Showing 63001 words to 66000 words out of 73076 words

Chapter 22 - Ciwon Ya Mace Book Compelet Lamido

18 Aug 2026

657

****
Cikin wata biyu aka gama maganar makarantar Nur, dan haka ta fara zuwa, shigar mutunci
take, ko da gyale zata saka to riga mai mutunci zata saka sannan ta tafi, hankali ta mayar akan
karaton sosai, duk da cewa tunanin Bilkisu da na Aliyu suna adabar zuciyarta, kullum Nur jira
take an ce mata Bilkisu ta haihu, ganin har an shafe wata hudu da faruwan abun ta zauna
gaban Mamy tare da cewa "Mamy wai har yanzun Aunty Bilkisu bata haihu ba?
Cikin nuna halin ko in kula Mamy tace "Ta haihu mana" Cike da mamaki Nur tace "Yaushe?"
"Yanzu ina jin za'ayi wata biyu."
"Mamy shine baki gaya min ba?"
"Nur ni da nasan halinki ai bana fada miki ba, duka-duka Yaushe kika dawo hayyacinki."
Jimmm Nur ta yi idonta cike da kwalla zuwa can tace "Me ta haifa?"
"Mace akace" Shigowan Abdallah yasa suka daga Kai suka kalleshi, bayan ya zauna ya gaida
Mamy ta amsa sannan Nur taci gaba da cewa, "Mamy babu wadda yaje ne daga nan gidan?"
"Aunty ku da Bashir sunje" Hawaye Nur ta matso sannan tace "Shine akaki gayamin barema aje
dani, kuma bayan an min alkawarin za'a dinga kaini wajenta, ni ma gobe zani."
"Babu in da zaki, yariyar da akace ma bata maga me zakije kiyo?" Jin haka jikin Nur ya kara
sanyi, mikewa tayi ta fita batare da takalli inda Abdallah yake ba, shiko Abdallah ta gefen ido
yake Satan kallonta, bayan ta fice yace, "Wai mene ne Mamy?"
Nan Mamy ta gaya mishi abin da takewa fushi, tabe baki yayi tare da kawar da zancen. Adaren
ranar tajewa Abba da zancen son zuwa gidan su Bilkisu, hakuri ya bata tare da nuna mata
Bilkisu bata da lafiya, bama ta gidan yanzun haka. Kuka sosai Nur taci, domin abun sai ya dawo
mata sabo, haka taci gaba da karatunta bata da walwala sosai, wata rana ta taso makaranta

