Showing 30001 words to 33000 words out of 43444 words

Chapter 11 - Arnan Daji Book 2 By Farida Feedyn Bash

19 Jul 2026

73

dubu 700 Kuma nasan Yana da ita Amma yace be da ita ya kawoni Nan ya yasar har yau
ban Kara ganinsa ba kitemakeni afra cike da tausayi tace Ni Banda kudi a yanzu Dan bikina
saura sati daya Amma bara na Kira jeddah tana fita taga wayam ta duba dakinta Bata Nan
bandaki ba kowa ta leka waje wayam ba motar ta ta gudu kenan itada uwarta bare ni tuni itama
ta karawa kafarta burki ta tafi gida itama tana Allah wadai dasu jeddah insha Allah alakarsu ta
yanke tana tafiya sai ga text dinta ya shigo idan kingaji Kya tafi ki kyaleta kwashe kwashen ta
na masifa taje wani yai Mata cin dayafi karfinta ya rubata Dan Haka ki kyaleta Naga uban daze
Kara cinta a Haka tunda ita batasan ta girma ba Tofa lallai wayannan Basu da mutunci cewar
afra tuni tasa number dinta a divert




Jeddah Bata zame ko Ina ba sai gidan wata dillaliya a Yan lemo Tai Mata bayanin komai ta
amince akan kudi dubu dari biyu sunyanke maza za'a nema su karbi lefe su daura aure Baki
alaikum haka ko akai ansamu wasu dattijan biri zauna gari banza aka tsadance su uku ta Kira
alhaji labaran ta Gaya Masa komai dariya kawai yai ba matsala gobe karfe goma na safe
zasuzo su kawo Haka ko akai washe gari ta Kama asabar aka kawo kayan lefe akwati Sha biyu
sai kace wata budurwa budurwar ma ta yayan gata da sadaki dubu dari biyu da kudin gaisuwar
iyaye dubu dari uku gaba daya dari biyar suka kawo murna kamar jeddah ta zuba ruwa a kasa
Tasha daya tambayeta meyasa aka kawo Nan bayan da tace a dangwauro take sai ta waske
kawai




Ai chan din babanta dama ya mutu mamanta Kuma Bata garin sunyi waya tace azo Nan gidan
kanwarta Haka suka bar maganar bayan sati daya akai bikin afra aka kaita me Dile batai party
ko daya ba sai dinner da ango yai bayan daurin aure an kaita gidanta suka Sha dinner dinsu
tadai yi walima agidansu anyi biki lafiya angama lafiya duk wata kawa datasan ta barikice Bata
gayyaceta ba iya Yan unguwar sune da Yan uwanta matar babanta bataso Tai wannan auren ba
bakin ciki kamar tayime gashi ta samu mijin marainiya akwati takwas yai Mata komai Masha
Allah sai muce amarya Allah ya bada zaman lafiya

Haka jeddah tadinga shirye shiryen ta tsaf dangane da nata bikin tasha gyaran jiki tayi kyau
dama jikinta me kyau ne sai ta dawo tamkar wata fure Dan kyau tayi fes abunta gwanin
Sha'awa biki ya rage saura kwana uku duk wasu fitinannun kawayenta ta gayyacesu Dan party
suka shirya har kala biyar zasu watsu su lalace ya bude Mata bakin aljihu sai bindim bindim
take a ciki gashi komai ya sauke mata na daki tasan ita me sa'a ce a rayuwarta bazata taba
auren wahala ba wata kawarta ta hadata da wani hatsabihin boka megani har hanji yagama
shiryata yadda zata tunkari gidan alhaji labaran Tofa maji magani jeddah koza a Kara dacewa


_*To fans sai naji comment dinku gaskiya na yanke shawarar Dena posting kowane book nawa
a wasu groups din sai nawa Dan bakwa mun comment wahar dakaina kawai nake iya fans Dina
kemun comment wallahi indai Banga sanji ba daga yau nadena posting din book Dina a kowane
group nice taku a kullum a Koda yaushe*_





