Showing 12001 words to 15000 words out of 23776 words

Chapter 5 - Biyu Babu Book 3 By Fatima Tijjani Ahmad

10 Aug 2026

296


"Fatima ya dai?"
Na ce, "Ba komai ruwa zan sha, Kishirwa na ke ji".
Ya mike ya ba ni ruwa na sha, jimawa kadan likita ya shigo ya ce.
"Me ya ke damunki Fatima?"
Na ce, "Ba komai".

Ya ce, na tuna dai ko ina jin ciwo?
Na ce, ba na jin komai sai na ji bude kofa an shigo mahaifin Umar ne, shi ma Umar ɗin bai san
ya zo ba sai yanzu da ya shigo ya durkusa ya gaida mahaifinsa.
Mahaifin Umar ya zo gaban gadona ya jawo kujera ya zauna, ya dube ni ya ce.
"Fatima Zahra'u".
Na ce, "Na'am, na'am, barka da yamma".
Ya ce, "Ya jikinki".
### Shafi 75
Na ce, "Jiki kuma? Da ma ba ni da lafiya?"
Ya ce, "Fatima ba ni hankalinki".
Na ce, "To, na ba ka Baba".
Ya ce, "Da ma ba na yana daga cikin imani da al'amarin Ubangiji?"
Na ce, "Da ma ba akwai wanda ya isa ya ba yarda da kaddara mai kyau da kuma akasinta ba?"
Na ce, "Haka ne".
Ya ce, "Fatima, wa ke ba da wa ne?"
Shi ma na ce, "Allah".
Ya ce, "Idan Allah ya ba ki abu akwai wanda ya isa ya hana ki?"
Na ce, "Babu".
Ya ce, "Ko kin manta da hadisin Manzon Allah (S.A.W) da ya ke cewa, wajibi ne mumini ya
yarda da kaddara mai kyau da mara kyau?"
Na ce, "Ban manta ba".
Ya ce, "Lokacin da Manzon Allah (S.A.W) ya yi wafati, Nana Fadimatu ihu ta yi ko hakuri?"
Na ce, "Hakuri ta yi".
## 384849.jpg
### Shafi 76
Ya ce, "An dauke ran manzon Allah (S.A.W) a kirjin Nana Aisha, me ta yi? Kuka? Ihu? Har ta
fita daga hayyacinta?"
Na ce, "A'a".
Ya ce, "To me ya sa ba za ki yi koyi da manyan bayin Allah ba, idan masifa ta afka miki?"
Na yi shiru, na ce.
"Na gode, insha Allahu Ubangiji ya ba mu ikon koyi da bayinSa na gari".
Na maida dubana ga Umar, na ce.
"Umar, ina abokinka?"
Nan da nan na ga hankalinsa ya tashi, fuskarsa ta sauya, mahaifinsa ya ce.
"Ba yanzu na ke faɗa miki Nazir ya yi hadarin mota ba?"
Na ce, "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".
Mahaifin Umar ya ce, "Yauwa".
Na dubi Umar idona yana fidda hawaye, na ce.
"Umar, Nazir ya mutu ko?"
Ya ɗaga min kai, ya ce.
"Eh".
Addu'a na kuma yi masa, Allah ya jikansa, Ya kuma sa aljanna Fiddausi makoma.
### Shafi 77
Na jima ina yi wa Nazir addu'a, mahaifin Umar ya ji daɗi sosai yadda ya ga na ɗauki ƙaddara.

