Showing 3001 words to 6000 words out of 19635 words
da tausayi.amma fa idan ka shiga gonar shi to fa ba mutunci
sai da ya idar sallah sannan yayi cikin gidah umma ce hakimce a falo tana kallon tv tana jefa
fruit a bakinta,,wucewa yazo yi ta gabanta ko kallon inda take bai yiba,,babanka na hanya
gobe,, juyowa kawai yayi ya kalleta kafin ya wuce..da harara ta bishi kafin tayi kwata ka kusa
kama gabanka ai,,shidai baima samd tanayi ba..kicin ya shiga ya dakko abincin sa ya fice daga
sashen gaba daya,,,yana gama cin abinci ya shiga wanka be dade ba ya fito shiryawa yayi cikin
wasu riga da wando rigar me dogon hannu ce wandon kuwa jeans ne amma duk amma sa
crazy,wata sarka ya jawo me uban nauyi ya dora ta a wuyanshi..sannan yasa pcap a kanshi,,ya
fito a dan dabanshi sak amma hakan bai hanashi yin kyau ba..ficewa yayi a gidan a 360,,,
kiran sallah magribtne yasa ta mikewa dakyar ta rarrafa ta dauki buta alwala tayh kafin ta kara
komawa cikin dakin dakyar ta samu tayi sallan ta kara komawa ta kwanta dan har yanzu
zazzabin bai sake ta,,tana jiyo hayaniyar inna asabe da yayanta dan dama su sallah ba damun
su tayi ba ,,kwala mata kira taji anayi kuma muryar inna asabe ce..cire lullubin tayi ta maida tasa
a jikinta sannan ta nufi kofar dakin,,sallama tayi ba wanda ya amsa a cikinsu.sai wurgo mata
kudi indo tayi tana fadin wuce ki siyomin pad a shagon sile bana son na shagon rabe,toh kawai
tace tare da amsar kudin tayi hanyar waje,tafiya take kamar zata fadi amma haka ta cigaba,,
fitowar shi kenae daga masallacin su uku ne ammar auwal da kuma nura,tafiya suke da sauri
domin time din wasansu ya fara,,tun daga nesa yake hangota tana tahowa a yanayin daya
ganta yasa fuskar shi sauyawa,ina zuwa yace ma su auwal kafin ya isa inda take kallonta yake
tun daga sama har kasa,dagowa tayi tana murmushin dole wanda yafi kuka ciwo,,waya miki
haka kawai ya ce dan sai data dago kanta sannan yaga bakin ta a fashe ga kuma idonta daya
kumbura,,kan uban can yace da karfi tare da zaro mata idanu,, tambayarki fa nakeyi yace a
hasale,,a hankali ta fara fada mai abinda ya faru tare da fashewa da kuka,,,,,kutumar uba yau
sai naci uban uban asabe sai na karya wa haladu kafa,,kai yau duk wani daya shafh asabe sai
mun mai operation huci kawai yakeyi a lokacin da zai ga su haladu ba abinda zai hana bai cire
ma tsohuwar nan da yayanta kafafuwa ba,,,maganar dayake da karfi ne ya janyo hankalinsu su
auwal dama sun tsaya saboda karsu damesu,,, auwal yace yadai my man dogon tsaki yaja
kafin ya basu lbrn abinda ya fara,,,,yeeeehuuuu,,cewar auwal kace yau anta bomu tunda aka
taba jidda kai nura jeka tattaro su duna da bahago dukakasu da sauri nura yayi hanyar barin
wajen domin cika aiki,,kara kallonta ammar kafin jeki gidan maman sahala zanzo in sameki,,,,
Toooh yaufa su inna asabe an taro pillars
yawan comment yawan typing
Ur's princess deejerhí ½í²
[16/01, 18:47] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON
SHIBA✨✨
By Princess Deejerh
New Writer
wannan shafin sadaukarwa ne gareku daukacin members na zahra surbajo novel facebuk
commen dinku namin dadi I HEART U ALLí ½í¸˜í ½í¸˜
Page 2⃣1⃣
to 2⃣5⃣
Sai daya ga ta shige gidan maman salaha sannan ya juyo ya fara tafiya yana saka irin rashin
