Showing 3001 words to 6000 words out of 17626 words
Chapter 2 - Tawa Ta Sameni Book 2 Complete by Halima Abdullahi k Mashi
mamanta zaku,ya kashe wayar na
dubi agogo takwas da rabi na dare nace anya mama zata
barni na tafi kuwa mami ta shigo dakin itama cikin less
fari tayi kyau nace zakije ne?tace zanje kinsan nasir
zanbi nace yawwa har naji dadi tace su Bilki da Sa'a da
kyar ne zuwansu amma suna dai can gidan amarya nace
har an kaita ne?mami tace an kaita mana daga can zaa
dauketa nace mami mamanmu na falo ne?ina son fita
bana son ta ganni zata iya cewa na koma dare yayi tace
aa bata nan shigowata na ganta da tire tayi sashin Alhj
nace yauwa dama yaynmu ne yake kirana nayi kyau
mami banji kin yaba ba mami tace kinfa hadu wllh nace
nagode,bari naje daga can fa zan wuce sai mun hadu
don nima Nasir yace yana hanya sai yazo nan ya daukeni
sannan yaje ya dau sauran kawayen Amarya,muka fito a
tare tana fadin gara nayi damadama da abuna kada inje
wata ta kwace min an ganni yar yarinya mukayi dariya
muka tafa kowa ya kama gabanshi,nayi waje ita kuma
tayi dakinsu jiran Nasir dinta,na dubi motar da ita kadai
ce a harabar gidanmu ban san motar ba na dan tsaya
nesa da motar ina ta dube dube to ina yayanmu yayi ne?
din din naji hon daga motar gun motar na nufa ba dama
kaga na ciki ya sauke glass din motar sai da jikina yayi
yarrr yanda na ganshi yayi masifar kyau kyanshi ya kara
fito tamkar shi yayi kanshi ya bude min mazaunin
gaba,shigo kawai yace min sannan na shiga wow wani
kamshi da sanyi baa magana motar sabuwa ce dal,bai
min magana ba muka fita munyi tfy sosai ba tare da yayi
min magana ba sai wakar mutuniyarshi wato celine dion
ke tashi a cikin motar,can wayata ta soma ringin a jaka
na ciro ta mama ce,gabana ya fadi na dauka mama tace
cikin tsawa ina kika fita yanzu?wurin dinner fa zamu
tafi,wa kika tambaya nace don Allah mama kiyi hakuri
tace karfe nawa zaku dawo?wllh ban sani ba,to ki kula
da kanki ki tsare mutuncinki kinji ko?nace to mama in
Allah ya yarda zan kiyaye,tace to don gsky da ina dakin
ba zaki fita ba,tara saura sai yauamsh za'a fara bare a
gama nace kiyi hkr zamu dawo da wuri,ya juyo ya dubeni
bayan na gama wayar sannan ya dauke ido yamai da kan
titi sannu a hankali ya tsaya a gefen titi ya kuma dubana
kinyi kyau sosai nayi murmuahi nagode,ya zuba min ido
ni kuma na kasa dubanahi sai dai wani farin ciki da nake
jin shi yaja wani dogon numfashi sannan yace
Imman!...ya ja sunan tare da kama hannuna wani irin
yanayi mai wuyar fassara na shiga ban taba jina cikin irin
wannan yanayin ba ya dan murza min yatsuna sannan ya
tsare ni da ido tare da fadin baki amsa min ba na kira
sunanki iman nace umm....ya cigaba dan Allah iman ko
bana nan kada ki tsaya harkar samari ki taimakeni ki
cigaba da karatunki kinji?ki barni na zaba miki miji dai
dai da ra'ayinki wanda kike so shima yake mutuwar sonki
kinji little sister di ta,wani haushi ya kamani na zunburo
baki a raina nace dama nasan ba wani sona yake ba
Amira tace min ta ga kamar yana sona ne,ya kai
