Showing 18001 words to 21000 words out of 23776 words
shi ya shigo Kano.
Na dan ji ba dadi amma na daure na yi masa maraba, ya same ni a gida kuma da zuwansa da
ya akwo shi, na kokon bararsa da na amshi soyayarsa.
Kasa ba shi amsa na yi, na sunkayar da kaina a kasa ji na yi ban iya auren Umar ba, amma
kuma ba zan iya cewa ba ni sonsa ba. Saboda idan na ki Umar ban yi halacci ba.
Da ya ga ba ni da niyyar magana sai ya mike ya ce shi zai wuce gida.
Ban iya cewa da shi ko ya gaida gida ba, ina jiyo Karar motarsa daga kofar gidanmu.
**Page 107**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Na kuma shiga damuwa, wannan fa shi ne ga koshi ga kwanan yunwa.
Nan da nan na rame na zama kamar wata mara lafiya, na yi zuru-zuru idanuna kamar na
shekara ban yi bacci ba, na koma wata iri.
Ya daina yi min waya ni kuma na daina kiransa.
Yusuf ne ya zo ya ce ya kawo min wasu atamfofi guda shida ya ce na dinka, na karba na kuma
yi godiya. Muna ta faman hira cikin jin dadi.
Yusuf bai tambaye ni waye Nazir ba, sai da ya koma gida ya kira ni a waya ya tambaye ni waye
Nazir?
Yusuf ba shi amsa na yi saboda na rasa abin da zan ce da shi, haka ya hakura domin na kasa
ba shi amsa. Damuwa ta kuma damuna na rasa me ye abin yi, da ma Umar ne ya ke ba ni
shawarwari to yanzu ya zo da wani salo wa zan nema saboda mu tattauna wannan al’amarin?
Damuwa ta kuma karuwa a gare ni, don haka na dauki carbi na koma ga mabuwayi gagara
misali Sarki Allah.
Yau na tashi da wuri na yi wanka saboda Kawata Fati za a yi bikinta, don haka zu mu shiga.
**Page 108**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
kasuwa da wuri. Na dawo daga wanka zan shiga dakina sai kafa ta yi kara, na dan tsaya
jimawa kadan na ji ta sake yi, don haka na shiga harkata.
Ai dare ya yi kafa sai ta hana ni bacci.
Ba kwana ban yi bacci ba, sai da safe na yi wa Babana waya na fada masa, ya zo ya ce mu je
asibitin kashi na Dala, ya kira wani abokinsa da ya aiki a can ya fada masa abin da ya ke
faruwa, ya ce mu zo.
Muna zuwa asibiti aka ce mu je a dauki hoto ga ke daamun kafar tawa.
Bayan mun dawo daga daukar hoton ne aka ba wa likita ya ce, ai tsagewar kashi na yi, saboda
haka za a yi min aiki amma da yamma.
An ba mu gado, kuma babana ya yi duk abin da ya dace a yi tura ni dakina da za a yi guri biyu
ya tsage. Mun fito daga dakin amma ni allurar dda aki yi min ba ta sake ba, haka na ke bude ido
da kyar na rufe da kyar.
Umar ne a kaina yana kallona na dan yi yake, ya ce.
"kar ki ce komai, bari ki samu sauki."
Yana nan bacci ya dauke ni, ban farka ba sai wajen sha daya na dare.
**Page 109**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Har yanzu Umar ne a zaune ya sa ni gaba yana kallona, na ce.
"Umar yaushe ka zo?"
Na ce, "Sannu da zuwa?"
Ya ce, "Yanzu".
Na ce, "Yauwa."
Sai kuma ga likitoci sun zo suka ce a ba ni ruwan sha ban da madara na sha.
Umar ya hada min na sha, na koma na kwanta, ciwon kafa ya tashi na fara wash! Wash tun
Umar yana ha ni baki har ya daina ya rike hannuna. Nafisa ce ta kira likita ya zo ya yi min allura
na koma bacci.
Washegari na tashi jikina da sauki sosai, domin har hira muke da Umar, na tambaye shi wa ya
fada masa ba ni da lafiya? Ya ce a jikinsa ya ji shi ya sa ya taho.
Damuwa ta kuma karuwa ni ya kuma guda.
Kafin su tafi sai da Mama ta hada ni da mahaifin Umar ta ce mu gaisa.
"To na turo Mamanku domin idan da bukata a fita waje sai a maida ke U.S.A ki ga likita."
**Page 110**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Ya ce, "Allah ya saka."
Na ce, "Amin."
Da yamma ta yi Umar ya ce zai koma gida, na ce ya gaida su Mama, ya ce za su ji su ma sai
sun zo.
Na ce, "To me zai sa? Kar ka gaya musu."