*Feedyn bash*
[10/23, 2:33 PM] 👯🏻Ummu Subai'a🎭: *🎭ARNAN DAJI🎭*


*NA*


*FAREEDA ABDULLAHI*




*_🌈KAINUWA WRITERSâœí ¼í¿¼ ASSOCIATION_*í ¾í´í ¼í¿»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*Assalamu alaikum my fans inafatan Kuna lafiya Dan Allah kuyi hakuri na rashin jina kwana biyu

hakan ya farune sakamakon rashin lafiyar danake fama da ita kuyi hakuri kumin uziri ba kullum
zan dinga muku typing ba Dan Allah kudinga kokari Kuna posting zuwa wasu groups din wallahi
bazan iyaba abun dayawa nagode my fans nagode da kaunarku a gareni da tarin addu'oi in da
kuke mun suke Kara bani karfin gwiywar faran ta muku kamar yadda bakwa gajiya dayimun
addua akara hakuri dai danií ½í±í ¼í¿»í ½í±í ¼í¿»í ½í±í ¼í¿»í ½í±í ¼í¿»*

95-100




Jeddah duk wani shirye shirye ta Gama tayi gyara na tashin hankali ko budurwa albarka har
wani yalo yalo take wankan inji akai Mata jikin ta yayi smooth ga alhaji labaran ya sakar Mata
bakin aljihu facaka kawai take da kudi ta tattaro ta dawo gidan hafsa dillaliya hankalinsu kwance
suke shirye shiryen biki wadda hafsa ta Zama uwar amarya ga wayanda aka debo haya a
matsayin iyayen ta maza tunda dama mahaifinta ya mutu a matsayin abokans da Dan uwansa
suke Tayo gayya ta manyan Mata matan dasuka amsa sunansu Mata wasu zawarawa ne wasu
matan aure wayanda suka gagari mazajensu wayanda suke haduwa a shargallensu yammata
ma ba'a barsu a baya ba bikine ta shirya shi nakece raini anshirya karya a bikin ko dayake da
abun ai




Kawarta ce ta rakata gun boka sangamu ya Bata lakanunnuka da magungunan dazata mallake
mijin ita kadai ta juyashi San ranta sannan ya Bata Wanda zata haukata haleema saboda
bala'in haushin dukan datai Mata ya Bata Amma sai yai wata wata daya yake Fara aiki sannnan
ya Bata Wanda zata kashe yayan Amma da sharadin indai aka kuskure wani ya ganta sanda
take aikin ita zata haukace Kuma a haukan zata mutu ba magani ta yarda da hakan gears yaran
su mutu nata su tsira ai ko tana tafiya Bata zame ko Ina ba sai gidansu ita da haleema ta Gama
shirya duk wani plan ita da kwayenta ta ajiye su a hanya ta danna horn megadi ya bude Mata
direct part din haleema tayi




Tana shiga ta tayi nocking aka bude Mata sannan ta zauna haleema ta hade fuska tan jiran Taji
taima ta wani haukan na daban ko zancen banza Amma sai taga ta durkusa kasa tana hawaye
kiyi hkr Yar uwata da duk abunda nai Miki ki ya femun nazo neman gafararki dama bikina za ai
na kawo Miki iv nazo na Gaya Miki na nemi gafararki gaban haleema yai wani irin faduwa ta
ringa addu'oi a ranta tana rokon Allah ya kareta daga sharrin Jeddah idan da wani mugun abun
tazo Allah ya maida Mata da kayanta kanta ba komai na yafe Miki jeddah cike da farin ciki sai
washe Baki take nagode sosai Yar uwata Nan suka dinga kwasar Hira Amma Jeddah Anya ko