yatsansa kan lebe na ya dan buga kadan sannan ya ce
kina da wanda kike so ko?nace a'a cikin kulewa da
shagwaba kamar zan yi kuka yace to menene na jin
haushi umm?na kara turo baki gami da girgiza kai.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
kafaduna ya dafa,ina kyafta ido sai ga hawaye,kawai ji
nayi ya jawo ni ya rungume wai yana lallashina,sorry my
sister bar kuka,kan uba jina cikin kirjinshi sai na manta
duniyar da nake, kai SO! ba dama ne,duk da na san bai
kamata na biye mashi mu hada jiki ba amma sai na kasa
janye nawa jikin,cikin taushin murya yace kince
min,zakiyi krtn ko?ban motsa ba ya cigaba na san kina
kokari da hazaka ki gyara paper ki wannan shekaran kinji
ko?karki damu da maganar aure yanzu barshi nan da
shekara biyar nan gaba,ya dago ni daga jikinshi yasa
hannunshi ya rike fuskata yana duban idona hawaye na
zuba, idonshi cikin nawa yake kallona,kin min alkawari
zaki yi krt ba sauraron samari?na rintse idona dan ba zan
jure kallonshi ba sonshi sai ya kasheni a raina nace ni ba
wani krt da zanyi tunda kai kayi naka auran ko menene
matsalarshi da karatuna?me zai karu cikin krt oho?kamar
yasan tunanin da na keyi sai naji ya ce karki yi tunanin
ina ruwana cikin harkar krtn ki akwai dalili kin gane
bance komai ba ya sakar min fuska sannan ya bani
hankici gashi share hawahenki na karba shi kuma ya
anshi jakata yace nasan ba za'a rasa yan kayan shafe
shafe cikin jakar ba ko?ya dubeni ko babu?nace akwai
yace ni kike wa magana kina yanga?daidai lokacin ya
cire sinkin hotunan jiya menene wannan?bai jira amsa ta
ba ya cigaba da kallon hotunan yana cewa kai mun yi
kyau amma duka nawa ne ni dai kallonshi nake kawai na
gyara fuskata sosai shi kuma ya bude wani aljihu yasa
hotunan sannan ya dauko wayarshi yana fadin bari na
kunna wayar nan na san za'ayi ta nemana a jita a rufe
shi yasa nabi wayoyin na rufe, ni sai mamakinshi nake yi
kamar ba shi ba, ya dubeni zaiyi magana wayarshi ta
soma ringin ya dauka hello Nas yayane?ina juyo muryar
Nasir na fadin Maska kai wane irin dan iskan mutum ne
kana duba agogon ka kuwa?kasan ynxu tara da rabi kai
fa kace tara daidai ba African tym shine ynxu dan iya
shege daga dauko mota sai miji ka shiru kama kashe
wayoyi,to ka samemu a wajen dinner domin har Amarya
tana gun,yayanmu yace ni ake jira kenan yace eh mana
kai kadai muke jira Amarya bata shiga gurin ba gata nan
a mota sai ka iso ku shiga tare,gani nan yace sannan ya
kashe ya ja mota muka tafi,ya dubeni kece mutum ta
farko da ta soma shiga motar nan, naso Mimi ta soma
shiga sai gashi kin mata shigar sauri kin shige mata
mota sannan hotonki shine na farkon zama ajiya cikin
aljihun motar kinsan ko a kannena kina da babban
matsayin da kannena basu taka ba, nayi murmushi
sannan nace nagode,muka isa gurin ya ajiye motar ya
fito yana neman Nasir a waya can ya sameshi Nas na
iso kuna daidai ina ne,yace gamu na bayanka kai baka
ganmu ba,ya dubeni to fito Hajiya,na fito daidai sanda
Anty mimi ta fito daga motar Nasir muka dubi juna ni da