mutuncin da zaiwa haladu da uwarsa,,a bakin layin ya hadu dasu auwal ni kaina sai dana
tsorataí ½í¸³ganin irin mutanen dake tare dashi,gaba dayansu ba alamun murmushi a fuskar su
jira kawai suke ace kule suce cass...duna ne ya fara magana yana ciccezewa..yadai baba wai
aina za ayi operation din ne kasanfa kwana2 ban fede ba,,murmushin mugunta ammar yayi
kafin yace ku biyoni muje..duuu kuwa suka bi bayanshi kusan su 15 ne amma duk shine a gaba
kowane da makami kuma a hannun sa tun daga nesa da an hango su zaa fara gudu..dan
mutane sunsan ba alheri bane ke tafe dasu ba,,wasu daga cikin mutanen kuwa har sun
tausayama wanda zasu je gurin shi..domin kuwa ba yau aka saba ganin haka ba sai dai kowa
yayi gumm ba bakin magana,,
jidda zaune a acikin dakin maman salaha amma hankalinta gaba daya baya jikinta tana tsoron
abinda ammar zaije yayi...da karfi maman salaha ta kira sunanta sannan ta dago a firgece,,ke
kuwa jiddah me yayi zafi haka,,cikin kuka ta labarta mata halin da ake ciki,,allah na gode maka
maman salaha ta fada tare da kwashewa da dariya..tabbas ammar ya cika dan halak kuma
yamin daidai,,da sauri jidda tace amma fa kada su mai wani abu daga baya,,hmm tace kafin ta
fara magana jiddah kenan kinsan uban ammar nada kudi ba abinda zasu iya yimai,,sai da ta
kwantar mata da hankali kafin taje taci gaba da aykinta
zirga zirga kawai suke a cikin gidan daga ita sai haladu domin su rabi tuni suka fice yawon su
amma fa indo ta kullaci jiddah a ranta tun dazu ta aiketa amma bata dawo ba..da tunanin rashin
mutuncin da zata mata inta dawo ta fita aranta,,,,,kofar gidan sukaji ana bugawa..da karfi kamar
zaa cire inna dake tace kamu ta duro ashar kafin tace wani matsiyacin ne zai ballamin kofa
shegu yan bakin cikin unguwa zasuja min asara,,shiko haladu da fitowar sa kenan daga
bandakin ya fara zubo nashi ruwan ashariyar dan kuwa karan buga kofar ne yasa shi fitowa ba
shiri,,,daga can waje kuwa ammar ne da gang dinsa tsaye mamakin zagin da tsohuwar da
danta ne sukeyi ya kamasu duk da shi ammar yasan zasu iya fiye da haka,,,cikin fushi yama
kofar zuwa daya sai gata a gefe.shiyya fara shiga cikin gidan sannan sauran suka biyo
bayanshi..mute bakin inna asabe yayi ganin ammar da yan jagaliyanshi sai da kirjinta ya buga
domin kuwa bata manta warning din daya mata kwanaki ba...shiko haladu me danyen kai
zaburowa yayi wai zai naushi ammar zuwa daya ya kamashi hannun ya murda.ihun azaba
haladu yasa naushin bakinsa yayi tare da jefar dashi a kasa gwajab kamar kayan wanki,,cikin
daga murya ammar yace dasu operation start...aiko basu yi wata wata ba suka fara fasa duk
wata roba ko bokiti dake tsakar gidan wasu kuma dakuna suka shiga suka fara tarwatsa kayan
tsummokaran data tara kai hatta igiyar shanya basu barta ba,,,tukwanen kuwa sai da duk suka
taka su duk suka lauye,,nuna musu haladu yayi dake kwance har yanzu yana jinyar hannun
sa,,ku kawo min shi nan dakko shi suka yi suka ajeyi a gabanshi baiyi wata wata ba ya kai mai
naushi a fuska sai ga jini nabin gefen fuskarsa,,inna asabe na ganin haka tasa ihu tana neman
agajin makota,,,jama'a ku kawo mana dauki ku taimako ga jujal nan da mukarraban sa...naushin
da duna ya kai matane ya sata rufe baki bata shirya ba ai ko jini ya fara malala mangareta
