Showing 6001 words to 9000 words out of 17626 words

Chapter 3 - Tawa Ta Sameni Book 2 Complete by Halima Abdullahi k Mashi

ku je Rimi Clinic zan
sameku ina yin wanka mama tace kodai a siyo mata
magani a chemist?Alhj yace a'a ku daije in ciwonta ne fa
kinsan da kirji yake farawa sannan ta suma ku dai tashi
kafin suman yazo,ko wanka banyi ba muka tafi bayan
mun ga likita ne sai ya bani gado raina baiso ba amma
dole na kwanta an min allurai na samu bacci ya daukeni
da sauri ba ni na farka ba sai wurin Azahar mama ta rike
min hannu tana min sannu,na yunkura na tashi har yanxu
saitin zuciyata bai daina zugi ba,da taimakon mama na
samu naje bayi bayan na dawo ne na samu likita ya
shigo zai dubani daidai lokacin yaynmu ya shigo shima
suka gaisa da mama ya tambayeta jikina tacemashi da
sauki,sannan ta fita likitan yace na kwanta sannan yace
ya nake jin saitin zuciyata?nace da sauki sosai saidai
yana min zugi har ynzu na dubi yayanmu da ya kafa min
ido na kauda kai dan ni ko ganin shi bana sonyi,Doctor
ya juyo gurin yayanmu yace yallabai tun safe nake
neman ka a waya ban sameka ba ko da dai kana Amarci
don Allah kayi hakuri na taso ka ko?yaynmu yace no ba
komai matsalar ntwk ne shi yasa baki sameni ba,ya
cigaba da cewa sanda kika yi min waya ina kan hanyar
zuwa nan don Alhj mu ya sanar dani da na kirashi,likitan
yace ciwonta yana barazanar dawowa da karfinsa abinda
ya haifar mata ada ciwon ta sa wani abu a ranta sosai
ta matsa ma kanta da tunaninshi gabanta yana mugun
faduwa inta ganshi,ya batun da kai wancan lokacin?
kasan fa sai da lallashi sannan zaku san matsalar ta,ku
san kuma maganinta sannan muma namu aikin yayi
kyau,yayanmu ya dubeni sannan yace kamar yanda na
sanar da kai na san matsalarta fiye da kowa a gidanmu
ita dai ta cika zafafa abu ne,bata son bin komai a hankali
shine matsalarta,yaja kujera ya zauna kusa da gadon
Iman!ya kira sunana na dubeshi har ynxu mamakin

maganarshi nakeyi yasan matsalata?ke nan ya san ina
sonshi?dan ni dai a sanina bani da wata matsala da ta
wuce wannan.Anty yagana na shigowa Adams da mami
da Amira suka shigo ya rusuna ya gaida mama taja Anty
yagana suka fita,Adams ya dubeni ke yar gidana ya haka
ta faru?nayi murmuahi sannna nace ikon Allah kenan
Adams ba abin mamaki bane ko da mutuwa aka ce
nayi,ya tsare ni da ido kar ki ja mon yar gidana karki min
fatan mutuwarki dan ban san halin da zan shiga ba a
raina naji zan iya auran Adams gsky ba zan tabbatar ma
da yaynmu zancenshi ba shi kuma maye ne yake in har
zai zauna da mutum sai ya san halin da yake ciki,Adams
ya dawo dani daga tunanina kinyi shiru yar gidana ko
jikin ne?a'a kadan kadan kirjina ke min ciwo su mami
suka min sannu yaynmu ne yayi sallama ya shigo ganin
Adams ya bashi mamaki sai naga ya dauke fuska a
daure,hannu yaba Adams suka gaisa sannan yace dama
naso daga nan gidan Nasir zan sameka muje ku gaisa da
Amarya sannan mukai ku airport,ina su john suke?sun
fita da Nasir nima ynxu naje sallama da yar gidana shine
na samu su mami sukayi min bayanin tana nan sai
mukazo amma fa ina ganin ba zamu tafi tare da su john
ba,because of what?yaynmu yayi saurin tare shi da
tambaya,Adams yace kana son sani ne?to saboda sister
dinka yaynmu yace yana da kyau ka san su ma ta lagos
zasu tafi dan haka muje mu sallamesu,Adams ya dubeni
zan dawo yar gidana kinji ko?gira na daga shiko yaynmu
harara ya sakar min ya wuce abinshi,mun jima dasu
mami sannan mukayi sallama,sukan su yaynmu suna fita
sai gidan Nasir inda rigima ta sarke tsakanin yaynmu da
Adams yaynmu ya nunashi kai Adams kana mantawa da
halina kasan fa in har nace no ba mai canja min ra'ayi
ko?kasan haka kafi kowa ma sanin hakan amma kana
bata ma kanka llokaci ne a banza,Adams ya dafa yaynmu
Maska na maka alkawarin barin kanwarka akan sharadi
guda biu na farko in tace bata sona na biu kuma in ka
gaya min hujja mai karfi da ba ka son na nemeta ka
fahimta?yaynmu yace don so bata sonka maganar hijja
kuma babu kasan baka isa in maka karya ba baya ga
tana da wanda takeso da na tsaya maka ka aureta amma
ynxu am sorry to say bazata aure ka ba in kuma ba zaka
bata lokaci ne to shi kenan,Adams ya kule Maska na
gama sanin cewa kaima son yarinyar nan kakeyi tun

