Showing 69001 words to 72000 words out of 98825 words

Chapter 24 - Budurwar Kauye Book Compelet Miss Dijerh

09 Aug 2026

1221

ko ina da qamshi

Breif case nasa ya dauka da woyoyinsa ya fito hannunsa riqe da car key nasa

Babu wadda zai kallesa bai sake ba koda kuwa tare suke kwana daki daya dan papa yayi no lie

Yana fitowa ya tarar anwanke masa mota sai sheqi take

Maaikatansa sukazo one by one suka gaidasa sannan ya bama Abdu kudin Abincinsu yace
idan yaqare yayi magana shi ya wuce office idan ya dawo zaije gida ya taho masa da motocinsa

Ya amsa cikin ladabi sannan ya masa adawo lfy

Motarsa ya shiga ya kunna Ac hadi da wani daddan music

Ahankali yake tafiya harya fice direct gidan daddy ya nufa cos he wanna see his darkan(heart
beat)

Lokacin daya shiga bakowa afalo sai talatu mai aiki

Bayan sun gaisa yace ina masu gidan

Tace yanzu hajiya ta koma amma bada jimawa ba zasu fito karyawa tunda 8 tawuce

Zama yayi abinsa ya danna wayarsa

Momcy ce ta fito daga side din daddy ganin papa zaune yasa tace papa lfy kuwa kaxo early
morning

Dago kansa yayi yana murmushi yace morning momcy

Morning dear baka ansamun tambayar danayi maka ba

Dan shagwabe fiska yayi yace haba momcy mutum da gidansu danyazo sai antambayesa
kawai nayimissing naku a lot that's why naxo early morning naganku kafin na tafi office

Dariyama abin ya bata cos ta fahimci abinda yake nufi

Tabe baki tayi tace good saikataso kayi break toh

Yana tashi daddy na fitowa shima cikin mamaki yace Alamin qalau kuwa naganka sassafe

Lfy lau daddy nazoyin breakfast ne fa

Yace yayi kyau to muje

Saida ya gaidashi kafin ya haura dinning ya zauna a permanent seat nasa

Fauziyyah ce ta fito cikin shirinta yau takusa makara dan jiya batasamu bacci da wuri ba

Ganin papa yasa tadan hade rai shikuma sai wani mayetaccen kallo yakebinta dashi

Saida ta gaida daddy da momcy tukun tadanyi kasa da murya kamar dole tace morning ya
Alamin hakanma dan su momcy na zaune ne yasa ta gaishesa

Da faraasa yace morning dear kesi ho tum(yaya kike)

Me tikke ta amsa masa(lfyna lau)

That's great ya fada sannan ya cigaba da cin abincinsa

Itama zama tayi tayi break nata kafin ta miqe ta masu daddy sallama wadda dama shi ya koma
falo ya zauna

Tsulum papa ya miqe yace shima ya tafi idan ya biyo to idan kuma bai biyoba sai gobe

Suna fita ya nufi motar fauziyyah tana budewa ya shige gefenta ya zauna abinsa

Juyowa tayi tana kallonsa akufule tace yeh he kya karehe tum(meye haka kake aikatawa)

Dubanta yayi yace kyah(kamar yaya)

Tace taya zaka shigomun mota haka baicin kanaga fita zanyi


Oh sorry dear nima ai fitan zanyi shine nakeso kuragemun hanya


Tace pls kafitamun amotana

Yace eyyerh pls kiragemun hanya mana tinda office zani

Tace no i cant pls kafita if not gashi ta miqo masa key namotar tace nisai infita

Qarema hannunta kallo yake wadda yasha lallen rani

Yace aakam keda motarki daman tawance tasami problem amma tinda kinqi shikena

Duban jerin motocin sa takeyi amma yace baya da motar da zaifita tabe baki tayi tace shikenan
kafin ta tada motar suka tafi

Ahanya ba yadda baiba kan tayi maganar amma sam taqi



Haka ya haqura ya kyaleta......