Baki garajan daura aure ba baku da tabbacin mutuwar suhail fa dariya tayi haba sadiya inbanda
abinki suhail ai ya Dade da mutuwa shekara kusan daya ba amo ba labari ai Dole mu fidda Rai
Kuma anga takalmansa a wajen da hularsa to shi Yana Ina har zaman makoki anyi Masa fa
Kuma ai nayi takaba ko haleema dai kallonta take cike da mamaki ai kema kawai ki auranki Dan
Kinga gaskiya da kyanki gwara ki Mori lokacin ki ki auren ki kema




Shiru kawai Tai Mata tana ta nazari chan Jeddah tace haleema Baki da abinci ne Tai murmushi
Yana cooler a flask naci nawa saura na Yara debo kici to tace ta nufi kitchen din maryama ta
koma bangaren haleema dama tunda Jeddah tabar gidan Al ameen yai Mata korar Kare tunda
ta shigo tana jinta tana bayan kitchen tana wanke wanke ta Gama Kuma Tai zamanta bataso su
hadu Sam Dan tanajin tsanarta fiye da yadda haleema ke tsanarta ta shiga kitchen din harda
cire mayafi haleema Bata kawo komai ba ta debo hadaddiyar jelop din shinkafa taji kayan
lambu da nusashshen kifi ta zuba a plate maryama na hangota tana ta mamaki kodai da gaske
ta sauta




Ta bude freezer ta dakko drinks me sanyi ta duba ba kowa dake hangota ta warware zaninta ta
kwanto maganin yaran ta barbada musu a ciki tana karkade hannunta maryama ta Kara lekowa
Bata ga komai ba Amma jikinta ya Bata wani abun ta zuba ta dakko abincin ta dawo parlour
tanata zurawa sunata hirarsu kamar gaske sai da taci Tai Kat Tai Mata sallama ta fito zata
rakota ta hanata itako Maryama Sam hankalinta be kwanta da zuwan Jeddah gidan ba bataga
dai me ta zuba ba Amma tabbas tayi wani abun tana Nan tana jiran ta tafi bacci me nauyi ya
dauketa a wajen dama wajene me kyau




Tana fita ta fito da maganin da akace idan dai halima ta shaki kamshin sa zata haukace ta fef
fesa shi yadda ze shiga wajenta abun tsautsayi me wanki yazo kawo kayan wanki ya ganta tuni
ya kunshe bakinsa ya juya Dan shi tsoronta yake ba ruwansa Haka ta ja motar ta Tai gaba cike
da murna tana fita direba na sako hancin motar yaran suka fito ansar ya taho da gudu ya fada
kan haleema momy abinci to Dan gidan momy autan momy bara na zubo ma ta mike taje ta
zubo masa Nan ya Fara cin abincin magriba tayi Jin Ana kwalla Kiran sallah firgigit maryama ta
tashi ta shigo gidan da gudu taga yaran duk suna parlour ansar na cin abinci da sauri ta karbe
ya saka ihu Yana Kiran momy

Lafiya waya taban autana cewar haleema ranki ya Dade nice banyarda da abincin bane Allah
yasa ba Wanda yaci no ba Wanda yaci menene wato hajiya Ina taga Naga kamar maman asra
tasa wani Abu a abincin to Kuma bacci ya daukeni kafin nazo na dauke na zubar ikon Allah
wallahi dama sam banyar da da itaba maza jeki zubar shi Kuma insha Allah ba abunda ze same
shi nasan dama Dan Ni da yayana tayi ba yayanta ba Dan ba yarda za ai taima yayanta Haka
ko akai ta zubar ta Dora musu indomie suna ta Kiran abinci cikin 10 minutes ta kawo musu suka
ci hankali kwance sunata hirarsu hankali kwance suna Al ajabin Hali irin na jeddah tunda duk
cikinsu ba Wanda take bakon sa