ita, shadda galila tasa dark green shima yaynmu ita yasa
ankon kenan sukayi tayi kyau na fitar hankali ta sa sarka
kirar dubai ga ashoben da aka sa mata a kanta ya dauru
gashi har kan kafada duk sai naji na raina kaina,ganin ta
daure fuska kuma tayi fushi hatta Nasir na kula yayi
mamakin ganinmu tare,shi kam gogan ko a jikinshi ya isa
gurinta madam kin jirani ko?sorry zo muje ana jiranmu
ya kama hannunta muka bisu ni da Nasir sauran abokan
ango sun taryi Amarya da Ango,wuri yayi wuri kowanne
teburi mutum hudu mata biyu maza biyu,Amarya da
Ango su biyu ne a gunsu mu kuma mu uku ne ni sai
Mami sai Nasir,can an soma ciye ciye sai ga Adams
bansan ta inda ya fito ba sai ganinshi nayi ya dubeni,yar
kyakkyawa ina kika shiga ne yau duk banganki ba?kafin
nayi magana ya juyo gun Nasir Assalamu alaikum
abokina ai min afuwa 'yar kyakkyawa ta tsone min ido
bana ganin kowa sai ita yace to ai shi kenan tunda ka
ganta ynxu sai mu gaisa waalaikassalam,mu kayi dariya
sannan ya zauna bakici komai ba yar gidana ya miko min
cinyar kaza saitin bakina ci wannan mana na kauda kaina
sannan nace a'a Adam bana cin komai juice zansha,yace
sha mana ko na danji sanyi kinga Nasir yasa yar gidanshi
a gaba sai ciyar da ita yake ba ruwanshi dake,Mami tayi
dariya tace to tunda ynxu kaxo ai sai ka bata yace to ba
gashi taki ci ba na fa dade ina kallonki naga shigowarki
tare da Maska da Amarya na dubi gun yayanmu ga
mamakina duk hankalinshi na gurin mu ya cika yayi fam
tamkar ya fashe Adams ma ya dubeshi yace yar gidana
kin ga yanda Maska ke faman hararata?nace to ya maka
kashedi kaki ji ba?Adam kana son bata ma kanka lokaci
ne kawai yardar yayanmu shine tawa,Adams ya dubi
Nasir yace Nasir yi mana sharia,Nasir yace ina
jinku,naga yar kyakkyawa ina so ina ruwan yaynsu,Nasir
ya nuna mami yace baga yar gidana ba da muka shirya
kanmu dole ya barmu,Adams yace to shi ne ta kasa
ganewa tabbas in kin yarda na san halin Maska in har
yace yes baya yarda yace no kin gane?so in har da
gaske kike sona zan aureki kuma zakiji dadi sosai yanda
nake jinki a raina, ko! na dubeshi,yace ba sai kin sha
wahala wajen zuwa gurin malami ba zaki mallakeni son
ranki,Allah sai yanda kikayi dani na rantse miki,na soma
dariya shima yana dariya mami suna ta hirar su suma
yace a makaranta wane matsayi kike son ki taka?
Masters ko Degree ko Professor kikeson zama?zan barki
da karfina da Aljihuna burina dai ki aureni ki haifamani
yara masu kama da ke har da wannan dan dimple din
naki, ya kai hannu zai taba min kumatu na goce ina
dariya,sai yaynmu na gani akaina sai huci yake yace
tashi a kaiki gida sha daya yayi ,nace yaynmu ka bari a
tashi mana mama tasan wannan kuma zan kula da
kaina......,ya katse ni tashi ko na mareki,tsoro ya kamani
na soma kyarma adams yace Maska ya zaka ruda tane
haba.....shima ya katse shi please Malam yi min shiru
kajiko,na nuna Mami ga Mami ma nan yace ni na
kawota?wanda ya kawo ta shi zai maidata na mike ya
dafo min baya har gurin motoci,shiga nan ki jirani tunda