�🏻Faty Mmn Faty







Budurwar Qauye🤷🏼�♀🤷🏼�♀🤷🏼�♀

Written by Faty Mmn Faty

September, 2017

*I dedicated this page to Rahima Aminu Azare (Ummu Afreen), thanks 4 ur prayers, luv n
support, I really appreciate,Mmn Faty 😘�*

5⃣8⃣
Har suka iso hospital kallonta kawai yake yana murmushi cos ta matuqar birgesa

D way take driving anatse shiyasake birgesa gashi ta tsuke dan qaramun cute bakinta

Saida tayi parking tana daukan jakarta sannan ya bude ya fita

Zagayowa yayi ta side nata ya sunkuyo sosai lokacin itama ta bude zata fita

Wani killer smile ya mata cikin wani soft voice yace mata shukhriya(nagode)

Yana fadin hka ya wuce abinsa baijira amsarta ba dan yasan abune mai wahala ta kulasa

Kallo ta bisa dashi kafin ta dauke idanunta ahankali

Azuciyarta tace jibesa kamar mutumin kirki baicin dik wata kalar iskanci babu wadda bai iyaba

Tsaki tayi kafin ta fice itama dan kada ta makara

Shikuna yau hankali kwance ya shiga office nasa koba komai yau ya jima kusa da
pyarinsa(mosoyiyarsa)

Saida ya kusa tashi kafin ya kira Abdu yazo office ya samesa ya bashi key din motarsa akan
yaje ya kawo masa

******
Kwanci tashi babu wuya awajen Allah kwanaki sun shude hakama satittika tareda watanni

Yanzu biki saura sati uku kacal duk wasu shirye shirye babu wadda baa gamaba

Kama daga kan gidan da zasu zauna su lefe komai anshirya masa sai sauran abinda baa raasa
ba

Papa kuwa yafi kowa doki da murnan karatowan bikin sai dai haryanzun ya gagara gane kan
amarya

Daidai da maganar fatan baki bata hadsu sai yazama dole

Bayadda baibi da itaba taxo suje gidanta tagani amma fir taqi yadda
Haka ya haqura saidai shirye shiryensa bai fasa ba dan biki zaayi na kece raini

Biki saura sati dasu wuce dambam acan zaayi hidimar biki sai bayan biki dasu dawo bh

Aunty mabarukha kuwa yau take hanya yaranta kuma sai saura two days biki zasuzo da
babansu sabida exams dasuke a school

Acan dambam ma baa barsu abaya ba dan shiri sosai su Abba suke suma

Momcy kuwa tunba yauba tafara hidimar gyara yarta ta kuma surkarta

Ita dai fauziyyah dik abinda ake bai dametaba hasalima ma da zaa qara lokacin tanaso

Kullum tunaninta ko wanne irin zama dasuyi da ya Alamin

Dik da sosai tana ganin canji atare dashi amma dik da haka zuciyarta taqi aminta da shi sabida
sanin halinsa boyayye datayi

Ita tasan kawai jikinta yakeso yadda kullum bai gajiya da fada mata da turo mata messages na
soyayyar qarya

Tabarwa Allah zabin alkhairi kawai amma batajin zata yadda tasakeyin zaman qunci agidansa

Da daddare suna zaune afalo tare da aunty mabarukha suna ta hira harda aunty niima itama
tazo masu sai anjima mijinta zaizo sutafi

Aunty mabarukha tace mata sis dubamun abinda na daura awuta mana kada ruwan ya qone
sosai idan yayi kauri kawai kisauqeshi ya huce

Tace toh sannan ta miqe
Tana shiga kitchen papa nashigowa hangota da yayi saiko yayi saurin wucewa yabi bayanta

Tana sauqe tukunyar yana shigowa

Juyowa tayi taga wane ne ganin shine yasa ta dauke kanta ta kunna famfo tana wanke
hannunta

Qarasowa yayi ya tsaya abayanta matsota yayi sosai hartana jin sauqar numfashinsa akan
dokin wuyanta

Shiru tayi tanajin wani iri hakanan ajikinta

Murya qasaqasa yace meri darkan(my hrt beat)
Menayi ne kike guduna uumm

Shiru tayi batace komaiba

Sake maimaita mata yayi cikin wata iriyar murya mai kashe jiki yace yakamata ya zuwa yanzun
kimfahimci kyakykyawar manufata gamedake

