Showing 30001 words to 33000 words out of 34100 words
Chapter 11 - A Jininsa Yake Book 3 Zulaihat Sani Kagara
yafe maka yayanmu. Ya wuce."
Ya dago ya ce,"Na gode." Kin san wani abu? Ta
kada kai. Ya lalibo aljihunsa ya dauko kudi, ya
kamo hannun ta ya dora mata, ta ce "Na
menene? Kudin ki ne, canjin ki dubu 15 da ki ka
ba ni a asibiti. Ta saki baki tana kallon sa,"Kai
yayanmu, shekara 2 da rabi? Ya sake kwantar
da kan sa, ya ce,"Ba zan ta6a mancewa da su
ba Nusaiba, domin daga ranar da ki ka miko
min su. Allah ya manna min son ki a raina. A
lkcn ba wai ba ni da su ba ne, amma ba su da
amfani, tunda ban san yadda zan yi in ciro su
ba. Alhalin ina matukar bukatar su. Da gaggawa.
Kin min abinda ba zan ta6a mancewa da ke ba
rayuwa, kin taimake ni a lkcn da na wulak'anta
ki na.......... Ta rufe bakin sa."Na ce ya wuce
yayan mu, ka daina tunawa."
Ya dube ta ido cike da kwalla,"Kar ki yi
kokwanto Nusaba, Ina son ki! Ina son ki!! Ina
son ki Nusaiba!!!
Ta ce ,"Na sani." To kice kina so na in ji, ko sau
1 ne."
Ta yi dan murmushi ta ce, "Ina son ka yayan
mu.
Ga kuma kudin ka har canji na bar ma ka."
Yahayo shimfidar sosai, ya ce,"Kin saye baki na
ke nan? Ta yi 'yar dariya,"Na siya."
To me ki ke sha'awar sha? Ta
ce,"Uhm.......Cock, irin mai dan inabin nan. Ka
gane ai? Ya tsura mata ido, tana masa dariya.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaman lafiya mai ban sha'awa ga kowa ya dore
a gidan Naseer. Hankalinsa kwance, ba shi da
matsala. Ya k'are Digirinsa. Shine gwarzon
shekara, wanda ya fito da ajin farko a fanni da
yake karanta, sannan ajin farko cikin jerin
wadanda suka zo na farko a sauran kwasa-
kwasai a wannan shekara.
Don haka yana daya daga cikin masu rubuta
jarabawar tantance masu tafiya Turai don karo
ilimi tare da tallafin gwamnati. Kowa yayi masa
murna. Shi kan sa ganin abin yake kamar a
mafarki. Allah yayi gaskiya ya ce tashi in
taimake ka.
Tabbas hake ne, Naseer ya ga Zahiri.
A Kaduna suka rubuta jarabawa 'yan makwanni
tsakani sakamo ya fito.
Naseer ya haye ya ci Nasarar tafita Ingila.
Shirye-shirye ya kankama a lokacin cikin Nusaiba
ya fara tsufa, domin kuwa ya shiga wata na 7.
Ranar da zai tafi daren kasa barci yayi, saboda
tunanin shekara 1 ba zai ga iyalansa ba,
wad'anda ya riga ya aje su cikin ransa, baya son
kasancewa da kowa sai su.
A duk inda yake. Allah.Allah yake ya yi yadawo
gida, saboda tsabar son da yake musu.
Amma babu yadda zai yi, yana son ci gaba kuma
a yanzu ya tauna dadin karatu ya dandana ya
gane fa'idar sa. Kan dole ya dake zuciyar sa.
Washe gari karfe 8 na dare jirgi ya cilla da su
birnin Sarauniya. Sun kama karatu gadan-gadan,
amma kodayaushe cikin waya suke da iyalansa.
A haka watan haihuwar Nusaiba ya tsaya.
Umma ta sa ido sosai a kan ta, babu ranar da
bata zuwa Hanwa. Allah da ikonsa da safe ta
fara nakuda, ga shi Zarah na da jarabawa kuma
ta karshe ce, don kammala NCE din ta. Duk da
haka ta hada kayan haihuwa ta wuce da
Nusaiba asibiti.
Sai da ta tabbtar an shiga da ita dakin haihuwa
kafin ta kira Umma ta gaya mata asibitin da
suke.
