Showing 21001 words to 23776 words out of 23776 words

Chapter 8 - Biyu Babu Book 3 By Fatima Tijjani Ahmad

10 Aug 2026

297

ce za ta fito da ita.
**Page 122**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
ga filin bakin, to na mike na fito da amarya a ka nemi da mu taka rawa ni da ita. Umar ne ya fito
a hannunsa dauke da dala wato kudin amerika ya soma lika min amma kuma ya fahinci ya ga
raina ya baci, rada ya yi min.
"Me ya faru?"
Na ce, "Da ka daina watsa kudi haka haka".
Sam ya ki amincewa da abin da na fada masa.
Umar ya ba da mamaki a gurin bikin hatta abokansa suka zo tare daga Kaduna, ya bin ya ba su
mamaki.
Daf da kammala biki ne sai wani abokin Umar ya zo inda muke zaune. Yana zuwa ya dauki
lemo ya sha sannan ya zauna, ya ce.
"Wai Umar ba mu fahince ka ba, mu dai ba mu sanka da wata mace ba, amma kuma yanzu ga
shi ka zo mana da wani juyayyen al'amari ma'ana mun ganka da mace, kuma ba ka ce da mu
komai ba".
Umar ya ce, "Ka yi hakuri ina so da ma na gabatar da ku ne gare ta, idan an jima mun hadu sai
na gabatar muku da Fatima a matsayin matata da izinin Allah".
**Page 123**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Na dubi mutumin da ya ke zaune kusa da Umar na ce.

"Umar ban sanshi ba, shi ma abokinka ne?"
Ya ce, "Abokina ne, zan kuma ba ki labarinsa, amma sai nan gaba".
Na ce, "To ba komai, na gode".
Ya jima yana taya mu hira kafin daga bisani ya tashi ya koma cikin mutane ya ci gaba da
zarafinsa.
Umar ya tambaye ni, ko da ma na san amarya Aisha?
Na ce, "Na santa a zaman na asibiti a nan na santa".
Ya ce, "Ai da ma ku mata ba ku da wuyar sabo da juna".
Sulaiman ne ya iso inda muke zaune ya gaida Umar ya kuma ce da ni, "Ya maganar tafiya, ko
sai anjima?"
Umar ya ce, "Da me ku ka zo?"
Na ce, "Motata mana".
Ya ce, "Ai ita aka hau kuma?"
Na ce, "Eh".
Ya ce, "Sulaiman, ka dauki mota ka tafi gida zan kawo ta gidan anjima".

**Page 124**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Ya ce, "To na gode, zan tafi sai kun taho".
Umar ya dauko kudi a cikin aljihunsa ya mika wa Sulaiman. Jimawa kadan na ce da Umar ya
kamata ya kai ni gida, domin ya samu ya koma gida da wuri, gudun kar su yi dare.
Ya ce, "Ai yau a Kano zan kwana, saboda ke inyaso gobe sai na wuce".
Ba mu muka bar gurin bikin Aisha ba sai sha daya na dare, muka nufo gida Umar ya sauke ni
ya koma masaukinsa da safe abokansa sun nemi da ya zo su tafi, amma ya ce su tafi sai ya
taho shi yana kano.
Da safe misalin karfe tara na safe sai ga Umar ya zo, a lokacin na tashi na shiga wanka. Ina
fitowa na sa doguwar rigata, sannan ya shigo dakina.
Ya sami guri ya zauna, na tambaye shi ya ci abinci ko zai ci don ni yanzu na tashi domin yanzu
zan sha shayi.
Ya ce, zai sha shayin shi ma. Na dauko fulas na hada shayi muka sha, da muka gama shan
shayin sai ya gabatar min da cewa, zai turo malam ya zo gidanmu don nema masa aurena.
Na dan yi dariya na ce.
"Ka yi hakuri kafin dan wani lokaci".
**Page 125**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Umar ya ce, "Wane irin lokaci kuma?"
Na ce, "Malam ya gabatar min da kai a matsayin na yarda da kai a matsayin mijina, na kuma
amince wa kudurin Malam, don haka yanzu abin da na ke so bai wuce na samu nutsuwa ba
tukunna".
Umar ya ce, "Wace irin nutsuwa kuma? Ai nutsuwarki tana tare da ni".
Na ce, "Na ji, kuma na yarda amma dai ka ba ni lokaci".
Ya ce, "Gaskiya fa Fatima a bari ya huce shi ke kawo rabon wani".

