Showing 30001 words to 32871 words out of 32871 words
Chapter 11 - Abu Naka Book 1 Compelet Book By Sodangi
ranta ta ji daxi, an sanya bikinsu da Sadisu sati biyu
kawai aka xiba. Qunci da takaici ne suka gallabeta, sai dai in an tambayeta ba za ta ce ga
taqamaiman abin da ya haddasa mata hakan ba.
Tana kwance cikin kasala da rashin sanin abin yi, wayarta ta yi motsi alamar saqo ya shigo a
cikinta. Duk da ta daxe ba ta samu wayar Mus’ab ba saboda daxewar da ta yi ba ta riqe wayar
ba, miqa hannu ta yi ta xauko wayar, ga abin da ya ce mata.
Aisha!
Mutane suna rayuwa, mutane suna mutuwa, wasu su ce sai anjima, wasu za su iya mantowa
amma ni kam har abada kina cikin zuciyata.
Mus’ab Abdullahi!
Ta sake kallon kalmomin cikin tunani, ba ta gane komai game da kalamanshi ba. Ya ji labarin
bikin ne? Ta tambayi kanta. Ta yi kamar ta kira ta tambaye shi sai kuma ta fasa.
Mus’ab yana kwance a xakinshi wasanni suke yi da Jennifer lokacin da wayarshi ta yi qara, a
haka ya miqa hannu ya xauki wayar cikin sauri ya kaita kunnen shi.
“Hello Ishaq”.
Qoqarin faxin hakan ya yi saboda yanda Jennifer ke sarrafa shi.
“Yaushe rabonka da Misau?’
Cikin hanzari ya bar komai ya miqe zaune.
“Me ya faru?’
Ishaq ya ce, “Na fa ji kamar sun sanya bikin yarinyar nan, don shekaranjiya na je gai da Abu
ita take bani labari”.
Mus’ab ya zama tamkar mutum-mutumi a zaune a kan gadon, ya rasa me zai ce in ban da
gumi babu abin da ke keto mishi a jikinshi.
Jennifer ta kixime tana faxin “Me ya faru? Anyi mutuwa ne?” Tana qoqarin qanqame shi take
faxin “Maman ka ce ta mutu”.
“Shut up Jennifer!”
Ya faxi da qarfi tare da yin jifa da ita ta faxa can gefe. Banxaki ya shiga ya yi wanka ya fito ya
kama shirin tafiya ba tare da ya jira wayewar gari ba.
Sani ya shigo xakin saboda kiran da Jennifer ta je ta yi mishi saboda tsoratar da ta yi da
yanayin Mus’ab da ta gani.
Cikin harshen Hausa yake yiwa Sanin bayani za su kasheni ne Sani, za su aurar da yarinyar
nan Aisha suna son ganin na yi mutuwar tsaye.
Ita kuwa Jennifer sai faman sorry take cewa tana qoqarin rarrashi da kwantar da hankali.
“Bari in fito mu tafi tare kawai don bai kamata ka yi wannan doguwar tafiyar a wannan tsohon
daren kai kaxai ba kana kuma tuqi”.
Tare suka fito da ‘yammatansu su biyu da dama suka kawo don su taya su kwana, suka
sauke su a hanya suka wuce suka kama hanyar Misau.
Qarfe shida da rabi na safe Mus’ab da Sani suna zaune a falon Mus’ab xin a gidanshi na
Misau, yana yiwa Saddiqa waya lokacin ta idar da sallar asuba.
“Me yasa za ki yi min haka Aisha? Me yasa?”
A kixime ta tambaye shi cewa, “Me na yi maka kuma daga ina kake maganar?”
A hankali ya ce mata, “Gani nan a gidana Aisha na zo Misau yau kuma maganar aurenki ya
kawo ni, ina son ganin ki yanzu, ina so mu tattauna al’amuran dake tsakaninmu, mu gamu
yanzu a gidan Abua ina son sanin abin da ake ciki”.
Mus’ab yana zaune gaban Abu yana kallon agogon hannunshi yana kuma kallon hanyar da
Saddiqa za ta vullo.
Ita kam Abu haquri take ba shi tana kuma gaya mishi wai har ta samar mishi wata yarinyar da
take shirin sawa ayi xaurin auren rana xaya da na Saddiqan sai gata ta shigo.