Nan take Umma ta watsar da abinda take, ta
biyo hanya.
Tana isowa 8 dai-dai, sannan Zarah ta bar mata
Ameer, ta wuce jarabawa, ta iske an shiga, sai
da ta sha surutu, ta samu aka ba ta fefar.
Da namiji Nusaiba ta sake Haifa, lafiya lau daga
ita har Bebin.
Umma da Ameer na murna. Nan da nan ta kira
wayar Ummi, ta shaida mata ta sake sabon
ango....
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Ajinisa Yake3-06
Posted by ANaM Dorayi on 12:04 PM, 25-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
Suka yi farin ciki. Ta lallatsa ta nemo lambar
Naseer.
Suna gaisuwa, kudinta suka kare.
Tir!
Haushi ya kama ta, sai ga shi ya kira,"Menene
Umma?
Ta ce,"Ka yi Da. Nusaiba ta haihu yanzu." Farin
ciki kamar yayi tsuntsu ya baro Ingila." Ina take
Umma? Ta ce,"Ai tana ciki ba su riga sun fito da
su ba, amma sun ce lafiya kalau suke ita da
Bebin."
Alhamdu-lillah! Allah ya amfana mana." Ta
ce,"Amin. Haka ya kasance cikin doki, kamar
yadda Zarah ke makaranta cikin zakuwa da son
ta koma wajen Nusaiba.
Kafin yamma gidan su ya cika da baki 'yan barka,
angon karni kuwa ya ki barin mai jego sakat da
waya, shi so yake ji kukan Bebi, "Bebi kuma ya ki
yin kukan.
Barcin sa kawai yake kwasa.
Ranar suna, yaro ya ci sunan Alhj. Haka kuwa
suke kiran sa(Alhaji) Ya ci gaba da girma tamkar
Ameer, shi yasa idan Naseer ya rufe ido, baya
ganin kowa illah 'ya'yan sa, tamakar 'yan 2.
Watanni 3 bayan haihuwar ta. Alh.Basheer zai tafi
harkokinsa Turai, ya wuce wa Naseer da hotunan
dan sa, ya gan shi. Hankalinsa ya kwanta. Ya cire
na Ameer daga firem ya zira wanda suke su 2.
An ci gaba, renan Naseer Jah-Jah. Shi kansa yana
mamakin kansa.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Kwanci tashi, shekara ta zagayo. Naseer ya dawo
cikin iyalansa, kamar yadda yake so. Bayan ya
huta sati 1. Alhj ya kira shi suka tafi bargar
dawakansa. Abin ya ba shi mamaki, irin
dawakan da ya gani suna harbin iska.
Sake da baki ya dubi Alhj yace "Abba za'a fara
wasa ne? Ya dafa shi ya ce,"Haka na ke zato,
idan na sami amincewar Jah-Jah."
Bakin sa har kunne ya ce,"Abba in dora sirdi in
hau? Yayi murmushi ,"Why not."
Ya kira mai kula da wajen, ya ce,"Je kawo sirdi."
Nan da nan ya dora Naseer ya haye jikin sa na
rawa ya zagaye bargar dawakan.
Kamar kar ya sauka, dokin yayi masa dadi."
Abba yaushe za'a fara? Ya ce,"Yau da yamma
za'a fara a tisaye, sannan akwai club guda 3 da
na ba takardar gayyata wasan sada zumunci.
DABAI ta dawo sabuwa."
Ya ce,"Insha- Allah kuma gagara gasar masu
gasa." Ya kamo shi suka nufo mota yana
fadin,"Akwai wani kokari da na ke maka, amma
ba zan gaya maka ko menene ba, sai Allah ya
tabbatar da abin, za ka ji.
Ka ci gaba da addu'a.
Allah za6a mafi alkhairi." Ya dan rankwafa ya
ce,"To Abba, na gode.
Allah ya saka da alkhairi."
Wasa ya kankama. (DABAI RIDERS) ta dawo
duniyar tseran Polo. Tutar Naseer Jah-Jah ta yi
sama ta neman ta wuce yadda take da can
baya.
Watannin 9 yana ketawa cikin kungiyoyin Polo,
yana ba su mamaki.
Kwatsam!
