Showing 72001 words to 75000 words out of 98825 words

Chapter 25 - Budurwar Kauye Book Compelet Miss Dijerh

09 Aug 2026

1229

sai ranan biki kawai ake jira

Fauziyyah kuwa tayi natuqar kyau na birgewa dan baqaramin gyara tashaba ga wani sheqi da
da santsi da fatarta tayi

Washe gari suka tattara suka nufi dambam amma gidan Abba aka kaita sabida dagacan zaa
dauki amarya

Kuma washegari zaa fara shagalin biki

Papa kuma sai aure saura 3days zai iso sabida wasu abokansu sa zasu taho tare kuma ananne
zaayi hidimarda zai halatta.....

�🏻Faty Mmn Faty





🌾🌾🌾🌾🌾🌾


🌾🌾🌾🌾


🌾🌾🌾



Budurwar Qauye🤷🏼�♀🤷🏼�♀🤷🏼�♀

Written by Faty Mmn Faty

September, 2017


*This page goes to Mmn Faty Novel Fans, Mmn Faty ta �🏻 maku 😘�*


6⃣0⃣
Washe hari aka fara hidimar biki amma na gargajiyar aladarsu

Amarya tayi kyau kamar ba gobe,dikkannin wadan da suka halarcin wannan hidima sunyi san
barka dayima papa murnan samun mace kam tare damasa adduar Allah yasa yadda yanayinta
yake haka halayenta suke

The following day ma haka akasake wani hidimar nanma haka aka watse taro lfy lau

Papa nacan bauchi jiyake wane yayi tsuntsu ya taho yaga gimbiyarsa

Bayadda baiyiba da Aunty Mabarukha kan ta turo masa pics din Fauziyyah na hidimar biki
amma fir taqi tace mene kake sauri badai kaima daka xoba kuma gidanka zaakawo maka ita so
nothing to worry about

Haka ya dami aunty niima itanma sammaqal dan hada baki sukayi sunfison yaganta azahiri
yaga yadda tadawo akwanakin da baiganta ba

Ana gobe papa zasu iso da abokanansa akayi sakun lalle namma guri ya burge dan yan uwa
anhadu both side na ango da amarya

Sai wajen 10pm aka tashi daga taro

Jamaar garin dambam sun shaida ana biki afada dan yadda tako ina manyan motoci ke
shawagi abinka da bikin manyan mutane maaikata da yan kasuwa

Ga yan uwan Abba dana Mama gari gari dik sonzo saikace shine aurenta na fari

Papa kuwa yayi juyin duniya akan tadau wayarsa koda muryartane yaji kozaiji sauqin abinda
yakeji azuciyarsa

Amma sam taqi text kan text daya dametama saita kashe wayartama dan gaba daya bata son
damuwa

*****

Tunsafe suka kamo hanya inkagansu kace daukar amarya akatafi yadda sukayi comboy na
motoci

Zumudin papa har bai boyuwa burinsa kawai yasaka tauraruwarsa a idanunsa

12:30pm suka shigo dambam
Direct gidan daddy suka wuce inda zasu zauna da friends nasa acan tunda su daddy afada
suka sauqa

Bayan sunci abinci suka dan kwanta kafin lokacin tafiya KAMU

Amma sam papa ya gagara kwanciya burinsa kawai 4pm tayi su wuce wajen KAMUN

Ana kiran sallan laasar sunayin sallah suka fara shiri daya daga cikin abokansa guda uku da
sukazo daga india yace shikam yau jumper zaisa dan yana shaawar kayan shiyasa yasaka aka
dinka masa dan yayi shigar hausawa

Ango ne nagani ya dau wanka cikin wani coppee brown yard mai kyau da sheqi

Kyansa shiya bayyana tsadarsa
Sum matuqar karban fatan jikinsa abinka da farin mutum
Ya kafa wata tsadaddiyar huwa
Brown covvers yasaka aqafarsa sai agogon azurfa dake daure ahannunsa