Ramar da ya gani a tare da ita, ita ce ta fara sanyaya mishi jiki. Mus’ab ya kalle ta cikin
nutsuwa.
“Kin yi ciwo ne Aisha?”
Ta sunkuyar da kanta qasa hawaye suka soma zuba daga idanunta.
“Daina kuka ki gaya min Aisha kina sona?”
Da sauri ta xago ta kalle shi idanuwansu suka haxu, ta yi maza ta sake sunkuyawa.
“Gaya min kawai Aisha, ai ni na daxe ina sonki, na daxe ina burin mallakar ki a matsayin
matata, na daxe ina buri da fatan in samu damar da na sanyaki a gabana na gaya miki wannan
kalmar ina sonki Aisha, ai bani da wata budurwa a Misau in bake ba, kece yarinyar da nake so
ban samu damar da muka zauna muka tattauna matsalolin da masoya ke fuskanta ba saboda
tsoro”.
“Tsoro kuma?”
Ta yi tambayar cikin wani yanayi.
“Yanzu tsoro ne ya hanaka gaya min abin da ya kamata a ce tuntuni ka gaya min?”
Ya yi maza ya ce, “Eh, Aisha tsoro ne, in ban da haka ai da tuni na gaya miki cewar duk
duniya bani da abin da nake so kamar ki”.
Ta miqe da niyyar tafiya ta barshi. Ya yi maza ya kama hannunta ya riqe.
“Kar ki tafi ki barni Aisha, kar ki yi fushi dani taimakeni ki rufa min asiri, ki taimakeni kamar
yanda Innata ta taimake ni a farko, ai ita ta haifeki Aisha, taimakeni ki yi min kwatankwacin
gatan da ta yi min a farko”.
“In ma ban yi ba, ba laifina bane kai ne tsoro ya hanaka yin abin da ya dace ka yi”.
“Ai tsoron ni kar a rabani dake ne Aisha, Inna ta ce in na ce ina sonki za ta baki labarin
mugun halina, tana qina dake ne wai a dalilin tana tsoron kar in cutar dake. Na rantsre miki ba
zan iya cutar da ke ba Aisha, don haka ki toshe kunnuwan ki a kan abin da za ki ji an gaya miki
a kaina”. Ta kalle shi cikin nutsuwa ta ce, “Kana nufin ba gaskiya bane?”
Da sauri ya ce mata, “Gaskiya ne Aisha, gaskiya za ta gaya miki, ni ban tava jin wata
magana ta fito bakin Inna ba sai gaskiya, don haka gaskiya kawai za ta faxa, ni xin ne ita ta
haifaeni ta fi kowa sanina, tana qina dake saboda wasu halaye nawa da take ganin basu yi
mata ba. To amma kar ki manta na zauna gaban Innata ta tausaya min ta taimakeni ta rabani da duk
wani abin da nake yi a wancan lokacin, don haka na roqe ki duk abin da za ki yi a kaina ki
tausaya min kar ki juya min baya”.
Saddiqa ta miqe da nufin tafiya gida Mus’ab ya biyota.
“In kin je gidan za ki yiwa Inna maganar ne?”
Ta ce, “Ai nima tsoro nake ji”.
“Haba Aisha, ki taimakeni mana kar ki bari su aurar dake ga wannan mutumin na fishi
dacewa dake, na fishi sanin darajarki, zan fishi girmamaki in kika daure kika toshe kunnuwanki
kan abin da za ki ji a kaina kika amince kika aureni. To ni kuwa ba zan tava baki kunya ba”.
Suna isowa qofar gidan ta shige ciki ta barshi nan a tsaye.
Innarta tana ta aikin qunshe goron da take aikewa da shi na gaiyatar mutane biki, ta kalli
Saddiqa yanda fuskarta ta canza.
“Hala daga wurin yayanki kike?”
Ta koma gefe xaya ta tsuguna alamar tana son yin magana, sai dai ta kasa, ta rasa ta inda za
ta faro zancen.
Ta kalli Inna cikin rawar jiki da rawar murya ta ce mata, “Inna mene ne?” Ta yi shiru saboda
yanda jikinta da muryarta suke rawa.
Inna Habiba ta zubawa Saddiqa ido cikin tausayi, zuciyarta ta tabbatar mata da cewar son
Mus’ab take yi, sai dai ba za ta barshi ya yi nasara a kan yarinyar ba.