wata zuciyar ta bata shawaran ta biya gidan su Bilkisu, karkacewa ta yi ta nufi hanyan gidan
nasu, duk da cewa bata taba zuwa ba, mashin tahau ta sauka a daidai kofar gidan, sannan ta
shiga, bayan ta shiga cikin gidan ta ne ta iske mace daya a tsakar gidan kishiyar Maman
Bilkisu ce Kawai a tsakar gida, bayan sun gaisa ta Gaya mata Bilkisu take nema, kallonta ta yi
daga sama har kasa sannan ta tabe baki tare da nuna mata wani daki da baki, hanyar dakin
Nur ta nufa nan ta hangi Bilkisu zaune da goyo a bayanta, wanni irin kallon Bilikisu tai mata mai
cike da Mamaki, itako Nur da gudu ta fada jikin ta suka rungume juna sannan tai saurin sa
hannunta ta kwanto yariya ta koma bakin gadon ta zauna tare da zubawa yariyar Ido, cikin
zubar da hawaye take cewa "Allah sarki Aunty Bilkisu, ji yariyar mai kyau da ita, rungume
yariyar ta kara yi sannan tace "Yaya sunan ta?"
Jin Bilkisu batace komaiba Nur ta dago ta kalli fuskar Bilkisu, gani ta yi tana hawaye dan haka
ta sake cewa "Aunty Bilkisu Yaya sunanta?"
Wannan karon ma batace komaiba illa Murmushi da take ga Kuma hawaye a gefen
kumatunta, tunawa tayi da zancen Abba da yake cewa Bata da lafiya bata magana dan haka
sake kallonta tare da cewa "Baki da lafiya Aunty Bilkisu da gaske bakya magana?" Zama Bilkisu
ta yi abakin gadon dan haka Nur ta kara fashewa da kuka ta kalli Bilkisu ta kuma kalli yariyar,
tana cikin wannan yanayin ta ga matar data hado da ita a tsakar gidan ta turo kofar tare da
cewa "Idan kinga dama kizo ki dauki abincin" Mikewa Bilkisu ta yi ta fita, zuwa can ta dawo da
kular abinci ta aje gaban Nur, sannan ta koma ta zauna, kallonta Nur ta yi tare da cewa "Kici
Aunty ni akoshe nake, dauka ta yi ta fara ci Nur kuwa wasa takewa yariyar tare da kuka lokaci
guda, tas Bilkisu ta cinye abincin, sannan Nur ta Bata yariyar tare da cewa Zan tafi Aunty, sai
na sake zuwa, Allah ya baki lafiya, ya Kuma saka miki koma waye yake da sa hannu a shigar ki
cikin wannan masifar, wannan karon kai Bilkisu ta jinjija, cike matsancin kuka Nur tabar gidan,
har Nur ta isa gida kuka take, dakinta ta wuce, kafin wani lokaci kanta ya dauki ciwo, acikin
zuciyarta take cin alwashin in Allah ya yarda sai hukunci ya hau kan wadda ya yaudari Aunty
Bilkisu, saiya amsa 'yarsa, sannan ita Kuma da yardan Allah saita dawo gidan Yaya Abdallah.
Insha Allah wannan bazai zama karshen auren su, duk kokarin da take kada su Mamy su gane
tana cikin damuwa saida su ka fahimta, Washegari fito tawa Mamy sallama zata wuce
makaranta Mamy ta kalleta ta ce "Kukan me kikayi Ido duk suka kunbura haka?" Cikin kawar ta
Kai tace "Ba kuka nayi ba, tashi kawai nayi na ganshi a haka" Kai kawai Mamy ta daga badan ta
gamsu ba, itako Nur ficewa ta yi tun daga lokacin bata hada sati biyu ba tare da taje gidan su
Bilkisu ba, yawan zuwan da take ta fahimci iyayen Bilkisu suna nuna mata halin ko in kula,
wadda hakan ke sosa ranta, wannan dalilin yasa ta fara yiwa Bilikisu sayya tana kaimata,
karutun da ta fara ya fara tasiri ajikinta ko da wasa bata taba barin wani ya gane tana zuwa
gidansu Aunty Bilkisu ba, tsayon shekara ta dauka tana zuwa gidan, wata rana tana zuwa
akace mata kanwar mamanta tazo ta tafi da ita, cikin rashin jin dadi Nur ta fito daga gidan Gashi
babu sakin fuskan da zata tambayi inda aka kaita, wannan yasa Nur ta dawo gida ta bakin ciki
da ta jima bata dawo cikin walwalaba, kullum dare suna waya da Poul da wayar Aunty, dan
haka ta maida hankali kan karatunta sosai, yayin da soyayya mai karfi ke dadashigarsu.

BAYAN SHEKARA SHIDDA
Abuwa da dama sun faru zuwa wannan lokacin, sati biyu ya rage Nur ta kammala karatunta,
sosai ta kara gogewa tare da waye da wayau baki daya, duk inda ake neman kyayawan mace