Ba mu dawo daga U.S.A ba sai da na samu lafiya sosai, na kuma huta mahaifin Umar ya ce kar
na dawo sai labarin mutuwar Nazir ya ɗan ragu a cikin mutane.
Haka kuwa aka yi da muka dawo zancen ya ɗan ragu a garin, sai dai masu yi min addu'a Allah
ya jikansa, ni kuma ya ba ni wani.
Yanzu Umar ne ya dawo zuwa Kano duk sati yana debe min kewar Nazir, ina jin daɗi sosai duk
abin da ya dame ni sai na yi masa waya na faɗa masa wani lokaci kuma ya ce sai ya zo mun yi
maganar.
Yanzu na saduda, na haƙura, na maida rayuwata kamar da, bani da kowa da zan yi magana da
shi a matsayin saurayina, ko na ce masoyina, na ma daina tunanin zan yi wani abu wai shi
aure.
Yanzu har mahaifin Umar ya kan tambaye shi ya je Kano kuwa gurin Fatima?
Idan ya zo zai ce ya zo, idan kuma bai sami damar zuwa ba zai faɗa masa zo ba.
## 384853.jpg
### Shafi 84
Ya amsa cikin girmamawa muka tashi gabadaya muka bar falon, muka dawo falon da muke da
a zaune.
Kukun gidan ne ya iso inda mu ke, ya ce da Umar.
"An gama".
Ya ce, "To".
Umar ya ce, "Mu je mu ci abinci ko?"
Mikewa ya yi, mu ma muka mike muka rufa masa baya, mun ci abinci kuma mun sha abin sha
abinka da gidan akwai.
Bayan mun gama muka sake dawowa falon muka zauna, shi kuma Umar ya ce yana zuwa.
Ya jima bai dawo ba, domin sai da muka yi sallar la'asar sannan ya dawo falon ya ce.
"To, ku taso".
Na mike na ɗauki jakata, da kuma mayafina, na ce.
"Ina Mama? Ya kamata ta san mun fita ko?"
Ya ce, "Au kina gudun kar na saida ku?"
Na ce, "A'a, ba za ka saida mu ba, amma bai dace a ce mun fita ba sai ta sani".
Waya ya ciro daga aljihunsa, ya ce.
### Shafi 85
"To bari a kira ta".
Jimawa kaɗan ta ɗau waya ta ce.
"Umar ya ya?"
Ya ce, "Za mu fita ne, amma Fatima ta ce ba inda za ta sai ta ganki".
Ta ce, "Ba ta wayar".
Ya miƙo min waya na amsa na sa a kunnena ina faɗin, "Hello".
Ta ce, "Fatima, ku je Allah ya kiyaye, kin ji ni ma mun ɗan fita ne da Babanku, kin ji".
Na ce, "To Mama".
Na miƙa masa wayar ya ce.
"Shi ke nan?"
Na ce, "Eh".
Ya ce, "To mu je".
Mun yi yawo wurare da dama, sai kuma na ga magriba ta soma yi na ce.

"To mu koma gida ko?"
Ya ce, "Sai kin jima, bari mu je gidan Najib ku gaisa da matarsa".
Na ce, "To, Umar waye kuma Najib?"
Ya ce, "Ba damuwa idan muka je muka dawo zan faɗa miki dangantakata da shi".
Mun isa gidan Najib, kuma mun yi sa'a domin mun same shi yana gida.
## 384854.jpg
### Shafi 86
Najib da matarsa Fauziyya sun karɓe mu matuka domin bayan mun gaisa ta gabatar mana da
yin sallah, ni na fara yi sannan Nafisa da tuni gidan ya ɗauke mata hankali.
Bayan mun idar sai ta gabatar mana da kayan abinci da kuma na sha.
Duk da cewaba wata yunwa muke ji ba, amma dai mun ci. Bayan mun gama ne Najib ya yi min
gaisuwar Nazir shi da matarsa, sannan muka shiga hira. Idan ka ganmu muna hira za ka yi
tsammanin mun daɗe da sanin juna.
Muna cikin hirar ne mai kula da yara ta shigo da yara 'yan tagwaye guda biyu a hannunta duka
maza masu kama ɗaya.
Binsu na yi da kallo, sannan na ce.
"Yan biyu ne ko?"
"Eh, 'yan biyu ne".
Da sauri Umar ya ɗauki ɗaya ya ɗora a kan cinyarsa, na ji yana tambayarta waye Fawazas a
cikinsu?
Ta yi dariya, ta ce.
"Ga shi nan".
Ya ce, "Au, kina gane su?"
Ta sake yin dariya ta ce.
### Shafi 87
"Ina gane su mana, ɗaya ya fi ɗaya haƙuri, Fawwaz ya fi haƙuri shi ya sa kuma ba shi da
damuwa".
Na ce. "Kai amma na daɗe ban ga 'yan biyu masu kama ɗaya ba, tun waɗanda muka yi
makaranta da su Hassana da Usaina, su ma kamarsu ɗaya, ko Babansu ba ya gane su don ba
na mantawa Usainar ita ce a makarantarmu, ita kuma Hassana a Tudun Wada ta ke amma an
sha kawo mana Hassana a matsayin Usaina". Umar ya ce, "to ya aka yi ku ke ganewa?"
Na ce, "Da ya ke muna tare da ita, ɗakinmu ɗaya, komai namu tare muke yi, to dole wani
lokacin sai mun fahinici ban banta ba, haɗa baki suka yi suka sauya guri. Kuma ta taɓa faɗa
mana cewa, idan suna son abu a gurin mahaifisu sai su je masa su biyu kuma idan za su komai
nasu iri ɗaya suke sa wa, idan suka je gabansa sai su zuba masa ido suna kallonsa, to shi
kuma abin da ba ya so ke nan ya ce da mahaifiyarsu tsoro suke ba shi, shi ya sa ma ya ke
musu waɗa, *biyu kyautar Allah, ido biyu mai ban tsoro*. Yau kuma ga wasu na gani".
Umar "Ko kina so?"
## 384855.jpg
### Shafi 88
Na ce, "Ah ya zan ce ba na so? Kyautar Allah fa Umar ban da Allah wa zai ba ka, ya kuma ƙara
kara maka, ya sake ƙara maka? Sai Allah ko?"
Ya ce, "Gaskiya ne".