lokacin da nasamu lbr ba dadynka ya haifeta ba,yaynmu
yayi wata dariya mai kama da yake sannan ya dubi su
nasir wayanda sukayi cirko cirkk suna duban abokan juna
mafi kusanci da juna a england suna rigima a kan yar
yarinya kamar yanda maska ke kiranta,kunji shi da wani
magana kai kanka ka san in ina sonta baka isa ka
nemeta ba bayan haka ba ni da ra'ayin auran kananan
yara don bana son raini so please and please kabar
maganar nan ma dan zamu iya rabuwa da juna,Adams
yace and so what idan mun rabu?na shirya,Nasir yace
dan Allah ku saurara haka kai Maska kayi hakuri mana
tunda ka san ko shi wane ne in yana da wata matsala ne
sai ka mishi bayani ga matsalar ka shi yasa kaga in da
gyara sai ya gyara,yaynmu yace Adams yace namiji
ne,bashi da wata matsala sai dai ya nemi matarshi a
gaba Adams yace ai na samu yanxu kai kuma baka isa
ka hana ba,Ok! zamu gani kana proud din baka taba
neman abu ka rasa ko?to zaka fara akan wannan inji
Maska,su John dasu Nasir sune suka bada baki kafin
sukayi sallama amma banda Adams yace sai ya kara
kwana biu,sun kaisu airport sannan suka wuce gidan
amarya wacce ta cika fam da fushi,yaynmu ya dubeta
madam kimin afuwa kinsan ina tare da baki yau zasu tafi
ko shiyasa ya fada lokacin da yake zaunawa kusa da ita
su Nasir da Adams ma suka zauna,ta dan yatsina fuska
sannan ta gaishe su yace yunwa fa mukeji fa,ta dube shi
baku ci binciba?ayya gashi nayi bakin kawaye momina ne
ta rako su shine suka cinye Dukda,ranshi ya sosu amma
bai nuna ba sai yace shi kenan kawo masu wani dan
abin sha mana,ta mike tana karairaya Nasir ya bita da
kallo sannan ya dauke kai shima irin matan nan basa
birgeshi sam bata son mutane yaci ace yanda suke
abokan Maska ace sun saba amma ita sai girman kai
kamar yar wani da wata gashi daga gani za tayi rowa kai
shi kyanta ma bata birge shi mace a bushe haka?fari ne
da hanci kawai shi kuma bai ma cika son dogon hanci
ba,tunanin shi ya katse lokacin da taje musu da robar
ruwan Cway da kofuna,kunya ta kama yayamu ya dubeta
ke ba wani mai dan zaki ne?bana yiwa Kabir waya ya
kawo drinks ba?ta dan yatsina fuska zata tashi Nasir
yace no yi zamanki don ni dam nake sai dai ko Adams,
Adams da ya zuba tagumi yana tunanin Iman ya ce am
ok nima a koshe na ke,sun dan yi hira sam ita bata sa