Na yi dariya, na ce.
"Au yanzu kana jin tsoro ne a matsayinka na soja? Ko kana gudun kar wani ya yi maka kwace?"
Ya ce, "Ai jiya ma da na yi da wasa da an min sakiyar da ba ruwa".
Na ce, "Ta ina kuma?"
Ya ce, "Wallahi, kin san ban san akwai sanayya tsakaninki da Aisha ba, don haka ban san da
zuwanki ba, amma lokacin da ki ka mike don gabatar da tarihin amarya sai na ji wani mutum da
ya ke kusa da ni yana tasbihi, yana kuma fadin, yau ya ga matar aure ko ta wane hali sai ya
aure". **Page 126**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
ta, domin tana daga cikin matan da ya ke so. Kin ji dalilin da ya sa na nuna wa mahalarta taron
da ma ke, ko ba ki mamaki ba?"
Na ce, "Wallahi Umar na yi. amma kuma ya jiya na kasa tambayar ko me ye dalilin yin hakan".
Ya ce, "To ga dalili na fada miki yanzu".
Na yi dariya, haka muka kusa yini tare sannan ya ce zai koma gida, kuma ya fada min sati mai
zuwa zai koma U.S.A domin za a cite masa ragowar bullet din kafarsa guda biyu.
Na yi masa fatan alheri, ya kuma ce da ya sauka zai kira ni.
Bayan Umar ya tafi na shiga tunani kala-kala, a game da rayuwa. Na tausaya wa kaina a game
da rashin Nazir, na kuma kasa maida makwafinsa da Umar.
Wayata ce ta tsayar da ni daga dogon tunanin da na ke yi, Yusuf ne na gani. Ina matukar murna
na dauka, sai na ji muryarsa kamar a fusace, ya ce.
"Fatima ko waye ya rungume kia gurin bikinka ja ki jiya?"
Na ji abin kamar daga sama.
Fada ya kama yi.
**Page 127**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
"Kin ha ni mamaki, ashe da ma ba za ki hake da halin da Allah ya dora miki ba? Fatima don
zubar wa kai mutunci da kuma zubar wa iyaye mutunci sai kawai ki rungumi namiji a cikin bainar
jama'a?"
Na kasa daure zuciyata sai hawaye shar yana bin wani, raina ya baci ainun sam na kasa samun
nutsuwa. Ko da Yusuf fada ya ke min bai kamata ya fada min irin wadannan kalaman ba, domin
ba kunnuwa suka dauke, suka daina tuna komai sai kara jin wayar da na ke ji a jiyewa na yi na
shiga tashin hankali matuka. Ko da hankalina ya dawo jikina na koma tunanin abin da Yusuf ya fada, sai na ga kuma fa
hakan ne, na zubar wa kaina mutunci, na ci mutuncin iyayena da suka wahala wajen ni ke ya sa
hakan ta faru? Amma na kasa ba wa kaina amsa.
Cikin lokaci Kankani na ji zuciyata ta tsani Umar, na ji na tsane shi ainun, idanuna na runtse
alamun nadama. Ina cikin wannan hali ne wayar Yusuf ta kuma shigowa, na daure na dauka na
kara a kunne amma ban yi magana ba.
**Page 128**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**

