Showing 12001 words to 15000 words out of 17626 words
Chapter 5 - Tawa Ta Sameni Book 2 Complete by Halima Abdullahi k Mashi
in har na sameta?kana ma shakka
kenan?kar ka manta fa har na biya sadaki an sa mana
rana kuma kaine ma ka tsaida min har na sanar da
manya,Maska yayi wani murmushi Adams ya kalleshi
Maska bana son wannan murmushin naka fa tuni na sa
mashi suna murmushin mugunta dan ko a fili muke
gurin wasa abokan wasa suka sako mu a gaba kana
irin wannan murmushin sai kaga Allah ya bamu
nasara,Maska yace tashi mu tafi a can zan yi break
kafin mu shiga fili. Ni kam lokacin ina kauye ranar
kwana na sha takwas daga sati daya ina jikin tsohuwa
kakata tana fadin daga ni takwara kar ki karasa ni nace
kai dan Allah ki barni na dan huta mana infa na tafi sai
na dade zan zo tace ai ba zaki kawo min Adamu mu
gaisa ba?nace ni ina naga wani Adamu yana can
kasashen turawa yana kwallo tace ai Ball yake?ynxu
dan Ball din zai rike ki?nace to ai tasu ta gaske ne ba
irin ta nan ba,ta tureni ke ja can da ban haushi baga su
nan muma muna dasu ba yan bal din yanxu jibi yaron
nan na gurin karima shima aikinshi kenan bal asubar
fari yasa gajeran wando da wani kwandallelen takalmi
raf raf ya tafi bal kusan shekara biyar ance har yau baa
taba nuno shi a cikin talabijin ba shi bai tsaya yayi
noma ba shi kuma bai tafi rani ba,sai dai yau yana
waccan unguwa gobe yana waccan yawon bal,tunda ta
soma magana nake dariya,tace dariya ma na baki?
dama wannan shirmen Adamun keyi shine za'a bashi
mata?ko mu da muke karkara dan gidan karima an
hanashi mata,na kuma tuntsurewa da dariya ta dau
mafici ta bini kki bani guri ta kai min duka da gudu na
fita ina kwasa dariya sai naji tsayuwar mota da sauri na
leka motar babana na gani da gudu na fita na
taroshi,Ya kira wasu yan samari suka shigo da kayan
abinci na rike mishi hannu muka shigo, dakin Baba ya
soma shiga kafin ya shiga dakin Tsohuwa na nufi
madafi na dauko masa abinci a kwano na debo masa
ruwa a randa na aje a gabanshi ina fadin Babana kamar
nasan zaka zo na yi abinci da yawa,yace to na
gode,nace yasu Mama?yace suna lfy sune ma suka
matsa min akan na daukoki daga sati har kin kusa wata
jiya Alhj ya kirani a waya yace in mashi kwatance yaje
ya daukeki,nadan yatsina fuska nace ni ban son tfy
tsohuwa tace to ai ya zama dole nace muna gama
bikin su Mami zan taho nan,baba yace a'a muma muna
son ki zo mana kafin bikinki daga nan nayi shiru ban
sake magana ba,tsohuwa tayi caaraf tace yawwa ashe
kai yanzu Adamun dan bal ne?shi ne zaku bashi yar?
Babana yayi dariya sannan yace ai sana'a ce sosai
suna samun kudi fa shima dan mai gidan Habiba
kwallon yake tare ma suke, ai shi kenan amma ko ga
tarihi bal ance bata da kyau,yace to ai wasu malaman
sunce za'a iya yi in ta zama lalura saboda kishin kasa
tace tunda kuna so ai komi ma cewa zakuyi ni dai ina
jin su har suka gama.