ke bakya jin magana,kin je kin saki baki kina faman yi
ma Adams dariya zanyi purnish dinki,ya rufe motar da
karfi ya tafi.haka na zauna shiru can da na gaji ga wuri
yayi shiru sai sautin kidan can gurin dinner kawai sai na
kira wayar mami nace wai yayanmu fa?tace gashi can
wurin Amaryar shi suna zaune suna hira nace to na
kashe wayar duk haushi ya isheni nace wato shi yana
can yana hira da matarshi ni kuma ya hana ni neman miji
ba wani jiranshi da zanyi tfy ta zanyi abuna wato ga mai
gadi! na soma kici kicin bude kofa abin haushi sai na
kasa hala kulleni da key ne in ba haka ba na jijjiga murfin
ko motsi baiyi ba na kari masifa ta nakoma na zauna na
hada kai da cinya na matse nayi shiru,har misalin sha
biyu da rabi ni lokacin ma barci ya soma dauka,ta ban
ankara ba naji an bude motar an shigo dan ma baccin
nawa a dar dar na keyinshi kun sanni da shegen tsoro sai
na kware baki zan tsala ihu sai naji an rufe min baki
gami da cewa shishit!,ya kunna wutar motar duk da naga
yaynmu ne har ynxu jikina bai daina bari ba kin cika
tsoro Iman saidai kin fi burgeni in kina cikin tsoro
idanuwanki su kan birgeni ya kai yatsansa saman idona
na lumshe ido jikina yana wani irin tsuma saboda yanda
yake sosa min saman idona ya janye yatsansa sannan ya
daure fuska ya dubeni yauwa dazu me Adams ya ce miki
kike dariya?nace ba komai yace karya kike yi zan gaya
maki abinda ba ki sani ba shi kike so ba kuma ba zaki
aure shi ba,kafin ya rufe baki wayata ta soma ringin shi
ya rigani daukan wayar yana duban sunan sai yaga ashe
mama ce sai ya bani na karba gabana yana faduwa,Iman
yayi maki kyau kinji ko,nace dan Allah mama ki yi hakuri
yanxu zamu dawo yanzun nan fa aka tashi tace bana ga
mami ta shigo ba ynxu nace to ai ni yaynmu ne yace
tunda shi ya kawo ni zai maidoni ya min magana a
hankali yace kice mata kuma na tsaya sallama da
mutane ne,tace to kiyi sauri sha biyu ta wuce banda ma
bana dakin kika fita da babu inda zakije ta kashe
wayar,na dube shi yayanmu ka kaini gida ni mama ke jira
dan na san itace da girki zata sashen Alhj shi yasa yayi
wata yar dariya to bari mu tafi kar Alhj na yayi ta jiran
mamanki gashi kuma na tsare ki anan yana magana da
wata fassara ne na kula sai na kauda kaina gefe,ya tada
mota yace yauma gidanku zan kwana ance wai sai gobe
zanje gidana suna son yi mata budan kai gsky sun bani
haushi menene kuma budan kai?nace nima ban sani ba a
raina nace me ya dameni da zaka dameni dube shi
kawai, wayarshi ta soma ringin daidai sanda muka tsaya
a harabar gidanmu zan bude na fita naji ya jawoni ba
tare da ya min magana ba ya dauki wayar na ji yace Alhj
Iman gata nan na kawo ta kome Alhj yace mashi sai
yace to ynzu zata shigo,ki shiga Alhj na jiran matarshi
nima zan shiga daki ne na kira tawa a waya dan kece
kika hana na maidata gida sai dai Nasir ne ya kaita,cikin
mamaki nace ni?da yaushe nace?yace au baki ma san
san da kikace ba ko?to shi kenan sai da safe ya bude
min na fita ina dubanshi koda yaushe na ce kar ya kai
matarshi oho?yazo ya min sharri kawai.
