haka ya dawo gida,

baya gani wuri sosai. Ya rasa inda zai je, sai yayi
fakin kofar shago, ya shiga ya sallami su Abbas
ya ce duk su tafi gida. Ya kulle kansa ciki, ya rasa
abinda ke masa dadi a duniya. Cikin gidansu
kuwa kamar anyi mutuwa, shiru ba ka jin motsin
kowa. Jim kadan Zarah ta fito da jakar kayan ta,
ta lallabo zuwa sasan su Umma. Ta leko a
hankali, ta ga babu kowa, ta cire takalmanta ta
wuce sadaf-sadaf kamar 6arauniya. Tayi waje kan
ta tsaye tayi gidan su. Inna ta zura mata ido,
kafin ta ce,"Ke kuma fa? Ta shige uwar daki da
gudu. Inna ta biyota,"Na ce ke kuma fa? Kin
shige da gudu. Menene na ce? Ta ce,"Allah Inna
ni ma ba zan zauna ba. Haba ai wulakancin yayi
yawa, ko alama yayana baya jin magana. Ta
balbaleta da fada,"Laifin waye? Ai duk ku na
sane, aka rasa wacce za ta gaya wa manya, don
ayi maganin abin, sai yanzu da zance ya lalace,
za ki ce Naseer ne baya jin magana? Maza dauko
jakar nan, ki koma inda ki ka fito, tun kafin
Babanki ya k'araso gidan nan, ya sameki." Ta
6arke da kuka, tana fadin,"Ba inda za ni Inna,
idan har na koma gidan nan, to yayana ya dawo
da Nusaiba. Kuma ku matsa min ku gani. Wallahi
tafiya ta zan yi." Inna tasa mata ido tallafe da
baki. "Ki ka ce me? Lallai wuyanki ya isa yanka,
to zan ji idan kke ki ka haife mu." Ta yi zamanta
bakin gado, har Inna ta gama babatun ta, ta
fice." Na rantse da Allah ba zan koma ba, ya je
ya ci kan sa a gidan, tunda shi ba'a gaya masa
ya ji." Koda Malam Umar ya dawo, babu yadda
ya iya yi da ita, ya gama fadansa da barazanarsa
ko gezau zuciyar Zarah bata yi ba, kuma ta
rantse ta maya, muddin suka bari ta bar nan, ba
za su sake ganin ta ba. Shi yasa da ta dauko jaka
ta fito. Inna ta dauko muciya ta kora ta daki, ta
ce,"Koma daki marasa kunya, idan Naseer din ya
zo ya dauke ki! Ta maida jaka ta yi zamanta cikin
dacin rai da takaici tare da tausayin Nusaiba da
karamin goyonta.

Sageer ma da ke zaune a dakinsa, babu abinda
ya fi damun sa irin dan karamin yaron da aka
aje. Alhalin bai san komai ba. Fa'iza ta

ce,"Yakamata ku taimaka wa yaron nan a maida
shi wajen Maman shi,"Wallahi shi ne abin
tausayi, ba ka ji yadda na ke ji ba, kamar inyi
tsuntsu kai shi wajen ta." Ya ce,"Shirun nan da ki
ka ga nayi. Ameer kawai na ke tunani." Yayi
hucin zafi, ya dauko waya daga aljihu ya nemo
lambar Naseer. Ta dan jima tana bugawa kafin ya
dauka, ya ce,"Ka na ina ne? Murya dishe ya
amsa,"Shago." "To ina zuwa." Ya kashe waya, ya
dubi Fa'iza,"Wai yana shago, bari in je in same
shi." Ta ce,"To ba za ka dan ci komai ba? Ya kada
kai, bari dai in je in dawo. Ya fice, tana fadin a
dawo lafiya. Ya kwankwasa kofar shagon, ya zo
ya bude, suka koma ciki tare. Daga kallon Naseer
kawai. Sageer ya gane yayi nadama, gaba daya
ya jeme ya fita hayya cin sa. Ya dube shi a
sanyaye ya ce,"Ka ga irin abubuwan da na ke
gaya maka ko? Yanzu ina ribar wannan abu?
Kullum ina gaya maka yi wa iyaye biyayya ibada
ce, duk kuma mai yin sa ba zai ta6a ganin 6acin
rai ba. Amma Naseer na ka ji, ni ban san abinda
ke damun ka ba. Dan yaro jariri an ajiye maka
shi, ina amfanin sa? Iyayen ka na ta kuka saboda
kai, wacce irin masifa ce wannan? Ka farka daga
bacci Naseer, kai ba yaro ba ne."Ya dube shi
kwalla suka zubo ya ce,"Ban san abinda zan ce
ba Sageer, domin ni kaina na san mai laifi ne,
saboda haka duk hukuncin da aka yanke min,
yayi dai-dai. Sai dai babu wanda ya san cewa na
dade da yin nadama, sannan in na ce ba son
Nusaiba yanzu, na yiwa raina karya. Shi ya sa na
dage ba dare ba rana wajen kula da ita tare da
rokon Allah ya bata lafiya, don in samu in nemi
gafarar ta, na kuma nuna mata iya so da kaunar
da na ke mata yanzu. Allah da ikonsa sai ta sami
sauki, hankalinta ya dawo jikin ta, a lokacin da
iyayen ta ke wajen, sannan bata 6ata lokaci ba,
ta zayyane masu komai. Ka yarda da ni Sageer?
Ka taimake ni, domin ni yanzu ban san yadda zan
yi ba." Sageer yayi shiru, yana kada kai