masu baki ba TV kawai take kallo ko da zasu tafi ba tayi
musu magana ba sai Nasir ne yace mu mun wuce,to
kawai tace suka fita yayi masu rakiya ya dawo su kuma
su ka nufi gurinmu a Asibiti.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Washegari aka sallame ni na dawo gida da kundurin cusa
son Adams a zuciyata don haka duk sintirin da yaynmu
yake yi bai burgeni ba duk da in har ina ganshi sai
gabana ya fadi, kuma sonshi na nan daram a raina,daren
ranar sai ga Adams ya zo mani sallama yana min
bayanin dan dai zasu yi wani wasa ne a club dinsu kuma
wasan yana da muhimmanci sosai da ba zai tafi ba gashi
ba Maska bai kamata kuma shi ba ya nan ba,nace ba
komai naji sauki kuma ga waya ai,ya ce to bani no naki
in yaso in naje sai na dinga kiranki sannan ki bani
tabbacin kina sona dan Maska ya gaya min kina da
wanda kike so,haka ne?nace batun wanda nakeso dai bai
taso ba dan babu sai dai game da kai,in mun waya zan
sanar da kai ina jin kunya ne yanxu,yayi murmushi shi
kenan yar gidana a zuciyata nace kunyar karyar da zan
maka ne ya sa ba zan iya fadama baki da baki ba dan na
san ba wani sonka nakeyi ba ne burgeni kawai
kakeyi,kyautar wani kyakkyawan agogo da turare ya yi
min nayi mishi godiya mukayi sallama sannan yace min
idan ya sami sukuni zai zo ba da jimawa ba kuma jiya ya
gabatar da kanshi a gurin Alhj,da sauri na dubeshi me
yace maka?ya ce yace kar na damu gurin su manya ba
matsala in dai sunyi bincike sun gano asalina a
Ghana,nace yauwa Adams kana da yare ne?ya ce eh
yace mu asalinmu fulanin yola ne yan Adamawa zama ne
yakai kakaninmu suka haifi iyayenmu muma aka haifemu
a Ghana,nayi karatuna duka zuwa Degree wasan kwallo
kuwa ina primary nake zakara kuma ni ne babba a kaf
gidanmu kanne na hudu maza da mata,matan babana
biyu ne kuma har ynxu muna zuwa Adamawa kuma suna
zuwa babana yana da sarautar matawalle dan haka duk
salla familynmu a can muke yi ko ni in ina gida tare
muke zuwa,kin fahimci takaitaccen tarihina? nace na