Abinda Alhj ke masa kokari ya samu. Ba wani
abuba ne, illa samun shiga shaharrariyar
kungiyar wasan Polo ta kasar Potugal.
Naseer fa kamar yayi hauka, don murna.
Haka Malam Balarabe, bai san abinda zai ce da
Alh.Basheer ba.
Kamar yadda aka bukace shi, daya iso 15 ga
wata, haka yayi sallama da kowa suka tafi tare
da Alhjn.
Sun gwada shi, sun ga iya kwarewar sa a zahiri
ko dama Alhj ya sha kai masu SD filet din
wasaninsa na gida da waje.
Kwarai sun gamsu da wasan Naseer, kuma da
alamun za'a samu da shi. Can Alhj ya baro shi
yana fafatawa cikin turawa.
A lokacin ne ya k'ara tabbatar cewa komai in ka
na da ilimi ya fi tafiya dai-dai, musamman a
wannan zamani.
An bashi gida da motar hawa. Naseer ya
kasance ba shi da wata matsala sai ta kewar
iyalan sa.
Ita ma sun kusa magance ta.
Cikin watanni 2 takardun zamansa dindin a
Potugal suka kamala, ya sami izinin shigowa da
iyalansa. Babu son kai. Zarah ce ta fara zuwa a
matsayin ta, ta babba. Ameer yayi kukan son
biyo ta, amma ina makaranta, ta hana.
Wai! Wa ya gane min Zarah a Potugal?
Ta shakata kwarai tsawon wata 1, ta koma
Nusaiba ta damk'o hanya. Haka suka kasance
suna yi wata guda-guda babu matsala balle
tashin hankali. Kowacce ta zo Naseer yana jin
dadin kasancewar tare da ita, bisa adalci da
tsoron Allah.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Shekara 5 Naseer yayi karfi sosai a k'asar
Potugal a fagen tseren Polo. Yayi farin jini kwarai
da gaske, kowa na son shi. Sau da yawa wasu
kungiyoyin na kawo masa cafka ta hanyar ninka
masa abinda yake samu, amma ya kauda kai,
saboda Alh.Basheer. Domin a halin yanzu arziki
sai dai ya ba wani, bai ma san iya wadanda
suke cin gajiyar sa ba a gida Najeriya.
Duk shekara idan ya je hutu. Bayan dawowa ba
tare daya buda wata cibiyar siye da siyarwa ya
zuba matasa sun samun abinci ba. Hatta Naseer
B dan hassada, ya saduda ya nemi gafara, ya
dawo yana cin arzikin da Allah yayi wa Naseer.
Yayi farin jini ba na wasa ba a Potugal, domin
har tallace-tallace yake wa manyan kamafoni ta
hanyar sana'arsa.
Ba kananan dololi yake kamawa ba, kowacce
talla yayi. A 'yan shekarun nan biyar. Nusaiba ta
hada 'ya'yanta 4 a gidan Naseer, 2 maza, 2
mata.
Hakika hankalin Naseer a kwance yake, kuma
Alhj ya lura karfi sosai a club din sa, tseren
dawaki sai dai ya ba 'yan baya tirenin. Saboda
haka yayi iya yin sa wajen Injiniya Ahmad Kaita
ta hannun sa ya samar masa a aikin yi ta
6angaran karatun da yayi, don kar ya tafi a
banza.
Allah mai ko! Takarda kawai aka ba Naseer ya je
inta-biyu ofishin(Internet Globl Services) reshen
Potugal, take nan suka yarda da takardunsa. Ya
sami shiga aiki. Duk da haka bai bar Polo ba,
amma ya zama na manya, wanda ake son tafiya
da shi, musamman a gagarumin wasan duniya.
A farkon wannan watan Zarah ce ke da zuwa
Potugal, a filin jirgi ya je ya dauko ta. Suka shiga
harkokin su kamar yadda suka saba. Zarah na
nason ziyartar Singafo da Malesiya, don haka
washe gari suka wuce suka kwana 4. Kwana
bibbiyu a kowace k'asa. Sun ci gaba da hutawa
a Potugal.
Sati 2 dai-dai da zuwanta, ciwon ciki mai
tsananin gaske ya murda. Zarah kamar ba za ta
yi rai ba. Naseer ya gaggauta kai ta asibiti.