------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga

labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Tabbas ya yarda da maganganun Naseer, saboda
yana daya cikin masu mmkin yadda Naseer ya
rinka kula tare da ririta Nusaiba, sai dai a lokacin
ya dauka saboda halin da ta shiga ne, kuma bata
son kowa ya kusance ta, sai shi. Ya nisa kafin ya
ce,"Yanzu tinkarar Abban, tashin hankali ne ba
karami ba, kuma dole ne aje a same shi, tunda
shine jigon komai. Abin yi shine, ka taso mu je
wajen sa, ayi ta ta kare ko kashe mu zai yi." Ya
kada kai,"Gaskiya Sageer ba zan iya ba.ka je kai
kadai tukuna, ni na fi kowa sanin halin Abba." Ya
ce,"Shi ke nan. Za ka jira ni a anan din ne? Je ka
dawo ina jira. Ungo key din mota don ka yi sauri.
Ya kar6a ya fito a sukwane, ya fada mota, yayi
gidan su Naseer. Yayi sallama falon Abba, a
lokacin Umma tana goya Ameer ta fito ta siyo
masa madarar jarirai, bayan ta nemi Zarah ta
rasa a cikin gidan, don bar mata ajiyar yaron
kafin ta dawo. Shi yasa zuciyan Abba ke kara
tafarfasa, ya sani babu makawa ita ma tafiyar ta
ta yi. Da kyar ya amsa sallamar Sageer. Ya shigo
a darare, ya nemi gefe ya makure, ya ce,"Sannu
Abba." Ya ce,"Me aka yi Sageer? Ya ce,"Abba
Naseer ne................Ya dakatar da shi da
hannun sa kafin ya ce,"Tashi ka tafi! Sannan idan
ka je, ka gaya masa ita ma wacce yake son ta tafi
abinta, saboda haka ya zo ya kwashe kayan sa,
ta bar min gidana in huta." Ya tashi ya durk'usa
Abba................Ya runtse idanuwansa,"Sageer ina
ganin mutuncinka, don Allah, don son Annabi ka
tashi ka tafi. In dai akan maganar abokinka ne,
na riga na datse magana, na yi rantsuwa Naseer
ba zai sake sani kaffara ba. Saboda haka ka je ka

gaya masa, shi 'yantacce ne, kar ya dami kan sa.
Tashi, kanzil ban ka kara fadi ba, idan har ni ina
isa in gaya maka. Idan kuma ban isa ba, to
kacigaba da zama. Sageer ya shiga 3, Abba ya
daddaure shi, ga magana bakin sa babu damar
fadi, yana ji, yana gani, ya tashi ya fice. Yayi
tsaye jikin mota ya rasa tudun dafawa. Ga wata
sabuwa, kuma ita ma Zarah ta yi gaba. Duk da
dai yana ganin na ta mai sauke ni, amma ba
dadi ace ita ma tana gidan su.Ya fi minti 5r a
tsaye, sannan ya bude mota zai shiga. Ya hango
Umma tafe. Ya tar6e yana mata sannu da Zuwa.
Ta amsa za ta wuce cikin gida, ya ce,"Umma ku
taimaki ni Naseer na cikin wani hali, komai za iya
faruwa da shi. Ta ce,"Shine me? Sai aka ce
karshen Umma ya zo? Ya ce,"Ba haka ba ne
Umma. Wallahi Naseer yayi nadama, tun ranar
da ta sami kan ta cikin wannan yanayin, kuma ba
shi da wani buri daya wuce idan ta ji sauki, ya
bata hkr akan abinda yayi mata. Sai kuma aka
sami akasi, komai ya yamutse. Ta yi dan
murmushin takaici ta ce,"Yaro man kaza. To
yanzu da ka zo nan ka na ta dogon bayani, akwai
Nusaiba a nan ne? Tana fa Kaduna, a gaban Ka
Babanta ya dauke ta. Ba sai ya je can ba, ya roke
ta. Menene abin zafi? Ya durk'usa bisa guiwa, ya
ce,"Ku yi wa girman Allah Umma ku yafe masa,
ke ma kin san duk abinda ki ka fadi, ba zai yuwa
ba. Sai da goyon bayan ku." Yana sa aya Abba na
tsayawa kofar zauran, bai ce wa Umma komai
ba, ta wuce cikin gida. Shi ma ya bi bayan ta.
Sageer ya sauke numfashi, ya tashi ya fito ya
tafi.