Ga wani uban qamshi dayake xubawa na musamman

Tabbas ya fito a Ango sak👌🏻

Nan fa su Dr khalid suka fara tsokalansa anata barkwanci

TJ ne ya kirasa awaya yana dauka yace yane kuna inane

Papa yace muna gida amma yanzun zamu wuce

TJ yace shine ka azalzalemu ashema baku fitoba to gashinan yanzun haka muna hanya mun
dakko amarya

Papa yace to sarkin mita naga dai munfiku kusa dawajen ko kafin ku qaraso mun iso muma

Ok toh saimun hadu

Nan suka fito suka shishshiga motocinsu suka wuce wajen da zaayi KAMUN

Su papa suna isowa su TJ ma suka iso

Sunsamu angama taruwa amarya kawi da ango ake jira

TJ yace basai kunfitoba barin su qaraso naga suna tahowa sannan shima ya fice

Ta cikin glass take hangosa shida abokansa suna tahowa sunkuyarda kanta kawai tayi wadda
ita kadai tasan yanayin datake ciki

Suna qarasowa yasa hannu ya bude motar datake ciki

Ya salam shine abinda ya furta ahankali ganin irin kyan datayi

Sanye take cikin wani less pich colour mai toches na coppee brown

Dinkin riqa a siket wadda yamatuqar qarbanta kaman ba gobe

Fiskantannan yasha makeup
Dan qaramin bakinnan anlailayesa da pinks jambaki

Kyaukam baa magana gashin kantannan sai sheqi da qamshi yake andaureshi waje guda da
pich ribbon

Sai head na kanta shima coppee brown jeweries natama wasu passion ne dik suma coppee
brown masu adon duwarwatsu pich n white

Takalminta da purse nata dik coppee brown

Ahankali yake sakin wani murmushi wadda shikadai yasan maanarsa

Daurewa yayi ya daidaita muryarsa ya kira sunanta cikin wani tattausan murya yace my
princess

Dago daradaran idanuwanta masu yarwar lashes tayi ta amsa da muryarta mai dadin gaske
naam

Wani lumshe idanu yayi sannan ya bude yana kallon kwayar idonta wadda yasha kajol da
maskara tare da siririn line eye liner

Sannan yace meet my friends yana kirga mata sunansu

Dik saida suka gaisa kuma sun yaba da zaben abokin nasu

Daga qarshe ya introducing mata abokansa uku da sukazo daga india yace yeh he
Himesh(wannan shine Himesh), Salman aur Imran(da)

Cikin sakin fuska suka gaisa nan TJ ya qaraso yace man kukadai ake jirafa

Papa yace ok muje toh duban Fauziyyah yayi yace my princess muje ko

Cikin natsuwa ta sako qafarta nan yasake shagala wajen kallon lallen da aka qawata qafarta
dashi na zallan jan rani

Jerawa sukayi cikin takun qasaita dan jin kansa yake asama qasaisatar ta motsa jinin sarautar
ya tsinke

Fauziyyah kuwa dik saita jita atakure dake ita bawasu qawaye ke gareta ba kwakwata su
shidane sai

Suna shiga cikin hall din waje ya kaure da tattausan waqa mai dadin gaske

Wajenda aka qawatashi da ado sosai kuma kalan kayansu hatta ballons da aka decourating
wajen pich n coppee brown ne

Wasu kujeru ne guda biyu iri daya masu kyan gaske suka qarasa suka zauna sai kuma na
abokanai da qawaye da aka ajiye daga bayansu

Kowa ya shashe ranan angwangwaje naira tayi kuka ko motsi tayi saiyace yadai baby kingaji ne
sabida yadda yakeji kamar ya maida ciki dan so

Fans na Mmn Faty Novel ma baa bassu abayaba dan sun nuna murnansu sunkuma nunama
ma fauziyyah gata

Kodagakan irin liki da sukaringa mata shima abin ajinjina masu ne

Baa tashi ba sai gabda magriba sannan taro ya watse

Ahanyar su ta komawa gidane papa yaga canji yayi juyin duniya fauziyyah tayi magana amma
taqi sam shikuma harga Allah baison shirunta shifa ko zaginsane garatayi yasan tayi magana
dan baimanta lokacin data kullaci abu aranta tadaina masa magana