Adamssalin tara text din da aka saba yi min tsawon
watanni kullum ba fashi ya shigo,very soon zamu
kasance tare domin nasan i am always lucky akan duka
abinda nakeso,ban ma gama dubawa ba na kashe yau
kamna gane Adams ne yake min text yana boye no
haushin shi ya kara kamani na hau fada ina cewa nufin
shi sai ya min haka zan so shi?to yayi kuskure ni ba
sonshi nakeyi ba zan dai aure shi ne dan hujjar da na
ba yaynmu nace kai bari ma in mashi karara don ya
daina damuna na soma neman layinshi ai cikin sa'a na
sameahi ashe lokacin suna tare da yaynmu a wani club
ya dubi yaynmu yace ga yar gidana sannan ya dauka,in
kaga yaynmu zaka dauka bai damu da wayar da Adams
keyi ba amma ya tattara dukkan hankalinshi gurin
sauraron Adams dan ta maganr da Adams keyi zaka
gane me nace,ni kam Adams na dauka nace hello
Adams menene na boye no kana yi min text in ma kana
yi ne dan ka birgeni to wllh haushi ma kake bani,tunda
na soma maganar bai tare ni ba sai da nayi shiru,yace
calm down my wife wllh ba ni bane ba ban ma taba yi
maki text ba nace to wanene?ina zan sani inji adams
sannan yace don Allah kiyi hakuri karki damu kanki
kashe na kiraki,nace yanzu zanyi shafai da wutiri ne sai
da safe yace sai da safen yanda ya amsa har tausayi
ya bani,Maska ya dubi Adams dan san jin karin
bayani,Adams me Iman tace maka ne?Adams yace wai
cewa tayi ina boye no ina kiranta wai bata so Maska
yayi murmushi to dama kai kake mata ko?Adams yace
bani bane Allah maska yayi tsaki sannan yace kaga
abinda nake gaya maku ko ku nemi manyan babys ynxu
gashi kana yi ma yar cikinka rantsuwa ita kuma sai
masifa take maka ynxu ina girma?babu babba wani
abun ma sai taga gadon kwananka Adams yayi
murmushi yace wannan ra'ayinka ne kawai niko ina son
in auri yarinyar dan na more sadakina da kyau Maska
yace in ka samu big girl shine zaka more sadaki Adams
yace mu bar zancen haka Maska yace kai dai ka sani
yaushe zan bar yar yarinya ta juyani? ai ni in babbar ce
ma sai ta raina kanta in tace zata kawo min iskanci
Adams yace in baka sonta ba ba in kana sonta komai
zatayi maka zaka jure sai kaga karamar ta juya ka
babbar bata juya ka ba,tsaki Maska yayi sannan yace
baka gama sani na ba har ynxu don ina son mace tayi
kadan na jure iskanci, sannan ya mike ya tafi Adams na
mishi dariya.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Muna zaune a dakinmu muna aikin gyaran katunan
bikin su Mami yau saura kwana takwas bikin kuma
yaune su yayanmu zasu iso shine babban abokin ango
kuma babban yayan Amare,na dubi Mami nace ya kan
Badarawa,Malali,da Unguwar sarki ya kamata muje dan
yan skull zamu gayyace sosai mun dade bamu hadu ba
mami tace haka ne yi sauri mu biyama Amira,tare
muka shiga gari sai magriba muka dawo sai dai in
lokcin sallah yayi mana mu tsaya muyi,shirye shirye
sunki karewa saboda wasu abubuwan bada su Sa'a
zamu hada ba walima ce kawai tare sai Sisters day da
su Anty Mariya suka shirya a gidan yaynmu in sun iso a
Yakubu Avenue amma mu zamuyi lunchn sannan
angwaye sun shirya dinner,mun dawo mun sami yaynmu
ya iso saboda gidansu sai an gyara da yan share share
gurin su Sagir na sami lbr isowarsu sai ga kuma wayar