Babu 6ata lokaci ta ga Likita ya bata kwararrran
bincike. Allah da iko tare da yin yadda yaso.
Wai Zarah ciki gare ta na sati 2 a wajen mahifa.
Naseer yayi wa Likitan ta bayanin matsalarta.
Nan da nan aka buda bakin mahaifa aka maida
cikin mazaunin sa. Ta sami kulawa sosai a
asibitin har ta wartsake.
Yayin da Naseer tuni yayi waya gida, ya shaida
masu halin da ake ciki. Kowa ya sha mamaki.
Shi yasa tana murmurewa ta fara amsa
wayayinsa masu gaishe ta, musamman Nusaiba
da ta kan bugu sau 3 zuwa 4 a rana. Mafarin
zamanta a Potugal kenan tana samun taimakon
daya kamata.
Anyi wa yara hutu. Nusaiba ta aje su wajen
Umma, ta zo duba Antinta, sati 2 ta koma gida.
Sannu a hankali cikinta ya wuce wata 7, ya shiga
na 8 kuma Bebi lafiya lau, kowa na ta murna,
musamman Naseer da yake tausaya wa Zarah.
Rashin da, ga ta ita ma ita kadai wajen iyayen
ta. Satin da za ta shiga wata na 9, jini ya goce
kamar famfo.
Da kyar suka tsaida jinin suka shiga binciken
mai ya kawo hakan.
Ai da gudu Likita yasa aka gara ta tiyata, bai yi
bayanin komai ba, sai da ya ciro k'aton Bebin
namji, sannan yayi mata duk abinda ya ga ya
dace, don tsira da lafiyar ta.
Daga Bisani ya kira Naseer ofishinsa yake gaya
masa matsalar da Zarah ta samu. Mahaifarta ta
fashe gaba daya, wanda dole ya kasance ya
fitar da ita baki daya, hakan shine wajibi a gare
ta, don zaman lafiyar ta.
Kuka ne kadai Naseer bai yi ba, amma ilahirin
hankalinsa ya tashi. Gani yake yi kamar ma cire
mahaifar, zai iya jawo mata wata matsalar, sai
da likita yayi masa bayani sosai, sannan ya
gamsu. Yayi addu'ar Allah ya k'ara mata lafiya,
ya kuma bar mata abinda aka samu, ita ma ta
rink'a ganin abin ta.
Ko gida Najeriya hankalin su ba kwance yake ba,
duk Nusaiba ta k'osa a kammala mata biza ta
tafi.
Bayan kwana 3 kuwa ta isa Potugal.
Antin tana a kwamce, duk ta rame ta dushe,
bata san lkcn da ta fara zubda hawaye ba.
Ga Bebi kato, gwanin sha'awa kuma duk 'ya'yan
Naseer da shi suke kama, har matan.
Nan ta zauna tare da Bebi (Aliyu), zuwa lkcn da
Zarah ta yi sarai, tsawon kwana 12 a asibiti,
kafin Likita ya bata sallama suka dawo gida.
Sai da Zarah ta yi 40, ita da Aliyunta, sai k'ara
murjewa suke, ita dai Zarah ta ki sakin jinkinta
dashi, gani take kamar shi ma mutuwar zai yi.
Sun dawo gida Najeriya yana da kwana 45, gaba
dayan su da Naseer.
Gagarumar walima ya shirya, bata wasa ba,
'yan uwa da abokan arziki suka taru, aka taya
juna murnar samun Aliyu tare da fatan Allah ya
raya shi cikin danginsa, rayuwar Islama. Sati 1
Naseer yayi ya dawo Potugal.
Tun Zaran na fidda rai da Aliyu, tana ganin yau
zai mutu ko gobe har ta zo ta saki jikinta,
zuciyar ta ta zauna waje daya ta daina ba Aliyu
mutuwa. Watansa 9 kenan yayi girman mamaki,
da kan shi yake mikewa tsaye, yana nema cira
k'afa yayi tafiya.
Yana kuwa shan ja wajen 'yan uwan sa suna son
yayi tafiya dole.