Ya ce, "ke sai sun zo."
Na ce, "To na gode, Allah ya kai ku gida lafiya."
Ya ce, "Amin."
Washegari kwana na biyu likitoci suka zo duba kafata daya cikinsu ya tambaye ni, komai ya ke
damuna yanzu?
Na ce, "Ba komai."
Ya ce, "Haka ake so, don ma tsagewar Kashin ki yi tana da yawa ai da tun sanda aka gyara za
ki tafi gida, amma yanzu ma ba za ki wuce sai daya ba."
Na ce, "Allah ya sa."
Ya ce, "Amin, ke dai ki dage da cin abinci da kuma kaza."
Kwana na hudu da safe ranar asabar ina Zaune a kan gadona Nafisa ta hada min shayi, ina
**Page 111**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
sha sai na ji kamar muryar Mama mahaifiyar Umar ta zo duba ni tare da Anty Sa'a.
Mun gaisa na kuma nuna musu na ji dadi sosai, domin sai da na kira Babana ya zo suka daina
gida, Allah ya Kara lafiya.
Mamansa ta sa hannu a cikin jaka ta dauko
"Abin da ba a yaba sai a yi, idan kuma wani abu ya taso a kira ni a waya."
Ita ma Anty Sa'a ta sa hannu a cikin aljihun jaka ta dauko rafar ta Kanawa, wato wazobiya guda
biyu ta miko min, ta ce.
"Fatima a sha madara."
Duk na amsa na kuma yi musu godiya.
Kafin su tafi sai da Mama ta hada ni da mahaifin Umar ta ce mu gaisa.
"To na turo Mamanku domin idan da bukata a fita waje sai a maida ke U.S.A ki ga likita."
**Page 112**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Na ce, "Na gode, Allah ya saka da mafificin alheri, amin."
Ba su jima da fita ba, sai ga Nafisa na ce.
"Yanzu Maman su Umar ta zo ita da Anty Sa'a ga ma abin da suka ba da, na nuna mata kudin."
Nafisa ta dube ni ta ce.
"Anty shi fa alheri da alheri ake rama shi, kada ki manta mutanen nan sun miki abin da ko
mahaifinki ai yana da hali zai yi miki. Sun mai da ke kamar 'yarsu sun damu da damuwarki mai
zai sa ki yi kokarin saka musu da son dansu? Kar fa ki manta yanzun ne fa suna iran su ji abin
da ya sa zai ce a game da abin da a ji daga bakinki, amincewa ko akasin haka." Idanuna ne suka ciko da hawaye, na ce ta a ni wayata, mahaifin Nazir na kira Malam attijon
arziki. Ya dauka muka gaisa, abin amaki sai na ji ya ce.
**Page 113**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
"Ya kuma jiki? Ni ma yau na dawo, amma gobe insha Allah zan shigo na ga jikinki Fatima, Allah
ya ba ki lafiya kin ji?"
Na ce, "To Malam, na gode."
Bayan na ajiye waya ne Yusuf ya shigo hannunsa dauke da lemo da aya a leda. Ya karaso ya
ajiye ya ce.
"Fatima ya jikin?"
Na ce, "Da sauki, wa ya fada maka?"
Ya ce, "Wallahi dazu na je gidan sai ake fada min kina asibiti shi ne na tambayi inda asibitin ya
ke, suka ce a Dala ne shi ne na taho na ganki."
Na ce, "To na gode."
Muna ta faman hira da Yusuf, sai ga likita ya shigo. Ko da likita ya fahinci muna da alaka da
juna da Yusuf sai ya ce masa ya ba shi guri, ma'ana ya koma waje zai duba kafata ya ga ya
aikin ya ke.
Bayan fitar Yusuf likitan mai suna Adnan ya ce.
"Fatima, ba a so fa ki fiye surutu, don wannan aikin naki ya fi karaya wahala, don haka ya
kamata ki kula da kanki, kin ji ko?"
**Page 114**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Na ce, "To likita, na gode sosai Allah ya kara fahinta."
Ko da likita ya fita ya ce Yusuf ya dawo, amma sai zai kara kira ni aa waya, amma zai koma
Abuja ne yau.
Na ce, "To na gode, sai mun yi waya, Allah ya kiyaye hanya."
Na sami kimanin sati biyu a cikin asibitin Dala kafin na fito na dawo gida.
Malam mahaifin Naziru shi ne ya zo yau a karo na biyu ya sake duba ni, da shi muka kusa wuni
a cikin ranar domin bai tafi ba sai da ya yi sallar la'asar sannan ya dauki hanyar Kaduna.
A zaman da muka yi da malam yau ya tambaye ni ko ya Fatima.