Nur ta kai, domin komai nata ya gama bayyana, ayanzu shekaranta 21, tuni Bashir ya saya
mata waya tare da nuna mata lokaci yayi da ya kamata ace ta yi aure, sai dai har yanzu
nunawa take tafi son karatu sama da auren, Tsakaninta da Aliyu kuwa soyayya ce mai karfi, sun
aminta da juna bayan waya da suke kuman lokaci bayan lokaci suna haduwa a makaranta,
hakanne yasa duk wanni wadda yasan Nur amakaranta ya san Aliyu, kuma tunda ya ke zuwa
babu wadda ya taba gane musulunta yayi domin akwai Hausa radam abakinshi, a daddafe ya
bari a ka kawo wannan lokacin a kullum bashi da magana sama tada aure, sai dai har yanzun
duk wata kofar da zata saka agane tana tare da Aliyu Nur ta tosheta, Abdallah kuwa sauda
yawa saidai ta jiyo muryansa domin tuni ya koma gidanshi can yake rayuwarsa sun jima sosai
basuyi gaba da gaba ba saidai taji Muryanshi ko ta hango gilmawarshi.
Yauma kamar kodayaushe bayan Nur ta dawo makaranta tana kwance adaki Aliyu ya kira
wayarta, bayan sun gaisa yace "Ya maganar da muka yi jiya?" jimmm Nur ta yi zuwa can "Tace
nace kadan Kara hakuri ai"
"Haba Nur? mai yasa bakyajin tausayina, bakya gajiya da kiran hakuri, gaskiya na yi hakuri iya
wadda zan iya, na lura laifinki ne, ke ce bakyason auren ba iyayen ki" Kasa ta yi da murya tare
da cewa "Ba haka bane fa"
"To Yaya ne? tsayon shekara shidda kenan kina gaya min hakuri, har yanzun a gidanku
ba'asan Ina yi ba, kince sai kin gama karatu, mai yasa bazaki bari akai maganar gida ba?
amman shikenan tunda haka kike so" Katse wayar yayi batare da ya bari sunyi sallamaba, dan
haka Nur ta kalli wayar tare da ya mutsa fuska, sam bata son bacin ranshi, duk da cewa ta sani
yayi hakuri, afili ta ce "Ni fargaba nake, bansan mai Abba zaice ba, aduk ranar da yaganshi a
gidan nan, wayar ta dago ta sake kiranshi saidai harta katse bai dauka ba, dadadre ma sake
kira ta yi nan ma be dauka ba, wannan karon Murmushi Nur ta yi tare da fadi afili tace "Yayi
fushi" kwanciya ta yi a gado ta rubuta sakon ban hakuri, nan ma koda ta tura bece komai ba,
dan haka washegari da safe bayan ta yi shirin islamiyya ta biya gidan, tana tura get din ya juyo
ya kalleta fuskarshi dauke da murmushi, ahankali ta karasa wajen ta tsaya tare da wasa da
yatsunta, kallonta yayi sama da kasa yayi murmushi sannan yace "Kin tashi lafiya? Cankasan
makoshi tace "Ai baka damu da lafiyataba"
"Mai yasa kikace haka.?"
Karya kai Nur ta yi sannan tace "Tun jiya nake kiranka baka dauka ba, na turo sako ma baka
nuna ka gani ba" idonshi akanta yace "Na gani."
"To mai yasa baka dauka ba.." Kamar jira yake ta rufe baki yace "Saboda ba bukatata in tajin
muryanki kina daga min hankali ba, a yanzu nafi bukatar in ganki kusa dani a matsayin matata,
nagaji da hakuri Nur" Shiru Nur ta yi tsayon lokaci zuwa can tace "Kayi hakuri to"
"Ni ba wani hakurin da zanyi, jeki abinki"
Tsayon lokaci Nur ta dauka tsaye zuwa can tace "To yanzun Yaya kake son ayi.?" Batare da ya
kalletaba yace "Dama nake son ki bani in tura gidan ku" Shuru Nur ta yi tsayon lokaci sannan
tace "Ai na ce maka ka kara hakuri kadan."
"Shikenan na ji kije makaranta karki makara" ganin ya dauke kansa tabishi da kallo acikin
zuciyarta take cewa "Bani da jarumtar da zan iya turashi wurin Abba, ina shakkar Abba sosai
akan wannan, Juyawa ta yi ta fara tafiya har ta fice a get din be kirata ba, haka Kuma ko juyowa
ya kalleta be yi ba wannan ya tabbatar da lallai ya yi fushi. Koda taje islamiyya rasa walwala ta yi, bayan an taso gida ta wuce cike da damuwa, har dare