------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi




------------------------------------------------------------------------------------------------


Yana shiga shagon zama kawai yayi, ganin haka
Naseer din ma yayi shiru, ya san babu nasara.
Sun dau minti goma a haka, kafin Sageer ya
ce,"Wai Zara ma ta tafi gidan su."Ya dube shi da
sauri." Me na yimata ita kuma? Kashe ni suke so
su yi ko? Shi kenan." Ya goge kwalla. Wayar sa ta
hau bugawa, da kyar ya dauka. Yakubu ne ke
kiran sa. Ya rasa ta yadda zai yi ya dauka. Ya
dubi Sageer, ya ce,"Zo mu je gidan Yakubu." Ya
tashi suka tafi. Ya maida masa bayanin komai.
Yakubu yayi masa fada kamar zai ari baki, shi
kansa ba karamar kunya ya ji ba lokacin da Alhj
ya kira wayarsa, yana gaya masa Naseer ya ci
amanarsa. Duk da haka yayi masa alkawarin
shiga maganar, sai inda karfin sa ya kare. Shi
kuwa Naseer B ana maganar, yana kallon kowa a
dage, zuciyar sa gwanin haske, har yana addu'ar
kada Allah yasa su shirya. Amma bisa fuskar sa,
ya fi kowa nuna damuwa kamar yayi kuka. Daga
gidan Yakubu, wajen Zarah suka iso, misalin
karfe 1 na rana. Sun shigo gidan. Inna na kwashe
abinci cikin kula. Ta daga ido ta dube su, tana
amsa sallamar su. Gaban ta ya yanke ya fadi,
ganin yadda Naseer yayi wanu duhu lokaci guda.
Ta ce,"Dan Inna! An gaishe ka da aiki. Ku shiga
gani nan zuwa." Ya wuce simi-simi. Sageer ya bi
bayan sa, suna zaune. Inna ta gama abinda take
yi a kicin, ta bi su dakin. Zarah ta leko daga bayi
ta ga Inna, ta shige sai ta sadado ta aje buta, ta
suri hijabin Inna dake shanye bisa igiya ta yi waje
ta bar unguwar. "Sannu dan Inna, ka sha aiki
Wallahi, ya gajiya? , Ya sunkuyar da kai Sageer ya
ce,"Inna kuskure ne, kin kuma san ajizanci irin na
Dan-adam. Amma a yau ya gane, har ya
tuba........ Ta katse shi, tuban mazuru? Sau nawa
Naseer ke cewa ya tuba a gidan na ma kawai,
wanda na sani? Ai ba zan iya fadi ba. Yanzu wa
gari ya waya? Babu abinda ba mu gaya maka ba
D'an Inna, tun kafin ayi auran nan. Bayan anyi
kuma, ba mu fasa ba, sai dai in kafar ka bata

shigo da kai gidan nan ba, amma ba ka ji. A
fuska lafiya lau ka ke, halin ne kawai ka kasa
gyara shi, su yi dai-dai da fuskar ka. Me yasa? A
yanzu wa ka ke ganin zai iya tunkar Alhj? Babu
abinda za mu iya gaya masa, ya yarda, saboda
ka riga ka rushe ginin tun ranar zane. Naseer ya
ce,"To Inna shi kenan, haka za'a sa ido, auran ya
kare kenan? Ta ce, "Eh mana, ta riga ta gayawa
Babanta ba ka son ta, wa ka ke zaton zai je ya
ce, karya ne? Ya ce,"Gaskiya Inna ban yarda ba,
na san ana zuwa biko Inna. Sai dai in ba za ki je
min ba ne kawai