Ya ce, "Fatima?"
"Na'am". Na fada.
Ya ci gaba da fadin.
"Kin ba ni mamaki, na dauka yadda muka rabu da ke za ki iya hakura ashe abin ba haka ba ne?
Fatima kin ba ni mamaki, na yi tsammanin za ki iya ci gaba da rike kwambonki na mace mai riko
da gaskiya, haba ya za ki zabi mu'amala da maza a maimakon kame kanki da na sanki da ya yi
a baya, ko bayan rabuwarmu kin sauya ne?" Yusuf ya shiga fadin magana a karo na biyu ya fadi iya yinsa, ina jinsa da na gaji da jin abin da
ya ke fada sai na kashe wayata na koma na wkanta na ci gaba da kuka.
Damuwata yanzu ba ta komai ba ce ta maganganun da Yusuf ya fada min ce, kuma wani abin
da ya fada gaskiya ne.
Na kashe wayata na daina dauka, na koma kurma ba waya. Shi kuma Umar ya nemi wayata
shiru ga shi kuma lokacin tafiya ya zo dole ya hakura ya dauki hanya ya tafi U.S.A ganin likita.
Satnsa hudu a can sannan ya dawo, ya tambayi mamansa ko na kira wayarta, ta ce a'a. Dole
ya dauko hanya washegarin da ya dawo ya taho Kano gurina.
**Page 129**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Umar ya same ni amma bai ji dadin ganina ba, domin ya same ni na rame ba na wata walwala,
Umar ya yi tsammanin ko ba ni da lafiya amma na ce masa a'a, lafiyata lau.
Umar ya sha wahala ya shiga tashin hankali matuka kafin ya sami kaina na ma saurare shi na ki
sauraronsa, daga bisani ya tambaye ni abin da ya ke damuna.
Na ji tausayin Umar domin ya fada min cewa yana ganin ya dame ni ne shi ya sa.
Ya ce, "Fatima, gaskiya abin da na fahinta bai wuce ba kya sona ba, amma kuma kin kasa fada
min, sai dai kar ki damu tunda yanzu na ga ni ne matsala a cikin rayuwarki daga yau kuma daga
yanzu ba zan sake zuwa gurinki ba a matsayin manemin aurenki".
Ya mike ya dube ni, ya ce.
"Fatima ina yi miki fatan alheri, sai kuma wani lokacin".
Ya mike idonsa a cike da hawaye ya fice daga dakina.
Ko da ya fita cikin tashin hankali bai saurari kowa ba a cikin gidanmu, ya fice ya dauki motarsa
ya nufi Kaduna.
**Page 130**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Ina nan cikin mawuyacin tashin hankali, kwana biyu da tafiyar Umar sai ga Yusuf ya zo har gida
gurina, ya kuwa yi sa'a ya same ni na fito kofar gida muka gaisa, ya ce.
"Fatima ba ki da lafiya ne?"
Na ce, "Lafiyata kalau, ba abin da ya ke damuna".
Ya bude takardun da ke hannunsa ya fito da hotona ya mika min, ya ce.
"Ga shi ko?"
Na sa hannu na amsa ina dubawa, na ga hotona ne ni da Umar nake kwance, duk da cewa
raina a bace ya ke amma kuma hoton ya matukar yin kyau. Ya ba ni fatan alheri, sai watarana
idan da rabon za mu kuma haduwa.

Yusuf ya juya ya tafi ya bar ni a tsaye ina ta faman karanta wasikar jaki ni kadai, har na ji
kafadata ta soma rawa saboda tsayuwa, dole na tura kafa na shiga gida na sami guri na zauna.
Ba ni na shiga dakina ba sai da na yi sallar isha'i sannan na shiga daki, bacci kuma ya ki yarda
da idona, ina zaune na aksa fahintar karatun bayan allon.
**Page 131**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Rayuwa ke nan, yau da kyau ko ya za ta zamo gobe kuma? Sai Allah.
Na sami tsawon sati hudu a cikin tashin hankali matuka, sai na tuna da Aisha amarya ko ya zan
yi na je gidanta? Don jin yadda zan yi na sami ragowar hotunan da aka dauke mu ni da Umar,
domin na rage yaduwarsu ga al'umma.
Na kunna wayata, na kuma yi sa'a bugu daya ta dauki wayar tana dariya, ta ce.
"Na kira ki ya fi kirga ni yau, da ma wani abokinsa ya damu ya zai yi ya ganki. Yau ma wallahi
sai da ya zo ya tambayi ya za a yi ya ganki?"
Dariya na yi na ce.
"To da ma ni ma zuwa zan yi, amma tunda za ku zo bari na bari sai kun zo din".
Ta ce, "Fatima ki zo mana, da ma fa ba ki zo kin gaa gidana ba. Gaskiya ya kamata ki zo yau,
za ki zo?"
Na ce, "To zan shigo ga ni nan an jima idan rana ta yi sanyi zan zo".
Aisha ta ji dadi sosai kuwa.
Da yamma ta yi na shirya cikin doguwar baakar riga da mayafinta na fta a cikin jakata na
**Page 132**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
sa hotunan da Yusuf ya kawo min, na dauki hanyar zuwa bakin titi.
Ina tsaye ina jiran a daidaita sahu sai ga wani mutum dattijo ya tsaya a gabana, ya ce.
"Sannu".
Na ce, "Yauwa".
Ya ce, "Ina zuwa haka?"
Na yi dariya, na ce.
"Zan je Hotoro ne".
Ya ce, "To shigo na kai ki".
Na ce, "A'a, na gode".
Ya yi iya yinsa amma ban shiga ba, sai ya dauko wata takarda a cikin motar tasa ya ba ni, ya
ce.
"Don Allah idan kin sami lokaci ki kira ni mu yi magana".
Na ce, "To, na gode".
Na sami adadaita ya kai ni, na sallame shi na shiga gidan amarya, da ya ke gidan ba boyayye
ba ne a bakin hanya gidan ya ke.
Na yi sallama na shiga, Aishata fito ta kama hannuna muka shiga falon. Ko da muka shiga falon
sai na ga mutane a ciki don haka cre gilas din idona muka gaisa, sai kuma ta ce.
"Taso mu shiga ciki".
**Page 133**
**Biyu Babu-3**