“Me ya faru Saddiqa? Me kike son gaya min? Tambayi duk abin da kike son sani zan gaya
miki ba tare da raina ya vaci ba, ba zan yi fushi dake ba balle in je ina yi miki faxa, ai baki da
wata uwar da ta wuceni, nice uwarki. Yayanki ya gaya miki wata magana ne?”
Saddiqa ta soma kuka, ta ce, “Yana sona, Inna ya ce kece kika hanashi ya gaya min yana
sona bayan kuma shine xan’uwana”.
Gwaggo ta yi murmushi ta ce, “Ke yarinya ce Saddiqa shi yasa baki gane dalili ba, ke da
yayanki ‘yan’uwa ne da zumunci ya haxaku, sai dai halayenku da xabi’unku ba xaya bane, shi
ba abokin haxinki bane, hanyar jirgi daban ta mota daban, ba zamu iya dashi ba halayensa sun
fi qarfinmu”.
Ta ce, “A’a, Gwaggo ni zan iya da shi, ni shi nake so ba Sadisu ba, dama na yi shiru ne kawai
don bai riga ya furta min ba, amma yanzu tunda ya gaya min ya yi min rantsuwar bai da wata
budurwa a Misau in ba ni ba. To ki taimakeni ki yafe min kar ki baiwa Sadisu ni, Yaya Mus’ab
nake so”. Ta kai gwiwpyinta qasa ta durqusa a kansu alamar roqo cikin kuma kuka mai tsanani. Inna Habiba ta zuba mata ido tana kallon ta, ta ce, “To Saddiqa ni dama ai ba wai bana sonki
da shi bane, savanin dake tsakaninku ne na ga ya yi yawa na ce gara miki inda za ki samu
zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Amma tunda haka ne ai shi kenan, ni na gane ke ko warin sigari baki so a kusa dake, to shi
kuwa na ji labari an ce lokacin da kamfanin sigarin da yake sha na Rothmans suka yi bikinsu
har kyautar girmamawa suka yi mishi saboda cinikin da yake yi musu.
To wannan ma da xan sauqi a awurina da ya tsaya a haka nan, inda kike ganinshi mashayin
barasa ne na qarshe”.
Saddiqa ta qwalla qara da iyakacin qarfinta tare da kama kanta da hannayenta duka biyu.
“Wayyo Inna! Wayyo Allah!!”
Inna ta samu damar xora bayaninta da cewa, “To shi nake jiye miki, kin san halin mashayi bai
da wata amana, ga shi manemin mata. A nan garin ne kawai baya yi, amma an tabbatar min da
cewar duk inda yake in ba a nan bane bai rabo da matan banza suna biye da shi, shi yasa nake
tausayin quruciyarki. Kina da sha takwas ne yana da talatin da biyar, ina tausayin ki zama matar mashayi ko
manemin mata, shi yasa na zava miki Sadisu yaro qarami, bai girmeki da wasu shekaru masu
tsanani ba, za ku yi quruciyarku tare ne ku girma tare, a kan idonmu aka haife shi har ya girma,
bai da wani halin assha, shi yasa na zava miki shi ku biyun dukanku yaran kirki ne masu
biyayya masu ganin girman na gaba. Ko kuwa har yanzu kin fi son auren yayanki a kan
Sadisu?”
Cikin kuka ta ce, “Na haqura Gwaggo, na yarda da zavin da kika yi min na auren Sadisu”.
Daxi ya kama Inna Habiba, ta shiga sanyawa Saddiqa albarka, cikin zuciyarta kuwa faxi take
yi ja’irin yaro kawai, ba zan barka ka yi galaba a kanta ba balle ka sanyani in ji kunya, bayan na
riga na yi alqawarin baiwa xan aminiyata ita za ka zo ka bijirar min da ita.
Mus’ab kuwa yana can gidanshi tare da Sani suna tattaunawa kan yanda za ayi, sai dai
maganar kawai yake yi amma hankalinshi yana can wajen sauraron wayar Saddiqa, don ta
gaya mishi yanda suka yi da Gwaggonta shiru babu wayar.