duna yayi ta fadi kafin su rufe su da dukansu bame ceton wani
Ur's princes deejerhí ½í²
[16/01, 18:47] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON
SHIBA✨✨
By Princess Deejerh
New Writer
Page 2⃣6⃣ to 3⃣0⃣
Sai da ammar da yaransa suka musu wulakanci na bugawa a jarida shafin farko,,,sannan yasa
suka kara buge haladu.,inna asabe kuwa tunda aka mata zuwa daya har yau tana kwance
shame shame rike da kafarta da wani ya taka mata a cikinsu,,,sai da suka gama duk
wulakancin da zasu musu sannan suka fice suka barsu kwance anan bamai taimakon wani a
cikinsu,,
fitowar su yayi daidai da komawar kowa cikin gidanshi...dan dama duk mutane najin abinda ke
faruwa
sai da jidda taci abinci tayi sallai ishai sannan taiwa maman salaha sai da safe ta tawo
gida,,,tana zuwa kofar gidansu gabanta ya fadi ganin kofar a yashe a kasa tasan wannan aykin
ammarne..da sallama ta shiga gidan,,su rabi ta samu zaune kusa da inna asabe tana gasa
mata kafa da ruwan zafi ita kuma asiya da indo suna kan haladu suna goge mai jinin da ya bata
mai fuska duk fuskar nan ta kumbura sai ya kara muni kamar irin horror dinnan....kowa ido ya
bita dashi ba halin magana domin su rabi sunji labarin abinda ya faru shiyyasa ba wanda ya
tanka mata..daki ta shige kawai tayi kwaanciyar ta..
Tofa tun daga wannan ranar baima dukan jiddah a cikinsu sai dai abita da harara da kuma
tsaki..aikin gida ne dai haryau ba fashi,,
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya duk da gidan ba dadi amma yafi da tunda yanzu har abinci ana
bata kuma bata musu wanki saidai girki da gyaran gida,,a bangaren ammar kuwa har yanzu
umma tana nan tana hada mai tarko duk da abbansa baya yadda,,amma dai bata karaya ba
tayi alkawarin sai ya bar gidan duk daren dadewa,
A yanzu jiddah tayi jss c.e kuma ammar ne ya mata komai duk shima wannan shekarar
zaigama scondry skul,,da kansa ya mata registration anan makaran tarsu aka bata ss1 science
class,,tana makaranta cikin kwanciyar hankali da wuri take tashi ta gama duk ayyukanta na gida
sannan ta shirya ta tafi,,tana fitowa zata samu ammar a bakin layi shi zai rakata har bakin
makaranta sannan ya bata kudin break,tunda yabar makarantar haka yake mata duk da shima
abbansa na neman masa makaranta,,,
inna asabe ce zaune ita da lami,,lami kawar inna asabe ce tun yarinta dan wasu halayen duk ita
ta koya mata dan lami bata zaman aure ga bin bokaye,,inna asabe ce ke bata labarin abinda
ammar ya musu har gida,,,mtsww lami taja tsaki kina aikin me har haka ta faru idan hagu takiya
ai sai a koma dama,,tun farko sai da nace miki mukai sunanta gurin na bakin rafi amma kika ki
to yanzu wa gari ya waya ke mana,,duk layi anata yi dake yayanki sun lalace ita kuma sai
yabonta ake,,wannan yabon shi zamusa ya koma aibatawa,,yanda shikansa ammar din sai ya
kyamace ta,,tabbas kawata kin kawo shawara me kyau gobe da sassafe zan shirya in biyo ta
gidanki sai muje gurinshi,,yauwa ko kefa ki maidata abin kwatance,,ki dauki fansar abinda
ammar ya miki dan na tabbatar sai yafi kowa shiga kunci idan ya ganta ,,,ai fa nagode lami nida
duk banyi wannan tunananin ba,,,har kofar gida ta rakota suna kara tattaunawa akan muguntar
da zasu ma baiwar allah da bata rikesu a zuciya ba...