"Yanzu waye ki ke so domin ya kamata ki maida hankali domin ki yi aure, zama haka ba naki ba
ne, ki yi hakuri ki maida komai ga Allah kin ji 'yata?"
A cikin kuka na ce.
"To Malam, insha Allah duk wanda ya zo zan saurare shi."
Ya ce, "To, yanzu ba wanda ya zo?"
Na ce, "Malam babu."
**Page 115**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Ya ce, "Me zai hana ki amince da Umar, saboda ina ga ya dace da ki aure shi, kin ga kuma
abokin Nazir ne, yana da hakuri saboda idan kin auri wani ba lallai ba ne ya jure wa ambaton
Nazir a maimakon ambatonsa ba."
Ya ci gaba da cewa.
"Zan so ki amince da Umar, domin mutumin kirki ne, kuma Fatima ni kaina zan so haka don
yanzu jinki na ke yi a jikina kamar ni na haife ki, kuma na san ba za ki maida bukatata baya ba
Fatima. Allah ya yi miki albarka, ya kuma sa ki ci gaba da sunanki kin ji."
Cikin kuka na ce, "To Malam, kuma ya amince da zabin da aka yi min, domin na san abin da
Babana zai yi min shi kai ma za ka yi min."
Malam ya ji dadin abin da na fada masa, ya kuma sa min albarka.
Damuwata ta karu, na kuma lalacewa. A gaskiya ina son tsohon mijina matuka, ga kuma Umar
wanda shi da iyayensa suke ta faman dawainiya da ni a cikinsu, wa ya kamata ya zama
zabina?
Ina zaune a gida Yusuf ya kira ni a waya, mun jima munahira muna tuna wa juna da.
**Page 116**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
abubuwan da suka faru a baya, Nafisa ta shigo dakina duk da ina waya, amma na amsa
sallamar da ta yi, har Yusuf ya ce.
"Ke da wa?"
Na ce, "Nafisa ce ta shigo."
Yanzu dai mun yanke shawara ni da Yusuf za mu koma zamanmu na aure, duk da cewa da
Nazir yana gaskiya ba zan koma wa Yusuf ba, domin kuwa na so Nazir, irin son da idanu su ke
wa zinariyar ido wato gani na so Nazir irin son da mutumin da ya ke jin kishi ya ga ruwa a
lokacin tsananin zafin gari da ya sami tsawon lokaci a jeji tana neman barewa ba ta samu ba,
domin ta kai ina ji a jikina cewa, da Nazir ne na fara aura kuma ya rabu da ni, to da zan iya rasa
rayuwata, ina son Nazir matuka gaya.
Ko da na samu dama, lafiya ta samu yanzu domin ina zuwa duk inda na ke so da kaina, ba dan
yin dingishi sai na koma gurin Kakana domin ina son zama da shi, kasancewar yana sona
domin kullum bayan sallar isha'i idan muka zauna yana ba ni labarin irin yawon fataucin da suka
yi, amma fa fataucin na kamun kifi da ya ke kuma ni. **Page 117**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
in masoyyar kifi ce, kuma ina da son jin irin wannan labarin, domin kaan samun darasi a cikinsu.
Bayan na dawo sai na ce da Sulaiman idan Allah ya kai mu ranar juma'a a zai je gida ya dauko
min motata domin za ni bikin wata kawata da muka hadu da ita a kwanciyar da muka yi a Dala
mai suna Aisha, ita tana jinyar 'yarta ne ta fado daga bene ta karye waje hudu, to dakinmu yana
kallon nasu ta kan shigo ta gaida ni dda haka har muka saba kun san sabon mata ba shi da
wahala.
Da ranar juma'a ta zo Sulaiman ya je ya dauko mota tun da safe ya wanke min mota. Na shirya
cikin leshi mai ruwan madara da goggoro da ya ke haka a ka tsara mahalarta bikin za su sa. Na
dau dogon takalmi kai ni kaina da na kalli kaina a madubi sai na yarda da haduwar da na yi,
turarena fesa madaukaki da sanyin kamshi na fesa, na yarda da kaina gaskiya. Misalin karfe shida na yamma na fito ni da Sulaiman da ya so ya ja mota, amma sai na ce ya ba
ni na ja.
Na tuka motar muka dauki hanyar Daula Hotel.
**Page 118**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Mun isa guri ya yi guri, na fiddo gilashin ido na sa, na mika wa Sulaiman makullin mota.
A daidai lokacin ne wayar Umar ta shigo na daga cikin kulawa na gaida shi, na kuma tambayi
Sulaiman ya amsa suna lafiya, ya ce.
"Fatima, ina cikin garinku, mun zo bikin abokinmu, don haka komai dare sai na zo na ganki."