gane yace to muna da yawa sai ki shirya in munyi aure
duk sallah zamu zo daga England Adamawa zamu sauka
haka nan in kin haihu a can zaki zauna ko in baby yayi
kwari sai nazo na tafi da ku dariya nayi nace Adams
kenan har ka tsara komai yace yes haka kullum nake
mafarki nace to ba ka fadamin me kayi Degree a kai ba
sannan cikakken sunan ka,yace nayi Degree
akan,cikakken sunana shine Adamu Salisu Adamu,
Abokaina su suka sa min Adams sai ya zama har JC na
Adams suka samin kinji yanda abin yake,sai naji Adams
ya kara bani sha'awa kuma zan iya kukutawa in aure
shi,mun yi sallama dashi nayi mishi rakiya har wajen
gate mukayi sallama akan sai naji shi a waya.
Ni,Mami da Amira tafe muke kan hanyar mu ta zuwa
kasuwar unguwar Rimi zamu raka Mami ne amsar dinki
muna tafe muna hirar Adams,nace mami ni fa yanxu
Adams kawai na tsaida ma zuciyata duk da na san cewa
bashi ne zabin zuciyata ba zai fi min kwanciyar
hankali,Amira tace na goyi bayanki Mami tace sam ba
zata yiwu ba kina tunanin shi ba wata matsala daga
dangin shi?sannan ba shi kike so ba in kika jure wani
abu wani ba zaki jure ba musamman ma da yake ba shi
kike so ba gara wanda kake so zaka hakura da wani
abun albarkacin son nan shiko daban ne,nace Mami Haj
Yaya da Haj Laure ba zasu bari na zauna lfy ba sannan
da wanda na ke sonshi baya so na gara wanda nake ki
yake sona zan lallaba da Adams,mun tsallaka daidai
shagon Ubale zamu shiga cikin kasuwa sai ga wata mota
ta tare mana gaba baka ce wuluk Mami tace motar nan
tayi min kyau,kafin nayi magana har mai motar ya fito
wani mummunan fduwar gaba naji yayin da muka hada
ido da mai motar,shima ni ya tsura ma ido yana kallona
mami ta ce kin sanshi ne?nayi karfin hali nace a'a naja
hannun Amira jikina ba karfi sai mutumin yace uwata ni
zaki gani ki wuce uwata?kin bani mamaki uwata zo kar
ki tafi ina Habiba? Sai na soma kuka mai karfi mutane
kallona sukeyi ya bar jikin motar ya nufo ni da gudu na
tsallaka titi na nufi layinmu ina jiyo muryar shi yana fadin
uwata kar ki kuma tfy ki barni zo mana mamana,ai sai
gida ina tafe ina kuka kamar wadda aka ce uwarta ta
mutu ban damu da kallon da mutane suke min ba jikin
Mama na fada tana zaune a firgice ta tashi tana fadin
lfy?menene? Ina sai kuka ruri nake Mami da Amira suka

shigo a sukwane Mama tace Amira me ya faru?
hankalinta a tashe ta ke magana Amira tace mama
muna tfy zamu shiga kasuwa sai muka ga wata mota har
muna cewa kai motar ta hadu kawai sai mai motar ya
fito yana ganin Iman kawai sai mukaji ya hau cewa
uwata dama kina nan uwata?zo nan kawai sai muka ga
tana kuka ta rugo shine mutumin yace mun san gidansu?
mukace eh shine ya dauko mu ynxu yana nan waje wai
mu kiraki,mama tace baku da hankali daga ganin mutum
sai ku nuna masa gidanku?dama ya tafi daku,ta daka
masu tsawa me zakuje ku ce masa ba zan fito ba a ina
ya sanni,Amira da Mami suka kada baki wllh mama yayi
kama da Iman sosai mama tace ba shi bane nace kuje
ku sallame shi mana,cikin kuka nace mama baba ne
fa,mama tayi shiru dama nasan ta gane can sai tace
Amira kije kuce mishi mijina baya nan dan haka ba zan
iya ganinshi ba su Mami suka sameahi ya kifa kai jikin
sitiyarin mota mami tace baba da sauri ya juyo yaushe
rabon da yaji wannan kalmar yana kishin jin kalmar nan
ga zatonsa Iman ce amma sai yaga yaran dazu,ya
dubesu ina Habiban?suka ce tace mijinta baya nan shi
yasa ba zata iya ganinka ba ba.
Na idar da sallar magriba ina zaune a takure duk
tausayin mahaifina ya cika ni Alhj ya shigo da sallamarsa
ba sosai yake shiga dakin matanshi ba sai in bukatar
hakan ta taso ya karaso gurina yaya dai Iman?lfy dai ko?
nace lfy klau ka dawo lfy ya kasuwa?Amalhmdl Iman
kuma lfy lau muka dawo ina Habiban fa?nace tana cikin
dakinta,ya nufi dakin mama yana fadin Habiba sarkin
hidima hala wani aikin takeyi,sun jima sannan suka fito
naga fuskar mama murtuk babu alamar dariya ta zauna
kan kujera shima ya zauna kan daya kujerar dake kusa
dani yana fdin ban sanki da fushi ba ba halinki bane
ruko,kuma ba kya gaba,uhm kuskure mutumin nan yayi
ya kuma gane har kasuwa ya sameni shi da wani
Ibrahim ban san wanda ya nuna musu ni ba sai dai
ganinsu nayi nace miki har kuka yayi gabana yanzu kiyi
hakuri ki zo muje suna falona ku gaisa,mama ta ce cikin
fushi Alhj Mukhtar na taba yi maka musu?yace a'a tace
to tin da kaji nace ba zani ba itama ni na haifeta ba zata
ba to,ko kukan jini yakeyi ba zamu ba,yanzu ne ya san
damu?ba zan iya ba wllh in kuma ya matsa min sai na
maka shi kotu da sauri na dubi mama kalmar ta bani