Da daddare jiddah na zaune kofar daki itama inna asabe suna zaune ita da yayanta firar su
suke cikin kwanciyar hankali,,sai dai kawai taji suna shewa,,kadaici ne duk ya isheta ina ma
tana da iyaye da rayuwar ta bazata zama haka,,wani yaro karami ne ya shigo gidan,yace ana
kiran jiddah a waje,,ba wanda ya tanka a cikinsu itace tace kace gani nan zuwa dan tasan
ammar ne,,hijab kawai tasa tafita a tsaye ta same shi a kofar gidan,,gaeshe shi tayi ya amsa
cike da kulawa,,shiru ne ya biyo baya kafin ya fara magana cikin sanyin murya kamar ba ammar
ba,,,jiddah ya kira sunanta da sauri ta dago ta kalleshi domin kuwa yanda ya kira sunan nata ne
ya sanyaya mata jiki,,ce mata yayi ga wannan amsa kawai tayi ba tareda ta duba ko meye
ba,,shine yace atm carda dina ne sannan ga waya nan itama ya miko mata..amsa kawai tayi
tana jiran karin bayani,,,jiddah zanyi tafiya mai tsawo abbana ya sama min makaranta a noida
university india,,da sauri ta dago ta kalleshi domin kuwa maganar ta bugeta tuni har ta fara
hawaye,,shima dakewa kawai yakeyi amma da ba abinda zai hana shi yin kuka amma bayaso
ya karya mata zuciya,,,kuka ta fashe dashi da karfi domin ji take in ammar ya tafi kamar wani
abu zai faru,kiyi hakuri jiddah ai zan rinka zuwa hutu akai akai,,,ita dai bata saurare shi ba
kukanta kawai takey..jin kukan yake har cikin ransa,,,shima dan dai ba yadda zeyi ne abbansa
ya matsa masa amma da ba wanda ya isa yasa shi zuwa wata kasa karatu,,dakyar ya samu ya
lallabata har tayi shiru amma fa a zuciyarta ji take kamar ta mutu saboda bakin cikin tafiyar
ammar,,,da kyar ya lallaba ta har ta shige gida,,shima ya tafi
a wannan daren ba wanda ya runtsa a cikinsu ,,,dan jiddah kwana tayi tana kuka...shi kuwa
tinana shi wani hali zata shiga bayan tafiyar shi...
Ur's Princess Deejerhí ½í²
[16/01, 18:47] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON
SHIBA✨✨
By Princess Deejerh
New Writer
Page 3⃣1⃣ to 3⃣5⃣
Haka jiddah ta raya wannan dare tana kuka..da ta tashi da safe kuwa fuskar nan tayi jajirr
abinka ga farar mace,,idanuwan nan sunyi luhu luhu..a sanyaye take komai dan har yanzu
zuciyarta bata dena mata zafi na tafiyar ammar ba...
Zaune yake a gaban abban shi fuskar nan a daure..sai ya dawo sak ammar din dana sani mara
son wasa,,domin kuwa yayi tinanin abban shi zai goya mishi baya daya ce baya son
tafiyar,,,abban ne ya fara magana cike da fushi...ammar kenan kai bakaji kunyar tunkara ta da
wannan maganar ba kalleka fa shekara 22 sai yanzu ka gama scondry skul sa'annin ka duk tun
yaushe suka gama saboda kai bakason cigaba kome?to wannan karon babu fashi gobe jirgin
ku zai tashi da yamma ka gama duk wani shirinka dole ka tafi,,kai kafi so ka zaunj a gari kana
yawo da abokan banza ana maka gata amma kai baka gani baza ka gane gata ake maka ba
tukun sai nan gaba idan kayi hankali,,,tafiya kam ba gudu ba ja da baya na gama maka
komai...ka tashi kaje ka cigaba da shiri,,,tun da ya fara fadan kanshi na sunkuye amma fa ji
yake kamar zuciyar shi zata fashe saboda takaicin tafiyar shi,,,tashi suka yi duka kowa yayi
dakin shi,,,da sauri umma dake labe tana jin duk yanda suka yi itama ta shige dakinta,,,waya ta
dauka ta kira laraba ringing biyu ta dauka cikin farin ciki umma ta fara fesa mata duk halin da
ake ciki,,dariya itama kwashe dashi sannan tace,ai na fada miki idan har kika yi haka dole
yabar gidan tunda abbansa yana son yaga yayi karatu kafin nan da 5yrs din ai mun gama
abinda zamuyi mun kara gaba,,,aikuwa dai laraba akwai ki da basira,,,kin mantani kenan umma
wai dan ma nayi sanyi kenan,,,,to shknn jibi kizo da sassafe akwai magana tunda shi abban
nasa ba zama zaiyiba,,,to shikenan...