Adams yana ce min sun iso ynxu suna tare da ango
nace to sannu da zuwa me zan shirya maka?yace
komai ma nace to an gama nadai daure ne nayi
wannan maganar dan kar ya ce ban yi murna da
zuwansa ba amma zahiri hankalina yana kan yayanmu
da kuma masifar son ganinshi,nan na dan yi girke girke
na san Adams na zaci zan sameshi tare da yaynmu a
dakin yaya kabir din ina sai shi kadai na samu dan haka
shi kadai yayi ta surutanshi Adams ya dubeni kin kara
cika fa yar gidana ina son Maska ya ganki shi da yake
cewa zan auri yar cikina nace um! Sama sama mukayi
hira sannan na koma gida shi kuma ya nufi gidan Nasir
har ramar lalle banga yaynmu ba ko anty mimi ban
gani ba mu da yake gidansu Amira mukayi namu lallen
su kuma gidan Anty Hadiza sukayi,sisters day shine abu
na farko da kamar kar naje mami tace in banje ba
bazata ba dole tasa nace to zanje,da yake dama gurin
babana naje na amshi kudi na shiga kasuwa materials
da lace sai da naga karshen tsada na sai mana takalmi
da jaka ai fdi ma bata bakine ganin abin rabawa na
buga jaka na buga bokitai na roba sai na buga agoguna
har fada mama tayi min wai naje ina amso kudi masu
yawa haka shi kuma ya biye min,nace to mama kiyi
hakuri ni ban yana cewa in basu isa ba zai kara min
wasu wai dan ni kadai yake neman kudi,mama tayi
tsaki ta shige daki mu da Amira ba muje shirya gurin
da zaayi sisters day din ba dan gudun rikici sai bayan
an gama komai an soma kai kawaye sannan muka
shirya,jan material dan dubai shi na dinka riga da siket
nasa duk yanda mutum ya kai ga hassada ba zai
kusheni ba a wannan rana takalmi da jaka bakake nayi
amfani dasu kafin amira ta gama shiri na shiga gidan
mu na fito wata mummunar faduwar gaba naji sanda na
hangi yaynmu a kofar dakin yaya Kabir shi da Nasir
sanye yake da wando jeans baki da riga fara ta kama
jikinshi kyau annuri ne ke fita a fuskarshi yana da kyau
na karshe fatar shi ta kara zama smooth giran gashin
shi kuwa abin birgewa ne,kamar na juya sai na dake
tunda bai ganni ba gara na nuna ban ganshi ba sai da
nazo daf da su sai Nasir yace kai Iman wannan dauke
kai haka?na juya da sauri ango ban ganka ba ne,na isa
wurinsu na dubi yaynmu wanda yayi wani kicin kicin da
fuska nace sannu da zuwa yaynmu kunzo lfy?a ciki
yace lfy duk sai naji ba dadi dan haka sai nace Nasir a
kirata ne?yace a'a ba gurinta nazo ba sai na wuce
ciki,ganin yaynmu sai tsohon ciwona ya tashi wutar
sonshi ta soma ruruwa a cikin zuciyata ranar dai sai a
hankali mun isa gidan yaynmu sai naga ma ashe duk
yanda suke bada lbr haduwar gidan ya wuce nan gefen
da ake sister day lambu ne yanda suka shirya yayi kyau
Amare kaya iri daya suka sa tunda muka zauna bamu
tashi ba sai da aka soma liki sannan ne na shiga nima
na bada tsoro da kudi na fito,anty mimi tayi kyau sosai
cikin farin tattausan leshinta rigar fitet ce don haka
cikinta ya dan fito dan das daga mun hada ido sai ta
dalla min harara har Amira ta lura da ita tace ke kefa
matar can take harara nace tayi ta gama abinda yasa
ma bata neme ni da rigima ba dan tasan yanxu bama
shiri da mijinta ko ince an samin rana shiyasa Amira
tace haka ne kam,wayata ta soma ringin na duba sunan
yaynmu na gani gabana yayi mummunan faduwa na