Najib ya ce, "Wai don Allah Umar kai ba za ka yi aure ba? Shekarunka fa tafiya suke yi wallahi,
ko so ka ke ka kai 'yar wani a cikin abokai? Ka ga dai Muhammad 'yarsa har ta shiga firamare".
Ya ce, "Ba komai, na soma shiri yanzu nan ba da daɗewa ba za ku zo ku ma ku ɗebi girkin
amaryata".
Muka yi dariya gabaɗayanmu, na ce.
"Ya kamata mu koma gida fa".
Ya ce, "To mu tafi".
Mun miƙe, Najib da matarsa sun mana rakiya har bakin mota.
Najib ya ce, "Fatima, ita wannan ƙanwar taki ba ta magana ne?"
Na yi dariya na ce.
"Ba ta ga dama ba ne, amma Aku ma haka ta ganta ta bari".
### Shafi 89
Mun yo sallama da su muka shiga mota muka nufi gida, a kan hanyarmu ne na ke tambayar
Umar a ina matar da zai aura ta ke?
Dariya ya yi, ya ce.
"Kar ki damu za ki ganta, ina ga ma gobe na kai ki gurinta ku gaisa".
Na ce, "Amma fa na ji daɗi".
Nafisa ta ce, "Ya sunanta Uncle Umar?"
Ya ce, "Ba za ku ji ba, amma dai idan kun je za ku ji, kuma za ku ganta, me ye abin sauri a
ciki?"
Mun dawo gidan mahaifinsa, mun sami Mama a falo zaune tana kallo, ta yi mana maraba muka
gaishe ta sannan muka nemi gurin zama muka zauna.
Nafisa ta ke tambaya ya ta ga garin Kaduna?
Ta ce, "Wallahi Mama wani gida muka je na ga 'yan biyu masu kama ɗaya".
Sun jima suna hira ni kuwa da na miƙe na je na yi sallar isha'i, kwanciya na yi a ɗakin kanwar
Umar duk da dai na fahinci ba ta nan.
Ban san sanda Nafisa ta shigo ba, don na yi bacci, da asuba muka tashi muka yi sallah na sake
komawa bacci, ita kuma zama ta yi kallo.
## 384857.jpg
### Shafi 90
Ban tashi ba sai misalin ƙarfe goma da rabi na safe, a lokacin da na tashi Nafisa ba ta ɗakin.
Banɗaki na faɗa na yi wanka, na kuma wanke bakina, sannan na ɗauro alwala domin gudanar
da sallar walha.
Bayan na fito na tarar da Nafisa ta shigo, hannunta ɗauke da leda, na ce.
"Ya aka yi?"
Ta ce, "Anty, Mama ta ce a kawo miki".
Na amsa na buɗe, dogayen riguna ne a ciki guda huɗu, na ce.
"Amma na gode, ɗauki wanda ki ke so".
Ta yi dariya sosai, ta ce.
"Ga nawa nan".
Ta nuna min wata ledar a ƙarkashin madubi, na ce.
"Kai amma Mama tana da kirki wallahi wallahi ba mu da bakin yi muku godiya gi na har
mahaifina, sai dai mu yi musu addu'a, Allah ya saka da alheri Ya kuma kare su daga sharrin
mutum da kuma aljan".