Rayuwar su mai dadi suke sha, tare da abokan
huldar shi, domin a halin yanzu Sageer yana
lakcarin a nan (State Poly) da yaransa 3. Kausar
na da 2. Zumunxin su kodayaushe k'ara k'arfi
yake tare da k'aruwar arziki. Ko Zarah ta gyara
gidan su dai-dai gwargwado tare da taimakon
Naseer. A cikin su da iyayen su babu wanda bai
keta hazo ba, ya sauke faralinsa. Komai maka
Allah shekaruna mikawa hada da tarindaukaka.
Naseer ke zaune shi kadai bisa kujeran alfarma
a farfajiyar bayan gidansa. Yayi shiru ya
zunduma taunan baya, har ya zo kan rayuwar
da yake cikin ta a halin yanzu.
Ya dubi tafkeken gidan sa a birnin Potugal,
mallakar sa wanda ya zuba makudan daloli ya
siya. Babu abinda ke ransa, sai dumbin godiya
ga Ubangiji da yayi masa baiwar da ba kowa ke
samun irin ta ba.
Sannan ya mallaka masa ingantattun mata na
nunuwa a fadin duniya.Zarah idan ya tuna irin
baiwar da Allah yayi mata na kaifin hankali da
sanin yakamata, ya tuna ita ta fara gaya masa
rayuwa shirin Allah ce, bai kamata Dan-adam
yana alkawari a hurumin da ba nasa ba, sai ya
ji son ta ya shafe ko'ina a jikin sa, yana neman
zautar da shi.
Nusaiba matar da yake wa yak'inin sa'a ce a
gare shi, Allah ne yayi masa arziki daga gare ta,
'ya'ya da dukiya tare da fice a duniya. In dai
ana maganar wasan Polo, duk masoya wasan
sun san da Naseer Jah-Jah.
Shi yasa idan ya dube ta, haka kawai ya kan ji
hawaye sun cika idanuwansa, sbd tsabar
tausayin kan sa, da ace ya rasa ta akan wautar
banza. Son ta ruwa ne, ya aje wa ransa, don ko
ya fadi, shi kansa yana ganin karya yake yi.
Yayi mika, take nan kewar su ta kama shi,
domin babu ko dayan su a tare da shi. Zarah
na jarabawar karshe ta kamala B-ed din ta.
Nusaiba kuwa ta na watan haihuwa ta 6.
Ita kadayaushe ta fi son haihuwa a gida. Gaba
daya hankalin sa ya koma gun sun, daren nan
ya kasa barci. Kamar wasa zuciyar sa ta rasa
sukuni, ba shiri ya nemi hutun shekara.
Bai hada sati ba, ya baro Potugal, sai ganin sa
suka yi kwatsam!
-----------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
'Ya'yan sa suka baibaye shi, tun isowar sa har
la'asar yana tare da su. Direba yayi kiran su
lkcn Islamiyya, kowanne ya fito cikin shiri, ya
shiga mota. Direba ya wuce da su. Zarah ta idar
da Sallah, ta fito babban falo ta iske Nusaiba
zaune tana kallo.
Kusa da ita ta zauna tana fadin,"Ki na nan ki na
kallon fadace-fadacen nan da ya ki ci ya
kicinyewa." Ta ce,"Ke dai bari, ai ni wannan
fadan na k'asashen larabawan nan tsoro yake
ba ni." Zarah ta ce, ke me kika fahimta daga
gare shi?
Ta ce,"Karshen duniya mana. Dama ance idan
zamani ya zo karshe, alamun har da 6arkewar
rikicin k'asashen gabas ta tsakiya. Yanzu dubi
k'asashe nawa ke rigima, ana kashe su, kamar
ana kashe kiyashi, tsakanin mu a musulmi
kenan."
Zarah ta tallafe kunci ta ce,"Wannan rayuwa
tana firgita ni, me mu2m ya kamata yayi, banda
ya kadaita Allah, yayi masa ibada, sannan idan
ya ci, ya bada sadaka, don neman karshe mai
kyau? Ta ce,"Wallahi kuwa Antina, musamman
na mu mata da aka ce mun fi yawa a gidan
wuta.
Biyayyar aure ce matsalar mu komai muka yi
gidan miji lada ne. Amma sai ki ga abin ya
gagara.
Kar ma ace miki akwai abokiyar zama, abin ya fi
kazanta.
Sai ki ga mace ta mance cewar akwai hikimomi
da yawa cikin auren mace fiya da daya