Ta yi dan murmushin dole ta ce,"Dan Inna
manya, ga laifi, ga saurin tuba. To shi kenan, ka
bari Baban na ku ya dawo, za mu san yadda za'a
yi." Ya numfasa ya ce,"Wai ita ma Zarah don ta
kara min hawan jini shine ta bar gida ko? Ina
take, sai ta ci dan banzan duka yau, in ni sa'an
ta ne, za ta gaya min." Dariya suke da Inna da
Sageer, kafin Inna ta ce,"Yanzu ta shiga bayi, za
ta yi alwala ta yi sallah." "Ina nan ina jiran ta ta
fito,." Inna ta mike,"Bari in kawo maku abinci
Sageer. To Inna. Sageer ya amsa. Ta fice,"Sageer
ya ce, "Na ciro maka wayar Rediyon can ne?, Me
zan yi da ita? Dukan mana harka mance? Tsaki
yayi ya dauke kai. Inna ta shigo da abinci ta
ce,"Ka fa ci. Sageer ka matsa ma sa ya ci. Ya
ce,"Ai zai ci Inna." Ta yi waje ta koma daki. Shiru-
shiru Zarah ta ki fitowa daga bayi. Inna ta fito da
wannan mamakin, tana tambayar kanta,"Ita
wannan zaman me take yi a bayi?" Tana sa aya,
ta aje ido bisa buta a gefe. Ta leko dakin ta
ce,"An gama dukan?" To ai ban ji kuka ba, bata
daku ba kenan." Suna dariya ya ce,"Ai bata shigo
ba Inna.." Ta gintse fara'a ya ce,"Ban gane ba?
Ga shi ta aje butar a waje. Ta juya ta fito tana
kwala mata kira, yayin da dukkansu suka aje
cokula suka fito. Kamar wasa, babu Zarah acikin
gidan. Mamaki ya ishi Inna. Ta kama baki, tana
kallon igiya babu hijabin da ta shanya. Sageer ya
ce,"Wai ita Zarah da gaske take yi? Inna tayi
shiru abin ya girmi shekarun ta. Naseer ya
numfasa ya ce,"Inna ki gaya mata, idan ta ji ina

asibiti kar ta sake ta zo guna. Zo mu je Sageer.
Ya yi waje. Sageer ya ce,"Inna ki ce Allah ya bata
hakuri. Sai anjima." Da kyar ta iya amsawa,"Allah
ya ba mu alkhairi." Shi ma ya wuce. Inna ta ja
kujera ta zauna, yau na ga zamani ni A'isha. Kiri-
kiri yarinya ta ban kunya? Suna tafe a mota
Sageer, ya ce,"Yanzu ina muka nufa? Ya
ce,"Gidan za ni, duk ayi ta ta kare, idan ma
yankana ni za su yi, su yanka. Ba shi kenan ba?
Idan kowa yayi min, ai bai kamata Zarah ta yi
min ba. Duk saboda wa na shiga wannan halin?
Ba saboda sonta ba ne? Duk ba ta ga hakan ba."
Ya furta. Sageer yayi shiru domin ya lura abokin
sa ya zare gaba daya, kar ya tofa wani abu, ya
kara masa zafi. Ya ci uban birki a kofar gidan, ya
fito yayi cikib gida, bai ko saurari Sageer ba. Sai
dai yana shigowa ciki ya tsinkayi Ameer na ta
tsala kuka. Nan da nan ya yi turus, guiwa sa ta
kwa6e, a salu6e yai sallama falon. Umma na
kokarin goya Ameer a lkcn Abba kuwa na zaune
gefe iya wuya yake. Kuma yana ji da kowa, duk
wanda ya kuskura yi masa wata magana akan
Naseer. Yana shigowa. Abba ya mike ya debi
takalman sa ya bar gidan. Naseer ya bi shi da
kallo, ya kasa cewa da shi komai, har Umma ta
gama goyon, ta sa hannu ta dauke gwangwanin
(Prisso-cream) din da ta siyo ta dora bisa firij, ta
dauki fidar ta yi waje. Ita ma ya bi ta da kallo,
sannan ya bi bayanta. Tana famfo tana wanke
fidar da soso da omo. Ya bi ta, ya tsaya a gefen
ta ya sanyaya murya,"Umma!Ji ta yi tamkar ya
watsa mata wuta. Ranta ya ci gaba da k'una
kamar ta rufe shi da dukan fitar hankali. Ya
durk'usa ya mika hannayen sa gaba gare ta.
Idanuwansa dauke da kwalla. "Umma, ki yi wa
girman Allah ki amsa min. Umma ki dube ni ki
saurari rokona. Na yi laifi Umma, amma tuni na
gane kuskure na, ku ba ni dama ta karshe
Umma. Da yardar Allah ba zan sake saba maku
ba, Umma ki taimake ni." Ta gama dauraye fida,
ta yarfe ruwan, ta juya ta koma daki tana
daddaure su yadda suke. Naseer ya nemi wuri
nan ya zanau dirshan! Sageer ya matso zai masa

magana, yayi sauri ya riga shi." Je ka gidan abin
ka Sageer. Na gode." Ya yi dan jim, yana kallon
sa,"Ka ta fi na ce, babu komai,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0