dauka yace ina jiranki a falon gidan nan cikin in ina na
ce ban san hanya ba ki tambaya sai ya kashe wayar na
dubi Amira kinji yaynmuda rikici ko wai na sameshi
falonsu bayan dazu da ya ganni sai ya wani daure
fuska Amira tace kije mana nace to ai tana kallona
matarshi Amira ta ce to zauna ina ruwana,na mike na
nufi hanyar waje nan na kirashi nace ban gane hanyar
ba gani a gurin bakin gate,yace ni kenan kike nufin in
zo ko?sai ya kashe,gun mai gadi na nufa nace mishi
dan Allah ina kofar falon,ya nuna min sannan na nufa
sanyi da kamshi da kuma laushi su naci karo dasu ina
shiga falon,yana zaune yana shan coke na isa gurinshi
har ya canza kaya daga bakin jeans zuwa blue da yar
shirt,na dan rusuna gefenahi yace tashi ki zauna kan
kujera na tashi nabi umarninsa yana kallona kamar hoto
ko TV yana shan coke na gaji kar matar shi tazo sai
nace gani yace na ganki sai yaci gaba da abinda yakeyi
da danne dannen waya,can sai yace ke kamar ni nazo
garin nan ace ki gagara zuwa ki gaisheni?sannan da
muka hadu sai kika wani dauke kai ke kin girma wai
shekarar ki nawa ne?nayi shiru dake nake na dubeshi
fuskata a daurena kauda kai,ba kya jina nace sha
takwas yace to me na miki kika kasa gaidani?nace ban
gane kaba ne shiyasa shi yasa kika manta dani ko?baki
taba yi min waya ba tun da natafi me yasa?nayi shiru
can nace to kayi hakuri,aikin ki kenan bada hakuri to
na hakura menene shirye ahiryen na ki bikin?na
dubeahi ni bani da wani shiri yace ki dai fada tun da
wuri kinsan ance mai kwarmin ido da wuri yake sa ma
kuka nine uban Amarya kuma nine abokin ango,haushi
ya kamani nayi kicin kicin yace to menene na bata ran
kamar ba ke kika zabi mijinki ba?sai ya canza magana
baba kwana biu ban kirashi ba kuma tun da nazo banje
ba amma zanje mu gaisa nace dama kana kiranshi ne?
sai ya share zancen,kun zan jarabawar?munyi,to Allah
ya bada saa amin ina yan waige waige yace me kike
kallo ne ki saki jikinki gidana kike ba na wani ba ni ko
yaynki ne,Amira da Mami sai doko min waya suke ina
cewa gani nan yaki sallamata,har suka tashi sai ga
mutane na mike da sauri harara ya sakar min ba shiri
na koma na zauna a raina nace kai dai kana shaawar
kowane biki sai ka sani a problem,sunyi mamakin
ganina sosai fuskar anty mimi a kaina,Nace don Allah
zamu tafi shi kuma sam ya ki sai da yayi raayi sannan
yace to wa zai kaiku?nace mashin yace bana son kina
hawan mashin fa nace to nabi motar Nasir ni da
Amira,to sai yaushe nace ai yanzu kuna nan zamu yi ta
gaisawa ko yaushe yace shi kenan,washe gari lunchn
tun safe ba hutu sun tafi gyaran gashi ni kam da bani
kona gashi sai na tafi kitso biyar daidai kowa ya shirya
sai mu kawaye da Amarya ake jira dan har an soma
dibar kawaye bayan na shafa mai sai inner wears na
dakko less wanda ya amsa suna less kalarshi ba zaa
kirashi milk ba kuma ba zaa kirashi yellow ba shi kuma
ba light brown ba yana dai tsaka tsaki na saka shi
sannan nayi shafe shafe kai ni kaina nayi mamakin
kyan da nayi sai da na gama shiri tsaf sannan na fito
kai Iman inji Mami gsky ko ni amarya kin fini haduwa
gsky cire inji Mami nayi murmushi nace ba wani kyan
da nayi,kafin tayi magana sai ga su Amira da sauran