tana cikin damuwa, Misalin karfe takwas na dare taji Mamy ta kwala mata Kira, mikewa tayi ta
fice, Abba ta samu zaune Yaya Bashir a gefen shi, gefe daya Kuma Aunty da Mamy ne, hira
akaci gaba dayi zuwa can Abba yace "Nur bani hankalin ki" Cikin Sauri Nur ta mike ta dawo
kusa da Abba, kallonta yayi kadan tare da cewa "Wai ni kwana nawa ya rage ki kammala
karatunki?
Kamar jira take ya dire tace "Sati biyu ne Abba"
"Ma sha Allah, burin Nur dina yana daf da cika."
Yar dariya Nur ta yi tare da cewa, "Abba saima ka ganni a gaban Alkali." Bashir ne yayi dariya
tare da cewa dallah saikace zata iya, ke kinsan aikin kuwa?masoraciya kawai ko karfi
bakidashi"
"Yaya Bashir ai abin ba fada bane ko kai yanzu nan saina kure ka ka kasa cewa uffan."
"Haba? Dan Allah fa? Ta yaya zaki kure ni?"
"Sabo da na karanta Yaya, yanzu ba da bane, duk wadda yayi irin karatummu dole ya zama
mai kaifin kwakwalwa da tunani, da iya hadda saboda low course ne da yake da bukatar
haddace abubuwa da dama, kuma sai ka zama mara tsoro mai karfin hali da juriya, ya zama
koda mutanen duniya aka tara maka zaka iya tashi ka gabatar da hujjojinka a gabansu batare
da kaji wani dar ba." Baki Bashir ya bude cike da mamaki, Abba kuwa cewa yayi "Yauwa Nur
gara ki gaya mishi ba lokacin banza kika bata ba" Jin haka Bashir da har yanzun be cire idonshi
akan Nur ba yace "Tun da hakane tashi ki kare kanki da tarin hujjojinki da yasa kika kasa kawo
mijin aure har zuwa wannan lokacin" Ya mutsa fuska Nur ta yi idonta akan Bashir, sannan ta
waiga ta kalli kowa na falon, da alama sunji dadin abin da yayi, domin gani tayi duk ita suke jira
suji mai zata ce, sunkuyar dakai ta yi tare da cewa, "Ai aure lokaci ne" Dariya Bashir yayi tare
da cewa dole kice haka tunda kinki sauraron kowa ba" Mikewa Nur ta yi tare da cewa, "Ni dai
abar mganar idan lokaci yayi ai zanyi" Tana kokarin barin falon "Abba ya ce dawo Nur ki zauna
ai magana zan yi dake" dawowa ta yi ta zauna kanta a kasa, yayin da Abba ya shiga cewa, Nur
ina ganin duk abin da ya kamata nai miki na adalci na yi, banso ace har ki kammala wannan
karatu batare da kinyi aure ba, kullum cikin jiran tsammani nake amman har yanzun shiru,
yanzun idan kin kammala kina nufin zakici gaba da zama a gida ne babu aure?"
Kasa dago kai Nur ta yi bare ta kalli Abba, ganin taki dago kai yace, "To dan Allah zan rokeki
yadda na cika miki burinki ni ma kiyi kokari ki cika min burina, ki kawo min mijin da zaki aura,
kafin ranar da zaki kammala karatun ki, a takaice dai, banson ki kara wata daya gaba batare da
kinyi aure ba" "Abba idan bata da saurayi akwai wani abokina dazan hadata dashi" Bashir ya fada cike da
tsokana, Dagowa Nur ta yi ta kalli Bashir kadan ta sunkuyar dakai tana matso hawaye daya cika
idonta, adaidai lokacin da Abba yaci gaba da cewa "Kina dashi ko ya kawo miki abokin nashi?"
Cikin sauri Nur ta juya baya tana mai turo baki tace "Ina dashi Abba"
Yar dariya Bashir yayi, shiko Abba cike da farinciki yace "Da gaske ko wasa?"
"Da gaske" Nur ta fada kanta akasa duk kuwa da cewa ta Juyawa Abba baya" Cikin murya irin
ma me lallashi yace "To ku daidaita kijin ko? Ku nake jira dazan kin amince dashi sai kice mishi
ya turo.
Amsawa Nur ta yi dakai tare da mikewa ta shige daki, cike da mamaki Bashir dasu Mamy
suka bita da kallo domin babu wadda yasan tana da saurayi.
Bayan Nur ta shiga daki bakin gadon ta zauna tare da kirga kwanakin da taji Abba ya yanka