Inna asabe da lami zaune a gaban na bakin rafi..lami ce zata fara fada mashi abinda ke tafe
dasu,,,da sauri bokan yace mun riga mun sani tun shigowar ku dajin nan,,,yar mijinki ke baki
matsala me kike so a mata a haukata ta ko a kashe ta,,,da sauri lami tace aa boka so mike a
lalata rayuwarta ta koma kaman karya yanda al'umma zasu kyamace ta ta koma abin
kyama,,,,katseta bokan yayi tare fadin ba yanzu ba,,,domin kuwa yanzu ba aljanin da zai iya
zuwa ya rabeta dan tana ibada kuma ko yaushe cikin karatun qur'ani take duk aljanin da yaje
kusa da ita kuwa yanzu to lalle sai ya kone,,,,inna asabe ji tayi kamar ta kurma ihu dan takaici
taga samu taga rashi,,da sauri tace to yanzu boka ya zamu yi,,,,,cikin daga murya yace zan baki
wani magani kullum ki zuba mata a cikin abinci indai tana ci to a hankali zata fara daina ibada
zai saka mata kasala to a wannan lokacin ne zamu aiwatar da shirin mu a kanta,,,,amsa lami
tayi tare da fadin mun gode boka,,kudi inna asabe ta ciro ta ajiyemai a gabanshi,,sannan suka
fita....tafiya ce me nisa sosai tsakanin gurin da bakin titi,,inna asabe ke cewa lami,,to yaya zan
bata maganin tunda kullum ne,,,mtsw lami taja tsaki kafin tace ta inda aka hau ai tanan ake
sauka...nuna mata zakiyi komai ya wuce ta yafe miki ke inta kama har kuka kiyi ta yanda zata
yarda kinyi nadama to ke kuma kinga kin samu hanyar yi mata komai tunda zata yarda
dake,,,,tabbas shawarar ki tayi lami muje gidan dae....
atm card din daya bata ne a hannun ta ga kuma wayar a gefe..duk wannan basu take bukata ba
tafi bukatar shi a kansu lokaci daya haka kwatsam...kuka ta kara fashewa da shi tana mai fadin
allah ka kawomin dauki a rayuwata,,sallamar inna asabe ce ta katse mata kukan da
takeyi...abin ya bata mamaki inna asabe da sallama bata kara jin mamaki ba sai da taga inna
asabe ta leko tana fadin sannu jiddah ya gida,,da sauri ta mike ta fito waje dan kuwa har yanzu
bata gama gyara gidan ba,,,kuma tana kara mamakin inna asabe,,zo nan jiddah taji ance daga
bayanta cikin tattausan lafazi,,juyawa tayi ta nufi kofar dakin indainna take a tsaye,,,jiddah''da
sauri ta dago kanta ido ta zare ganin inna asabe ido jajirr da alamu tasha kuka,,cikin muryar
kuka ta fara magana jiddah ki yafemin na zalunce ki na cuceki tun kina karamar ki,zubewa tayi
bisa gwiwarta tana mai kara fadin ki hakuri jiddah ki yafemin ko zanji salama a raina ina cikin
kunci kada in mutu da hakkin ki a kaina ki yafemin dan allah jiddah tare da fashewa da kuka mai
ban tausayi,,,,da sauri jiddah ta dago ta tana fadin inna kefah uwata ce bai kamata ki tsugunna
a gabana ba wallahi na yafe miki,,,ngd jiddah cewar inna asabe allah ya miki albarka yata ta
kaina,,bakomai inna komai ya wuce,,to jiddah jeki kwanta ki huta kema zatayi musu inna asabe
tace lallaifa saidai ta kwanta,,ba yanda zatayi ta juya ta shige dakinta tana mamakin abinda ya
faru ayau,,,inna asabe kuwa dariyar mugunta tayi kafinta tace yaro bai san wuta ba sai ya
taka.....
yanzu aka fara
masoya novel dina kuyi hakuri da jina shiri kwana2 hakan ya faru ne saboda wasu dalilai amma
yanzu