Wlh bantaba tunanin na aureki dan na walaqantaki ko wata manufa ta daban ba

Inason kisan cewar dik wani hali nawa da kika sani ada yanzun munyi hannun riga dashi

Idanma wannan kike tunani toh ki cireshi daga ranki

Jin tayi shiru ganan ruwa na zuba takasa qarisa wanke hannunta yasa ya qara samun courage
dan yaga kamar magangannunsa sun shigeta kuma sunyi tasiri akanta

Sake matsota yayi har kirjinsa na gugan bayanta ya saka hannunsa biyu ya riqo nata yafara
wanke mata hannayen dashi baiga wani abu ajikiba da harta tsaya wankewa

Santsin hannunta acikin ruwan shiya masa dadi har ya rajaa yana murzawa ahankali

Bakinsa ya kawo daidai kunnenta yana cewa idan kina tunanin wani abu nakeso ajikinki kinyi
kuskure

Nafara sonkine tun kina yanda kike abaya tunkuma banganki ayanzuba

Sonki acikin jinina yake pls My Fauzy kibani dama na nuna maki irin kalan sonda nake maki na
kuma wanke laifina na baya

Yana fadin haka ya kashe ruwan yace i luv u my pretty sannan ya juya ya fice

Nan ya barta kamar andasata dan gabadaya maganganunsa kemata yawo akwanyarta

Saidai dik da haka bataji wani canjin akan tsanar da tamasa ba

*****
Washegari da safe ya kira aunty mabarukha akan ta lallama masa fauziyyah da yamma zaizo
su fita zata rakashi wani waje

Saida aunty ta wanasa kafin ta amince

Haka ta fadama fauziyyah ta shirya 4pm papa zaizo sufita

Batayima ta musu ba dan tana matuqar ganin girmnta

Haka badan ranta yasoba ta shirya cikin wata doguwar rigar material rainbow colour wacce ta
matuqar qarbanta

Earing dogi tasaka blue colour sai bangles nata suma passion design ne combination colour

Saita yane kanta da blue veil madaidaici

Waya ya kirata yace pls ta fito yana mota yana jiranta

Takalmanta masu tsini tasaka suma blue colour saita riqe yar qaramar purse nata itama blue
colour

Masha Allah nan tafito kamar asaceta agudu dan kyau

Tunda ta fito ya zuba mata idanu yana kallon takunta cikin natsuwa dan tamatuqar birgesa
kuma kwalliyar tayimasa 100%

Saida takusa qarasowa ya fito ya bude mata motar

Tana isowa yace bismillah My preety

Shiga tayi ta zauna sannan ya rufe ya zagayo

Ko kallonsa bataiba baran ta gaidashi

Inayini rankishi dade yafada yana kallonta

Shiru tayi kamar bada ita yakeba

Marairaice murya yayi yace haba My Fauzy ko gaisuwan nawama bazaki amsaba

Sai anan ta juyo ta kallesa tace pls idan abinda yasa katakureni nafito kenan toh sai anjima
tafada tana kokarin bude motar

Da sauri yace aa am sorry idan ranki ya baci daga haka baikuma cewa komaiba

Ahankali yake tafiya dan yanajin dadin yanayin yau sosai

Saida ya iso wani babban super market yayi parking awajen

Kallonta yayi yace mujeko n pls kidauki abinda kikeso kinji

Rai ahade tace bana buqatar komai

I know baki buqatar komai amma irin kinmin rakiyan nan aibai kamata kikoma empty hand ba

Tace toh bani buqata

Muje to yafada atare suka shiga inda yayima kansa shopping abinda ya kawosa sanna
yacigaba jibga kayan ciyeciye da wasu abubuwan amfani na qamshi wannan na fauziyyah ne

Harta gaji tace nafa gaji

Yace ainagama muje sunzo daidai wajen teddy sai wata baby girl wadda shekatunta bazasu fice
uku ba tazo tasha gabansu tanata dariya tana cewa daddy ganan teddyna

