Showing 42001 words to 43444 words out of 43444 words
bandage nonon ma Babu ya hango
gawar dansa da gudu ya dakko ta likitoci duk sunyi cirko cirko suna kallonsu harda masu vedio
a waya Suma ne kawa Jeddah batai ba suhail ta ambata sai yanzu ya ganeta a firgice ya kalleta
Jeddah kece haka lallai muguwa azzaluma dama karshen maha'inci kenan kin rabani da
iyayena da yayana da matata kinsa na aureki ta asiri karshe Kika nemi kasheni Allah ya Isa
tsakanina dake haleema ta toshe Masa Baki ka yafe Mata kaddarar ka Kenan karka manta da
Bata nemi Kashe ka ba bazaka hadu da ahalinka ba nan ta Fara bashi hakuri sai haleema ta
tafi da sauri ta Kira alhaji da hajiya danya kekashe kasa akan baze yafe Mata ba Nan sukazo
suka ga ikon Allah Nan ta Fara basu labarin auren datai sun girgiza da wahalar data Sha matan
sai kuka suke hardasu ramatu dama gata gwanar kuka Kowa ya tausaya Mata
Nan daddy yasa Kowa ya yafe mata Kuma sunyi alkawarin neman alhaji malamalai da kungiya
su insha Allah za'a bi Mata hakkin ta Nan tabawa suhail number din account number dinta da
komai Tai Masa kwatancen gidan hajiya hafsa Dan komai nata Yana chan da takardun gidajen
ta yai Mata alkawarin karbowa Ana haka likitoci sukace abasu gawar ansar zasu kaita dakin
daza'a ajiye shi kafin ai cike cike Nan ta rukunkume Dan Wallahi karya ne Yana da Rai dakyar
aka kawace shi tana gunjin kuka Kowa kuka yake Dan tausaya Mata asra ce tazo ta rungumeta
momy Kara rungume ta kiyafemun yata na mallaka Miki duk abunda na mallaka Amma na halal
Banda na Haram kuka take sosai chan Kuma sai ta Fara dariya a'a sai suhail ya kwace asra
tuni ta diro daga gadon kamar ba Mara lafiya ba
Ta Fara yage kayanta tana tonawa kanta asiri asibiti yazam gidan biki Kowa sai kallonta ake
Ana Allah wadarai Dame Hali irin nata Nan ta Fara tsigar gashin gabanta tanaci hauka tuburan
Nan da Nan ma"aikatan asibitin suka kamata a ka Sanja Mata daki aka kulleta tamau Nan da
Nan akai refer dinta zuwa dawanau kome akasa Mata sai ta yage shi Allah yasa mi
kyakykyawan karshe ba irin nasu Jeddah ba kuka Kowa yake a wajen harda yarta data Fara
wayo kunya kawai takeji idan akace ga yarta Datai saura sai ta fashe da kuka tace haleema ce
mamanta ganin haka mazan sukace duk akai matan gida shikansa suhail dauriya kawai yake
kodan darajar yayansa data Haifa Masa karshen Jeddah haka yazo chab dijan Allah yasa
mudace suna tsaitsaye aka fito da Indo Aisha Amma Anja zani anrufe Mata fuska daddy na
ganin haka ya fara kwalla yasan Babu
Aka ajiyeta gabansu likitan ya girgiza musu Kai sumewa suhail yai a wajen nan Kai maza aka
Fara bashi temakon gaggawa uncle da daddy ne suka yi duk wani cike cike aka Basu gawar
Aisha data Ansar Nan sai ga suhail da kafarsa ya fito be warware ba Amma haka ya fito suka
taho gida akai musu sallah aka kaisu gidan su na gaskiya Ramatu fadeela subai'a kuka kamar
ransu ze fita har ririkesu ake to yaza'ai kullu nafsin za'ikatul maut haka suka hakura suka
dangana Basu da kowa yanzu sai suhail da ja'e da iyar ja'e to gasu daddy haka aka share
makoki bayan arba'in daddy ya Kira malamalai aka Raba dukiyarsa kamar yadda Allah yace shi
kaso biyu ita uku aka rabawa ramatu da suhail Suma sukaiwa Yan uwansu alheri dan ba
karamar dukiya suka samuba bayan wata uku aka shirya gagarumin biki
Dangin hajiya sunzo sunga Yar uwarsu da danta sunyi murna sun tafi da ita da Ja'e Ja'e taga
dangi ta Ja'e farinciki kamar me yaga danginsa Dan duk sunfito daga kauyen fata sun koma
garin Jos a chan tasamu wani Dan uwanta suka daidaita aka daura musu aure Yan uwanta
sunyi murna haka Ja'e suka dawo Kano saboda baze iya zama ba ga bikin su dayake gaba
towa iya tasamu miji me Santa me jiyar da ita Dadi sai yanzu tasan tayi aure tasan itama mutum
ce haka su Ja'e suka dawo Kano saboda shirye shiryen bikin su daya gabato
Suhail da subai'a ja'e da fadeela Al ameen da Ramatu anyi biki lafiya kowacce ta tare a gidanta