Ban fito daga ɗaki ba sai misalin sha ɗaya da rabi na fito. Ina zuwa falon ba kowa sai na sami
guri na zauna, na jima ba kowa a falon ba
### Shafi 91
kuma motsin kowa, ga dukkan alamu ba kowa a cikin falon.
Na jima a zaune ina ta faman kallo, Umar ya shigo, koda yake ban ji shigowarsa ba, sai da ya
ƙaraso kusa da ni na ji motsi na maida hankali zuwa gare shi.
Bayan mun gaisa ya ce, wai sai yanzu ki ka tashi?"
Na ce, "Na jima da tashi".
Ya ce, "Ashe ba a ci abinci ba?"
Na ce, "Wallahi".
Ya ki ra kuku ya ce, me na ke so? Na ce a soya min dankali da ƙwai sai ruwan shayi.
Kukun ya fita ya cika aikinsa.
Na ce, "Umar ina Mama?"
Ya ce, "Kai Fatima tare fa na bar ku da Maman jiya, za ki tambaye ni Mama yanzu? Wai ma ban
gane ba, ba kya tashi neman Mama sai na shigo, ko tsorona ki ke ji?"
Na yi dariya na ce.
"Umar ke nan, ya zan ji tsoronka bayan ka zama ɗan uwana? Yanzu fa da za a tsaga jikinka a
tsaga nawa jinin iri ɗaya ne".
Ya ce, "Allah da gaske?"
Na ce, "To kana kokwanto ne?”



**Fatima Tijjani Ahmad**
Najib da matarsa Fauziyya sun karbe mu matuka domin bayan mun gaisa ta gabatar mana da
yin sallah, ni na fara yi sannan Nafisa da tuni gidan ya dauke mata hankali.
Bayan mun idar sai ta gabatar mana da kayan abinci da kuma na sha.
Duk da cewaba wata yunwa muke ji ba, amma dai mun ci. Bayan mun gama ne Najib ya yi min
gaisuwar Nazir shi da matarsa, sannan muka shiga hira. Idan ka ganmu muna hira za ka yi
tsammanin mun dade da sanin juna.
Muna cikin hirar ne mai kula da yara ta shigo da yara 'yan tagwaye guda biyu a hannunta duka
maza masu kama daya.
Binsu na yi da kallo, sannan na ce.
"Yan biyu ne ko?"
"Eh, 'yan biyu ne".
Da sauri Umar ya dauki daya ya dora a kan cinyarsa, na ji yana tambayarta waye Fawazas a
cikinsu?
Ta yi dariya, ta ce.
"Ga shi nan".
Ya ce, "Au, kina gane su?"
Ta sake yin dariya ta ce.
**86**
### **Shafi na 87**
**BIYU BABU-3**