Daga bayansu sukaji ana cewa fauziyya stop there stop there

Jin an ambaci sunan fauziyyah yasa dik suka juya

Saidai wa fauziyyah zatagani mutuminda ko ta shekara dari rabonta dashi zata ganeshi dikda
kuwa canzawar dataga yayi

Shima kallonta ya tsayayi yana tabbatarma kansa itace bawai dikda rabonsa da ita yayi shekaru

amma kamanninta bazai bace masa cos her immage is in his heart

Qarasowa sukayi shida matar dake gefensa wata black beauty amma ita saita qarasa ta dauki
babyn tana cewa oh My Fauzy meyasa bakijin magana kinason kinasani gudune eh

Kallon babyn papa ya kumayi jin ankirata da sunan dayafi qauna

Murmushi Fauziyyah tayi masa tace uncle yasir dama zansake ganinka arayuwa

Shima murmushi yayi yace Fatima

Papa ne ya juyo yana masa murmushi tare da miqa masa hannu jin yadda fauziyyah ta kira
sunan saiya tuno masa da me wannan sunan

Gaisawa sukayi kamar sunsan juna

Bayan sungaisa da fauziyyah ya nuna mata matar dake riqe da baby yace this is my wife Jalila
n my dauther Fauziyyah

Kallonsa tayi tace wannan babynkane kuma sunanta fauziyyah

Murmushi yayi sannan yace yeah

Gaisawa tayi da matarsa tana kuma mamakin yadda yasir baimanta da itaba tasan kobai fada
mataba takwara ya mata

Ganin tadanyi shiru yasa yace wannan ne maigidannaki yafada yana nuna papa

Gyada masa kanta tayi tace eh nan suka sake gaisawa da papa sannan ya dauki little fauzy

Yace mata babyna kinason teddyne

Eh uncle tafada tana maqalesa yace ok zabi wadda kikeso insaya maki ko

Da fara arta ta dauki manya guda biyu yace sukadai kikeso

Tace eh uncle

Yana riqe da ita ya qarisa wajen biyan kudi katinsa ya bayar nan aka hadamusu kayayyakin

Yariqowa little fauzy nata ya dawo da ita wajen daddynta sannan sukayi sallama suka tafi

Haushin yasir ne ya kama papa ganin yadda mood din fauziyyah ya canza daga ganin yasir

saikuma aside guda yanajin son babynsu inama su barmasa ita......

�🏻 Faty Mmn Faty




🌾🌾🌾🌾🌾🌾


🌾🌾🌾🌾


🌾🌾🌾



Budurwar Qauye🤷🏼�♀🤷🏼�♀🤷🏼�♀


Written by Faty Mmn Faty


September, 2017



5⃣9⃣
Fitowa sukayi daya daga cikin masu daukan kaya na biye dasu har mota

Saida aka loda kayan a mota sannan ya zagayo side din datake tsaye ta jingina da jikin motar
da alamun hankalinta yayi nisa awajen tunani

Bude mata qofar yayi kafin yace shall we
Saida yasake maimaitawa kafin ahankali ta matso ta shiga ya rufe

Zagayowa yayi ya zauna sannan yama motar key yafara tafiya yana tunanin yanayin data shiga
one time
Zuciyarsa ce ta aminta kan ya tambayeta mene ne damuwarta

Juyowa kadan yayi ya kalleta kafin ya maida hankalinsa kan titi
Cikin sanyin murya yace My Fauzy kya hua(meke faruwa)naga mood naki ya canza

Shiru tayi kamar bada ita yake ba

Sake maimaita mata tambayar yayi yana cewa lokacin damuka fito ba haka yanayinki yake ba
but lokaci guda kincanza kyiu(meyasa)
Pls My Fauzy ki amsamun mana wlh bani qaunar ganinki cikin damuwa

Ahankali ta kallesa kadan tace ya Alamin dan Allah kadaina kirana da wannan sunan na roqeqa
ta karisa maganar kamar zatayi kuka hawaye na ciko idanuwanta