**Fatima Tijjani Ahmad**
A lokacin da na mike ne sai wani a cikin mutanen da suke a falon ya ce.
"Aisha, wannan ita ce balarabiyar nan ko?"
Ta daga masa kai alamun eh.
Cikin dakinta muka dosa, muka shiga muka zauna. Ta dauko min hotunan biki ta ajiye min a
gabana, na ji dadi kamar ta san saboda na zo gidanta.
Ko da na soma duba hotunan na sha kallo amma kuma abin mamaki shi ne, ban ga irin hotunan
da Yusuf ya kawo min ba, saboda haka na shiga damuwa.
Aisha ta shigo ta kawo min ruwan lemo da kuma taba kalashe. Bayan mun dan nutsa na dauko
mata hoton da Yusuf ya kawo min na mika mata.
Ta karba ta soma dubawa, ita ma ta dan ji mamaki. Na dube ta na ce.
"Ya aka yi?"
Ta ce, "A ina ki ka sami wannan hoton kuma, ga shi mu kuma sam ba mu da su".
Na ce, "Kina da masaniya a kansa ne?"
Ta ce, "Eh, abin da ya sa kuwa, kin san lokacin da Umar ya rungume ki ai wani ne ya ci
**Page 134**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
alwashi a gaban Umar ya ce sai ya aure ki, sai Umar ya ce ai matarsa ce wadda nan ba da
dadewa ba zai angwance da ita, a fa yadda Oga ya ke fada min wai Sayayyana ya ce, wallahi
bai yarda ba domin ya tabbatar masa da haka shi ne ya kamo hannunki zai fidda ke daga hall
din. Shi kuma yayan nawa wanda ya lakabi da Alhaji Kabiru Maiduniya ya turo yaransa ya ce su yi
yayyafi da daloli kin ji dalilin da ya sa Umar ya rungume ki ke nan. Domin oga ya ce a iya
saninsa bai taba ganin ya sa suka tambaye shi ko me ye dalilin? Shi ne ya fada musu
matsayinki a gurinsa". Idanuna ne suke zubda hawaye, na ce.
"Ya aka yi hoton nan ya ke yawo a cikin gari?"
Na kuma fashewa da kuka, a lokacin mijinta ya shigo ya zauna a gefen kujera da ta ke kai, ya
ce.
"Me ya faru?"
Ta dauko hoton da na ba ta, ta mika masa. Mikewa ya yi ya ce.
"Daga ina wannan hoton ya ke?"
Na yi dariyar yake kawai.
**Page 135**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Ya ce, "Fatima a ina ki ka samu wannan hoton, ni da na kira masu hotunan da suka je gurin?
Na ce kuma kar a wanke su a kawo min dodon".
Ya mike rai a face ya fita falo gurin abokansa, ya mika musu hoton.
Ina jiyo ihunsu sannan na ce da Aisha.
"Da ma mijinki soja ne?"
Ta ce, "Sooja ne wallahi, sati mai zuwa ma za mu wuce Lagos, da ya ke a can ya ke aiki, yana
Badagari da zama".

Nan na fayyace mata wanda ya kawo min hoton da kuma kalaman da ya fada min.
Ita ma ta ji dadi, ta ce.
"To me ya ke nufi Fatima? Yana nufin zarginki ne ko kuwa? Ai ba haka ya kamata ya yi miki ba,
saboda shi ne mutum na farko da ya kamata ya ba da shaida a kanki, amma kuma zai zarge ki?
Gaskiya bai kyauta ba, kuma dole a nemo wanda ya fidda wannan a cikin wadanda suka dauki
hotunan biki". Mai karatu biyo ni zuwa littafi na hudu ddon jin yadda za ta kaya.
**Page 136**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
*Shin Umar, Yusuf, ko mutumin da ya ba ta lamwar waya, waye Fatima za ta aura a cikinsu?*
*Waye ya fidda wannan hoton nata da Umar?*
*Wane hali Suwaiba ta ke kasancewa a ciki?*
*Kada ku damu ga na hudun nan kusa da ku, kawai ku dan huta ku dora.*
**Fatima Tijjani Ahmad**
**Kofar Nassarawa**
**08035409873**

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0