kawaye kowacce sai da ta raina kwalliyarta ynxu burina
inga yaynmu shima inji ta bakinsa mun fita harabar
gidan mu yan mata ne tsantsam nan kallo ya koma
kanmu Adams ne tsaye suna magana da sauran abokan
ango yana hango ni sai kawai ya wani washe baki yana
kallona amira tace iman ji mutuminki nace naganshi
share kawai,ya iso gurinmu Amarya gsky ba tare da
ango zamu kaiku ba sai dai ya haura ma kanshi daga
baya,Mami tace saboda me kace haka Adams?Ya nuna
ni yace ga yar gidana da Amira ku zauna tare a motata
don ni ne zan tuka ku na juya zan mishi magana sai
wata masifaffiyar hadaddiyar mota ta kunno kai
harabar gidan duk mutanen dake gurin sun raja'a ga
ganin motar, baka ce wuluk haka gilashin ta ni kam
shashancewa nayi ina duban motar dan tunda nake ban
taba ganin mota irin wannan ba,Adams ne yace sai
Maska dai dai lokacin da yayanmu ya fito cikin wata
shadda galila yar gaske sai maiko take,hatta
numfashina sai da ya dauke na yan dakiku sannan ya
dawo daga nesa damu yake amma kamshin sa har
gurinmu,Adams ya ce sai Maska yaynmu ya dago mishi
hannu ya mishi alamar yana zuwa 'yan mata suka bishi
da kallon birgewa yayin da wasu suka kyasa
A hankali nayi ajiyar zuciya sannan nace Adams kun
damu mu fito ga mutane ba'a gama kwashe su ba ya
za'ayi mu tafi?ya ce to ynxu ya za'ayi kenan? Amira
tace don Allah ku gama kwashe su mana sauran
abokan suka ce to,yaynmu ya kuma fitowa gurin
motarshi ya nufa Adams ya bishi ya bude mota suna
magana da Adams ko me suke cewa oho?sai Adams ya
dawo shi kuma ya shiga cikin motar sai kuma ya fito
ya dubi gurinmu da hannu ya yafito ni gabana ya fadi
nace Amira yayanmu yana kirana mami tace karki dade
fa banko iya magana ba na nufi gurin motar sai na
samu kaina da canza salon tfy cikin isa da kasaita na
iso gurin motar gefen kusa da dryva ya bude dan haka
sai na zagaya nayi magana sai naji yace shigo ba musu
na shiga kamshi da sanyi sukaimin sallama cikin isa da
jan aji ya tashi motar ba tare da ya dubeni ba cikin
gwaninta ya fusgo motar da gudu sai da muka hau titin
Bako Road sannan ya kara sautin wakar p square cikin
wakar su ta no one lyk u,na jingina da kujera ina
sauraro wakar na zata gurin lunchn zamu je sai fa naga
mun dau wata hanyar ban ankara ba sai gamu gaban
gidan yaynmu dake Yakubu Avenue gabana ya fadi
sannan tsoro ya bayyana a fuskata yaynmu ya dube ni
sai ya fito da waya yana yan danne danne shi ban sani
ba ashe hotona yake dauka ban sani ba,na rufe wayar
sannan yace bisimillah mu shiga nace me zan yi
yaynmu?kasan fa gurin Lunchn zamuje,yace nima
bazaniba dan haka kema ki hakura da sauri na dubeshi
cikin damuwa nace mami ba zata ji dadi ba fa yanda
muke da mami ban kyauta mata ba,dubana kawai yake
sannan yace to mimi taje mana ni dake dan haka ynxu
ma ni yunwa nake ji mu shiga ki min abinci na dubi
fuskar shi ba alamun wasa amma duk da haka sai da
nace bai dace matar gidan ba ta nan ba na shigar mata
gida ya daka min tsawa gami da cewa tsaran ki ne ni
kike yi min musu?bayan mun shiga ya tsaya da motar
na fito shine a gaba ina binshi a baya har falo ya zauna
nace inane kicin din bi nan ya nuna hanyar,na tafi
komai na kicin da ake bukata akwaishi dan