Jeddah ta cika da farinciki aikin ta yayi batasan yayanta suna hannun haleema batasan Dana
nata yayan ba ta dauka suna gurin hajiya shiyasa idan zaka Gina Ramin mugunta Gina shi
gajere Dan karya fada dakai Haka ta koma gidan hajiya hafsa tayi yadda boka yace Mata na
zubawa a abinci duk ta ajiye na cushe cushe duk ta tusa tayi kyau kyan Dan miciji idan Kika ga
Jeddah tamkar fure angama komai an na biki anfara biki anyi shagali iya shagli anyi lunch anyi
party ya ake dinner a Bristol palace guri yayi guri Mata masu ji da kansu sun hadu maza sugar
Daddy masu ji da kudi sun hallara matane manyan Mata matan aure wayanda suka gagari
mazajensu da zawarawa wayanda suka gagari gidansu da yammata wayanda suka gagari
iyayensu matan bariki manyan alhazawa ne ke ta faka manyan motocinsu Nan aka Fara dinner
anci an Sha




Anyi wadaka da nera amarya ta samu kyaututtuka daga hannun abokan ango ta samu kyautar
gidaje da motoci da makudan kudade ita kanta abun ya daga Mata hankali soboda Bata taba
ganin amaryar da akaiwa kyauta ranar bikinta ba kamar ta mahassada hassada ta cika musu
ciki masu kaunarta kodan su rabe ta su dangwali arziki sunyi murna ance arziki kashi tofa
Jeddah ta tako shi me shegen wari inji wasu kenan ba wani Abu daya daga hankalin jeddah
ganin yadda taga maza na hugging din juna manya masu ji da kudi masu mataye da yayaye a
gida amma sai Ta basar ba abunda yafi Bata mamaki irin yadda Taji Ana ambatar mijinta da
malamalai na duwai kowa Haka yake cewa chan sai ga alhaji duwai ya bayyana hankalin ta be
idda tashi ba sai da taga alhaji malamalai Yama manta da ita ya rungume duwai har dasu kiss
Nan aka Fara sabuwar chashewa aka Fara budiri Nan taga Ana kawo kwalabe ta tabbatar
giyace su kuma matan aka dinga hadasu da shamfen anci ansha anyi shagali




Ba a tashina sai karfe daya anan aka Kama dakuna Mata ganin yadda akaiwa jeddah Nan suka

Fara sake salon iskancin Taku ko wacce da kalar nata upwayanda ke neman Mata suka Fara
kamu masu neman junansu ko suka shige daki Dan wasu sun maku a cikinsu Haka ko akai
alhaji labaran ya lallabata suka shiga daki da sauran kawayen su da basi kasuwa wasu da
dama sun gane Dan homo zata aura Amma ba halin fada Haka suka shiga dakin sunata Hira
suna Tai Mata famfo Akan karta yarda ta zauna da kishiyoyi Dan ta Zama hamshakiyar hajiya
yanzu shiko alhaji malamalai nachan da alhaji duwai sunata buga Masha'arsu Dan an Dade
ba'a haduba tun kafin ya tafi Dubai Basu bar Juna ba sai gab da asuba ragowar ma Haka suka
dinga barzar junansu Jeddah tana complain din yadda suke rungume rungume sai kawayenta
suka nuna Mata tsabar wayewace da zaman turai suma ba Haka sukewa junansu ba ta yarda a
Haka hankalinta ya kwanta




Asubar fari Ta mike ta Fara shiri ko ta kansu Bata bi ba ta fice Dan Shirin daurin aure taje gidan
hajiya hafsa karfe takwas ta tafi kwalliya goma dot ta dawo tayi kyau kamar Yar tsana tamakar
fure an daura auren alhaji labaran da hajiya hafsa sadakinta dubu dari biyar lakadan Ba ajalan
ba andanyi chasu a green park sunci sun Sha karfe shida aka kawo motocin Kai amarya kowa
ya samu Yan gulma da Yan bani na iya Kai tsaye sashenta aka kainta Yan ganin gida sun
Gama gani dama ba dnginta ko guda hajiya hafsa ce ta tarasu tace Yar yarta ce wasuma sun
dauka budurwace Dan jikinta me kyaune bakace Tama taba haihuwa ba