Haka suka sauqeta suka dawo gida

Washe gari Thursday akayi Family n Friends day

Nanma sunyi kyau ba qarya

Ranan friday akayi Hafla

Sai washe gari Saturday misalin Qarfe sha daya na safe dubban jamaa manyan mutane
maaikata yankasuwa hadda sarakuna da sauran Alumma suka shaida daurin Auren Dr
Muhammad Alamin Abubakar n Fatima Usman abisa sadaki 100k lakadan ba ajalanba

Papa dai bakinsa bai rufuwa daka ganshi kasan yana yanayin farin ciki lura daga kayan jikinsa
komai fari tass

Sai gaisawa yake da jamaa kawai

Makada da maroka kuwa sai wasashi sukeyi abindai abin birgewa sai muce Allah ya kade fitina
kawai

Da yamma akazo daukan amarya

Wata goggonsu papa wadda take yace awajensu daddy ita tabada wata Alkyabba ta
musamman tace asawa amarya ita

Fauziyyah tai kuka harta gode Allah sabida nasihan da su Abba suka mata mai ratsa zuciya da
dikkan gangan jiki

Da mata adduan Allah yasa sai gawanta zaa fitar agidan Alamin

Haka aka wuce da ita fada su anty papa aka samu a side din da zaa sauqi amarya

Nan suka karbi amarya da murna da farin ciki gami da mutunchi

Nan suka shiga hidima da baki dan Aunty naja(Auntyn Papa ) batada rowa kuma batason
harkan qaranta

Dik wadda yazo kawo amarya ya yaba da irin kaunar da yan uwan papa kema Fauziyyah sai
fatan alheri suke musu

Bangare guda Aunty papa ta sauqi Fauziyyahs' team


Kuma sun yaba sosai dan Aunty papa bata musu qarantaba ta nuna musu cewar biki ake na
dan gata

Har wajen magriba fauziyyah taqi yin shiru sai kuka take
Saida Aunties dinta suka shigo suka lallasheta sannan tayi shiru

Anayin sallan ishai Aunty mabarukha ta kawo mai kwalliya akayima Fauziyyah

Wani mterial ne dinkin doguwar riga milk n golding colour tasaka wadda yasha ado sosai
yakuma matuqar yimata kyau

Kwalliya sosai aka mata sai dan veil din rigar wadda shima golding colour ne tayane kanta
dashi

Wani danqareren saitin gold Aunty Mabatukha takawo mata tasaka hadda bangkes dinsa
manya guda biyu

Takalmin hill ne sosai da purse dinsa suma golding colour

Wasu turaruka na musamman tafesa wadda dik aunty Mabarukha ce takawo mata su

Nan tafito a amaryarta ba qarya

Members na Mmn Faty Group sunsha anko dinsu na material
Fauziyyahs's team sunyi ankon material golding colour

Sai papas' team sukuma ankon material milk colour sukayi

Nan aka fara tafiya dinner kowa ya tafi sai Fauziyyah ita kadai akabari dan wannan umarnin
Ango ne

Tana zaune abakin bed shiru itakadai sai taji motsin bude qofa

Bata dago kanta ba amma qamshin turarensa daya gauraye dakin shiya tabbatar mata papa ne

Sanye yake da wani dhegen gezna maih danbanzan kyau da tsada Milk colour

Dikin yamatuqar amsansa ga hularsa da ta dace da kayan hafi da takalminsa

Qaremata kallo kawai ya tsaya yi yana yima ubangiji tasbihi acikin zuciyarsa daya mallaka masa
ita amatsayin mata

Ahankali ya tako har bakin gadon datake zaune

Maganama ya kasa kawai hannunta ya kamo ya riqe gam acikin nasa

Wani taushi dayaji shiya haifar masa da kasala lis ajikinsa

Dayan hannunsa yasaka yana murza bangles din hannunta

Da wata iriyar murya yace my princess pls na roqeki kimun magana kinji

Kallonsa tadanyi ta kasan idanunta ta dan turo baki tace to mai zance maka pls kasakemun
hannuna

Cos yadda yake wasa da hannun nata dik sai taji ta takura

Shikuma gyara zamansa yayi yama manta da yabar mutum awaje nan yafara barbada mata
maganganun soyayya

Qarar wayarsa yasashi yin dan qaramin tsaki dan yana tsaka da jin dadin yadda yake manne da
ita bata kuma turesaba

Ganin TJ ne yasa yace yane akayi

TJ yace lallema toh kawai kace inje insallami mutane tunda kai kasamu waje bazaka fitoba

Papa yace oh yaushema nashigo to naji gamunan fitowa

Baby nah mujeko kinga wannan dan damuwar da takurin yafara mita

Batace dashi komaiba hannunta ya riqo ta miqe suka tako ahankali suka fito....