Washegari budar kai da safe nice nayi musu abincin
breakfast musa dryva ya kai musu gidan Nasir,da rana
ana tafiya gidan Amarya ni kam ban fara ba don nasan
magana zai zama kai na gurin Amarya ko ince tamkar
naje neman fada,da daddare muna zaune a dakin Amira
ni da mami,nan mami ta sameni gidansu Amirar mami na
bamu lbr tsaruwar gidan,nace dama shi yaynmu ai dan
gayu ne sannan ya saba da rayuwar turawa kinga kuma
dole ne ya tsara gida na yan gayu,mami tace gashi kuma
da kudin ba,Amira ta dubi mami dama akwai zancen da
zamuyi dake,nan ta kwashe maganar son yaynmu da
halin da nake ciki ta gaya ma mami,mami ta cigaba da
mamaki dama yaynmu kike so Iman?gabana na faduwa
hawaye na zubo min wllh mami kinji halin da nake ciki
kenan,tayi shiru dan lokacin sannan tace to sai dai muyi
ta addu'a amma Haj Yaya da Haj Laure basu da kyau in
ma kin shiga gidan ba zasu bari ki samu kwanciyar
hankali ba sannan shi kanshi yaynmu a irin ra'ayinshi
baya son karamar yarinya yafi son babba nace na sani
Amira ta ce ni kam sai naga kamr sonta yake yi nace ke
ba wani so jiya kinji yadda yake min zancen matar shi
dan haushi ni ko kula shi banyi ba. Mun tsaida shawara
akan cewa zamu tsananta addu'a kawai
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Amira ta rakomu har gida dan zata karbi littafinta a
hannuna dai dai dakin yayanmu abokanshi ne sun sha
kwalliya sai kamshi sukeyi mami ta dubeni yau za'a kai
angonki gidan amarya na dubi wajen sannan nace to ni
ina ruwana ,dai dai nan Adams ya fito shima sanye da
waganbari blue ammy sky yace Iman na juyo ina duban
shi amma gurin na tsaya,yazo yau duk bangankiba yar
gidana ina kika shiga ne?ina nan banje ko ina ba na fada,
su mami suka gaisheshi yace mami ko?mami tace eh
yace kefa?ya nuna Amira mami tace Amira yace nice
name,suna ta surutunsu ni ko hankalina na can gurin
ganin ango ya fito sai ko gashi yasha kwalliya da wani
farin yadi mai shara shara fari tas komai fari yasa har
glass ban taba ganin yasa glass ba sai yau yayi kyau har
ya gaji,takaici da kishi ne ya kamani raina ya sosu sosai
na zuba mishi ido duban shi kawai nakeyi ba mamaki
ganin karshe ne nake mishi dan yanzu ba gidan mu daya
ba bani zan dinga dafa mishi abincin ba ba zan dinga
dafa mishi lipton da daddare ba ba zai aikeni ba bare na
mishi gyaran daki sai dai anty mimi bayan kwana kadan
kuma su tafi England shi kenan nayi rashin yayanmu,nayi
zurfi cikin tunani ban san su mami na min magana ba sai
da suka dafani nayi ajiyar zuciya na dubesu yayane?
Adams yace don Allah ki daina irin wannan tunanin wai
ma tunanin me kikeyi?ban ma saurareshi ba na juya ina
duban yaynmu ya shiga gaban motar Nasir,Nasir ya iso
gunmu Adams zo muje mu kai angon can tun kafin ya
kai kanshi,sai masifa yake mana wai in ba zamu je ba ya
tafi abunshi,hankalina ya kuma tashi na juya nayi gida na
barsu a nan mami da Amira suka shigo, kuka riris suka
sameni ina yi dukkansu sun tausaya min tare da bani
hakuri sunce na ringa danne kishina a gaban mutane dan
kar suni,cikin kuka nace ba zan iya ba dan wani
zazzafan so nake mishi ga mugun kishin shi dana ke
fama dashi ku tava kirjina kuji ji nake kamar zai bude
dan azaba kun san Allah Amira ko mimi bata kaini son
yaynmu ba,sai dai tabi bayana,sun zubo min ido suna
mamakina daga baya suka koma bani baki gami da
kwantar min da hankali suka ce nayi shiru kar mama
taji,nayi tsaki sannan nace ynxu bana shakkar kowa ya
sani yanda nakeji ni kadai na sani nan dai suka dan
lallasheni suka tafi..
So masifa ne yanda naga rana haka naga dare sai bayan
nayi sallar Asuba sannan barci ya daukeni nannauyan
barci mai cike da mafarkai kala-kala,mama ta tasheni
karfe bakwai tayi lokacin da ciwon kirji mai karfi na tashi
hankalin mama ya tashi sosai ta yiwa Alhj waya yana
dakinshi sai gashi yazo,yace shirya