Bayan kowa ya tafi ta mike ta zagaye sashen nata tsaf bala'i gida yayi gida Bata iya ganin
sashen nata ba ta koma ta rufe fuska koma zata rufe oho taci kwalliya tayi kyau chan Taji
hayaniya ta dauka abokan angone harda gyara Zama Nan aka Fara nocking Tai shiru tana jiran
ya shigo da karfi Taji an hankado kofar Ana zage zage ke Dan uwarki kinaji muna bugu Baki
bude ba dayar ce ta janye mayafin eh lallai wannan kyau haka ga kwalliya duk a gidan Nan to
daga yau Zaki dau darasi Dan uwarki matane manya su biyu da yammata uku ko wacce rike da
zabga zabgan bulalai keba kwadayi Yasa Kika aurar Mana Miji ba wallahi na lahira sai ya fiki Jin
Dadi zakisan kin shigo gonarmu suwaye ku cewar Jeddah Bata rufe Baki Taji an waska Mata
Mari tana dagowa aka Kara Mata ta saki wani ihu momy ta matso ta daki bakinta sai da ta cire
Mata hakori ihu ta saki na azaba




Ku daketa kuyi Mata dukan mutuwa tamu sannu da zuwar kenan tunda Baki da mutuncin daza
a kawoki ki gaishemu Nan suka zage balaga sukai Mata lilis Tana ihu tana komai Amma ba
Wanda ya daga Mata kafa sai da ta daku sukaga da kyar take motsi suka fice suka barta a
yashe face face cikin jini cikin kukan ma ta gagara yinsa Nan da Nan fuska Tai him ko Ina jikinta

ciwo yake jitai anturo kofar da karfi bakaramin firgita Tai ba




_To fans Bari mu kwana anan sai zuwa gobe insha Allah koya Labarin su ja'e sai gobe zamu
leka musulman daji muga halin dasuke ciki akara hakuri dani😂😂😂yanayin jikina ne sai a
slow nice taku har kullum a Koda yaushe_





*Feedyn bash*
[10/23, 2:33 PM] 👯🏻Ummu Subai'a🎭: *🎭ARNAN DAJI🎭*


*NA*


*FAREEDA ABDULLAHI*




*_🌈KAINUWA WRITERSâœí ¼í¿¼ ASSOCIATION_*í ¾í´í ¼í¿»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_~Assalamualaikum masoyana bazan gaji da godiya agareku ba fans musamman feedyn bash
real fans da kainuwa fans da komai mukaddarine fans da matan aljanna Ina Jin dadin yadda
kuke nuna min kauna bakina baze iya furta adadin kaunata agareku ba hannuna baze iya
rubuta sakon godiya a gareku ba Sai dai nace Allah ya biyaku da gidan aljanna nagode da
addu'oin ku agareni nagode nagode nice taku kullum a Koda yaushe maman yan.......kundai
gane beauty😂😂😂😂😂~_*





*Bismillahir rahmanir Raheem da sunan Allah me rahma me Jin Kai*

*Book 2*




100-105




Alhaji labaran ne ransa a mutukar bace ya bude kofar da karfi Yana zuwa ya dauke Jeddah da
mari Wanda sai da taga wuta Dan ubanki su hajiya sa anninkine daza a kawo ki baza a kaimusu
ke ki gaishesu ba suna gaba dake to wallahi idan kinasan kanki da arziki ki musu biyayya yi
nayi bari na Bari Dan dasu Zaki zauna a gidan Ni idan nasa kaima sai kin ganni ba'a wulakanta
mun iyalai na bazan dauka ba fada yake kamar xe Ari Baki Jeddah da take kuka kamar ranta ze
fita na shiga uku Ni Jeddah yau Kuma gidan danazo Kenan Ni za'a yiwa duka a Daren aurena
zancen da take Kenan a zuciyarta tana ta kuka mtsww dadine yai Miki yawa Ni Zaki tasa agaba
kinawa kuka ubanme akai Miki Dan wannan Marin danai Miki ai shafar Mai ne dago fuskarta Tai
jage jage da jini da majina ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login