�🏻Faty Mmn Faty





Budurwar Qauye🤷🏼�♀🤷🏼�♀🤷🏼�♀

Written by Faty Mmn Faty

September, 2017

*Banmanta dakeba takwarata Fatima Muhammad(Miyatti Allah), nagode da kulawarki gareni
Allahu ya bar qauna, Mmn Faty 😘�*

6⃣1⃣

Hannunsa riqe acikin anata har bakin mota

TJ dake tsaye yana jiransu shiya bude mata

Da murmushi afiskansa yace bismillah Amaryanmu

Batace komaiba sai murmushi datayi sannan ta shiga tazauna

Ya rufe kafin ya zagaya ya shiga shima

Papama ta gefenta ya zagaya ya zauna
Tafiya suke suke bamai cewa komai itadai ta sunkuyar dakanta tana wasa da ring din yatsanta

Papa kuwa ya wani matso jikinta kamar wadda zai shige cikinta amma baicewa komai cos
hakanma he is totaly satisfied

TJ kuwa katse shurun yayi da kunna wani tattausan music mai dadin sauraro

Da haka har suka iso

Batare da bata lokaciba abokai da qawaye suka rufa musu baya zuwa cikin hall din

Lokacin da suka shigo nan aka fara musu ruwan wasu flowers masu kyan gaske da qamshi mai
dadi

DJ kuwa waqar da aka masu ta biki ya kunna nan waje ya birge sosai

Cikin takun natsuwa suka qarasa wajen zamansu kafin kowa ya sami waje ya zauna

Baqarya wajen ya qayatu ya kuma matuqar birgewa dan naira tayi kuka

Nan aka fara gudanar da programs iri da ban da ban

Idan ka kalli Amarya da Ango ka rantse kace wasu couples ne masu mutuwar son junansu

Yadda fauziyyah tasake fiskarta kamar bawani abu aqasa
Shikuma uban gayyar dama sai faraa yake kamar gonan auduga yana wani shige mata ganin
yadda ta saki jikinta tamkar ba itaba

Kowa ka gani awajen yasha ado da kwalliya gaskiya bikinsu papa ya matuqar tsaruwa sai fatan
zaman lfy

Sai wajen 12 aka tashi

Saida kowa ya watse ya rage su papa aka bari kafin suka taho suma

Ahanya papa yacema TJ man kadaukomin saqona daiko

TJ yace waneni namanta yana gaba nan qasan seat

Papa yace ok thanks

Suna isowa gida TJ ya bude mota ya miqo masa ledan take away sannan ya fice

Itama bude qofar motar take qoqarin zata fice

Riqo hannunta yayi

Juyowa tayi ta sauqe daradaran idanuwanta akansa kafin dan qaramin bakinta ya motsa gami
furta lfy daiko

Yadda tai maganar ba walwala afiskanta yasa ya marairaice murya yace pls kiban 15mins acikin
lokacinki

Pls mana dear badan niba dan Allah

Komawa tayi tazauna
Thanks yafada sannan yasake mata hannu

Take away din ya bude pepper chikchen ne wadda yasha hadi sosai

Kallonta yayi da kyau kafin yace baby pls bawasa nakeba kici abinci kuma kada kice aa dan
nasan wunin yau kaf da wuya idan kinci wani abin