su subai'a na zaune lafiya bazaka taba cewa kishiyoyin junane ita da subai'a ba komai tare suke
itama haleema ta cire kishi tana koya Mata abubuwan duk da tasan bazata dauka lokaci daya
ba sai a hankali danma tanada kokari shiko suhail komai zam zam ya samu subai'a yadda
yakeso tana bashi hadin Kai ga gardi duk da anty saudat tayi kokari wajen hada yayayenta
gidan ja'e ko ya dibi gara besan Mata suna suka taraba sai a kan fadeela ihu yake Yana Kiran
bani ba mace me kyau kyan ashe yana Nan wajen suhail harda suman Dadi kullum sai yai kuka
idan yazo saduwa da matarsa ranar da fadeela Tasha gabansa Suma yai warwas sai da ta zuba
masa ruwa betaba sanin wannan abun ba yo ina zaka sani ja'e kana daji harka sai birni ai duk
ansasu makarantar yaki da jahilci suhail ya budewa ja'e katon shago a Kano kantin kwari Yana
zuwa Koda yaushe alhamdulillah yana sabawa da kasuwanci a hankali dake akwai yaran dake
nuna Masa
Suhail ya cika alkawari inda sukabi kwatancen da Tai musu cikin ikon Allah sun samu alhaji
malamalai a gida inda aka iza keyarsa anyi anyi ya fada yaki aka kaishi sas suka ragargaje shi
dakansa ya kaisu gidan dan yaga abun ba sauki suna zaune suna meeting akai musu raf aka
kame su aka Nike gidan tsafin nasu harda dodon tsafin aka Kone shi aka gufanar dasu gaban
alkali ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya dukansu karshen su malamai yazi Allah
yasa mi kyakykyawan karshe yaje ya karbo duk wasu kadarorinta da ATM dinta da komai
Amma be barwa yarsa komai nata ba gidan marayu aka Kai da gajiyayyu gidajen Kuma yabawa
marasa karfi kyautarsu bayan wata uku suka samu labarin rasuwar jeddah duk ta kwakuke
gabanta ta cinye Haka take jiwa jikinta ciwo ga wani ruwa me wari dake zuba daga jikinta
saboda rubewar da kirjinta yai mutuwa tafi Mata sauki yai Mata addu'oi ya tausayawa yarta
Allah yasa mudace Yasa miyi kyakykyawan karshe ba irin nasu Jeddah da malamalai
Al ameen kodauke Ramatu yai gaba daya suka koma Istanbul Nan yanema Mata makaranta
tayaki da jahilci ta fara soyayya suke me tsafta ramatu akwai kwai akwai kyan hq ma sai dai
matsalar kauyanci Wanda dukansu suke fama dashi haryau idan Ja'e ya manna wani haukan a
kasuwa sai ansha dariya haka akadinga bashi magunguna da rubutu saboda yana Sha'awar
naman mutane dan Yana ganin mutum zece wannan ze Mai ko Kai wannan baze Mai ba
wannan baze nama ba ganin haka yasa ake Masa rubutu Dan Kar adauka mayene
alhamdulillah Kuma ya Dena dukansu ciki ne dasu inda subai'a ta Riga haihuwa ta haifi mace
suhail yayi farinciki ya maida sunan babarsa Aisha yaso yasa sunan hajiya alhaji ya hana sai
fadeela matar Ja'e tagwaye ta Haifa akasa musu hassan da usaini sai ramatu mutanen turkey
achan ta haihu ta haifi da namiji akasa sunan Alhaji
Alhamdulillah garin kuguru ya gyaru fiye da tunanin me tunani yayi kyau anyi musu gyara da
makarantar Boko data islamiyya domin gwamnati ta shiga maganar garin Yana karkashin Kano
Dan haka ansoke sarki a garin sai dagaci da aka nemi wani babban mutum akai Masa
gwamnati da kanta ta jinjina wa suhail ya samu lambobin yabo masu yawa daga wajen manyan
gwamnati da manyan masu kudi su fadeela sun samu kyaututtuka alhamdulillah malamai suna
kokari a garin Dan suna fahimtar addinin su sosai arnan daji sun Zama musulman daji hasken
musulunci ya shiga garin ya mamaye harda gefen garin wato beguwa mado ya dawo wajen
matarsa akoda yaushe idan mutanen garin suka tuna da suhail sai sun Masa addu'a
*Alhamdulillah tammat bi hamdillah Allah nagodema daka bani ikon sauke wannan littafi nawa
alhamdulillah darasin dake ciki Allah yasa mu amfana dashi kuskuren dake ciki Allah ya yafe
Mana masoyana Ina godiya da yadda kukai jumurin Bina harma kammala wannan book nawa
insha Allah zaku dinga samun Dan iskan namiji akan Kari yanzu da sabon novel Dina me suna
FACCALATA nice Tak a kullum a Koda yaushe*
*FEEDYN BASH*