mamaki sam ban taba tunanin mama tana fushi haka ba
hawaye ya soma zarya a kumatuna sam ba zan so haka
ba Alhj da shima mamaki ya hana shi magana sai ya
mike ya fita falon shi ya sami babana da yaya Ibrahim
hakuri ya basu gami da ce masu su je su sami kawu
malam can kuwa suka tafi kawu malam ya jima yana
yima babana nasiha sannan ya ce je gobe ya dawo suje
unguwar Rimi
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Misalin karfe biu saura kwata 1:45,zaune nake kan
sallayar da nayi sallah na jima ina adduoina game da
matsalolina, mama dake kan kujera ta dubeni Iman ynxu
ya zaki hada lesson da comp school din na ce nifa
mama ynxu duk basu dameni ba krt ma ya fita daga
raina mama ta kafa min ido sannan tace to me zakiyi in
baki krt ba?nayi shiru ta saka salati ku jimun yarinya
aure kike so ke nan ko?nan ma banyi magana ba tace
shi kenan kudina sun huta sai ki fito da mijin ko,na dubi
mama nace bafa dan haka dan haka bane dan....sai
kuma nayi shiru,yi min magana dan menene?nace dama
wani abokin yaynmu da yake can England yake sona
yace kuma a can zamu zauna can zanyi karatuna,mama
tace Alhj yayi min maganar shi yo koma zakiyi krt ai dai
sai da sakamako mai kyau ko?nace to wane ma lesson
zan shiga,mama tace ga wata nan ramat road ki shiga
tunda an kusa fara jarabawar ina gama salamat tsohuwar
makarantarku zaki zana jarabawar a can,nace yauwa
dama yafi,...Alhj ne yayi sallama mama tace lfy Alhj?na
ganka da rana yace lfy lau ya dubeni nayi mishi sannu da
zuwa yace kuzo Habiba ke da Iman ku sameni a dakina
gabana ya fadi mama tace in fa baban Iman ne ba zani
ba yace ina dai jiranku,falon cike yake da mutane Alhj ne
a kujerar bakn kofa 2 sitter sai kawu malam can gefe na
gane yaya Ibrahim da kuma babana sai wasu mutane
uku da ban sansu ba nan da nan mama ta dunke fuska
kusa da Alhj ta zauna nima na zauna kasa gefen
mama,sai baba yace uwata zo nan kusa dani mana ,na
dubi mama sai naga bata kalleni ba dan haka sai na nufi

babana kasa na zauna ya jawo ni kaina ya dora kan
gwiwowinshi naji wani irin muguwar soyayya irin ta da da
mahaifi na ratsani kawu malam ne ya soma magana
Habiba ga uban Amina ya zo bada hakuri akan irin
kuskuren da ya aikata a can baya,mama tace ai bai min
komai ba,babana yayi karfin hali yace haba Habiba nasan
nayi maki kuskure dan Allah ki yafe ni nasan baki da
ruko habiba,mama tace ai ni Idris dan ka sakeni ba laifi
kayi ba tunda halas ne sannan Allah ya bani wani mijin
wanda yafi ka komai nima sakamakon hakurina kenan,na
dubi mama banji dadin maganar data fada ba babana
akafi?na kuma gyara kwanciyata a jikin shi ni ina sonshi
nace a raina,kawu malam yace yanzu dai yace ki yafe
mashi babna yace yauwa nidai kimin aikin gafara mama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login