Hankalin Mus’ab ya kai matuqa wajen tashi. Sani ya kalle shi cikin raxa ya ce, “Ina ganin
tunda ni a gida ba a san na zo ba, tunda da sauran duhu muka iso muka kuma taho nan kai
tsaye, ko in ka ga da matsala abin zai mana gardama in xauke maka yarinyar mana in tafi da ita
sai kai ka yi zaman ka, ka yi ta taimakawa wajen neman ta, ka ga babu mai gane kana da
hannu cikin vacewar tata, in yaso daga baya in hankula suka kwanta sai a dawo da ita sai a
xaura muku aurenku”.
Mus’ab ya zuba mishi ido cikin nazari ya ce, “Da zan yi jarumtakar yin hakan to da na ji daxin
shawarar taka, to ba zan iya ba saboda dalilai guda biyu.
Na farko bana so wani savani ya sake shiga tsakanina da iyayena, a yanzu mun shirya ni da
babana, ni da shi muna da fahimtar juna, zamu zauna tare mu yi hira, zai bani shawara zai yi
min nasiha har muna zuwa unguwa tare. Inna ce bani da wannan fahimtar da ita, ina kuma
qoqarin ganin mun samu daidaituwa sai kuma in zo in tafka musu irin wannan laifin? Bana
zaton in ya bayyana zamu sake samun wata fahimta dasu.
Na biyu duk matsanancin son da nake yiwa Aisha ina son mallakarta ne ta hanyar aure, in
babu auren to bani da wata buqata irin wannan a tare da ita, don ba zan iya keta haddinta ba,
don haka na fi so iyayenmu su yarda su bani ita in mallaketa ta zama matata da izininsu don mu
samu albarka, in kuma yi qoqarin gyara abin da na riga na vata a baya. Yanzu fatana bai wuce komai za a gayawa Aisha ta yarda ta daure ta bani haxin kai ba, in har
ta yi min haka, to komai zai zo min da sauqi. Don in har ta dage ta ce ni take so, ina ganin
kamar Innar za ta yi sassauci”.
Gajiya ya yi ya xauki wayarshi ya danna lambobin Saddiqa, kwance take a xakinta har
lokacin kuka take yi ba ta daina ba.
Kamar kar ta xauki wayar sai kuma wata zuciyar ta ce ta xauka.
“Na ji shiru ne Aisha shine na ce bari in bugo in ji me kike ciki? Sai dai na ji kamar kina kuka,
me ya same ki?”
Ta ce, “Kukan baqin ciki nake yi”.
Gaban Mus’ab ya faxi ras! Ya daure ya tambaye ta.
“Baqin cikin me kike yi Aisha?”
Ta ce, “Baqin cikin da ka yi min dalilin shi”.
Ya sake wani mummunan faxuwar gaban mai qarfi.
“Ki taimakeni Aisha ki tausaya min ke kaxai nake dake, Aisha in kin barni za ki barni cikin
qunci da wahala, taimakeni ki bani haxin kai ki zama matata”.
Ta yi maza ta katse shi da cewa, “Kana nufin in zama matar mashayi?”
Ya ji tamkar guduma ta buga mishi. Ya yi qarfin hali ya ce, “Ba haka nake nufi ba”.
Ta ce, “To abin da Gwaggo ta gaya min kenan game da kai, ko kuwa me ka ce game da
maganganun da ka ce za ta gaya min?”
Ya ce, “Na ce miki gaskiya ne ban tava ji ta faxi wata magana ba sai gaskiya, ita ta haifeni ta
fi kowa sanina. Sai dai komai ta gaya miki ki daure ki taimakeni…….”
Kafin ya qarasa ta katse shi da cewa, “Ba zan iya ba, tunda ban ga alamar kaima kana
taimakon kanka ba, don haka ka yi haquri ka taimakeni ka fita hanyata, ka taimakeni kar ka
sake shiga al’amurana ka barni in yiwa iyayena biyayya. Dama ni abin da na saba kenan, don
haka daga yau bani ba kai……” Ta katse layin ta bar Mus’ab riqe da kan wayarshi a hannu cikin kaxuwa da firgita, a
zuciyarshi kuwa cewa yake yi “Wayyo Aisha! Za ta tilastani yin abin da bani da niyyar yi a
kanta!”
Mu haxu a littafi na biyu.
ABU NAKA wai maganin a kwaveka.
Taku;
Aunty Hafsat.