mata, tsintan kanta ta yi dason kiran Aliyu dan haka ta dauki waya ta kirashi, bayan ya dauka ta
sanar mishi da halin da ake ciki, shima cike da tashin hankali yace 'Ai kinga irin abin da nake
fada miki kenan, kina son ki samu cikin matsala, ni a shirye nake, gobe zan tura" Lumshe Ido
Nur tayi tare da cewa, A'a kafin ka turo ka fara zuwa gidanmu tukuna ina ganin hakan zaifi" Batare da wani tunaniba Aliyu yace "Shikenan goben zanzo."
Hakance ta kasance Washegari da daddare Aliyu ya aiko Kiran Nur, yayin da hakan ya
faranta ran su Mamy, bayan Nur ta fice addu'a Mamy tai mata akan Allah ya daidaitasu ya kuma
sa abokin zamanta ne nagari.
Fitan Nur ba jimawa Bashir ya shigo, kokarin zama yake tare da cewa "Mamy baki kuka yi ne
naga mota a kofar gida.?"
Aunty ce tace "Ina jin bakon Nur ne" Shiru Bashir yayi zuwa can "Ya ce to acikin motar zatayi
Hira? Mai yasa bazata shigo dashi cikin gida ba, ai wannan be dace ba" Ganin su Mamy
basuce komaiba ya daga waya yakira Nur tare da bata Umarnin ta shiga da bakonta falon
Abba, amsawa Nur ta yi sannan ta sanar mishi, farin ciki sosai yaji tare da addu'ar Allah yasa
komai yazo mishi da sauki Kamar hakan.
Shiko Bashir jira yaitayi Nur ta shigo ganin dare na kara yi bata shigoba yayi sallama ya fita,
ita ko Nur sai kusan sha daya ta shiga gidan, dan haka Mamy ta dubeta tace "Nur kalli agogo,
daga Kai ta yi ta kallah tare da yin raurau da ido, sannan ta sunkuyar da kai, Mamy ce ta sake
cewa Daga zuwa mutum yau-yau sai ki saki jiki har kiyo dare haka? Idon Nur akasa tace ban
kulla bane Mamy, kallo Mamy ta kare mata sannan tace "To ina miki fatan alheri amman ki
kiyaye da irin wannan, kin dai san halin mazan gidan nan, musamman Bashir.
Can kasan makoshi tace "Bazan kara ba" Hira suka dan taba, sannan Nur ta wuce daki cike
da farinciki wadda ta jima bataji irinshiba, acikin zuciyarta tace ashe haka tadi yake da dadi, sai
naji kamar karya tafi, yau daya naji kamar ankara min sonshi, cike da farin ciki ta kwanta, dan
haka ko a bacin ta mafarkinshi taitayi har gari ya waye. Washegari ma Aliyu yazo da daddare, falon Abba suka zauna hirar yau ma, hira suke mai
cike da kyauna, yayin da Nur ke sanye cikin hijjabi, gaba dayansu murmushi suke domin sosai
suke jin dadin haduwar tasu ta biyu, wadda suke ganin daren na masifar zura gudu, agogon
dake wayarta taita kallo, domin karta sha'afa ta kuma yin dare, karfe goma na bugawa Aliyu ya
mike tare da cewa ki je gida sai gobe, kar a sake miki fada.
Cikin kwalkwal da Ido Nur tace "Ka bari sai da darabi ta yi mana."
Cikin wani irin yanayi dake nuna jarumta kawai yake yace "Kije gida gobe zanzo da wuri."
"To ka bari saida kwata to" Cike da murmushi Aliyu ya kalli agogo tare da cewa "Ai da kwatar
ma yanzun zata yi, nifa banki in kwana anan ba, kawai Ina lallabawa ne kar mu samu matsala
da gidan ku, ko zamu canza lokacin haduwa ne domin cikin kwana biyun nan na fahimci dare
jaren lokacine, Adaidai wannan lokacin aka ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0