Meye laifi danna kiraki da My Fauzy keba tawa bace uum ko kina manta cewar remain few days
kizama mallakina so banga wani damuwaba danna kiraki da My Fa...
Baikaiga qarisawa ba yaji tafashe da kuka sosai

Subhanallahi haba dear danna fada maki wannan sunan shine bakiso harda kuka to kiyi haquri i
promissed u barin sakeba

Ganin yanata surutansa ko kulasa bataiba saima cigaba da kukanta da tayi yasa ahankali ya
gangara gefen titi yayi parking

Lallaminta yafara hadi da bata haquri kancewar bazai kuma mata abinda batasoba kuma tayafe
masa

Amma fir taqi sauraronsa saima kuka datake sosai

Shikuma jin kukan yake har cikin zuciyarsa ganin baya da option kawai saiya dan matso ya
jawota jikinsa ya rungume

Cikin muryar lallashi yafara magana yana cewa swt hrt am begging u kiyi haquri kibar kukan
nan namaki alqawarin koda wasa barin kuma fada makiba tunda bakiso
Banason jin kukanki yana tabamun zuciya har cikin raina nakeji

Cikin kuka tafara qoqarin janye jikinta tana cewa kadaina bani haquri kabarni nayi kuka
shikadaine zai ragemum radadin abinda nakeji

Sake riqeta yayi sosai ajikinsa yana patting bayanta smootly
Yace nasan abinda yasaki kuka n banson tuna maki kuma saidai inason roqonki kibani damar
na gwada maki kalar sonda nake maki wlh nayi alqawarin zan kula dake har qarshen rayuwata
bazan taba cutardake ba

Kuma da kike kuka sabida ganin yasir bagashiba shima harda matarsa da yarsa

So pls kimanta da baya da abinda yafaru kidauka komai Rubutaccen Alamarine bazai kuma
canzuba

Haka yaita lallaminta da kalamai masu dadi harya samu ta tsagaita kukan sai ajiyar zuciya
datakeyi

Sunfi 30mins kafin yasamu kanta ahankali ya janye jikinsa daga nata ya tashi motar

Suna isowa gida tafice cikin saa tasamu bakowa acikin falo sabida haka ta wuce dakinta kawai
ta kwanta

Shikuma fitowa yayi ya dauki iyaka kayanta ya wuce ciki dasu
Dakinta ya shiga nan yasameta kwance

Baice da ita komaiba ya ya ajiye mata ya fice

*****
Afannin yasirma ganin fauziyyah ya tayar masa da abinda ya jima yana damunsa amma haka
ya danne zuciyarsa ya haqura gudun kada matarsa ta fahimta

Kuma baya samum matsala da ita so baison tawajensa asamu rashin jituwa tunda dama tasan
da labarin fauziyyah yaukuma taganta ido da ido

Kimanin shekaru hudu kenan da auren yasir

Bayan sundawo daga dambam akan baisamu auren fauziyyah ba lokacin ya shiga matsanancin
hali sosai

Saida ya kwanta jinya tun abin yanabawa iyeyensa haushi yafara basu tausayi

Da kyar suka samu kansa yadan warware shinefa baffansa ya bashi yarsa ya aura

Baiyi musuba ya amince dan yanason ya manta fauziyyah aransa tunda yasan tamasa nisa har
abada

Itama bataqiba dan dama tajima tanason yasir babanta yana fada mata ta amince

Bayan bikinsu da yadda take kula dashi take nuna masa qauna har ta shiga cikin ransa yafara
sonta
Koda ta haihuma baiboye mataba yace sunan yarsa fatima yakeso kuma ana kiranta da
fauziyyah

Nanma bataqiba dan burinta ta faranta masa

Wannan kenan

*****
Tunda aunty mabarukha tazo bata zaunaba sai hidimar gyaran amarya take musamman da
wadanda ta dakko masu gyara

Dinkunanta ma dik ita ta bada wadda zatayi fitan biki

Kuma tundaga ranan papa baikuna saka fauziyyah a idonsaba

Saidai yaqaraci surutansa awaya nanma text dan bata daukar wayarsa kam

Cikin sati biyu babu abinda ya rage na shirin biki komai ya kankama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0