Dariya na yi, na ce.
"To ni ma na fito, ina gurin bikin kawata".
Ya ce, "Da izinin wa ki ka fita?"
Na ce, "Da izinin Allah".
Ya ce, "To ba komai".
Sai wayar ta dauke, na kuma yin kokarin sake nemansa amma na saka samunsa.
Mun yi waya da Aisha amarya, ta kuma fada min tana nan zuwa na jira saboda tare za mu
shiga hall din, ni ta ba wa kawar da zan gabatar da tarihin rayuwarta a cikin hall din.
Jimawa kadan guri ya dau harami mawaka suka soma aikinsu, jimawa kadan sai ga motar
amarya ta shigo ta same ni a jikin mota a tsaye, shi kuwa Sulaiman tuni ya bar gurin ya fada
cikin mutane abinsa, kodayake ya ga wani dan makaranta a gurin shi ya ja shi.
**Page 119**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Ta karaso gurina ta kama hannuna muka gaisa, ta ce.
"Kai Fatima, gaskiya kin yi kyau da yawa fa".
Na ce, "Na gode".
Muna cikin gaisawa wasu 'yammata suka karaso inda mu ke, muka karaso mu ake jira mu ya
gama haduwa.
A hankali muka karaso cikin hall din da aka tanada domin yin dina din kai amma fa gurin ya
ahdu matuka, mun shiga cikin falo a lokacin da aka mike domin taryarmu don zuwa
masaukinmu da aka tanada mana.
Bayan mun zauna aka fara gudanar da abin da ya hada mu a gurin, an gabatar da tarihin ango
da amarya ta bakin aminininsa, sai kuma aka gabatar da ni domin gabatar da tarihin amarya
Aisha.
Na mike daga gurin zamana na yi sallama kamar yadda addinin islama ya koyar mana, sai
kuma na yi shiru kamar mai tunanin abin da zan fada. Hall din ya yi kamar ba mutum a cikinsa,
na dako kai na ga kowa yana kallona, yana kuma sauraron abin da zan fada.
**Page 120**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Gyaran murya na yi a karo na farko na kira sunan Aisha da angonta Murtala, na kuma nunata
da hannuna maimakon na yi bayani cikin harshenmu na Hausa, ko kuma na yi cikin harshen
Nasara kamar yadda abokin ango ya gabatar ai sai na dauka cikin yare mai matukar daraja
wato yaren larabci, kai jama'a larabci kuma so ne, domin ya zamo yaren Annabinmu, kuma
yaren 'yan aljanna.
Hall din ya yi shiru wanda ma ba ya yi sai jijjiga kai ya ke yi kamar ya san abin da na fada.
Ina cikin bayyana halayen kawata cikin harshen larabci sai fa masu daukar hoto suka ce da wa
Allah ya hada su? Sai kuma na ga ana yi min ruwan kudi, sai kuma wani mutum da na ji a kusa
da ni a tsaye.
Ban ankara da wanda ya ke kusa da ni ba, sai da na gama na yi godiya na mika abin magana
ga wanda ya ba ni. Ina juyowa zan zauna sai muka yi ido hudu da Umar shi ne a kusa da ni, na
dube shi na yi murmushi na ce.
"Ranka ya dade, ya aka yi na ganka a nan? Da ma ka san nan na zo kun yi waya da Sulaiman
ne?"
**Page 121**
**Biyu Babu-3**
**Fatima Tijjani Ahmad**
Umar bai ba ni amsa ba, sai ma kama hannuna da ya yi alamun na zo mu bar gurin. Ai ko da na
sauko daga inda aka ba ni na zauna sai wasu samari suka yo kanmu suna wasa da kudi kamar
su suke bugawa, sun hana gaba kuma sun hana mu yin baya, da gani har Umar din. Wasu ne
suka kuma tasowa su ma suka bude bakin aljihu shi kuwa dije sai ya kara kida a binsa. Umar ya fahinci wani abu yana neman faruwa a gurin, saboda haka sai na ji ya manna ni a
kirjinsa ga mamakina sai na sami kirjinsa na maida kaina na aje, kai nutsuwa na samu a lokacin
kamar da ma shi ne Nazir din nawa da na rasa.
Ko da mutane suka ga haka sai wasu samari suka mike suna min likinan suka tsaya da yi min
likin sai kuma hall din ya dauki sowa da kuma ihu samarin, jim kadan da faruwar haka Umar ya
ce mu je mu zauna ko?
Na ce, "To".
Na bar gurin zamana na koma gurin zaman Umar da kuma abokansa.
Biki ya yi biki, yanzu kuma an bukace ni da na fito da amarya fili domin taka rawa, sabon salo
yanzu kuma kawar amarya