Shiru tayi tana tuna tabbas yau bataci wani abinkirkiba

Bude motar yayi ya balle bottle din ruwa ya dauraye hannunsa

Naman ya kutsiro ya miqo mata saitin bakinta

Ba musu ta karba tafara tauna ahankali

Ganin yadda batai gardama yasa yaci gaba da bata abaki tanaci

Matsowa yayi sosai yana lallabata harta ci sosai kafin ta kauda kanta

Ruwa ya bata tasha sannan ya bude mata roban juice sai anan ta kauda kanta tace umum

Murmushi yayi yace thanks a lot wifey nagode muje narakaki ko

Aa kawai tace dashi tafice abinta

*****
Washe gari sunday akayi walimah dasafe daganan wasu suka fara tafiya garuruwansu

Amma su papa sai gobe dasu koma bh

Abdu yasa ya maida su Himesh bh sabida gobe jirgin safe zasubi zuwa lagos dagacan su wuce

Abokanansu dik sun koma TJ ne bai tafiba sai gobe zasu wuce tare da Ango

Itama qawayenta dasukazo daga bh guda biyu sun koma sauran ukun dama yan uwane

Haka ta yini shiru itakadai su aunty mabarukha ma basu zannaba sabida sallamar baqi

Shima haka ya wuni sallama da baqi gashi sunje gidan Abbama sunjima acan

Sai dare aunty mabarukha ta shigo nan tace tana da magana da ita

Gyara zamanta tana sauraronta

Aunty mabarukha tace abinda zan fada maki kidauka ni yar uwarkice kuma ciki daya kikuma
dauka bansan papa banida alaqa dashi

Taci gaba dacewa inason kidauki wannan auren yana cikin kaddaranki arayuwa wanda baki isa
kikaucewaba

Kuma tunda har Allah ya rubuta haka inason ki haqura kidauki qaddara ki rungumi mijinki
kimasa biyayyar aure

Dik halin da kuke ciki da papa ina sane amma yanzun tunda andaura maku aure zance ya qare

Kuma bama fata abinda zai kuma rabaku sai dai mutuwa

Jikintane yayi sanyi kuma ko itama tunanin datake aranta kenan tunda Allah ya qaddari haka
tafaru gara ta dau haquri suzauna lfy

Aunty mabarukha tace sabida haka kidauka dik abinda yafaru abaya kamar bai faruba kuma
bama fatan ya kuma faruwa

Kuma ina da tabbacin hakan bazai faruba sabida yanzun papa yana sonki so mai tsananin
gaske kuma zai iya komai akanki

Amma bawai ina nufin dakunkoma bh kibada kai bori ya hauba aa ki nuna masa cewar kema
mace ce

Saikin dan wanasa tukun saiki saqqo ku zauna lfy Allah ya albarkaceku

Sannan kada ki kuskura kiyadda kunya ta cuceki dan matuqar zakiji kunyan yin wani abin toko
zaki kwari kanki

Gobe akwai kayan dazan kawo maki idan kinkoma bh

Su zaki ringa sawa agida kina kwalliya tareda yin qayataccen girki kuma kada kihanasa

Kibashi dik tarkone yadda zaiji kawai bazai iya rayuwa bakeba kuma komai kikace yamaki zai
maki

Amma kada kimanta kina riqe da class naki harsai yagane kuransa yadda koda kudi akabasa
bazai tabayin gigin batamaki raiba

Dafatan kinfahimceni

Cikin sanyin murya tace insha Allahu aunty zanyi yadda kikafada

Aunty tace yawwa qanwata Allah ya maku albarka sannan zanyi magana da Aunty naja(Aunty
Papa )tace zatana aiko maku da abinci zance tabari kawai sabida musamu tarkon ya kamashi

Tace toh aunty nagode Allah yabar zumunci

Miqewa tayi tace barinje wajen momcy sabida shirin tafiya amma zandawo mukwana tare

Tace toh saikin dawo itakuma ta fice

Shiru tayi tana tuna maganganun da aunty tafada mata tabbas gaskiyane

Da haka har bacci ya kwasheta sabida dama agajiye take batamaji shigowar Aunty ba

Washegari wajen laasar suka iso bh

Direct gidanta aka wuce ta da ita wannan umarnin daddy ne

Shima papa gidan ya taho yayi wanka sannan ya fita amsa kiran daddy baiko leqa taba dan
yasan tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0