**Fatima Tijjani Ahmad**
"Ina gane su mana, daya ya fi daya hakuri, Fawwaz ya fi hakuri shi ya sa kuma ba shi da
damuwa".
Na ce. "Kai amma na dade ban ga 'yan biyu masu kama daya haka ba, tun wadanda muka yi
makaranta da su Hassana da Usaina, su ma kamarsu daya, ko Babansu ba ya gane su don ba
na mantawa Usainar ita ce a makarantarmu, ita kuma Hassana a Tudun Wada ta ke amma an
sha kawo mana Hassana a matsayin Usaina". Umar ya ce, "to ya aka yi ku ke ganewa?"
Na ce, "Da ya ke muna tare da ita, dakinmu daya, komai namu tare muke yi, to dole wani
lokacin sai mun fahinci ba ita ce tamun ba, hada baki suka yi suka sauya guri. Kuma ta taba
fada mana cewa, idan suna son abu a gurin mahaifinsu sai su je masa su biyu kuma idan za su
komai nasu iri daya suke sa wa, idan suka je gabansa sai su zuba masa ido suna kallonsa, to
shi mahaifiyarsu tsoro suke ba shi, shi ya sa ma ya ke musu waka, 'biyu kyautar Allah, ido biyu
mai ban tsoro'. Yau kuma ga wasu na gani".
Umar ya ce, "Ko kina so?"
**87**
### **Shafi na 88**
**BIYU BABU-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Na ce, "Ah ya zan ce ba na so? Kyautar Allah fa Umar ban da Allah wa zai ba ka, ya kuma kara
kara maka, ya sake kara maka? Sai Allah ko?"
Ya ce, "Gaskiya ne".
Najib ya ce, "Wai don Allah Umar kai ba za ka yi aure ba? Shekarunka fa tafiya suke yi wallahi,
ko so ka ke ka auri 'yar wani a cikin abokai? Ka ga dai Muhammad 'yarsa har ta shiga firamare".
Ya ce, "Ba komai, na soma shiri yanzu nan ba da dadewa ba za ku zo ku mu debi girkin
amaryata".
Muka yi dariya gabadayanmu, na ce.
"Ya kamata mu koma gida fa".
Ya ce, "To mu tafi".
Mun mike, Najib da matarsa sun mana rakiya har bakin mota.
Najib ya ce, "Fatima, ita wannan kanwar taki ba ta magana ne?"
Na yi dariya na ce.
"Ba ta ga dama ba ne, amma Aku ma haka ta ganta ta bari".
**88**
### **Shafi na 89**
**BIYU BABU-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Mun yo sallama da su muka shiga mota muka nufi gida, a kan hanyarmu ne na ke tambayar
Umar a ina matar da zai aura ta ke?
Dariya ya yi, ya ce.
"Kar ki damu za ki ganta, ina ga ma gobe na kai ki gurinta ku gaisa".
Na ce. "Amma fa na ji dadi".
Nafisa ta ce, "Ya sunanta Uncle Umar?"

Ya ce, "Ba za ku ji ba, amma dai idan kun je za ku ji, kuma za ku ganta, me ye abin sauri a
ciki?"
Mun dawo gidan mahaifinsa, mun sami Mama a falo zaune tana kallo, ta yi mana maraba muka
gaishe ta sannan muka nemi gurin zama muka zauna.
Nafisa ta ke tambaya ya ta ga garin Kaduna?
Ta ce, "Wallahi Mama wani gida muka je na ga 'yan biyu masu kama daya".
Sun jima suna hira ni kuwa da na mike na je na yi sallar isha'i, kwanciya na yi a dakin kanwar
Umar duk da dai na fahinci ba ta nan.
Ban san sanda Nafisa ta shigo ba, don na yi bacci, da asuba muka tashi muka yi sallah na sake
komawa bacci, ita kuma zama ta yi kallo.
**89**
### **Shafi na 90**
**BIYU BABU-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Ban tashi ba sai misalin karfe goma da rabi na safe, a lokacin da na tashi Nafisa ba ta dakin.
Bandaki na fada na yi wanka, na kuma wanke bakina, sannan na dauro alwala domin gudanar
da sallar walha.
Bayan na fito na tarar da Nafisa ta shigo, hannunta dauke da leda, na ce.
"Ya aka yi?"
Ta ce, "Anty, Mama ta ce a kawo miki".
Na amsa na bude, dogayen riguna ne a ciki guda hudu, na ce.
"Amma na gode, dauki wanda ki ke so".
Ta yi dariya sosai, ta ce.
"Ga nawa nan".
Ta nuna min wata ledar a karkashin madubi, na ce.
"Kai amma Mama tana da kirki wallahi wallahi ba mu da bakin yi musu godiya daga ni har
mahaifina, sai dai mu yi musu addu'a, Allah ya saka da alheri Ya kuma kare su daga sharrin
mutum da kuma aljan".
Ban fito daga daki ba sai misalin sha daya da rabi na fito. Ina zuwa falon ba kowa sai na sami
guri na zauna, na jima ba kowa a falon ba
**90**
### **Shafi na 91**
**BIYU BABU-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
kuma motsin kowa, ga dukkan alamu ba kowa a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0